36
1 GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, wanda ya halicci mutum daga gudana jini kuma ya sanar da mutum da alkalami, ya sanar da mutum abinda bai sani ba. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (SAW) cikamakon Annabawa, wanda Allah ya haskaka duniya da shi. Bayan haka, ya yan'uwa musulmi, wannan littafi yana fadakarwa ne da kwadaitarwa a kan muhimmancin waqaf a musulunci, wato kebe wata kayyadaddiyar dukiya, kudi ne ko kuma kayan aiki don taimakawa addinin musulunci da musulmi, musamman da daukan nauyin wasu mahimman abubuwa da a yau musulmi basu damu da su ba, kamar gina gidan marayu ko kuma gina wani wuri inda marasa gata zasu rabe, kamar Makafi, Kutare, Guragu da kuma kula da Mahaukata. Duk wadannan bayin Allah dana ambata a sama, hakkine a kan musulmi su dauki nauyinsu, maimakon a barsu haka kawai a wulakance, kamar yadda muke gani a wasu hanyoyi da ke a nan yashe suna kwana a kan tituna. A nan suke kwana da iyalansu da 'ya'yansu. Wasu ma a nan suke haihuwa. Ba ma inda tausayi zai kamaka sai in ruwan sama ya sauko, sai dai su rinka jawo laidoji suna kulalluba da ita. Amma ga mawadata a cikin kasan nan Allah ya saukaka. Saboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya da lahirarsa. Kuma ko ba komai ma dukiyar nan da take hannun mawadata, Allah yace tsaro ya basu don su dauka su gudanar da ayyukansa da ita. Soboda haka, ya ku bayin Allah ku dauki dukiyar Allah ku yi aikin da ita, tunkafin ranar nan tazo (ranar da dukiya da 'ya V a basu da wani amfani a wajen masu ita, sai kawai wanda ya zo wa Allah da kubutattar zuciya). Saboda haka, duk wanda Allah ya baiwa dukiya, ya bashi mabudi ne na bude kofar gidan Aljannah in yana son shiga, haka kuma ya bashi mabudi ne, na bude kofar gidan wuta in ita yake so ya shiga. Muna fata Allah ya shiryar da mu. Saboda haka ne ma manya- manyan bayin Allah na farko, wato sahabban Annabi (SAW) da suka yi zamani da shi, wadanda ake saukar da Alqur'ani anan take suyi aiki da shi suke gudun su mutu su bar wata dukiya mai tarin yawa, saboda tunanin in sun mutu , Allah zai tambaye su yadda a kayi suka tara wannan dukiya, duk da cewa dukiyarsu ce ta halas, ballantana mu a yau da muke cikin wani irin zamani

GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

1

GABATARWA

BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, wanda ya halicci mutum daga gudana jini kuma ya

sanar da mutum da alkalami, ya sanar da mutum abinda bai sani ba. Tsira da aminci su tabbata ga

shugaban mu Annabi Muhammad (SAW) cikamakon Annabawa, wanda Allah ya haskaka duniya

da shi.

Bayan haka, ya yan'uwa musulmi, wannan littafi yana fadakarwa ne da kwadaitarwa a kan

muhimmancin waqaf a musulunci, wato kebe wata kayyadaddiyar dukiya, kudi ne ko kuma

kayan aiki don taimakawa addinin musulunci da musulmi, musamman da daukan nauyin wasu

mahimman abubuwa da a yau musulmi basu damu da su ba, kamar gina gidan marayu ko kuma

gina wani wuri inda marasa gata zasu rabe, kamar Makafi, Kutare, Guragu da kuma kula da

Mahaukata. Duk wadannan bayin Allah dana ambata a sama, hakkine a kan musulmi su dauki

nauyinsu, maimakon a barsu haka kawai a wulakance, kamar yadda muke gani a wasu hanyoyi

da ke a nan yashe suna kwana a kan tituna. A nan suke kwana da iyalansu da 'ya'yansu. Wasu ma

a nan suke haihuwa. Ba ma inda tausayi zai kamaka sai in ruwan sama ya sauko, sai dai su rinka

jawo laidoji suna kulalluba da ita. Amma ga mawadata a cikin kasan nan Allah ya saukaka.

Saboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi

wa mutum amfani duniya da lahirarsa. Kuma ko ba komai ma dukiyar nan da take hannun

mawadata, Allah yace tsaro ya basu don su dauka su gudanar da ayyukansa da ita. Soboda haka,

ya ku bayin Allah ku dauki dukiyar Allah ku yi aikin da ita, tunkafin ranar nan tazo (ranar da

dukiya da 'ya Va basu da wani amfani a wajen masu ita, sai kawai wanda ya zo wa Allah da

kubutattar zuciya). Saboda haka, duk wanda Allah ya baiwa dukiya, ya bashi mabudi ne na bude

kofar gidan Aljannah in yana son shiga, haka kuma ya bashi mabudi ne, na bude kofar gidan

wuta in ita yake so ya shiga. Muna fata Allah ya shiryar da mu. Saboda haka ne ma manya-

manyan bayin Allah na farko, wato sahabban Annabi (SAW) da suka yi zamani da shi, wadanda

ake saukar da Alqur'ani anan take suyi aiki da shi suke gudun su mutu su bar wata dukiya mai

tarin yawa, saboda tunanin in sun mutu , Allah zai tambaye su yadda a kayi suka tara wannan

dukiya, duk da cewa dukiyarsu ce ta halas, ballantana mu a yau da muke cikin wani irin zamani

Page 2: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

2

gurbatacce da Annanbi (SAW) ya yi wa lakabi da cewar: (wani zamani na nan zuwa, babu wanda

zai rage a cikin zamanin face yaci riba, in kuwa baici hakikanin riba ba, to, sai kurarta ta shafe

shi). Saboda tunanin waccan magana da ta gabata, sai wani sahabi ya ce: Ya Rasulullahi inyi

wasiyar bada dukiya ta gaba daya sadaka bayan na mutu? Sai Manzo Allah ya ce: masa ina, ai

kabar 'ya'yanka wadatattu, ya fi ka kwashe dukiyarka gaba daya ka bada, a karshe ka zama ka

barsu suna roke-roke ga mutane. Sannan yace: To ya Manzo Allah zan kasa uku in bada kashi

daya. A nan ma dai Manzo Allah ya sake ce masa to shikenan, kayi hakan amman dayan bisa

uku yana da yawa).

To, la'akari da wannan Hadithin shine ya sa muke ganin akwai matukar mahimmanci ga masu

dukiya da su maido da hankalinsu, akan aiwatar da \vaqaf, don kebe wata dukiya saboda masu

raunin su, don kuma karfafa musulumci da musulmi. A karshe, ina sanarda vyan'uwa musulmi

cewar: Rubuta wannan littafi da ke yin magana a kan 'waqaf hadin gwiwa ne, tsakanina da

Danmasanin Daura "Aihaji Sani Zangon Daura" a'omin shine ya neme ni a kan yin wannan

rubutu, bayan dawowarsa daga wata tafiya da ya yi, yayin da yazo da wani littafi da aka rubuta

na Turanci wanda ya yi magana a kan 'waqaf wanda a ka rada masa suna "WHAT IS WAKF".

San nan shi da kansa ya fara fassara wani shashi a iitiafin, a karshe ya bani wannan fassara da ya

yi hade da littafin, domin in ci gaba da gudanar da aikin in nemo Hadithai da Ayoyin Al-qur'ani

mai girma da suka dace a kan wannan littafi. To haka din a kayi.

Wanda dama wannan shine dadadden ra'ayinsa kan ya ga ya assasa wani asusu da zai ci gaba da

a'aukan nauyi irin wadancan ayyuka da muka ambata a baya. Saboda haka, ya assasa wani asusu

mai suna kamar haka: "MARYAM EDUCATION TRUST FUND". Haka kuma, ya saya wa

wannan asusu hannun jari a wasu wurare. Ya kuma mallakawa wannan asusu wasu gidaje da ma

wasu abubuwa wanda in Allah ya so za kuji bayanin su a babin bayaninsa da zai yi.

Saboda haka muke masa Addua, da fatan Alheri, da kuma fatan Allah ya sanya zuriyyarsa su

gajeshi, bisa ga irin wadannan ayyukan alheri da yake yi don cigaban musulunci da musulmi.

Domin ya ishemu misali ni mai magana daya ne daga cikin ma'aikatansa dake kula masa da

gudanar da makarantar kofar gidansa, wadda ke hade da masallacin Juma'a wannan gini ayau na

tabbatar miliyan goma ba zata yi su ba, saboda yadda kimar kudinmu ya lalace ayau. Kuma a

Page 3: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

3

duk lokacin da ake bukatar wani abu a makarantar ko masallacin shi keyi da kudin da wannan

asusu ya ke dauke da nauyinsu, kamar Tahfizil Qur'an Rigachikun, da wata makarantar

Islamiyya a nan Tudun Wada Rigachikun.

Haka kuma duk watan Azumi yakan debi wani abu daga ciki don sayawa masu musulunta littafai

da tufafi. Haka kuma likkafani in anyi Rasuwa, da daukar nauyin wasu marasa lafiya a Asibiti da

tallafawa makarantar yara marayu da basu da gata, da ma sauran wasu abubuwa da ni ban sansu

ba. To, a gaskiya assasa irin wadannan ayyukan da koyi dasu shine babban abinda ya kamata

masu dukiyarmu su maida hankali a kai don samun zaman lafiya a kasa da cigabanta.

A karshe nake fatan Allah ya saka ma shi Dan Masanin Daura da Alheri bisa sunnanta wannan

aiki da yayi wanda da dadewa gashi nan a rubuce a littafi, amma ba'a aiwatar da shi. Kuma muna

fatan Allah ya sanya aikin ya zama karbabbe wurin Allah mai bayar da sakamako, kuma Allah

ya sanya tsarkin zuciya cikin aikin ya kuma sanya Albarka a ciki. Masu dukiyarmu kuma dake

da fatan tara dukiya ta halas ko ma ta hanyar Haramun, don su kece raini, babu zakka, ba sadaka,

ba taimakon yan'uwa, bare makwabta da masu rauni. Su kuma muna fatan Allah ya ganar dasu

su gane wannan ba alheri bane gare su, a'sharri ne gare su, domin za'a tattara abinda suka boye

ba zakka, ayi masu tsakiya da ita ranar Alkiyamah. Su kuma malaman da za'a jawo a dora kan

irin wadannan ayyuka na Amana masu nauyi muna fatan Allah ya sa su bada hadin kai kada su

zama fitila mai haske jama'a mai kona kanta. Allah ya yi mana jagora, amin.

AssalamuAlaikum Dan'uwanku

YUSUF MUH'D SAMBO RIGACHIKUN

Sugaban Makarantar Maryam Qur'anic,

School T/Wada - Rigachikum

Page 4: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

4

GODIYA

Godiya da Yabo sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon gudanar da

wannan aiki mai girma cikin kankanin lokaci, wanda kuma wannan aiki, na waqaf, ba bakon abu

bane a littafan Fiqun Larabci, amma bakon abune a Hausa. Saboda haka dama ni mutum ne mai

sha'awar rubuce-rubuce ganin an nemi in rubuta wannan littafi sai na fara kawai, saboda

sha'awata da aikin. Kuma ina mika godiya ta, ta musamman ga Alaramma Malam Ridwanu

Muhammad Kaduna da ya taimaka mani wajen fitomin da wadannan ayoyin fili dake magana

akan taimako da dukiya kojikida rai ma gaba daya. Haka kuma a kullum na kanyi Addua ga

dalinaina dake taimaka mani akan wannan aikin. bayan Sulaiman Shehu akwai kuma Jibril

Muh'd Sani Rigachikun, ina fatan Allah yayi masu Albarka bisa taimako na da sukeyi wajen

kwafe mini rubutu da kuma karbar shifta in ina fadi, suna rubutawa, Allah ya saka masu da

alheri, Amin.

Haka kuma shima asusun da ya dauki nauyin bugawar mai suna MARYAM EDUCATION

TRUST FUND da Alhaji Sani Zangon Daura ya kafa Allah ya saka masa da alheri, mu kuma

Allah yasa wannan littafi ya zama tunatarwa ga masu dukiyarmu da rayar da ayyukan Allah da

taimakawa musulunci amin. AssalamuAlaikum

Dan'uwanku

YUSUF MUH'D SAMBO RIGACHIKUN

Headmaster, MaryamQur'anic School

T/Wada, Rigachikun.

Page 5: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

5

BAYANIN SANI ZANGON DAURA

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ALHAMDU LILLAHI RABBILALAMIN

WASALLALLAHU ALANNABIYIL KARIM

Bayan haka: Da farko dai ina kara mika godiyata ga Allah mai girma mai daukaka wanda yake

daukaka wanda yaso ya kuma kaskantar da wanda yaso.

Wanda ya rabawa kowa abinda zai samu anan rayuwar duniya da kuma can lahira. Saboda haka,

muna fatan Ni'imar da Allah Ya Ni'imtardamu da ita anan duniya, muna fatan Allah Ya bamu

gidan aminci da dauwiwama, kuma in ya tashi bamu muna fatan Allah ya bamu Aljanar Firdausi

amin.

Bayan haka, ni Sani Zangon Daura babu shakka ina cike da murna da farin ciki da Allah Ya bani

ikon ganin kammala wannan littafi na waqaf da muka hada hannu ni da Malam Yusuf Muh'd

Sambo Rigachikun mukayi. Domin tun tasowata Allah Ya nufe ni da cudanya da ayyuka daban

daban. Na jagoranci jama'a, kuma galiban ina ganin halin da jama'a suke ciki na al'amurran

rayuwa na yau da kullum, balle kuma rayuwar mu ta yau, da za'a wayi gari mutum zai tashi da

safe ga yara kanana tare da shi suna neman kudin makaranta ko kuma littattafai don gudanar da

karatunsu da kuma lalurar biyan kudin Asibitin yara ko iyali, ko kuma yanda ma za'a sami wata

makaranta gaba daya, yara da mata suna son koyon Addininsu, amma babu yanda za su yi,

saboda rashin samun wanda zai dauki nauyi biyan malaman, da sauran abubuwa na makarantar.

Sa'annan ga kuma ‘ya'yan 'yan'uwa da abokai wandanda suma suke da bukatar a dauki nauyin

al'amuran gudanar da rayuwarsu ta ilmi na sana'a da na sanin Addininsu, don ya zama rayuwarsu

ta zama tsararriya, saboda haka shi yasa kullum tunani na shine:

In ga na nuna wa 'ya'yana cewar su tashi da wuri suma suga sun nemi abin kansu, ta yanda koda

Allah ya nufa na riga su mutuwa kada suyi dogaro da Dan abinda suke ganin Sani na da shi,

domin larabawa sukan yi wani kirari cewar: "innai fada man qala ha na za, laisal fada man qala

kana ably" wato, ma anar itace kamar haka: (Nagar taccen saurayi shine: wanda ya ce gani nan

nima, amma ba saurayi bane wanda ke cewa da ubana shine kaza.)

Page 6: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

6

Saboda haka, ni babu abinda nake kyama kamar zaman banza, ba aikin yi ba zuciya ba neman

abin kai, ba neman abin dogaro wannan ba rayuwa bace, mai dorewa. Amma kullum ina tunanin

masu bara wadanda, basu da yanda zasuyi su nemi abu, imba sunyi bara ba. Kamar Makafi,

Kutare, Guragu da wasunsun.

Saboda haka nayi tunanin bude wani asusu don daukar wannan nauyi gwargwadon iko, da kuma

taimakawa wasu ayyuka dake da bukatar hakan. Asusun na rada masa suna kamar haka:

MARYAM EDUCATION TRUST FUND (WAQAF) kuma na budewa wannan asusu abubuwa

kamar haka:

GIDAJE

1. 8A da 8B Mambila Close Malali, Kaduna C of 0 No. NC15355

2. KW14 Alkalawa Rd., T/Wada - Kaduna C. of 0 No. NC 17 383

3. 46E/47E Hausa/Ibo Rd., S/Gari Kano C of 0 No. LNK/COM/RC/29/309

4. 12 A Keffi Rd., Barnawa GRA, Kaduna C of 0 No. NC857

5. No. 5 U/Kaji, Kaduna, inda su Auwali Dankuwu suke zaune (formerly property of Habiba

Isa Kaita)

6. AC 7 Kano Rd., Kaduna (wanda Sarkin Daura marigayi Alhaji Muhammadu Bashar ya ba

Sani Zangon Daura, shi kuma ya ba M. E. T. F. (WAQAF)

7. Gidajen Kado guda 64 da aka gina akan kasa mai fadi kadada 35+ duka na WAQAF ne.

(Kado Estate) C of 0 No. MISC 20674 Abuja.

FULOTAI, GONAKI DA GARAKE

1. GonarlemuakanhanyarZaria,T/Wada R ig a c h iku n (2) (na wajen Alhaji Umaru Audi da

marigayi Marafan Sokoto Alhaji Danbaba

2. Fuloli na New Malali Extention behind Kaduna North Water Works C of 0 No. KD 3394

3. Plot adjescent to Air Force Workshop, Zaria Rd., Barakallahu, Kaduna.

4. Orchard Farm adjescent to Dr. Shehu Lawal Giwas Farmland (wataka Muhammadu Jabbi

Bungudu)CofONo. NC18

5. Plot na Bye-pass Sabuwar, Panteka Kaduna (filin gina Masana'anta) C of 0 No. KD 9486

6. Fuloti Katampe, Abuja C of 0 No. MISC 51337

Page 7: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

7

7. Filin dake gaba da gidan Alhaji Duna U/Kaji Kad.

8. Fulotin dake adjescent da gidan Alhaji Duna, U/ Kaji kaduna (Gidan Shanu)

9. Filin Gona mai girman Kadada dubu goma a Gadan Malamman, Kachia L. G. A. Kaduna

State.

HANNAYENJARI

1. Nortex Nig. Limited Kaduna - 17%

2. Afribank Pic, N 1,136,600.00 (Asalin hannun jari da abinda ke karuwa)

3. Balm Holding Co. Limited, Kaduna, Maryam Education Trust Fund tana da jari na milliyan

biyu (N2m)

Ko bayana iyalina ko 'ya'yana, ko xyan'uwana babu wanda yake da ikon yayi amfani da wannan

asusu ta wata hanya daban imba, ta hanyar da na kafa asusun dan ita ba. Kuma cigaban wannan

asusu shine samun gudanar sadaka mai gudana bayan mutuwa, kamar yadda Hadisin Manzon

Allah (S. A. W.) ya nuna. Cewar: Idan Dan Adam ya mutu duk ayyukansa sun yanke sai kawai

sadaka mai gudana:

1. Ya zama ya bar ilmi da ake amfana da shi.

2. Ko kuma ya bar wasu ayyuka na Alheri da ya assasa. Kamar gina rijiya, dasa itaciya, Gidan

baki, Kebewatadukiya donaiwatar da wasu Ayyuka.

3. Barin yaro, na kirki da zai rika yi maka addu'a bayan ranka.

Saboda haka nikam ina ganin babban abu wajena shine inga na sami rahmar Allah kamar yadda

kowane musulmi Kirki yake bukata/fata.

Dukiyar nan da Allah Ya sanya ta a hannuna fata nake ta zama mabudin shiga Aljanna gareni, ba

ta zamar mani mabudin shiga gidan Azaba ba. Manzo Allah (SAW) Ya taba tambayar ahabbansa

kamar haka: Cewar "wa yake so dukiyar magajinsa ta zama tafi soyuwa zuwa gareshi?"

Kowannensu sai ya amsa da cewar babu wanda ke son haka. Saboda sanin wasu basu fahimci

ma'anar ba, sai ya kara bayani kamar haka:

Page 8: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

8

Dukiyar ka itace abinda, ka cida kanka kuma ka kyautar kuma kayi sadaka da kuma sauran wasu

ayyukan alhairi daka gudanar da kanka.

Amma dukiyar magadanka kuwa itace abinda ka mutu kabar masu gado. Saboda haka, mutumin

duk da bai sadaka, fidda zakka, da gudanar da sauran ayyuka na alhairi a rayuwansa, to, kusan

yafi son dukiyar magada tayi yawa ne kawai ba tashi dukiya ba. Saboda haka, nake kira ga

sauran wadanda Allah Ya rufa masu asiri da su yi kokarin kebe wani abu daga dukiyarsu don

tabbatar da wani aiki daga cikin ayyukan Allah, wanda in aka samu dukkan wadanda Allah Ya yi

wa rufin asiri, sun daddafa, sauran bangorori to in Allah yaso za'a sami saukin koke-koken masu

rauni. Bala'i ma zaiyi sauki a kasa, rashin albarkar abubuwa zai yi sauki, sata, fashi da makami

duk zai yi sauki, gaba tsakanin mai shi da mara shi zai yi sauki. Hatta kuma'ya'yayenmu ma da

suke kin maida hankali suyi karatu a makarantu, saboda tunanin akwai dukiyar banza da aka tara

masu zasu yi sauki, da zarar sun ga cewar muna gudanar da dukiyarmu ta hanyar aiwaitar da

aikin Allah.

Muna fatan Allah Ya yi mana jagora ya fadakar damu, ya gafarta mana zunubanmu.

AssalamuAlaikum

Nine Sani Zangon Daura

BANBANCINWASIYYADAWAQAF

Wasiya ana yinta ne yayinda mutum yake cikin halin rashin lafiyar da yake jin ba zai tashi ba.

Shi yasa Shugabannin musulunci suka tsaya akan kashi daya cikin uku 1/3 na dukiyar da mamaci

ya bari. Wadansu ma suna ganin cewa kada ya fi kashi daya cikin biyar 1/5. Sayyadina Abubakar

Saddiq Allah ya yarda dashi yana gaba akan haka wato kashi daya cikin biyar 1/5.

Amma WAQAF anayinsa ne a halin ana cikin koshin lafiya. To anan an yarda da cewa mutum

yana iya bada duk abinda yake son badawa daga abinda Allah ya hore masa saboda ayyukan

Allah (SWT) Madaukakin Sarki.

Kuma inya badata akwai yadda ake gudanar da ita, da kuma masu tafiyadda ita har zuwa karshen

duniya. Bata shiga cikin gado, koda mutumin da ya kafata ya mutu - sadaka ce mai gudana.

Alhamdulillah.

ASSALAMU ALAIKUM.

NINE SANI ZANGON DAURA

Page 9: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

9

WAQAF

MA'ANARSA

Ma'anar "Waqaf a Luggar larabci ita ce: "Kebewa", ko "Tsarewa/' Amma idan an ce "Waqaf" a

shariance ana nufin: "Tsare asalin abu, ta hanyar hore amfanin abin da wata jama'a ko ga wani

aiki na musamman".

Ma'ana: "kebe dukiya sarrafar da amfaninta Fi-sabi-Lillahi, ga wani aiyanannen aiki na musulmi

da musulunci, ko wani abinda suke bukata wanda basu da hanyar iyayin abin.

Saboda haka, kebe dukiya da sunan Waqaf yana nuna babu dama a sayar da abin da aka kebe din

ko a bayar dashi ko a kyautar da shi, ko a gada. Domin ya riga ya zama wani kaya na aiwatar da

aikin Allah.

Kuma mutumin da ya ba da dukiyarsa, ko yankinta, saboda Allah don a gudanar da ita akan

taimakawa masu bukata, sunansa "WAQIF". Kamar yadda musulmi zai bada dukiyarsa, haka

kuma wanda ba musulmi ba ma yana iya yin haka. Kuma ana iya bada kadara.

HUKUNCINSAAMUSULUNCI

Hukuncin 'Waqaf a musulunci abin so ne, wato Mandubi ne. Abinda ya sa aka ce abin so ne,

domin aiwatar da wani aiki ne da yake sanya mutum ya samu kusanta ga Ubangijinsa. Kuma

zamanin Jahiliyya kafin zuwan musulunci Larabawa basu san da 'Waqaf ba, basu san da ware

wani abu ba don wata rayuwa ta gaba. Ban manta ba da wani abu da na taba karantawa game da

wani dattijo wanda ya zo yana shuka dabino, sai wani sarki na zamaninsa ya zo wucewa ya same

shi cikin wannan hali (na shuka dabino) kuma ga shi dattijo, shiko dabino a al'adar tsirarsa yakan

kai shekara dari (100) ba a fara amfani da shi ba; kafin baiyanar ilimin kimiyya. Sai ya ce masa:

"Yaya kake shuka abinda kafin ka ci amfaninsa Rayuwarka ta kare? Sai dattijon ya amsa masa

da cewar: "Haka ne kamar yadda sarki ya fadi, amma ai nima ina shukawane don wadanda zasu

biyo bayanmu, su ci kamar yadda wadanda suka gabace mu suka shuka ba don kansu ba, sai don

Page 10: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

10

na bayansu ma su ci." Amma kuma duk gaba daya ma kowane abu a musulunci yana bukatar

asamo masa hujja daga wurare biyu (2) ko hudu a kataice:

1. Hujja daga Littafin Allah (AI-Qur'ani)

2. Hujja daga Sunnar cikamakon Annabawa, Annabi Muhammad (SAW)

3. Ijma'in Sahabbai ko Malaman Sunnah

4. Kiyasin Sahabbai ko Malaman Sunna.

Saboda haka, akwai Hujja mai karfi akan gudanar da "Waqaf sakamakon Istinbadin Hadisin

Annabi (SAW), ta hanyar, wato Hadisin da Abu-Hurairata (R. A.) ta ruwaito daga Annabi

(SAW) inda yake cewa: "A yayin da mutum rayuwarsa ta yanke ta dalilin mutuwarsa, to,

fa aikinsa da ya saba yi a raye ya yanke kenan sai guda uku kawai ne zasu ci gaba da saduwa da

shi a Kabarinsa, (wato kafin tsayuwar Al-kaiyamah)

1. Sadaka mai gudana.

2. Kowaniilmidaakeamfanidashi. :

3. Ko kuma barin wani nagartaccen yaro da zai rika yi masa addu'a

SABODA HAKA, ANAN SAI MALAMAI SUKA

FASSARA MAANAR SADAKA MAI GUDANA DA

"WAQAF"

Ina fatar za a yi min ahuwa, don na fara gabatar da hadisi kafin ayoyi. Amma ni na yi haka ne ba

don fifita shi akan ayah ba, sai don in jawo hankulanmu da nuna cewa wannan hadisi gare shi

aka sami hujja mai kwari ta tabbatar da "Waqaf" domin an ambaci sadaka mai gudana bayan

mutuwa. Ashe ka ga waqaf kenan.

Haka ma in muka dubi hadisin da Dan Majah ya ruwaito cewar: Manzon Allah ya ce: "Lallai

yana daga cikin abinda ke riskar mumini na daga aikinsa, da kyawawan aikinsa bayan

mutuwarsa:

1. Waniilimidayayadashi.

2. Ko wani da na kirki da ya mutu ya bari.

3. Ko Qur'ani da ya bari gado, ana karanta shi.

4. Kowanimasallacidayagina.

Page 11: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

11

5. Ko wani gida da ya gina, don matafiya.

6. Ko wani ruwa da ya tanada, kamar gina rijiya/ rijiyoyi.

7. Ko wata sadaka da ya ware daga dukiyarsa a lokacin rayuwarsa. (AL-HADITH)

Saboda haka, Manzon Allah (SAW) ya yi waqaf kuma sahabbansa su ma sun yi waqaf na gina

masallaci da bayar da filin da suka mallaka da gina rijiyoyi da bayar da lambuna da ke cike da

'ya'yan itatuwa, da bayar da dawakai don kebe su saboda yaki. Kuma mutane ba su gushe ba suna

yin waqaf daga dukiyoyinsu har zuwa ranarmuwannan.

Idan dan Adam ya mutu, to, babu kuma wani abu da zai ci gaba da gudana nasa na alhairi in ba

abubuwa goma ba

WATO SUNE KAMAR HAKA

1. Rayardailmidayadashi

2. Samunnagartacciyaraddu'a

3. Dashukadabino

4. Da sadaqamai gudana

5. Dagadardalittafin(AI-Qur'ani)

6. Datoshekofardamaharakeshigowa

7. Da gina rijiya/riyoji

8. Ko biyan kudin wani gulbi don amfanin jama'a

9. Ko kuma gina gidanbaki

10. Ko kuma gina wani wuri da za a cigaba da raya ambaton Allah, (wato makaranta ko library

(Dakin karatu), ko waniofis, dontsare-tsaren ayyukan musulunci da dai makamantansu.

KWADAITARWA GAME DA MUHIMMANCIN WAQAF

(KEBE WANI ABU) DON GUDANAR, DA AIKIN ALLAH

DAGA LITTAFIN ALLAH AL'QUR'ANI MAI GIRMA

ASSALAMUALAIKUM

Page 12: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

12

Bayan haka, ya yan'uwa musulmai kamar yadda ya gabata munyi bayanin cewar ya kamata mu

nemo Hujja daga littafm Allah AI-Qur'ani mai girma don fadakar damu muhimmancin waqaf a

musulunci da kuma, amfanin sa ga musulmi; domin shi AI-Qur'ani mai girma shine tsari

tabbatace kuma jagora, kuma haske ga duk wanda ya yi riko da shi. Saboda haka duk abinda

musulmi suke nema na Addininsu da Rayuwarsu, da Shugabancinsu, da Hukuncinsu, da tattalin

Arzikin Kasarsu, da abinda ke farfado da tattalin arziki da abin da ke Rusa shi, dukyana nan

cikin littafin Allah AI-Qur'ani mai girma da Rayuwarsu bata gurbata ba;

Domin shi AI-Qur'ani ga Dan Adam kamar "manual" (Jagora) ne ga kayayyakin Electornics

yanda in ka bi tsarin da aka tsara wajen amfani da abin kamar yanda "Manual"ya nuna maka, sai

ka dade kana amfani da shi baka sami wata matsala ba;

To haka ma, AI-Qur'ani yake ga Dan Adam da Allah ya hallicce shi sai ya bashi manual da zai

jagoranci Rayuwar shi shine AI-Qur'ani mai girma. Don haka ga abinda AI-Qur'ani yace game

da muhimmancin tanadin aikin Alheri, wato waqaf:

SURATUL BAQARAH AYAH TA 3

"Wadanda suke yin imani game da gaibi, kuma sun tsayar da sallah, kuma daga abinda muka

azurta su suna ciyarwa".

SURATUL BAQARAH AYAH TA 110

"Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bayar da zakka, kuma abinda kuka gabatar domin kanku

daga alhairi, zaku same shi a wurin Allah, lallai ne Allah, ga abinda kukeaikatawamaiganine."

SURATUL BAQARAH AYAH TA 177

"Bai zama addini ba domin kun juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini

shi ne ga wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira da Mala'iku da littafan sama da

Annabawa, kuma ya bayar da dukiya, a kan yana son ta, ga mai zumunta da marayu da matalauta

da masu neman taimako saboda gajiyarsu, kuma ku ba da zakka, ku tsare amanar da aka ba ku,

kuma ya bayar da zakka, da masu cika alkawari idan sun kulla alkawarin da masu hakuri a cikin

tsanani da cuta a lokacin yaki. Wadannan su ne suka yi gaskiya. Kuma wadannan su ne masu

takawa".

Page 13: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

13

SURATUL BAQARAH AYAH TA 215

"Suna tambayar ka mene ne zasu ciyar. ka ce: Duk abin da kuka ciyar na daga alhairi ga mahaifa

da mafi kusantar dangantaka da marayu da dan hanya, (matafiyin, da ya sami kansa cikin larura).

Kuma abinda kuka aikata daga alhairi, to lallai ne Allah gare shi masani ne".

SURATUL BAQARAH AYAH TA 254

"Ya ku wandanda suka yi imani! Ku ciyar daga abinda muka azurta ku tun gabanin wani yini ya

zo maku wanda babu ciniki a cikinsa, kuma babu abuta, kuma babu ceto, kuma kafirai sune

azzalumai"

SURATUL BAQARAH AYAH TA 261 - 262

"Siffar wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu a cikin hanyar Allah, kamar siffar kwaya ce wadda ta

tsira da zangarniya bakwai, a cikin kowace zangarniya akwai kwaya dari. Kuma Allah Yana

ribinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani". 261

"Wandanda suke ciyar da dukiyoyinsu a cikin hanyar Allah, sa'annan kuma ba su biyo bayan

abin da suka ciyar din da gori, ko cuta ba, (to, wadannan) suna da sakamakonsu a wurin

Ubangijinsu, kuma babu tsoro a kansu ranar tashin Al-kiyama kuma ba su zama suna

bakincikiba"262

SURATUL BAQARAH AYAH TA 265

"Kuma siffar wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu domin neman yardojin Allah, kuma da

tabbatarwa daga kansu, kamar misalin lambu ne a jigawa wadda wabilin hadari (maimakon

ruwa) ya samu, a kanta saboda haka sai ta bayar da amfaninta ninki biyu. To, idan wabilin ruwa

bai same taba sai yayyafi (ya ishe ta), kuma Allah ga abinda kuke aikatawa Mai gani ne.

(wannan shine misalin aikin Alhairi)

SURATUL BAQARAH AYAH TA 267

"Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ciyar daga mafi kyaun abinda kuka sana'anta, kuma daga

abinda muka fitar saboda ku daga kasa, Kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama masu daga

Page 14: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

14

gare shi kuke ciyarwa, alhali kuwa ba ku zama masu karbarsu ba (in da ku aka ba) face

kunruntse ido a cikinsa. Kuma ku sani cewa lailai ne, Allah mawadaci ne Godadde".

Saboda haka anan wannan aya tana nuna mana, matukar zamu bayar da kyauta ko sadaka ko

taimako, to mu bayar da mafi kyau, ba batacce ba, wanda inda mu aka ba, ba zamu so ba.

SURATUL BAQARAH AYAH 271 - 274

"Idan kun baiyanar da sadakoki to, yana da kyau kwarai kuma idan kuka boye su kuka je da su

ga matalauta, to, shine mafi alhairi gare ku, kuma yana kankare, miyagun zunubanku da kuma

miyagun ayyukanku, saboda haka duk abinda kuke aikatawa Allah na sane da shi. 271

"Shiryar da su ba ya a kanka, kuma amma Allah Shine Yake shiryar da wanda Yake so kuma

abinda duk kuka ciyar na alhairi, to, domin kanku ne, kuma ba ku ciyarwa face domin neman

yardar Allah, kuma duk abinda kuke ciyarwa na alhairi za a cika ladarsa zuwa gare ku, ba tare da

an zalunce ku ba". 272

Kuma "(Ciyarwar a yi ta) ga matalautan nan wadanda aka tsare a kan gudanar da aikin Allah, ba

su iya tafiya fatauci a cikin kasa, wadanda ake ganin su mawadata ne saboda kamewarsu kana

iya saninsu daalamarsu, domin ba su rokon mutane da nacewa, kuma abin da kuka ciyar daga

alhairi, to lallai Allah gare shi Masani ne".273

"Wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu, a dare da rana, boye da bayyane, to suna da sakamakosu a

wurin Ubangijinsu. Kuma babu tsoro a tare da su, kansu, kuma ba suyin bakin ciki". 274

SURATUL AL-IMRAN AYAH 134

"Wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani, kuma suke hadiye fushi, da kuma yafe wa

mutane laifi da akayi musu, saboda haka, ba shakka Allah Ya na son irin wadannan mutane masu

kyautatawa.

Page 15: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

15

SURATUL TAUBAH AYAH TA 121

"Kuma basu ciyar da wata ciyarwa, karama ko babba, kuma basu keta wani rafi sai an rubuta

musu (Laddan ibada) domin Allah Ya saka musu da mafi kyawon abinda suka kasance suna

aikatawa na alhairi." 121

SURATUL MUHAMMAD AYAH TA 38

"Ga ku ya ku wadannan! Ana kiranku domin ku ciyar da dukiyarku akan tafarkin Allah, sa'annan

daga cikinku akwai mai yin rowa. Kuma wanda ke yin rowa, to, yana yin rowa ne ga kansa.

Kuma Allah ne idan kuka juya baya (da yi masa da'a) zai musanya wadansu mutane,

wadansunku, sa'annan basu kasance kwatankwacinku ba (wato marowata)". 38

SURATUL HADID AYAH TA 7

"Ku yi imani da Allah da Manzon Sa, kuma ku yi jihadi da daukaka kalmar Allah game da

dukiyoyinku da rayukanku. Wannan shi ne alhairi a gare ku idan kun kasance kuna da sani." 11

ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA YA FADI

GASKIYA. ALHAMDU LILLAH

Page 16: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

16

KWADAITARWA GAME DA MUHIMMANCIN WAQAF

GA MUSULMI DAGA HADISAN MANZON ALLAH

SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

Idan Kuma muka sake dubawa wajen hadisai, akwai hadisin da Anas (RA) ya ruwaito ya ce: "A

lokacin da Manzon Allah (SAW) ya zo Madina, yana isowa farko abinda ya fara ginawa shine

sadaqa mai gudana, wato gina masallaci". Ka ga'waqaf ke nan.

To, bayan wannan sai Manzon Allah (SAW) yace: "Ya ku kabilar Baniy Najjar, ko kun amince

min akan in yi amfani da Lambunku, in biya kudinsa, don in gina masallaci a wurin? Sai suka ba

Manzo Allah (SAW) amsa da cewar, "Wallahi mu kam bamu bukatar a biya mu wasu kudi, don

kawai an yi amfani da wurinmu don yin dakin Allah (masallaci), sai dai kuma muna mayar da

neman ladanmu ne zuwa ga Allah". Saboda haka, sai Manzon Allah (SAW) ya amsa aka gina

masallaci a wurin. (ko da yake a wata ruwayar an ce yaki yarda sai da ya biyasu domin marayu

ne).

An ruwaito wani hadisin wanda Sayyidina Uthman bn Affan (RA) ya ruwaito. Inda yake cewa:

akwai wani lambu da ke cike da *ya'yan itatuwa mallakar wani Balarabe mai suna

"RAUMATIT, amman a karshe an koma ana kiran gonar da sunansa. Kuma akwai inuwa ciki

yadda ya kamata, har Manzon Allah (SAW) yakan shiga ciki, don hutawa a lokacin zafi, Mai

gonar yakan sayar da Qurba daya a matsayin mudu. Sai Manzon Allah (SAW)yace masa: "Ka

sayar da ita akan kimar gidan Al-jannah mana". Nan take ya amsa Umurnin Manzon Allah

(SAW).

Kuma an karbo wani hadisin daga Sa'ad Dan Ubbadata (Allah Ya yarda da Shi) ya ce: "Ya

Manzon Allah lallai Ummu Sa'ad ta mutu, saboda haka wace sadaqa ce ta fi lada?

Sai Manzon Allah (SAW) ya ba shi amsa da cewa: "Shayar da ruwa". Saboda jin haka, sai ya

gina rijiya, ya kuma ce: "To, wannan na yi ne domin Ummi Sa'ad (watau mahaifiyarsa). "kaga

wannan ma "waqaf” ne.

Page 17: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

17

Kuma an samo Hadisi daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: "Abu Dalhatu ya zamo mafi

soyuwar dukiyarsa dake kawo masa kudin shiga ita ce 'BAIRU HAA' takasance tana fuskantar

masallacin Manzon Allah (SAW). Har Manzon Allah (SAW) ya zamo yana shiga cikinta kuma

yana shan ruwanta mai dadi.

To, a lokacin da wannan ayah ta sauka, inda Allah Mai Girma da Daukaka yake cewa:

LAN-TANALULBIRRA HATTATUNFIQU MIMMATU HIBBUNA

Jin wannan aya ke da wuya sai Abu Dalhat ya tashi ya tafi ga Manzon Allah (SAW) ya ce mase:

"Ya rasulullah! Hakika na ji Allah Mai Girma da Daukaka Yana cewa: "Ba zaku taba samun

cikakkiyar (yin) biyayya ba game da ayyukanku har sai kun ciyar daga abinda kuke so".

"To, ni kam lallai mafi soyuwar dukiyata gare ni ita ce 'BAIRUHA'. A saboda haka, ya

Rasulallah! Ka sanya ta a inda duk haga ta dace."

Allahu Akbar! Ka ji inda ayoyin AI-Qur'ani suke tasiri nan da nan. Nan take sal Annabin Rahma

(SAW) ya rika fadin wata kalma kamar haka:

'BAKHIN, BAKHIN DHALIKA MAALUN RAABIN'

Wato kamar a ce: "KAI MADALLAH, MADALLAH wato ana farin ciki da aikin kuma ana

mamakin girman abindaakayi.

Sai Manzon Allah (SAW) ya ci gaba da cewa: Hakika na ji abinda ka ce game da ita, saboda

haka, ni ina ganin ka bayar da ita ga makusantanka ya fi alhairi.

Abu Dalhat ya zartar da umurnin da Manzon Allah ya ba shi, sai ya raba ta ga 'yan'uwansa da

kuma "ya'yan amminsa.

To, anan ma kafin mu wuce wannan Hadisi ya kamata mu dubi wannan Hadisi da kyau mu kuma

gano wasu abubuwa da Hadisin ke karantar da mu.

1. In zakaba Allah ranee - to kar ka yi da abinda bakaso, ko ya dame ka, a'a bada abinda ka ke

so wajen Allah.

Page 18: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

18

2. Kana iya bayarda dukiyarka ko kamfaninkaya zama waqaf don taimakon musulunci yana

iya sarrafa abin ga ko wani aiki, ko wasu jama'a yanda muka ga Manzon Allah ya tabbatar.

Abdullahi Dan Umar ma ya ruwaito Hadisi game da abinda mahaifinsa ya aikata na waqaf. Wato

Sayyidina Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce: "Umar ya sami wata kasa mai fadi, wato

yalwatacciya, a sakamakon yakin Khaibara wajen nasa rabon. Ganin haka, sai yazo wa Manzon

Allah (SAW) yana mai neman shawararsa game da wannan yakin rabo mai dimbin yawa. Sai

yace: 'Ya Manzon Allah! Lallai kam na sami makekiyar kasa a Khaibara, ban kuma taba samun

dukiyar da takai haka ba kuma ta zamo mafi soyuwa garani da dai, saboda haka, wane umurni

zaka ba ni game da ita? Sai Manzon Allah (SAW) ya amsa masa da cewa: "in har ka amince, to

ka tsare asalinta kawai, amma ka mallakar da amfaninta sadaqa, wato mai gudana", ma'ana

'Waqaf'.

Shi ma cikin wannan Hadisi akwai abin dubawa da kyau. Saboda haka, Sayyidina Umar (RA) sai

ya yi sadaqa da ita, ya mallakar da amfaninta kenan ga Allah. Babu dama a sayar, ko a bayar da

ita kyauta ko a gada.

Amma ana bayar da dukiyar waqaf ga mabukata, ko ga makusanta, ko'yanta baiwa, ko gudanar

da wani aikin Allah ko ga baki. Kuma Malamai sun ce babu laifi ga wanda aka ba amanar

tsaronta ya ci daga ciki. Shi ne a sa masa, ko masu lada (albashi). Saboda haka, duk Malaman

Sunnah sun yi littifaqi a kan tabbatar da waqaf.

Kuma a ruwayar da Ahmad ya ruwaito daga Abu Hurairah (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya

ce: "Wanda duk ya ajiye doki yana kiwonsa fisabilillahi, yana mai imani da Allah, yana mai

neman lada game da yin haka, to, ya sani kibar dokin da koshinsa da fitsarinsa duk za a tara su a

mayar da su aikin lada a auna shi a ma'auninsa ranar Al-qiyamah".

Kuma an samo Hadisi daga Khalid bin Walid (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) yace: Amma

kuma shi Khalid ya bayar da sulkunansa na yaki, ya tsare su fisabilillahi", wato waqaf.

Page 19: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

19

Har ila yau dai inda muka sake kwadaitarwa game da kebe kebantacciyar dukiya, don gudanar da

ayyukan musulunici, zamu kara samun Hadisai kamar haka:

1. An karbo daga Dan Mas'ud, (Allah Ya yarda da shi) shi kuma ya samo daga Manzon Allah

(SAW) ya ce: "Babu hassada (a musulunci) sai ga mutum biyu (2)

i. Mutumin da Allah Ya ba dukiya kuma ya sanya ta akan gudanar da ita cikin

Hakkin Allah;

ii. Da Mutumin da Allah Ya baiwa hikimah (ilmi) kuma yazamo yana hukuncida

ita kuma yana karantar da ita (hikimar ko ilmin).

2. Har ila yau an sake karbo wani Hadisin daga dai shi Abdullahi ibn Mas'ud ya ce: Manzon

Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanene daga cikin ku dukiyar

magadansa ta fi soyuwa gare shi fiye da son da yake wa tasa dukiya? Sai sahabbai suke ce:

"Ya Manzon Allah babu daya daga cikin mu da ya fi son dukiyar magadansa fiye da tasa.

Sai Manzon Allah ya ce masu: "To, hakikanin dukiyarsa dai kawai ita ce abinda ya

gabatar na aikin alheri da kansa, haka kuma dukiyar magadansa ita ce abinda ya bari

bayansa bai yi aikin alheri da ita ba". (Bukhari ne ya ruwaito Hadisin).

3. Kuma an karbo wannan ruwayar daga Adiyyi ibn Hateem (RA) ya ce: "Lallai ba shakka

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ku ji tsoron shiga wuta ko da tsagin dabino ne".

4. Ita kuwa wannan ruwayar Abu Hurairah (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: " Babu

wani yini da bayi zasu wayi gari cikinsa, face mala'iku biyu sunsauka.Dayan su yakan ce:

"Ya Allah ka ba mai bayarwa musanyar abinda ya bayar" shi kuma dayan ya ce: "Ya

Allah ka sanya halakar dukiya ga mai rikewa bai bayarwa".

5. A wata ruwayar ta Abu Hurairah, Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ciyar ya kai dan Adam!

kai ma a ciyar da kai".

6. An karbo Hadisi daga Abdullahi Dan Amruw ibn As: (Allah Ya yarda da su) ya ce:

"Hakika wani mutum ya tambayi Manzon Allah ya ce: "Wane musulunci ya fi alheri ga

Page 20: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

20

musulmi? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce masa: "Ka ciyar da abinci kuma ka karanta

sallama ga wanda ka sani da wanda ba kasani ba.

7. Kuma ya zo a cikin Hadisi Qudsi (wato maganar da Manzon Allah (SAW) ya samo daga

wurin Ubangijinsa). Allah Ya ce: "Lallai dukkan aiyukan dan Adam nasa ne ko gare shi

suke. Idan ya yi kyakkyawan aiki a ba shi misalinsa goma har a ribanya masa zuwa dari

bakwai (700) har ya zuwa ribi-ribi da yawa, sai azumi kawai. Lallai shi azumi nawa ne,

kuma ni nake sakamako da shi domin mai azumi ya bar abincinsa da abin shansa da abin

sha'awarsa, domin Girmana.

8. A wata ruwayar ya ce: "Babu yadda za a yi bawa ya kyautata sadaqa, face sai Allah Ya

kyautata mayewa baya akan zuriyyarsa.

9. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Sadaqa tana toshe

kafofin sharri gudusaba'in.

10. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Mai kyauta kusa yake

da Allah, kusa yake da mutane, kusa yake da aljannah, kuma nesa yake da wuta. Amma

marowaci, nesa yake da Allah, nesa yake da mutane, nesa yake da aljannah, kusa yake da

wuta. Kuma jahili mai kyauta ya fi soyuwa wajen Allah fiye da mai bautar Allah

marowaci."(RuwayarTirmidhiy)

KULLAWAQAF

Ana kulla waqaf ne ta dayan abubuwa biyu (2)

1. Aikata wani aiki wanda ke nuni akan cewa wannan aikin na Allah ne, wato 'waqaf' kamar

a ga mutum ya gina masallaci kuma ya tashi ya yi kiran sallah a ciki ba tare da bukatar

hukuncin wanishugaba ba.

2. Ko kuma ta hanyar magana. Ita ma maganar ta kasu kashi biyu.

a. Bayyananna:Kamar ya ce na bada abu kaza mallakata a matsayin waqaf, ko na kebe

abu kaza

Page 21: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

21

b. Ana kuma bayar da waqaf ta hanyar sakayyar magana. Misali shine: "Nayi

sadaqa, ina mai niyyar waqaf".

ABUBUWAN DASUKAKAMATAABADAA

MATSAYIN WAQAF

SUNE KAMAR HAKA:

1. Kudi tsaba, ko a ina suke matukar za a yi amfani da su kamar yadda shari'a ta ajiye.

Misali, kifi a ruwa, ko kudin da aka jefar cikin ruwa ba a ganinsu ba za a bada su ba. Duk

abinda aka haramta ayi amfani da shi ba za a bada shi a matsayin WAQAF ba.

2. Ana iya bada kadara, kamar gidaje, gonaki, fadamu, lambuna, dasauransu.

3. Kadara kamar su shanu, dawaki, tumaki, motoci, kanana ko manya na haya, jiragen sama

da na kasa. Masaku ko masana'anta amma banda wuraren giya; sai dai in an daina yin

giyar, a maida su masana'antu na yin abubuwan da addini ya yardadasu.

4. Ana iya neman gudunmawa daga jama'ar musulmi da kuma ma'abuta littafi (Ahalul

Kitabi) watau Kirista ko Yahudu.

5. Ana iya yin ciniki, don karuwar wannan asusu da karfafashi.

ABUBUWAN DA SUKA DACE A YI AMFANI DA

DUKIYAR WAQAF A KANSU

1. Ilimin 'ya'ya na 'ahira da na duniya. Jikoki \a'yan Van'uwa da Ya'yan gajiyayyu da

sauransu masu bukata da iyalin wanda ya kafa wannan waqaf.

2. Gina makarantun Islamiyya da na boko. Lura da su, biyan limamansu da makarantansu.

3. Gina ko gyaran makarantu, masallatai da biyan limamansu, da kuma masu tsare

maqabartu.

Page 22: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

22

4. Gina Asibitoci da makarantun koyar da ayyukan jinya da rike su gwargwadon hali.

5. Taimakawa mata da mazajensu suka rasu: haka kuma mata tsofoffi da musakai.

6. Gudunmawar barnar ruwa, wuta, mota da makarantansu.

7. Wadanda guzurinsu ya kare, alhali kuwa suna cikintafiya.

8. Taimakon 'yan'uwa gajiyayyu. Amma ba wadanda su kealmubazaranci ba: ko mashaya

ba.

9. Taimako ga almajirai wadanda ba su da gata.

10. Taimakon marayu, masu bukata, kuma ga su a matsecikinlalura.

11. Taimako ga asibitoci - taimaka wa marasa lafiya wadanda ba za su iya biyan kudin asibiti

ba: kuma ga su a matse cikin lalura.

12. Taimakon gyara, ko gina, ko kewaye maqabarta, ko, makarantar'yan mata kota yara.

13. Sauran ayyuka nagari wadanda musulunci ya yarda a taimaka a kansu. Sayen makamai da

badasu ga musulmi, don tsaron kansu, da mutuncinsu, da rayukansu da addininsu.

14. Taimakon musulmi, don gudun hijira, ko, wadanda aka kore su daga gidajensu, don fin

karfi da kiyayya kamar na Zangon Kataf, Tafawa Balewa, Numan da makamantansu.

Wato tanada masu wuraren matsuguni da abincinsu da kuma asibitinsu da tufafinsu.

15. Taimakon yunwa da koran yaki kamar mutanen kasarSomaliya.

16. Taimako ga muatanen da aka wa waso kamar sata, kowace iri.

Page 23: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

23

MASU GUDANAR DA WAQAF - (ASUSUN TAIMAKO)

1. Wanda ya kafa wannan Waqaf yana iya nada wanda zai gudanar da shi. Saboda amanace

mai karfi kwarai da gaske: kuma ana bukatar ta dore har ila masha Allahu ya zama wajibi

ya nemi mutane amintattu, masu hangen nesa, ya nada su, tare da shi, su gudanar da

wannan waqaf.

Haka kuma yana iya zaben shugaba daga cikin su, su cigaba da gudanar da asusun kamar

yadda aka zana. Har ila yau, waqif yana da iko ya nada shugabanni wato daga A sai B, C,

D,......... yana daga abinda ake bukata a sami hanyoyin da za su rinka kawo kudi ga

asusun, don ci gaba da ayyukansuduka.

AYYUKAN MUTAWALLI (MAI GUDANAR DA WAQAF)

1. Lallai ne ya gudanar da asusun da gaskiya, da rikonamana.

2. Lallai ne ya lura da kadarorin da ake da su. Ya gano hanyoyin da zai kara su - don su tofu.

3. Lallai ne a rubuta dukkan abinda ya karu a bisa abinda ake da shi a hannu.

4. Lallai ne Mutawalli ya tabbatar da an yi amfani da asusun akan abubuwan da aka yarda

ayi amfani dasu.

5. Lallai ne Mutawalli ya rinka ba da kasafin kudin da za su shigo, haka kuma abinda za'a

kashe kowaceshekara.

6. Lallai ne Mutawalli ya tabbatar da lissafin shiga da fita a rubuce kamaryadda ka'ida ta

aje.

7. Lallai ne Mutawalli ya ba da labari a rubuce yadda aka kashe kudi, da yadda aka same su.

Masu bincike lissafi (Auditors) su za su yi haka, don gabatarwa ga shugabannin zartarwa.

8. Lallai ne Mutawalli ya zartar da umurnin shugabanni kamar yadda suka ba da umurni.

Haka kuma shi zai ba da duk irin labarin da zartarwa.

9. Lallai ne Mutawalli ya zartar da umurnin shugabannin dukiyar asusun idan aka nema.

10. Yana kan Mutawalli ya biya kudaden da aka nema bisadokarkasa.

11. Mutawalli ba shi da ikon da zai ba da, ko jinginar da kadarar asusun ba tare da izinin

shugabannin ba.

12. Idan shugabannin sun ga ya cancanta a biya su wani abu, don taimakawa ga abinda suke

Page 24: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

24

Page 25: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

25

kashewa wajen halartar taro da sauran su, to, lallai Mutawalli ya lura da haka, kuma ya

biya, matuka akwai kudi a asusun a lokacin.

13. Ana son Mutawalli ya tabbatar da gudanar da asusun nan bisa yadda shari'a ta ajiye.

14. An samu a nada wata \ar karamar kungiya don duba wani al'amari na wannan asusun, ya

kuma ba da labari da shawara ga babbar kungiya.

15. Idan akwai wani abun asusun a gaban shari'a, mutawalli ba shi da iko ya janye shi, sai da

izinin shugabanni.

HAKKI DA IKON MUTAWALLI DA KUMA

KUNGIYAR MUTANE DA KE DA ALHAKIN

GUDANAR DA ASUSUN AMANA

1. Mutawalli yana da cikakken 'yanci ya gudanr da asusun amana da kuma tsara shi bisa kan

ka'ido din da aka shimfida masa.

2. Mutawalli yana da 'yancin ya yi amfani da kudin da ake da su ya kara gine-gine (gidaje,

hanya, kantuna da sauransu), don su rika kawo kudi ga asusun. Amma duk da haka sai ya

sami iznin masu bada umurni wato shugabanni (Board) bisa yadda zai gudanar da shi

sa'annan ya iya rushe wadansu wurare, don gyara, ko kuma yin kwaskwarima.

3. Masu bada umurni, don gudanar da asusun suna iya cire mutawalli idan an same shi da

laifin da ake tuhumar shi da shi (a fadi laifin a rubuce).

4. Mutawalli da aka cire yana iya kai kara ga Alkalin musulunci wanda aka yarda da

adalcinsa da tsoron Allah idan shi mutawalli bai amince da hukuncin cire shi ba.

5. Mutawalli yana iya bin sawun kayan amana ko kudi amma da izinin masu bada izinin

gudanar da asusunkudinamanar.

6. Mutawalli yana da ikon ya dauki ma'aikatan da za su taimaka masa gudanar da wannan

asusu. Haka kuma ya samu ya yanka masu albashi kamar yadda aka yi masa ka'ida.

7. Shi ma Mutawalli yana iya biyan kansa daga kudin amanar idan ka'idojin asusun sun

zartar da yinhaka.

8. Idan Kuma ka'idojin sun bada izini, Mutawalli yana iya nada wanda zai gaje shi ya dauki

aiki daga gare shi.

Page 26: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

26

9. Mutawalli yana iya ciwo bashi daga Banki, ko makamancinsa, don kara kyautata kayan

asusun idan an ba shi izini. Yana iya yin wanan kari idan shari'a ta yarda da yin irin

kyautatawar.

10. Mutawalli yana da iko ya yi amfani da kudin asusu, don gyaran kadara, ko, biyan takarda,

littafai, hayan wurin da ake ciki, da makarantansu, don kyautata ayyukan Waqaf.

LAIFUFUKA DA HORON MUTAWALLI

1. a. Idan Mutawalli bai kai waqafaka tabbatar da zamanta ba, laifine, ana iya yi masa

horo kanhakan:

b. Rashin shirya kasafin kudi a nunayaddaake samun su, da kuma yadda ke kashe su

(Render - Account)

c. In Mutawalli ya kasa shirya shugabanni su je, su duba kadara/dukiyar asusun,

da kuma litattafan lissafin dukiyar asusun, shi ma laifi ne;

d. Kin mika kadarar asusu idan aka nemi ya yi hakan laifi ne;

e. Rashin bada, ko, kin bada labarin halin da asusu ya ke ci idan aka nema, laifi ne;

f. Kin zartar da umurnin shugabannin asusu, laifi ne;

g. Kasa biyan, ko kin hakkin da ya tabbata a biya, misali: kudin haya, laifi ne;

h. Kasa zartar da dokar da asusun ya shimfida ko kin bin ka'idodin asusu laifi ne;

a. Saboda haka, idan aka sami mutawalli da yin daya daga laifuffukan nan da

aka zana a sama fiye da sau daya, ana iya cire shi, ko tube shi.

b. Idan aka same shi da cin amana, ko rashin tsare mutuncinsa, ana iya cire shi.

c. Taba kadarar asusun ba da izini ba, ko kuma cin kura, ta kadara, ko kudin

asusu, misali: boye wata kadara, don ya mai da ita tasa, ko, aje kudin ta, don

ya sami amfani, ko yin aringizo, don ya sami amfani, laifi ne.

d. Ko ya kasa biyan hakkin, shugabanni har shekara biyu.

e. Samun motsuwar hankali, kona jiki yadda ba zai iya aiki ba kamar yadda

ake bukata.

2. Idan shugabannai suka nada wasu mutane don gudanar da al'amuran asusun, sa'annan suka,

kasa ko suka wuce gona da iri, to, shugabanni sai su dauki nauyin gudanar da asusun da

kansu.

Page 27: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

27

3. Idan aka tube/kori/cire Mutawalli, lelle ne shugabanni su tabbatar da ya mai da kayan

asusun da ke hanunsa ga duk wanda suka nada.

4. Wannan umurni na a mika kayan asusun yana da karfin, Doka/Shari'a.

5. Duk Mutawalli da ka cire, baza a iya mai da shi ba sai bayan shekara biyar, idan har

halinsa ya gyaru sosaidasosai.

6. Shugabanni sun iya karbar hakkinsu da ba'a basu ba bayan Mutawalli ya riga ya yi masu

bayanin dalilan da suka kawo haka.

7. Idan akwai aikin lada/tausayi, ko na addini da Mutawalli ya kamata ya yi, sai bai yi ba,

shugabanni sun samu su sa Alkali ya tilasta masa ya yi aikin. Idan kuma an riga an yi

aikin lallai a tilasta masa yabiya.

8. Haka kuma kowane mutum da ke da hakki yana iya kai karan Mutawalli idan ya ki yin

aikinsa bisa ka'ida, saboda shari'a tana iya ba shi umurni kamar yadda ta ga ya dace.

9. Mutawalli ba shi da izinin ya sai da, ko ya ba da jingina, ko ya bada kyautar wani abu na

wannan asusun sai da izini. Yin haka ba daidai ba ne, kuma duk kullin da aka yi na

cinikin ko na jingina ko na kyautar ya warware.

10. Muhillil-Shadidisune: (SIV-58)&(SIV-10)

YAWAN SHUGANANNIN WAQAF DAGA UKU

ZUWA SHA DAYA

1. Waqafke da ikon nada su.

2. Waqifyakanzamashineshugaba.

3. Yana iya kuma nada wani daga Van kugiyar ya rikeamanar.

4. Yana kuma iya ba wanda ya nada dama su zabi shugaba.

5. Ana iya takaita lokacinsu a shekara biyar, sai a iya sake nada su, ko kuma wasu daga

cikinsu, don a kawosababbinjini, don kara ingantagudanarda asusun.

'YAN KADAN DAGA MANYAN AYYUKANSU (SHUGABANNIN)

a. Sutabbatardakomiyanadaidai.

b. Su tabbatar da cewa ana amfani da dukiya yadda akatsara.

c. Subada umurniga Matawalli.

Page 28: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

28

d. Su ba da bayanin yadda za a yi arnfanin da dukiya, ba su ba da haske kan yadda za a yi da

itaba.

e. Su bi kasafin kudi dalla-dalla, su tabbatar da shirinyayi daidai.Su tabbatar da masuduba

yadda a ke samun kudin da kashe su, suna dubawa kowace karshen shekara, kuma suna

ba da labarin yadda halin da dukiya ke ciki da yadda zata kasance.

f. Su nada Matawalli, ko su kuma tube shi bisa tsari.

g. Suna iya cire asusun idan an kai shi kara.

h. Suna iya canza wa ma'aikata wuraren aiki, sunaiyasayarda kayan asusun kamaryadda hali

ya kawo, suna iya jinginar da kayan asusun yadda ya kamata, suna iya yin musanya da

kuma bada haya.

i. Su kara tabbatar da cewa Mutawalli ko, mutanen da aka ba amana suna gudanar da

amanarkamar yadda ya kamata.

j. Suna iya bincikar, ko, duba dukiyar don su tabbatar da yadda yawanta ko kyawunta yake.

6. Shugabanni suna iya nada dukiya don tafiyar da ayyukan WAQAF.

7. Haka kuma suna iya nada magatakarda wanda shine mai zartar da abubuwan ayyukan

WAQAF.

8. Babban Magatakarda yana karkashin shugabanni. Shine mai gudanar da ayyukan sa suka

ce a yi na yaudakullum.

BABIN TSORATARWA GAME DA CIN AMANA

KO SALWANTAR DA ITA

Ballantana kuma abinda aka tanadawa musulmi don gudanar da ayyukansu na yau da kullum

game da wasu matsalolinsu.

Ya 'yan'uwa musulmai har wa yau dai bamu gushe ba, muna nan dai muna kan jaddada wajabcin

tsare wannan Amana da kuma daukar nauyin ciyar da ita gaba da tsare ta yanda ya kamata, ko

Alhaji Sani Zangon Daura na Raye ko bayan mutuwa, domin shi kam babu shakka ga abinda ya

bayyana gare mu ta gama nasa aikin, domin ya dai yi niyyar kaffa asusun kuma Allah Ya bashi

iko ya aiwatar ya gina makaranta, ya sayi hannun jari a kamfononi, ya sayi gidaje da filaye ya

Page 29: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

29

tanadi ma'aikata saboda haka babu abinda ya rage face a aiwatar da wadannan manufofi da

ayyuka na alhari saboda haka nake tsoratar da mu da kuma muji tsoron Allah, kamar yanda

wadannan Ayoyi da Hadisai da zasu biyo suke gaya mana:

SURATUL AL-IMRAN AYAH TA 75 - 76

"Kuma daga mutanen Littafi akwai wanda yake idan ka ba shi amanar kindari Dukiya mai yawa

zai bayar da shi gare ka, kuma daga cikinsu akwai wanda idan ka ba shi amanar dinari daya ba

zai bayar da shi gare ka ba, face idan ka tsaya-tsayin mai daka sa'annan ya mai da maka. Wannan

kuwa, domin lallai ne su, sun ce, ai "Babu laifi a kanmu a cikin Dukiyar Ummiyyai," kawai suna

fadar karya ga Allah, alhali kuwa suna sane.

"Na'am! Wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya yi takawa, to, lallai ne Allah yana son masu

takawa" 76

SURATUN-NISA'I AYAH TA 9

"Kuma wadanda suke, da sun bar zuriyya masu rauni a bayansu, za su ji tsoro a kansu, su yi

sauna sa'an nan su bi Allah da takawa, kuma su fadi magana madaidaiciya". Ma'ana, kuma kuji

tsoron abinda za ku bari na zuriya bayanku kada ku bar masu dukiya wani ya cinye ya halakar

masu da ita su tashi fakirai.

SURATUN-NISA'I AYAH TA 58

"Lallai ne Allah Yana umurninku ku bayar da amanoni zuwa ga masu su. Idan kun yi hukunci a

tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci. Lallai ne, Allah madallah da abinda yake yi muku

wa'azi da shi, Lallai ne Allah Yakasance mai jine, Mai gani."

KARIN BAYANI GAME DA SAUKAN AYAR

Masana sababin saukar ayoyin Al-qur'ani sunce dalilin saukar wannan aya shine, ranar fatahu

Makka ga Manzon Allah da sahabbansa sun shiga Makka tare da jama'a masu yawa amma anki

bude masu dakin Ka'aba domin mabudin yana hannun Uthman Bini Dalhat, saboda haka sai

Saiyidina Aliyu Dan Abiy Talib (RA) yazo wajen Uthman Bin Dalhat yace: A bani mabudin,

amma sai ya ce: Bazan bayar ba, domin wannan mabudi amana ce wajena kuma yanzu hakkin

shi wajena yaka saboda haka ba zan bayar ba. Jin haka sai haushi ya kama Sayyidina Aliyu, ace

Page 30: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

30

wai wani mutum ya bude baki yace ba zai bada mabudin dakin Allah ga Manzon Allah ba!

Kawai sai ya kama hannunsa, ya murde shi kuma ya amshi mabudin hannunsa, ya tafi ya bude

dakin Ka'aba. Daga nan sai Manzon Allah yace masa ya aje mabudin.

To bada dadewa ba sai Mala'ika Jibrilu ya zoma Manzon Allah da wannan aya daga Allah. Nan

sai Manzon Allah yace: Ya Aliyu dauki mabudin nan ka mayar da shi ga ma'abocinsa. Wato

Uthman Bini Dalhat. Sai Sayyadina Aliyu ya ce: Ya Manzon Allah don me? Manzon Allah Ya

amsa masa yace domin Allah Ya saukar da umurni akan haka. Sai ya karanta masa Aya daga nan

sai Sayyidina Aliyu ya dauki mabudi zuwa ga Uthman Bini Dalhat, yace: Ya Uthman ga

mabudinka amshi, yace: Bazan amsa ba, domin ka kwace shi daga hannuna da can. Sai

Sayyidina Aliyu yace: Kayi hankuri, ka amsa domin Allah Ya saukar da umurni ne. Daga nan sai

Uthman Bini Dalhat yace: Ashe wannan addinin ba wasa bane daga nan sai yace: "ASH HADU

ALLAA-ILA-HA ILLALIAHU, WA ANNA MUHAMMADA RASULULLAHI."

To ya jama'a in har za a saukar da aya ta musamman akan dan mabudi kawai, to yaya kuma

sauran hakkukuwan bayin Allah. To, ya kamata mu ji tsoron saduwarmu da Ubangijinmu, mu

rike kuma mu tsare

AMANA.

Page 31: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

31

ALLAH YATSAREMU

SURATUL - AHZAB AYAH TA 72 - 73

"Lallai mu, mun gitta amana ga sammai da kasa da duwatsu, sai suka ki daukar ta kuma suka ji

tsoro daga gare ta, kuma mutum ya dauke ta, lallai shi (mutum) ya kasance mai yawan zalunci,

mai yawan jahilci". 72

"Domin Allah Ya azabta munafukai maza da munafukai mata, da mushirikai maza da mushirikai

mata, kuma Allah Ya karbi tuba ga muminai maza da muminai mata. Kuma Allah Ya kasance

mai gafara, Mai jin kai". 73

To, la'akari da abinda wannan Hadisi ya nuna, babu shakka akwai abin kula ga wadanda aka basu

tsaron wasu amanoni a karkashinsu da su kula su tsare wadannan amanoni kamar yadda ya

gabata. In kuwa ba haka ba, to, su sani suna cikin hadari mai girma. Domin Annabi (SAW) ya

ce: "Ba a kankare zunubin cin amana da bashi koda kuwa mutum an kashe shi ne a wurin yaki

fisabilillahi".

An karbo daga Ibn Umar Allah Ya yarda da shi yace "Manzon Allah (SAW) yace: "Babu Imani

ga duk wanda ba shi da Amana". Kamar yadda kuma babu sallah ga wanda ba shi da tsarki.

AL-HADITH.

Dabrani ya ruwaito shi.

Saboda haka, ya kamata a lura da cewa a cikin wannan hadisi da ya gabata Annabi (SAW) ya

kore Imani daga maha'inci, mayaudari, kamar yadda ya kore Sallah dagamarasa alwala.

Kuma an ruwaito Hadisi daga Aliyu Dan Abiy Talib Allah Ya yarda da shi ya ce: "Mun kasance

tare da Manzon Allah (SAW) muna zaune, sai warn mutum ya bullo mana daga Kabilar Aliyah,

ya ce: "Ya Manzon Allah! Bani labari da abin da yake mafi Tsanani cikin wannan addinin kuma

da mafi saukinsa". Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mafi saukinsa shi ne'shaidawa babu abin

bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muh'd (SAW) bawan Sa ne, kuma Manzon Sa ne,

mafi tsananinsa ya Dan'uwan Jama'ar Aliyah! "Al -AMANAH" Hakika babu addini ga wanda ba

Page 32: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

32

shi da Amanah, kuma babu Sallah gare shi, kuma babu Zakkah gare shi". Bazzar ne ya ruwaito

shi.

Haka kuma idan muka yi la'akari da wannan Hadisi wanda wannan Dan'uwa ya zo daga kabilan

Aliyah, ya nemi Manzon Allah (SAW) ya gaya masa abin da ya fl tsanani da sauki cikin wannan

addini amma duk da haka abin da Annabi (SAW) ya gaya masa ya fi tsannani a cikin wannan

addini shi ne "cin Amana'. Don haka, duk wanda aka dora wa wannan aiki na "waqaf"

matsayinsa a biya shi hakkinsa. To, in ko har aka biya shi hakkinsa, to, ba ya halatta ya debi

komai daga ciki. In ko har ya kuskura ya diba, to, zai biya wannan abin a ranar tashin Al-

qiyamah, domin ya yi fince kenen. Don haka Manzon Allah (SAW) yake cewa: "Wanda duk

muka dora shi a kan wani aikinmu, kuma muka yanka mai albashin daya dace da matsayinsa, to,

duk abinda ya diba bayan albashin nan nasa, to, ya yi fince, saboda haka muna fatar Allah ya

tsare mu.

YAN KWAMITIN AMINTATTU DA SUKA GABATA

Yan Kwamitin Amintattu da suka gabata, yawacinsu Allah (SWT) yayi masu rasuwa. Sun hada

da

1. Alhaji Salisu (Walin Daura)

2. Alhaji Haru Zangon Daura (Matawallen Daura)

3. Dr. Ahmed Husaini, Shugaban Zane Zane da Aikin Bakin Karfe na Jamiar Ahmadu

Bello ta Zaria.

4. Alhaji Muhammadu Maude, Dankasuwa kuma Babban Dan Siyasa a Kano. Allah (SWT)

Ya jikansu, Ya saka masu da Al-jannar Firdausi - Ameen.

YAN KWAMITIN AMINTATTU A YANZU

1. Sani Zangon Daura

(Dan Masanin Daura) - Shugaba

2. AmbassadarKabir Ahmed

(Magajin Rafin Daura) - Mataimakin Shugaba

3. Alhaji Abba MusaRimi - Wakili

Page 33: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

33

4. Alhaji Suleiman Aliyu

(Kilishin Daura) - Wakili

5. Alhaji Abba Bala - WakiSi

6. Alhaji NasiruS. Zangon Daura-Wakili

7. Alhaji Zayyad Ibrahim - Wakili

Page 34: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

34

FADAKARWA

Saboda haka, ya zama tilas ga duk wadanda aka dorawa nauyin kula da "waqaf" da su tsare

wannan hakki tsakaninsu da Allah, domin dukiya ce da aka ware don taimakon gajiyayyu da

tsofoffi da marayu, da marasa galihu, da miskinai, da fakirai, da guragu, da makafi, har ma da

mahaukata wadanda basu da wanda zai kaisu asibiti, duk akan yi amfani da dukiyar'waqaf don a

taimaka masu. Ballantana kuma gina Makaranta, da asibiti, da gina rijiya, da gina hanya da dai

sauran ayyukanaalhairi.

To, in aka ce a rayuwar mutum wadannan hakkoki na wadannan irin jama'ar sune abincinsa, to,

Allah ya tsare mu daga irin wannan rayuwa. Saboda haka ne ma Allah (SWT) ya fadi a cikin

Littafin Sa mai girma kamar yadda ya gabata a baya cewa:

"Lallai ne waddanda suke cin dukiyar, marayu da zalunci, to hakikanin wuta kawai suke ci a

cikin cikkunansu, kuma za su shiga wata wuta mai tsanani."

Ga kuma inda (SWT) Ya ke Cewa: "Kuma masu kokarin cinye dukiyar jama'a masu rauni, to, su

ma su ji tsoron barin bayansu, suma su yi tunani su gani, shin da su ne suka mutu, aka cinye wa

"ya'yansu dukiyar da suka bar masu, zasu ji dadi? To, in har ba zasu ji dadin haka ba, to, suma su

ji tsoron Allah su bar dukiyar da aka tanada don marayu. "Allah Shi ne wakili akan abin da muke

fadi din nan. Saboda haka muna fatan Allah ya tsare mana imaninmu ya kurma bamu karfin

zuciyar kauda kai daga dukiyar duk da aka sanya ta Amana a hannun mu.

DALILIN RUBUTA LITTAFIN

Ina gabatar da godiya ga Allah Mai Girma da daukaka wanda ya halicci mutum ya sa masa ji da

gani da tunani don su zama masu amafani gare shi. Kuma ina shaidawa babu wani abin bautawa

da gaskiya sai Allah wanda bashi. da wani abokin tarayya, mai biya wa kowa bukatun, shi kuma

ba ya da bukatar komai daga kowa, kuma Annabi Muhammad Manzon Sa ne, cikamakon

Annabawa, Muhammad Dan Abdullahi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

Bayan kaha, dalilin wannan littafi shine: daya daga cikin maya-manya yan kasuwanmu, Sani

Zangon Daura Allah Ya saka masa da alhairi, shine kashin bayan rubuta wannan littafi. Domin a

Page 35: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

35

tsawon zaman dana yi da shi gwargwadon iko, a duk lokacin da yaga ya samu lokaci cikakke,

yakan kirawo ni ya bayyana mun manufarsa da dukiyar da Allah ya mallaka masa, burinsa

kullum shine yana son ya ga ya bar wani abu wanda zai zama "Sadaqatun Jiriyyah" a gare shi ko

bayan mutuwarsa. Duk da ma yana rayen, yana yin iyakar nasa kokarin ta hanyar gina

Makarantun Islamiyyah da daukan nauyin Makarantu da taimaka wa wasu bayin Allah da ya

cancanci a taimaka masu.

Yana cikin wannan tunani nasa na yau da kullum, har Allah Ya nufaya yi tafiya zuwa wata kasa,

saiyasamu wani littafi da yake magana akan xwaqaf, amma da ya yi ta tunanin yaya za a fassara

wannan littafin, cikin harshen Hausa ta yadda zai amfani 'yan'uwa baki daya.

Ni kuma sai ya yi mun magana kuma ya umurce ni da nima in yi nawa kokarin, to, Alhamdu

Lillahi, ni kuma sai na amsa masa da gaggawa a matsiyinsa na uba a muslunci. Maimakon ma a

ce nine zan kai masa wannan shawara sai ga shi shine yake karfafa ni kuma yake bani shawara.

Saboda haka, Allah ya saka masa daalhairiamin,

Daga cikin dalilan da ya sa hankalina ya karfafa zuwa yin wannan muhimmin aiki, nayi la'akari

da halin da wasu mawadatan kasar nan suka shiga tsakaninsu da 'ya'yansu ba a jituwa, Saboda

wai sun hana su su rika kashe kudi irin yadda suke so. To, ta irin wannan dalili, sai aka wayi gari

har 'ya'yan suna fatan ko Allah yasa iyayensu su mutu da sauri, don su mike kafa su samu

rayuwa ta jin dadi a ganin su. Saboda haka, sai aka wayi gari a kasan nan babban mutum mai son

addini, mai kula da addini, idan Allah ya yi masa rasuwa, ya bar Va'ya a bayansa, sai kawai su

shiga yin almubazzaranci da dukiyar da ya bari domin ba su san zafin tara ta ba. A karshe ma kai

in aka nuna maka su aka ce ai xya'yan wane ne, sai kunya ma ta kama ka.

Saboda haka, nake kira ga sauran 'yan'uwa musulmi masu dukiya da su mai da hankalinsu akan

yin irin wadannan abubuwa na alhairi, don su kara fiddo da hasken muslunci, (kamar yadda Sani

Zangon Daura yayi) wanda zai karama musuluncin kwarjini ya kara sa wadanda basu fahimta da

shi ba, su fahimta da kuma jawo hankalin dukkan mutane wadanda basu cikin Addinin

musulunci da su rungumi musulunci. Allah ya yi manajagorabakidayaAmin.

Page 36: GABATARWA BJSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM education trust fund (WAQAF).pdfSaboda haka, bayar da 'waqaf", taimakawa kai ne don ita sadaka ce mai gudana, wadda zata yi wa mutum amfani duniya

36

Domin Allah yana cewa: "Wallahi lahira ita ce ta fi alhairi fiye da ta farko" Domin da zarar ka

tara dukiya a nan duniya, ka tafi ka bar ta, to, hisabinta da tamboyoyi akan tara ta a kanka yake.

To, in kuwa haka ne, to, ya kamata ka yi kokari, ka yi aikin kwarai da ita tun kafin ranar

tamboyoyi akantatazo".

RUFEWA

Alhamdu Lallaihi muna mika godiyar mu ga Allah da ya bamu ikon gabatar da wannan

takataiccen littafi, mai albarka, don fadakarwa ga Van'uwa musulmi, gaba daya musamman masu

arzikin dukiya tararriya. Mun tsara wannan litafi ne don abinda kukayi ya gaba na barin wata

sadaka mai gudana bayan mutuwa kamar yanda Manzon Allah Ya kwadaitar. Saboda haka muna

fatan Allah Yasa wannan ya zama hanyar shiga Aljannah gare mu baki daya kuma ba zan gushe

ba in maimaita cewa Allah Ya yi kyakkyawar sakaiya ga Sani Zangon Daura, da ya nemi a

gabatar da wannan don taimako ga 'yan'uwansa musulmi, musamman, ma masu arziki don su san

hanyar da ya kamata subi da Dukiyarsu. Domin ita dukiyar Riko ce Allah ya basu, su zama

wakilin Sa wajen aiwatar da ayyukan Sa da ya yi umurnin ayi, na taimaka ma wasu bayinsa masu

rauni. Saboda haka da zaran mutum Allah ya bashi Dukiya kuma ya zama ya dora ta bisa hanyar

Allah Sai kaga ya zauna lafiya. Saboda haka toni shi Dan Masanin Daura da ya kafa irin wannan

cibiya don daukar nauyin gudanar da wasu ayyuka na taimakawa musulunci da musulmi, mai

suna :MARYAM EDUCATION TRUST FUND", wadda yanzu haka akwai wasu makarantu

dake karkashinta da kuma wasu yara ko jama'a da ake dauke da nauyinsu a karkashin asusun.

Saboda haka muna fatan Allah ya bamu ikon koyi da irin wadannan ayyuka naalhairi.

Don haka da zarar mutum ya mallaki wannan littafin ya samu mabudi ke nan akan aikin alhairi

game da dukiyar sa. Alhamdu lillahi.