133
FATAWOYIN DA SUKA SHAFI MATA MUSULMAI GUDA (150) NA DR. JAMILU YUSUF ZAREWA AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA FITOWA TA DAYA JULY, 2018 1

AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

  • Upload
    others

  • View
    40

  • Download
    1

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

FATAWOYIN DA SUKA SHAFI

MATA MUSULMAI GUDA (150)

NA

DR. JAMILU YUSUF ZAREWAAHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA

FITOWA TA DAYAJULY, 2018

1

Page 2: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

بسم الله الرحمن الرحيم

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da

amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad manzon tsira

da mutanen gidansa da sahabbansa.

Hakika ilimin fiqhun musulunci yana daga cikin ilimomi masu

muhimmanci wadanda mutane suke bukatarsu saboda

lamuransu na yau da kullum, wannan yasa malamai suka

himmatu wajen dawwana wannan ilimin da kuma karantar

das hi.

A cikin wannan takardu mun tattaro muhimman FATAWOYI

wadanda suka shafi ‘yan’uwa mata daga cikin amsoshin

tambayoyinmu da muka rubuta a kafafen sada zumunta

(social Media), muna rokon Allah ya sanya albarka a cikinsu

ya zamar da su ambato mai kyau gare mu bayan

rayuwarmu.

2

Page 3: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

1. SHIN MAI CIKI TANA IYA YIN HAILA ?

Tambaya: Malam mai ciki za ta iya ganin Haila ?

Amsa: Yawanci idan mace ta dau ciki jini yakan daina zuwa mata,

Imamu Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da

yankewar jini) Idan mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya

kasance kafin haihuwa da kwana biyu ko uku kuma a tare da

shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne, idan

kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa

da haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba

biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen

haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda

hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba? Anan

malamai sun yi sabani: Abin da yake daidai shi ne jinin haila

ne in dai ya zo a yadda ta saba yin jinin haila, saboda asali

duk jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai

ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba,

kuma babu wani dalili a alqur’ani ko a sunna da zai hana shi

ya zama haila. Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i,

kuma Baihaki ya hakaito hakan daga cikin maganganun

Ahmad.

Don haka yana tabbata ga mai ciki mai haila abin da yake

tabbata ga mai haila mara ciki sai a gurare guda biyu :

3

Page 4: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

1. SAKI- Ya haramta a saki matar da idda ta wajaba a gare ta

idan tana haila, amma mai ciki ya halatta a sake ta a cikin

haila, saboda sakin matar da bata da ciki ya sabawa fadin

Allah ( Kuma ku sake su a farkon iddarsu) Suratud Dalak aya

ta 1, wato a farkon tsarkin da bai take ta a cikinsa ba. amma

sakin mace mai ciki tana haila sakin ta ne ga iddarta,

wannan ya hada da tana cikin haila ko tana cikin tsarki,

saboda iddarta tana kasancewa ne da haife wannan ciki, don

haka bai haramta a sake ta ba, bayan an yi jima’i da ita.

2. Mace mai ciki idan ta yi haila ba za ta yi idda da ita ba,

saboda iddar ta tana kasancewa ne da haife cikinta, wannan

ya hada da tana haila ko bata yi, saboda fadin Allah

madaukaki ( Iddar mata masu ciki tana kasancewa ne idan

su ka haife cikinsu). Suratud Dalak aya ta 4 Don neman karin

bayani duba : Dima'uddabi'iyya shafi na 11.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA4/2/2012

2. HUKUNCIN SAKIN MAI HAILATambaya: Malam mun samu rikici da matata ko ya halatta na sake tana

haila?

Amsa:

Ya haramta a saki mace lokacin da take haila, saboda fadin

Allah "Ya kai Annabi idan za ku saki mata, to ku sake su a

farkon iddarsu) Suratu Addalak aya ta farko, wato a farkon

tsarkin da ba ku take su a cikinsa ba. Ana nufin a halin da za

su fuskanci idda sananniya, wannan kuwa ba ya faruwa sai

4

Page 5: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

idan ya sake ta tana da ciki ko tana cikin tsarkin da bai take

ta ba, domin idan ya sake ta a cikin haila to ba ta fuskanci

idda ba, saboda hailar da ya sake ta a ciki ba za’a kirga da

ita ba, haka kuma idan ya sake ta tana da tsarki bayan ya

sadu da ita, domin bai sani ba shin ta dauki ciki ta yadda

iddarta za ta zama irin ta mai ciki ko kuma ba ta dauka ba ta

yadda za ta yi idda da haila, saboda rashin tabbacin haka sai

sakin ya haramta. Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim cewa

: Ibn umar ya saki matarsa tana haila, sai Umar ya bawa

Annabi s.a.w. labari, sai Annabi s.a.w. ya yi fushi, sai ya ce

"ka umarce shi ya mayar da ita sannan ya rike ta har ta yi

tsarki sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so

ya rike ta ko kuma ya sake ta kafin ya sadu da ita, wannan

ita ce iddar da Allah ya umarta a saki mata a ita" ana togace

gurare guda hudu wadanda sakin mace mai haila yake

hallata :

A. idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya

sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila, saboda

anan bata da idda, sakinta ba zai zama ya sabawa fadin

Allah madaukaki (Ku sake su a farkon iddarsu) ba.

B. idan ta yi hailar ne tana da ciki

C. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, (KUL'I) to anan

babu laifi ya sake ta tana haila

D. Idan ya yiwa matarsa I'laa'i kuma aka yi watanni hudu bai

dawo ba.

Allah ne mafi sani.DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

21/2/2013

5

Page 6: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

3. MANUFOFIN DA SUKA SA AKA HARAMTA ZINA!

Tambaya:Assalamu alaikum malam Ina son karin bayani game da

manufofin sharia akan haramta zina.

Amsa:

Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya zo don ya kare

tsatson Dan'adam da mutuncinsa, don haka ya shar'anta

aure kuma ya haramta zina, ga wasu daga cikin hikimomin

da haramta zina ya kunsa :

1. Katange mutane daga keta alfarmar shari'a.

2. Samar da Dan'adam ta hanya mai kyau, ta yadda za'a

samu wanda zai kula da shi, saboda duk wanda aka same shi

ta hanyar zina, to ba za'a samu wanda zai kula da shi ba

yadda ya kamata.

3. Saboda kada nasabar mutane ta cakudu da juna.

4. Katange mace daga cutarwa, ita da danginta, saboda zina

tana keta alfarmar mace, ta zamar da ita ba ta da daraja.

5. Kare mutane daga cututtuka, kamar yadda hakan yake a

bayyane.

6. Toshe hanyar faruwar manyan laifuka, miji zai iya kashe

matarsa, idan ya ga tana zina, kamar yadda mace za ta iya

kashe kwartuwar mijinta, daga nan sai a samu daukar fansa,

sai fitintinu, su yawaita.

7. Zina tana kawo gaba da kiyayya a tsakanin mutane.

8. Kare mutuncin yaron da za'a Haifa, domin duk yaron da

6

Page 7: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

aka Haifa ta wannan hanyar zai rayu cikin kunci. Allah ne

mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA21/4/2013

4. SHIN YA HALATTA NA AURI WANDA BA

AHALUS-SUNNA BA ?

Tambaya:

Salam Malam ya halalta mace ta auri wanda ba dan Ahlul

sunnah ba? Don Allah ina son aba mu hujjoji saboda ta samu

abinda zata kare kan ta da shi.

Amsa:

To 'yar'uwa Annabi s.a.w. yana cewa : "Idan wanda kuka

yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura

masa" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba

ta : 1084, Malamai suna cewa wannan hadisin yana nuni

akan cewa duk wanda ba'a yarda da addininsa ba, ba za'a

aurar masa ba, wannan sai ya nuna cewa duk wanda

bidi'arsa take kaiwa zuwa kafirci, bai halatta a aura masa 'ya

ba, don haka duk dan shi'an da yake zagin sahabbai ko yake

kafirta su bai halatta a aura masa 'ya ba, saboda ba musulmi

ba ne, domin ya karyata Allan da ya yarda da su, haka sufin

da yake allantar da shehunansa, ko yake ganin sun fi

annabawa, kuma yana sane yake hakan, ba jahili ba ne ko

kuma wanda yake da shubuhar da za'a iya warware masa .

Amma duk mai aikata bidi`ar da ba za ta kai zuwa ga kafirci

ba, to ya hallata a aura masa 'ya, kamar wanda yake yin

maulidi saboda son Annabi s.a,w.

7

Page 8: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Allah ne mafi sani ,Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

1-12-2014

5. HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE SABODA KYANTA??

Tambaya: Malam: Akwai wani hadisi da yake Magana kan cewa kowa

ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jindadin

kyan, ko dan kudinta Allah zai hana masa jin dadin kudin,.

shin hadisin akwai shi kuma ya inganta?

Amsa: Ga yadda hadisin ya ke : DUK WANDA YA AURI MACE

SABODA KUDINTA, ALLAH ZAI KARA MASA TALAUCI, DUK

WANDA YA AURI MACE SABODA KYAWUNTA ALLAH ZAI KARA

MASA MUNI Saidai a cikin hadisin akwai Abdussalam bn

Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka

hadisin bai inganta ba, kuma ba za'a kafa hujja da shi ba.

Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA26/1/2014

6. YA YAGA TAKARDAR SAKIN KAFIN MATARSA TA GANI

Tambaya: Assalamu alaikum, malam shin idan mutum ya

rubuta takardar saki ya aje, sai wani ya gani shin matar ta

shi tasaku?

Amsa:Wa alaikum assalam To malam matukar ya rubuta da niyya

kuma yana cikin hayyacinsa ba takura masa aka yi ba, to ta

saku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi : "Allah ya yafewa al'umata abin da ta riya a

8

Page 9: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

zuciyarta, mutukar bata fada ba, ko ta aikata" ka ga kuma

rubutu aiki ne.Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi ya kasance yana zartar da abubuwa da yawa ta

hanyar rubutu, ka ga ya zama hujja kenan. Wannan shi ne

mazahar Abu-hanifa da Malik kuma shi ne zancen Shafi'i mafi

inganci. Duba Al-mugni : 7\486 Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA28/1/2014

7. SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCINSU

Tambaya:

Dan Allah Malam Ina bukatar bayani akan "KUDRA da kuma SUFRAH", Allah ya saka da Alkhairi.

Amsa:

To 'yar'uwa, wannan yana daga cikin mas'aloli masu

mutukar muhimanci, amma ga abin da ya sawwaka game da

hakan:

Sufra na nufin mace ta ga ruwa mai fatsi-fatsi kamar ruwan

ciwo, ya fito daga gabanta.

Kudra kuwa na nufin : ruwa ya ringa fitowa daga farjin

mace, wanda kalarsa ta ke kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da

baki wato kamar ruwa gurbatacce,

Dangane da hukuncinsu kuwa : idan daya daga cikinsu ya

kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana hade da haila

kafin ta sami tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan

kuma bayan tsarki ne to ba haila ba ne saboda fadin Ummu

adiyya mun kasance ba ma kirga sufra da kudra bayan tsarki

a cikin haila) Abudawud ya rawaito shi da sanadi mai

inganci,

9

Page 10: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

A hadisin A’isha kuma (Mata suna aiko mata da abin da suke

sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwan

da yake kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi

gaggawa har sai kun ga farin ruwa ya fito, ta yadda za mu yi

amfani da hadisin Ummu adiyya bayan an sami tsarki,

ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta kirga su a cikin haila

ba, hadisin A’isha kuma za mu yi amfani da shi idan tana

cikin haila ta yadda za ta kirga da su. Don neman karin

bayani duba: Dima'uddabi'iy a shafi na: 8

Allah ne mafi sani

6.12.2014Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

8. ADADIN SHAHIDAI DA INGANCIN SHAHADAR WACCE TA MUTU A NAKUDAR CIKIN SHEGE?

Tambaya:

Assalamu alaikum Allah ya gafarta Mallam don Allah ina

Matsayar Malamai akan wadannan Mas'aloli, tare da

ambaton dalilai daga Qur,ani/Hadithi: Mutane nawa ne Ya

tabbata a Alqur,ani/Hadithi Sunyi Mutuwar Shahada? Domin

wani Dalibi abokina ya ce: Albani ya Ambaci : 9 a cikin

AHKAMIL JANA'IZ na duba ban gani ba, sannan idan Mace ta

mutu ayayin haihuwar Cikin Shege, shin itama ta yi

Shahada?

Amsa :

To dan'uwa shahidai suna da yawa: sun haura guda tara :

Ibnu- hajar yana cewa : "Mun tattara hadisan da suka yi

bayani akan shahidai sai muka samu sama da nau'i ashirin

na shahidai, Fathul-bary 6/43 hakanan Suyudi a littafinsa mai

10

Page 11: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

suna : Abwabissa'adah fi asbabissa'adah, ya kawo sama da

guda talatin

Ka ga daga ciki, akwai wanda ya mutu a fagen daga, da

wanda ya mutu da ciwon ciki, sai wanda ya mutu a lokacin

kwalara sai kuma wanda ya mutu ta hanyar rusowar gini, sai

wanda ya nutse a ruwa, Hakanan wanda ya mutu wajan kare

dukiyarsa, da wanda kunama ko miciji ya harba, sai ya yi

ajalinsa, haka matar da ta mutu wajan haihuwa, dama

wanda namun daji suka cinye shi Haka wanda aka kashe shi

saboda kare iyalansa, duk wadannan sun tabbata a cikin

hadisai. Saidai wasu malaman suna ganin akwai sharuda

kafin mutum ya samu shahada:

Daga ciki kada ya zama: Ba ta hanyar gangaci ya mutu ba,

kamar mutumin da bai iya ruwa ba, ya shiga kogi, sai ya

mutu, sannan kar ya zama ta hanyar sabo ya isa zuwa

shahadar, kamar matar da ta mutu wajan nakudar cikin

shege, ko bawan da ya gujewa mai gidansa, sai ya mutu a

hanya.

wasu malaman suna ganinin hakan ba sharadi ba ne, tun da

hadisan ba su kayyade ba. Don neman Karin bayani duba:

Fataawal-kubra na Ibnu-taimiyya 3/22 da Mugni A l-muhtaj

3/166

Allah ne mafi sani9-12-2014

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

9. ANA YIWA IYALINA WANKAN JEGO, KO YA HALATTA?

Tambaya:

11

Page 12: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Salam malam don Allah ka taimaka min ka amsa tambaya

ta. ni dai malam gaskiya hankali na ya ki kwantawa

sakamakon al'adar wankan jego da ake yi a kasar hausa.

iyalina ta haihu an kawo wata tana yi mata wanka, to malam

ya hukuncin ya ke duba ga haramcin nuna tsaraici ga wani,

don Allah malam ka daure ka Amsa don hankalina ba'a

kwance yake ba.

Amsa:

To malam akwai hanyoyin na zamani wadanda za'a iya

amfani da su ba tare da an yi wankan jego ba, kamar amfani

da kwayoyi na asibiti, saidai idan ya zama babu makawa sai

an yi wankan na jego kuma wata ce za ta yi mata, kamar ya

zama haihuwar fari ce kuma babu halin da za'a iya sayen

kwayoyi saboda talauci, to hukuncin wannan zai yi daidai da

hukuncin likitan da take kula da lalurar mata, saboda shi ma

wankan jego ana yinsa ne saboda magani. A shari'ance ya

wajaba ga likita ya yi taka-tsantsan wajan kallon al'aurar

mara lafiya ta yadda ba zai kalli wani bangare na al'aurar

mara lafiya ba sai gwargwadon lalura, domin daga cikin

ka'idojin shari'a shi ne duk abin da ya halatta saboda lalura,

to ya wajaba a tsaya gwargwadon lalurar, wannan ya sa idan

da zai kalli sama da haka, sai ya zama mai laifi a wajan Allah.

Al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace tana farawa ne daga

cibiya zuwa guiwa a zance mafi inganci, don haka mai

wankan jego za ta kalli gwargwadon abin da ya wajaba ta

kalla don tabbatar da lafiyar mai jego, idan kuma akwai

12

Page 13: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

hanyar da za ta bi ta yi mata wankan ba tare da kallon

al'aurar ta ba, to wannan shi ne ya wajaba.

Duba kwatankwacin wannan mas'alar a Alkawa'idul kulliya naUsman Shabirr shafi na : 222

Allah ne mafi sani14-12-2014

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

10. TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWATambaya :

Assalamu alaikum, Mal Na kasance ina tsotsan azzakarin

mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin

mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.

Amsa :

To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saidai

ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin

mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin

haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da

wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar

cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda

neman kariya Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara

aya ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan

sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da

su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.

Domin karin bayani duba: Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul

Khalil 3/406.

Allah ne mafi sani.21-12-2014

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

13

Page 14: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

11. ABUBUWAN DA AKE SO MIJI YA FI MATARSA DA SU

Tambaya: Assalamu alaikum, malam da fatan kana lafiya,

wasu tambayoyi nake rokon Malam daya taimakamin da

amsoshinsu in Allah yasa malam yasansu, shin malam wai

akwai wasu abubuwa uku da ake so mace tafi mijin da za ta

aura da su,sannan shima akwai abu guda uku da akeso ya

fita da su?, sannan akwai wadanda sukayi musharaka

akansu, da fatan malam ya sansu, kuma za'a taimakamin da

su, nagode.

Amsa :

To dan'unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa,

ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku : ta fi shi a kyau, ta

fi shi kananan shekaru, ta fi son shi, sama da yadda yake

sonta . Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta

kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta Ana so su hadu a abubuwa

uku : ya zama akwai yaran da yake hada su, ya zama

addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya. Idan

aka samu wadannan uku-ukun, to za'a samu jin dadin aure.

don neman karin bayani ka nemi shirin minbarin malamai

da na yi a freedom radio Kano na ranar : 3 ga Ramadhan

1434 A.H

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

12. SHIN ZAN IYA YIN DILLANCIN HOTUNAN 'YAN MATA?

TAMBAYA:

14

Page 15: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Malam menene hukuncin 'yan matan da suke bada

hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure?

AMSA:

Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba

muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli

mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin

hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa: "Idan dayanku yana

neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi

zuwa aurenta,to ya aikata hakan" ABU DAWUD Malamai sun

yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin

mace lokacin da ya je neman aure

1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne

kawai.

2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da

take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta

juya baya ya kalleta.

Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum

zai san yanayin matar da zai aura.

Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya fahimtar cewa

aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga

ciki :

1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai

KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a

rude shi.

2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda

ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali

ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai

15

Page 16: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

in akwai lalura, sai ga wanda yake nufin aurarta, wannnan

yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman

aure ba , a face book, ko a jarida.

3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a

iya inda shari'a ta bada umarni.

4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yii dalilin aure, saboda in

namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna

ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a

cikin aikinta.

Allah shi ne ma fi sani.25-12-2014

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

13. INA CIKIN IDDA, SAI WANI YA YI ZINA DA

NI

Tambaya :

Malam mijina ya sake ni, bayan na yi tsarki daya, sai rikici ya

kaure tsakanin arna da musulmai a garinmu, sai wani christa,

ya dauke ni ya yi zina da ni, yanzu malam yaya zan yi game

da idda ta?

Amsa :

To 'yar'uwa ina rokon Allah ya kawowa musulmi dauki a

Nigeria, wannan mas'alar ta ki malamai sun yi sabani

akanta, akwai malaman da suka tafi akan dole sai kin yi

istibra'i bayan kin gama idda, saidai maganar da tafi zama

daidai ita ce : kawai za ki karasa iddarki ne, ba sai kin yi

istibra'i ba bayan kin kammala, saboda babbar manufar

istibra'i ita ce kubutar mahaifa, hakan kuma zai tabbata idan16

Page 17: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

kika karasa jinane biyun da suka rage miki na iddarki. Yana

daga cikin saukin addinin musulunci kasancewar duk

ibadojin da za su iya shiga cikin juna kuma manufarsu daya

ce, jinsinsu guda ne, to daya za ta shiga cikin daya, kamar

wacce ta yi jima'i sai kuma haila ta zo mata, wanka guda

daya ya ishe ta a karshen hailarta.

Domin neman karin bayani duba: Majmu'ul fawa'id na Sa'ady

shafi na: 141.

Allah ne mafi sani.

25-12-2014

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

14. INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINAYA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME?

Tambaya :

Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda, saura

kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome,

amma bai sanar da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki,

ko kuma na kyale shi na yi aurena? saboda gaskiya ina son

wancan, amma kuma ba na so na sabawa sharia ?

Amsa :

To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa

kome mutukar tana cikin idda, kamar yadda aya ta :228, a

suratul bakara take nuni zuwa hakan, Amma mutukar bai yi

mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan

ta, amma zai iya shiga cikin manema. Idan ya yi da'awar

cewa ya yi mata kome tun tana idda, amma bai sanar mata

17

Page 18: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za'a gaskata shi ba,

sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar

hakan. Yana daga cikin ka'idojin sharia toshe duk hanyar da

za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake

kin matarsa, zai iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan

yasa malamai suka ce sai ya kawo shaidu za'a gaskata shi,

idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auranta . Saidai

wasu malaman suna cewa : idan har matar ta gaskata shi, to

ya isa, ko da bai kawo shaidu ba . Duba: Al-mabsud 2\23 da

Mawahibul-jalil 5/408

Allah ne mafi sani.Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

25-12-2014

15. IDDAR MATAR DA AKA SAKA SHIKA NA

UKU

Tambaya :

Sheik shin dole ga matar da mijinta ya yi mata shika uku sai

ta yi jini uku, ko idan ta yi jini daya ya yi, tun da babu kome?

Amsa :

To dan'uwa Mazhabar dukkan manyan malaman fiqhu shi ne

za ta yi jini uku ne, ko tsarki uku, saboda fadin Allah a cikin

suratul Bakara aya ta : 228 "Kuma matan aka saka, to za su

jira tsawon jinane uku", wannan ayar ba ta bambance

tsakanin matar aka saka shika daya ba, da wacce aka saka

saki uku, don haka sai hukuncin ya zama daya, Jassas yana

cewa babu sabani a cikin hakan.

18

Page 19: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Saidai Ibnu Taimiyya ya hakaito wani kauli wanda yake cewa:

za ta yi jini daya ne tun da babu kome, saboda an shar'anta

yin jini uku ne don tsawaitawa miji lokacin yin kome, tun da

kubutar mahaifa tana tabbata da yin jini daya. Wannan kaulin

ya sabawa zahirin ayar da ta gabata, sannan kasancewar

iddar matar da mijinta ya mutu wata hudu da kwana goma,

yana nuna cewa, ba saboda tsawaita lokacin kome kawai aka

shar'anta idda ba, tun da ita babu wanda zai mata kome.

Don neman karin bayani duba: Ahkamul-qur'an na Jassas

2/67, da kuma Ahkamul-qur'an na Ibunl-araby 1/185 da

Majmu'ul fatawaa 32\342.

29-12-2014Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

16. HUKUNCIN AIKIN JARIDA GA MATAR AURETambaya:

Salam. Ina yiwa malam fatan alkhairi, Don Allah malam wata

Tambaya na zo da ita !, Ina hukuncin aikin jarida ga matar

aure ??

Amsa:

To dan'uwa Allah madaukakin sarki ya umarci matar aure da

ta zauna a gidanta, kada ta fita sai in tana da wata bukata

mai muhimmanci, kamar yadda aya ta : 33 a suratul Ahzab

take nuni zuwa hakan.

Aikin jarida aiki ne da yake bukatar cakuduwa tsakanin maza

da mata, saboda mai aikin jarida za ta iya zama mai dauko

rahoto, wanda dauko rahoto yana lazimta haduwa da maza,

kamar yadda za ta iya haduwa da wanda ba muharraminta

19

Page 20: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ba, wajan hada wani shiri da za ta gabatar, wanda hakan zai

iya kaiwa zuwa barna, domin duk lokacin da mace take

kadaita da namiji to Shaidan zai iya shiga tsakaninsu.

Lalura tana iya halatta abin da yake haramun, saidai anan

wurin babu lalurar saboda za ta iya samun wani aikin na

daban wanda za ta tallafawa rayurwarta da shi, sannan maza

za su iya gamsarwa wajan aikin jarida, ta yadda zai zama, ko

da mata ba su shiga ba, aikin zai ta fi daidai. Aikin Jarida a

gidan talabishin hanya ce da wani zai iya ganin matar aure ya

yi sha'awarta, saboda duk wacce take gabatar da shirye-

shirye dole ta yi kwalliya, wanda hakan zai iya kaiwa zuwa

barna, ka ga sai ya zama haramun.

Malamai suna cewa : Duk lokacin da aka samu aikin jarida

mai tsafta wanda bai sabawa ka'idojin sharia ba, to ya hallata

mace ta yi, saboda duk hukuncin da aka haramta shi saboda

wata illa, yana zama halal idan ta gushe, saidai da kamar

wuya a samu hakan a irin kasashen da ba'a aiki da shari'ar

musulunci, wannan yasa barin aikin ga mace shi ne daidai,

musamman na talabishin wanda ya kunshi barna mafi gima,

kamar yadda bayani ya gabata. Allah ne mafi sani Don

neman Karin bayani duba : Al-mar'atu Almuslima Almu'asirah

na Ahmad Ba-badin shafi na : 429.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa4/2/2015

20

Page 21: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

17. TSAKANIN KAFIRI DA MACE MUSULMA, WA ZAN

ZABA?

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Na karanta post din da kayi akan

Shugabancin Mata, inda ka nuna bai halatta mace ta yi

shugabanci ba in ba na gidanta ba, Ina so ka dan yi mana

Karin bayani idan aka samu takarar shugabanci tsakanin

Kafiri da kuma Mace Musulma, wanne ya kamata mutane su

zaba a matsayin Shugaba?

Amsa :

To dan'uwa amsa wannan tambayar yana da wahala,

saboda ban ga littafin da ya tattauna mas'alar ba, amma dai

na nemi taimakon Amsa tambayar wajan babban

malaminmu Prof. Muhd Sa'ad Al-yuby, don haka ga bin da zan

iya cewa: Farko dai zaben kafiri haramun ne, saboda fadin

Allah madaukakin sarki "Kuma Allah bai sanya wata hanya ba

ga kafirai akan muminai" Nisa'i aya ta : 141, hakan sai ya

nuna bai halatta musulmai su sanya kafiri ya mulke su ba,

Kamar yadda zaben mace a matsayin shugaba shi ma

haramun ne saboda hadisin Abu-bakrah inda Annabi s.a.w.

yake cewa ; "Duk mutanen da suka sanya mace ta zama

shugabarsu, to ba za su rabauta ba" kamar yadda Bukhari ya

rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 4425, Ibnul-kayyim yana

cewa: kore rabauta dalili ne da yake nuna haramcin abu.

Bada'i'ul-fawa'id 4/812.

Saidai kamar yadda malaman shari'a suke cewa: duk lokacin

da abubuwa biyu haramtattu suka hadu, ya zama dole sai an

21

Page 22: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

aikata daya daga ciki, to sai a dauki wanda ya fi saukin

haramci a aikata. Idan muka kalli manufar shugabanci a

musulunci, za mu ga ta kunshi: jagorancin mutane da kuma

tsayar da addini, wannan manufar za ta fi tabbatuwa idan

aka zabi mace musulma, fiye da kafiri Crister. Don haka

mutukar matar tana da kokari wajan addini, to ita ya fi

kamata a zaba, ba don kasancewar ya halatta a zabe ta ba,

sai don kawai hakan ya fi saukin haramci, kuma babu yadda

za'a yi a zauna babu shugaba.

Allah ne mafi sani.Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

March 2015

18. WAI ME YASA MUSULUNCI YA HANA MUSULMAAURAN CRISTA, AMMA YA HALATTAWA MUSULMIAURAN CRISTA ?

Tambaya:

Malam wasu Arna ne suka mana tambaya a makaranta

cewa: Yaya aka yi addinin musulunci ya halattawa namiji

musulmi auran crister mace, amma ya hana a baiwa crister

namiji auran musulma, malam mun rasa Amsar da za mu ba

su, shi ne muke so ka taimaka mana, don kar su samu hanyar

da za su aibanta addininmu.

Amsa : To yar'uwa sheik Addiyya mohd Salim ya yi kokari

wajan warware wannan mushkilar a karashen tafsirin

Adhwa'ul-bayan da ya yi, inda ambaci dalilai guda biyu,

wadanda suka hukunta hakan:

1. Kasancewar musulunci shi ne yake yin sama, amma ba'a

yin sama da shi, idan crister ya auri musulma, zai zama yana

22

Page 23: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

sama da ita, tun da namiji shi ne yake bawa mace umarni,

idan ya aure ta, sabanin idan namiji musulmi ne ya auri mace

crister, tun da shi zai zama a samanta .

2. Musulmi ya yi imani da Annabi Isa da kuma Injila, wannan

zai sa idan ya auri cristar zai girmamata, Shi kuwa crista bai

yi imani da Annabi Muhammad s.a.w. ba, don haka zai iya

wulakanta musulma idan ya aure ta, tun da bai san darajar

addinita ba, wanda hakan zai kai suka sa fahimtar juna,

zaman auran ya ta'azzara. Duba Adhwa'ul-bayan 8/164

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

13/2/2015

19. JINI YANA ZUWA MIN A YAYYANKETambaya :

Assalamu Alaikum Malam matata ta haihu sati biyu kenan, to

Malam yanzu takan wuni Jini bai zoba sai da Daddare in ta

kwanta sai Jinin yazo. To shin Malam za ta iya yin

wanka/tsarki da safe tayi sallolin Azahar zuwa Isha'i? Kokuma

yaya zatayi? Nagode Allah Yaqara illimi mai albarka.

Amsa: To dan'uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to

yana daukar hukuncin jinin biki ne , haka ma tsarki yana

daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk

yinin da ba ta ga jini ba, Saidai idan yana yayyankewa kusa-

kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta

ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci

akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: "Bai sanya muku

23

Page 24: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

kunci a cikin addini ba" Suratu Hajj 78. Don neman Karin

bayani duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1/214.

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

22/2/201520. JINI YA ZO MIN, BAYAN CIKINA YA KAI WATA

BIYUTambaya:

Assalamu alaikum, malam ya kokari malam tambayace

gareni, na yi wata biyu ban ga al'ada ba, sai yanzu ta rinka

zuwa tana daukewa, na zo asibiti sun ce juna biyu ne, to

inyazo min da safe shikenan sai ya dauke sai kuma gobe da

safe, sai in ya dauke inyi wanka in cigaba da sallah, malam to

ko ya halatta hakan?

Amsa:

To yar'uwa wannan jinin da kika gani mutukar yana kama da

jinin hailar da kaki saba gani, to zai hana sallah, kuma zai

dauki dukkan hukunce-hukuncen jinin haila, saboda asali duk

jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai ba

akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma

babu wani dalili a alqur’ani ko a sunna da zai hana shi ya

zama haila.

A zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila, don haka duk

yinin da ki ga jini to yana daukar hukuncin jinin haila ne ,

haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta

yadda za ki yi wanka duk yinin da ba ki ga jini ba, Saidai idan

yana yayyankewa kusa-kusa, to kina iya jinkirta wankan, sai

ki hada sallolin da ba ki ga jini ba a lokutansu, saboda yin

wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah24

Page 25: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

yana cewa : "Bai sanya muku kunci a cikin addini ba" Suratu

Hajj 78. Don neman Karin bayani duba Almugni na Ibnu

Khudaamah 1\214 da Dima'uddabi'iyya shafi na 11

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa26/2/2015

21. MAHAIFIYATA TANA ZUWA WAJAN BOKA, INA NEMAN SHAWARA

Tambaya: Assalamu alaikum don Allah malam a fitar dani

cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta

je gurin malami ai mata naganin ciwon mara dz yake

damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun

yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri

aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife

abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu

bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar

kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata

bata aminta da malaman bane, shi yasa na keso ka bani

fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a

addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zanbi wajen kin

biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda inada matsala, ta

bangaren aqida mun banbanta? Wassalam nagode Allah ya

qara basira.

Amsa :

To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai

ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu

malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta

hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da

25

Page 26: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai

kuma aya ta : 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da

aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a

ruwan da aka zuba magarya guda bakwai. Amma bai halatta

ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya

nema ba, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon

Allah. Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita

cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

yana cewa :" "Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi

wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in"

kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2230.

Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai

matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta

yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa : "Duk wanda ya

je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya

kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi" kamar

yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904,

kuma Albani ya inganta shi .

INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANARDA ITA, TA DAWO KAN HANYA.

Allah ne mafi sani .Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

8/3/2015

22. MIJINA BA YA SALLAH, KO ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI?

Tambaya:

Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira,

malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da

26

Page 27: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin

Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da

ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana

saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun

ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki

tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi?

na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka.

Amsa :

To 'yar'uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki

iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a

zance mafi inganci, kamar yadda Annabi s.a.w. ya fada a

hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta: 81. Ga shi kuma

aya: 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin

musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala

a addinance. Allah ya hana saduwa da mace mai haila a

suratul Bakara ayata: 222, Saduwa da mace da rana a

Ramadana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari

mai lamba ta: 616 ya tabbatar da hakan. Saidai zunubin barin

sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba,

za ki iya kai shi kotu, alkali ya rabaku. Don neman Karin

bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa6/3/2015

23. ZAN AURI KANWAR MATAR MAHAIFINA, KOYA HALATTA?

Tambaya:

27

Page 28: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Malam ya halata mahaifina ya aure mace, ni kuma na auri

kanwarta.

Amsa:

To dan'uwa ya halatta ka aureta, saboda ba ta cikin mataye

guda goma sha biyar wadanda Allah ya haramta a aure su a

cikin suratun-nisa'ai, ga shi kuma babu wani hadisin da ya

haramta a aure ta, Allah yana cewa a cikin suratunnisa'i aya

ta: 24, bayan ya ambaci matan da aka haramta a aura, "Duk

matan da ba wadannan ba, to an halatta muku ku aure su.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa10/3/2015

24. BUDURWATA BA TA HAILA, FALALACE KO MATSALA CE?

Tambaya: Assalamu alaikum dan Allah malam a taimaka min, matar da

zan aura a yanzu haka auren bai fi wata biyu ba, shekararta

20 amma ba ta taba jinin haila ba. To malam wannan

matsalace ko kuma falalace ? sannan kuma za ta iya

haihuwa? MALAM A TAIMAKAMIN DON ALLAH (S.W.T).

Amsa:

To dan'uwa tabbas haila tana daga cikin alamomin da suke

nuna cewa mace za ta iya daukar ciki, kamar yadda wasu

malaman tafsirin suka fada, wannan ya sa lokacin da za'a

yiwa matar annabi Ibrahim bushara da haihuwa, sai da ta yi

haila, saboda kasancewarta tsohuwa, haila kuma alama ce ta

haihuwa, don haka duk matar da ba ta yin haila da wuya ta

haihu.

28

Page 29: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Akan iya samun wasu matan 'yan kadan wadanda suke iya

haihuwa ko da ba su taba yin haila ba, saboda Allah mai iko

ne akan komai. Abin da nake ba ka shawara shi ne ku je

wajan likitoci, don su gwada ta, in har suka tabbatar ba za ta

iya haihuwa ba, kana iya hakura da auranta, saboda haihuwa

ginshiki ne, daga cikin ginshikan da suke sa ayi aure. Rashin

yin haila ba falala ba ce, saboda hadisi ya tabbatar da cewa :

"Haila jini ne da Allah ya hukuntawa dukkan 'ya'yan nana

Hauwa'u da jikokinta" kamar yadda Bukhari ya rawaito a

hadisi mai lamba : 290. Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa11/3/2015

25. MACE ZA TA IYA YIN LIMANCI?

Tambaya :

Malam a kaset din malam Jafar na ji ya halatta mace tai wa

mata yan'uwanta limanci toh in ramadan ya zo na kan tara

mata na musu, dayake duk anguwan na dan fi su karatu, toh

kusan anguwan ba malamin sunna ko daya sai 'yan bidi'a, shi

ne suke nema na ba su aya ko hadisi akan hakan malam,

ataimakamin don Allah?

Amsa :

To 'yar'uwa ina rokon Allah ya jikan malam Ja'afar, mu kuma

ya kyautata namu karshen, ya halatta mace ta yiwa

'yan'uwanta mata limanci, saboda abin da aka rawaito cewa :

Nana A'sha da Ummu Salama –Allah ya kara musu yarda- sun

yiwa wasu mata limanci, Nawawy yana cewa wannan hadisin

29

Page 30: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Baihaky ya rawaito shi a Sunan din shi, hakan nan Shafi'i a

Musnad dinsa da sanadi mai kyau, Almajmu'u (4/187).

Haka nan an rawaito cewa Annabi s.a.w. ya sanyawa Ummu-

waraka ladani, sannan ya umarce ta da ta yiwa matan

gidansu limanci, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi

mai lamba ta : 491, kuma Albani ya kyautata shi.

Bisa dalilan da suka gabata za ki iya yiwa matan unguwarku

limanci, tun da kin fi su karatu, Annabi s.aw. yana cewa:

"Wanda ya fi iya karatun alqur'ani shi ne zai yi limanci"

Muslim 1078. Idan za ki yi musu limanci za ki tsaya ne a

tsakiyarsu in suna da yawa, in kuma ita kadaice sai ta tsaya a

damarki.

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

13\3\201526. NA SADU DA IYALINA, INA AZUMIN NAFILA!

Tambaya :

Salam malam ina hukuncin wadda yana azumin nafila, sai

sha'awa ta zo mai sai ya karya kuma ya sadu da matarsa?

Amsa:

To dan'uwa malamai sun yi sabani game da wanda ya sadu

da matarsa, alhalin yana azumin nafila, akwai wadanda suka

ce sai ya sake, saboda ya bata aikinsa wanda ya faro, kuma

Allah yana cewa: "Kada ku bata ayyukanku" Muhammad aya

ta: 33.

Akwai malaman suka tafi akan cewa ba zai sake azumin ba,

kuma ba shi da laifi. Wannan maganar ta karshe, ita ce

daidai, saboda Annabi s.a.w. yana cewa: "Mai azumin nafila

30

Page 31: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

sarkin kansa ne, in ya ga dama ya cigaba da azumi, in ya ga

dama kuma ya karya" Albani ya inganta shi a sahihul-jami'i

hadisi mai lamba ta: 3854. Wannan hadisin sai ya nuna ba shi

da laifi idan ya karya, karya azumi yana tabbata da cin abinci

ko abin sha, ko jima'i, Don neman Karin bayani duba Tuhfatul-

ahwazy 3/356.

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

16/3/2015

27. INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN

BUDURWATA ?

Tambaya:

Malam ko ya halatta in kalli gashin macen da nike so in aura?

Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaman bayanin abunda

ya halatta in kalla a jikin macen da zan aura kafin muyi aure.

Na gode. Allah ya gafarta maka.

Amsa :

To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kake so ka aura,

kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake

cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar

kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan"

Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082. Malamai sun yi

sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace

lokacin da ya je neman aure :

1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne

kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni'imar jikin mace,

31

Page 32: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

kamar yadda fuska take nuna kyau, don haka sai a takaita

akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai. 2. 2. Zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka

bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya. 3. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da

take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta

juya baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa,

saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura,

yadda ya kamata. Saidai ba'a son yawaita kallon saboda

duk abin da aka halatta saboda bukata, to ya wajaba a

tsaya a gwargwadonta, wannan yasa yawaita zuwa zance

da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana

iya tayar da sha'awa, sha'awa tana iya kaiwa zuwa barna.Don neman Karin bayani, duba: Al'insaf 8/15 da Muhallah9/161.

Allah ne mafi saniJamilu Zarewa

21/3/2015

28. MATATA TANA NAKUDA, GA SHI KUMA AN TADASALLAR JAM'I

Tambaya:

Wani ne a office ana kiran shi a waya, matarshi na

matsanancin hali na naquda, ana buqatarsa, ikon Allah kuma

gashi an tada iqama za'a yi sallah sai wasu suka ce ya tafi

wurin mara lfy. Wasu kuma suka ce ya tsaya ya gama sallar,

me ya kamata ya yi ?

Amsa :

To dan'uwa abin da yake daidai anan Shi ne : ya tafi wajan

matarsa, saboda idan hakkin Allah da na bayi suka ci karo,

32

Page 33: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

akan gabatar da na bayi, saboda shi Allah mawadaci ne.

Sannan za ta iya hallaka idan ka bar ta ba ka je ba, sallar

jam'i kuma akwai sabani akan wajabjinta, ga shi kuma za ka

iya gamawa ka dawo kafin lokacinta ya fita, yana daga cikin

ka'idojin sharia, duk abin da ake bukatarsa yanzu-yanzu akan

gabatar da shi akan wanda za'a iya jinkirtawa, ko da bai kai

shi daraja ba.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa22/3/2015

29. ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN HARAM?

Tambaya:

Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani

ma'aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu'amalarsa

za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene

halarcin auransa a shari'a? Saboda tana tsoron kar ya rika

ciyar da ita da dukiyar haramun.

Amsa :

To dan'uwa Annabi s.a.w. yana cewa: "Allah ya la'anci mai cin

riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka"

Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598. Hadisin da

ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke

mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko

kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin

banki, kamar mai gadi, da dan aike. . Duba fatawaa Allajanah

33

Page 34: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

adda'imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin

2/401.

Idan ya zama abin da ma'aikacin banki yake amsa haramun

ne, kuma ba shi da wata sana'a sai wannan, akwai hadari a

auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun Malamai

suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin

halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa, saboda

Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa, kuma a

dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata

sana'a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa ba.

Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin

ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa10\4\2015

30. SHIN ABAYA TANA DAUKAR HUKUNCIN HIJAB?

Tambaya:

Assalamu alaikum, Malam don Allah tambaya nake da ita

kamar haka: Abaya da mata suke sanyawa tana iya daukan

hukuncin Hijabi ne, domin zaka ga ko harami za ka gan su da

irin wannan shigar, kuma nayi kokarin leka wasu littafai masu

alaka da hijab ban iya kaiwa ga magana akan hakan ba.

Malam ko akwai maganganun malamai akai? Allah ya saka

maka da alkhairi.

Amsa:

To dan'uwa, abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne : ta

sanya tufan da zai suturce jikinta, in ban da fuska da tafin

34

Page 35: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

hannu a wajan wasu malaman, wasu malaman kuma suna

ganin fuska al'aura ce, don haka ita ma ya wajaba a rufe ta,

tun da a nan kyawun mace yake, kayan da za ta sa su zama

masu kauri, ba ya halatta ta yi ado in ba a cikin gidan mijita

ba, ko tare da muharramanta. Suturar mace musulma ba'a so

ta yi kama da kayan maza, kamar yadda ba'a so su zama

kayan da za su ja hankali, ko wadanda aka fesa musu turare ,

Mutukar Abaya ko jallabiyya ta suturce jiki yadda ya kamata,

ba ta matse shi ba, za ta dauki matsayin hijabin da Allah da

manzonsa, suka yi umarni.

Don neman Karin bayani duba : Majmu'ul-fataawa 22/110 da

Hijabul- mar'atulmuslima shafi na : 54 zuwa 67.

Allah ne mafi sani .

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa15/4/2015

31. LAULAYIN CIKI YASA INA WAIWAYE A SALLAH,YAYA SALLATA?

Tambaya :

Assalamu alaikum malam Dan Allah macece take fama da

yawan zuban yawu a bakinta na laulayin ciki, Wanda yakai

kafun nayi raka'a daya ya cikamun baki sai na dan juya in

zuba akan tsumma, sallan yayi ko bani da halin juyawa kadan

?

Amsa :

To 'Yar'uwa Annabi s.a.w. yana cewa : "Waiwaye a sallah wani

faucewa ne da Shaidan yake fauta daga sallar bawa" kamar

yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lambata : 718.

35

Page 36: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Malamai suna cewa waiwaye a sallah makaruhi ne saboda

hadisin da ya gabata. Waiwaye yana halatta idan akwai

bukata, saboda akwai lokacin da sayyidina Abubakar ya fara

limanci, saboda Annabi s.a.w. baya nan, bayan Annabi s.a.w.

ya dawo sai ya shigo masallaci, sahabbai suna ganinsa sai

suka fara tafi, sai sayyadina Abubakar ya waiga lokacin da ya

ji tafi ya yi yawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi

mai lamba ta : 2544.

Malamai suna cewa : waiwayan da Abubakar ya yi yana nuna

hallacin yin waiwaye saboda bukata, tun da Annabi s.a.w. bai

masa inkari ba. Don neman karin bayani duba : Fataawaa

nurun Aladdarb 9/225.

A bisa abin da ya gabata, ya hallata ki dinga yin waiwaye

saboda zubar da yawun da ya zama lalura, saidai duk abin da

aka halatta saboda bukata, ba'a so a wuce gwargwadonta .

Allah ne mafi sani .Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

19/4/2015

32. ZAN IYA KARA GASHI, SABODA MIJINA?Tambaya :

Malam na yi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina yana

bakin ciki, in ya ga kaina, zan iya kara gashi, don zaman

auranmu ya kara dadi?

Amsa:

To 'yar'uwa wata mace ta je wajan Annabi s.a.w. ta ba shi

labari cewa: 'Yarta ta yi rashin lafiya gashinta ya fadi, kuma

gashi mijinta ya umarceta da ta kara mata gashi, shin za ta

36

Page 37: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

iya karawa? sai Annabi s.aw. ya ce mata : A'a, saboda an

la'anci masu kara gashi" Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai

lamba ta: 4831 .

Hadisin da ya gabata, yana nuna cewa : bai halatta mace ta

kara gashi ba, ko da kuwa mijinta ne ya umarceta, saboda

hakan zai sa ta shiga tsinuwar Allah .

Allah ne mafi sani .

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa22/4/2015

33. INA SON DALILI AKAN WAJABCIN SANYA SAFAR KAFA GA MACE ?

Tambaya :

Assalamu alaikum, malam ina son in san wajibcin sanya

safar kafa (socks) ga mace. Nagode

Amsa :To 'yar'uwa da yawa daga cikin malamai suna

wajabtawa mace rufe duga-duganta, suna ganin yana daga

cikin al'aura. Saidai Abu-hanifa yana ganin ba shi daga cikin

al'aura, hukuncinsu daya da fuska da tafin hannu, ya dogara

da fassarar da wasu sahabbai suka yiwa aya ta : 31 a

suratunnur, inda Allah yake cewa: "Kuma kada su bayyana

adonso sai abin da ya bayyana", inda suka fassara abin da ya

bayyana da fuska da duga-dugai, da tafin hannu.

Ummu Salma ta kasance tana tsawaita suturarta, ta yadda

take jan kasa, kamar yadda Malik ya rawaito a Muwadda'i a

hadisi mai lamba ta: 4547. Don haka har a wajan wadanda

suke ganin wajabcin rufe duga-dugai, to za ki iya rufewa da

doguwar rigarki, ba dole sai kin sanya safa ba. Don neman

37

Page 38: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Karin bayani duba : Al-mabsud 10\153 da Majmu'ul fataawa

22/114 .

Allah ne ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

27\4\2015

34. NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME?

Tambaya :

Assalamu alaikum don Allah malam ka warware mana

wannan matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya

sake matarsa shika Daya 1, ya koma da ita bayan wasu

shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya sake

biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa

shika daya 1, kuma suna son junansu akwai aure a

tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan bayan da ya

mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika

nawa ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai

naji daga gareka

Amsa :

To dan'uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to

babu damar kome, sai in ta auri wani mijin na daban, saboda

igiyoyin da suke tsakaninku sun yanke gaba dayansu . Auren

da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a baya ba, da ace ta

auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka sake auranta,

da ba'a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin

38

Page 39: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

maganganun malamai, amma tun da ba ta auri wani ba, ya

wajaba ku hakurewa juna.

Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu-Khudaamah

7/388 .

Allah ne mafi sani.Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

3/5/2015

35. YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?

Tambaya :

Malam mutum ne yana cikin halin rashin lafiya, ya saki

matansa har guda biyu saki daya, kuma bai dawo da su ba

har ya mutu, kuma ba su gama iddah ba, yaya za'a yi ? za su

yi masa takaba, kuma suna da gadonsa, ko ko a'a ?

Amsa :

To dan'uwa mutukar yadda ka sifanta, haka abin yake, to za

su bar iddar saki, su koma iddar mutuwa, kuma za su ci

gadonsa, saboda suna nan a matansa, tun da saki daya ne,

Ibnu-khudamah ya hakaito ijma'in malamai akan haka. Don

neman Karin bayani duba : Al-mugni 8/94.

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

9/5/2015

36. MATA ZA SU IYA YIN SALLAR JANA'IZA?Tambaya:

Salam, malam ya halatta mata su bi sallar jana'iza ? saboda

na ga wani malami lokacin da aka kashe masa ‘yaya har

mata ya tara aka yi musu sallar jana'ixa Ngd malam39

Page 40: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Amsa:

To dan'uwa ya halatta mata su yi sallar jana'iza, saboda

dalilan da suka zo akan sallar jana'iza ba su banbance

tsakanin mace da namiji ba.

Duk nassin da ya zo daga Al'qur'ani ko sunna, to yana hade

maza da mata wajan hukunci, in ba'a samu wani dalili ko

alama wacce ta fitar da su daga ciki ba . Sannan mata

sahabbai sun yiwa Annabi s.a.w. sallah bayan ya mutu, babu

kuma wanda ya yi inkarin hakan, sai wannan ya nuna shi ne

shari'a.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa11/5/2015

37. INA SON DALILI AKAN KACIYAR MATA ?Tambaya : Assalamu alaikum, don Allah malam a taimaka min da amsar

wannan Tambayar, ko Qur'ani da hadisi sun yi Magana akan

halarcin kaciyar mata, ko kuma wani daga cikin magabata na

kwarai ya yi Magana akan haka ?

Amsa :

To 'yar'uwa akwai hadisai da suka zo akan cewa : mustahabbi

ne, yin kaciyar mata, saidai an yi sabani akan ingancinsu,

wasu malaman sun raunana su, wasu kuma sun inganta su.

Baihaki a Sunanu Assugrah a hadisi mai lamba ta : 3712, ya

rawaito mustabbacin yin kaciyar mata daga Ibnu Abbas da

sanadi mai kyau.

Hadisin da Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a lamba ta :

108, daga Nana A'isha tana cewa : "Idan kaciya ta hadu da

40

Page 41: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

kaciya, to wanka ya wajaba" na nuna cewa : al'ada ne yiwa

mata kaciya a zamanin Annabi s.a.w.

Ibnu- Abi-zaid Al-kairawany ya ambata a Risala shafi na : 410,

cewa : yin kaciyar mata mustahabbi ne. Don neman Karin

bayani duba Al-mugni 1\101.

Allah ne mafi sani .

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa12/5/2015

38. 'YAMMATAN DAJIN SAMBINSA, ZA'A IYA ZUBARDA CIKIN DA SUKA DAUKO?

Tambaya: Don Allah Shehi me za Ku ce game da yanayin

mata masu ciki

ta hanyar fyaden Yan Boko Haram, wadanda aka kwato su a

Sambisa. Muna bukatar nusarwa a shariance game da me za

a yi da cikkunansu. A zubar Ko a Bari. Idan za mu samu

amsa a mafi kusancin lokaci za mu so haka. Na gode.

Amsa : To dan'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu :

1. Idan ya zama cikin na zina ba'a busa masa rai ba, kamar

ya zama bai kai kwanaki 120 ba, to wannan malamai sun yi

sabani akansa zuwa maganganu uku : A. Wadanda suka tafi

akan halaccin zubar da shi, saboda bai zama mutum ba,

kuma in an haife shi zai zama aibi ga uwarsa, shi ma kuma ba

zai yi rayuwa mai dadi ba.

B. Bai halatta a zubarba, saboda Annabi S.A.W bai umarci

Gamidiyya da tayi zina ba, ta zubar da cikinta, cewa ya yi da

ita: ta je ta haife, sai ta zo a tsayar mata da haddi, kamar

yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1696.

41

Page 42: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

C. Akwai malaman da suka tafi cewa: idan fyade aka mata,

za'a iya zubarwa, mutukar ba'a busa rai ba.

2. Idan ya zama bayan an busa masa rai, wannan kam bai

halatta a zubar ba, saboda kashe rai ne, wanda bai ji ba bai

gani ba, yana daga cikin manufofin sharia kiyaye rayuwar

dan'adam. Zance mafi inganci shi ne bai halatta a zubar da

cikin zina ba ko da ba'a busa masa rai ba, saboda hakan zai

iya bude hanyar yaiwaita zinace-zinace, tun da za'a iya zubar

da cikin ba tare da an shiga cikin kunci da kunyata ba, amma

idan Fyade aka yi mata, ko kuma likita ya tabbatar da cewa

za ta halakka idan ta cigaba da zama da cikin, to ya halatta a

zubar a irin wannan lokacin. Matukar an busawa ciki rai bai

halatta a zubar ba, ko da kuwa fyade ne. Don neman Karin

bayani duba Ahkamul-janin Fil-fiqhil Islamy na Umar Ganam.

Allah ne mafi sani.Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

16\5\201539.BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN MAGANIN HANA HAILA?

Tambaya :

Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na

sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani

yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce

min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan

tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske ?

Amsa :

To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta,

Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya

42

Page 43: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

haramta saboda fadin Allah “Kar ku jefa kawunanku a cikin

halaka” suratu Albakarah aya ta 1952.

Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka

gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta

taso, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa

kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa,

musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna

dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai

a kiyaye.Don neman karin bayani, duba : Dima'uddabi'iyya

shafi na: 54 .

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

22-6-2015

40. YA SAKI MATARSA SAKI UKU, AMMA BAI GAYA MATA, SHIN TA SAKU ?

Tambaya :

Assalamu alaikum Allah Ya gafarta Malam mutum ne ya saki

matarsa saki daya. Da yayansa yaji labari sai ya kira shi yake

masa fada ya nemi akan lallai ya mayar da ita. Sai kawai ya

gayawa yayan nasa cewa saki uku yayi mata alhali saki daya

yayi, ya fadi hakan ne saboda ba yaso a tilasta masa ya

mayar da ita. To Malam shin menene matsayin wannan

maganar da mijin yayi na cewa saki uku yayi wa matarsa

alhali saki daya yayi mata?

Amsa :

Ta saku saki uku, saboda ba'a wasa da saki, kamar yadda

Annabi s.a.w, ya fada, sannan kuma ya tabbatar da cewa :

43

Page 44: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Allah yana afuwa ne game da zancen zuci, amma abin da aka

furta yana da hukunci. Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa24-6-2017

41.ZAN SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR AIDS?

Tambaya :

Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce

tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce bani da

ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su

da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe

mu, amma ina neman shawara ?

Amsa :

To dan'uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi,

wadanda ba'a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci,

saidai idan muka duba manufar da ta sa aka shar'anta saki

wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin

ma'aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta,

tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai hadari

kuma ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda

wannan dalilin, tun da malaman Fiqhu sun halatta raba aure

saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul

Jalil Sharhu Muktasarul Khalil : 6\478 Cutar Sida kuma tafi

kuturta tsanani. Sannan ba za'a kalli cutuwar da za ta yi ba,

bayan an saketa, domin yana daga cikin ka'idojin Sharia : kau

da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar

da za ta game, Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki

44

Page 45: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za'a waiga

zuwa damuwarta ba a nan wurin. Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa30/8/2015

42. ZAN IYA NEMAN SAKI SABODA MIJINA BA YA HAIHUWA?

Tambaya: Don Allah malam na auri wani mutum, amma har

yanzu ba mu haihu ba, shin zan iya neman saki, don na ji an

ce Annabi s.a.w. ya ce matar da ta nemi saki ba za ta shiga

aljanna ba?

Amsa :

To Yar''uwa hadisi ya tabbata daga Annabi s.a.w. cewa : "Duk

matar da ta nemi saki ba tare da wani dalili ba, ba za ta ji

kamshin aljanna ba" kamar yadda Abu-Dawud ya rawaito a

hadisi mai lamba ta : 2226. kuma Albani ya inganta shi.

Wasu malaman sun tafi akan cewa mace za ta iya neman

saki, idan ba ta san mijinta ba ya haihuwa ba, sai bayan sun

yi aure, saboda wannan yana iya zama aibun da za'a iya raba

aure saboda shi,. Duba : Sharhul-mumti'i 12/ 220.

Saidai zai yi kyau kada ki yi gaggawar rabuwa da shi, saboda

a lokuta da yawa, Allah yana iya jarrbar miji da rashin

haihuwa, daga baya kuma sai Allah ya warware masa ya

bashi 'ya'ya .

Allah ne mafi sani .

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

1\9\2015

43. SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI?

45

Page 46: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Tambaya:

Salam malam yayata ta jidda ta ce in tambaye ka menene

hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan

bugowa suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in gaya ma

wai don Allah ka Amsa a facebook, saboda ana bukatar sanin

amsar.

Amsa:

To 'yar'uwa babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta

yiwa wani dawafi, sannan kuma ba'a samu magabata na

kwarai suna yi ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma

ibada ba'a yin ta sai da dalili daga Alqur'ani ko Sunna, amma

dai ana iya yiwa wani addu'a lokacin da mutum yake yiwa

kansa dawafi.

Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin yiwa

wani Umara ko Hajji, saidai ba'a samu na dawafi a karan

kansa ba.

Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda

dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne

da suka hada jiki da dukiya, duk ibadar da ta hada jiki da

dukiya, tana Amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki

kawai ba ta Amsar wakilci kamar sallah.

Allah ne mafi Sani7-9-2015

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

44. SHIN YA HALATTA MATAR AURE TA YI FACEBOOK?

Tambaya :

46

Page 47: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Assalamu alaikum, shin ko ya halatta ga matar Aure ta yi

facebook, harma da charting?

Amsa : Wa alaikum assalam Wannan tambaya ce mai

wahala. Saidai abin da zance duk abin da zai amfane ta za ta

iya yi a face book, saboda asali a shari'ar musulunci, duk abin

da mutane suke aikatawa a mu'amalarsu ta yau da kullum

halal ne, mutukar ba'a samu wani nassi wanda ya haramta

ba, ko kuma ya kasance cuta tsantsa, haka ma idan mafi

rinjayansa barna ne, ka ga face book kuwa babu wani nassi

da ya haramta shi, sannan ba cuta ba ne tsantsa, tun da ana

iya samun ilimin addini ta wannan kafa. Ya kamata ta daina

yin charting da wadanda da muharramanta ba in ba malamin

da ta yadda da iliminsa da tsantseninsa ba, za ta yi masa

fatawa, saboda akwai maza da yawa da suke bi ta hanyar

charting don lalata matan auren da ba su da kamewa.

Wannan ya sa barin charting da mazan da ba muharramai ba,ko kuma wadanda suke neman auran matar, zai iya zamawajibi, saboda hakan yana kaiwa zuwa barna, duk abin dayake kaiwa zuwa barna, zai iya zama haramun ko makaruhi,kamar yadda malaman musulunci suka tabbatar.

Allah ne mafi sani29-9-2015

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

45. NA AURI AMARE BIYU A RANA DAYA, YAYA ZANYI WAJAN TAREWA?

Tambaya: Assalamu alaikum. Malam mutum ne ya auri mata biyu

(sangaya) rana guda, to dakin wacce zai fara shiga? Nagode

Allah ya karawa malam imani.

47

Page 48: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Amsa: To dan'uwa wasu daga cikin malamai sun karhanta auran

mata biyu a yini daya, saboda hakan zai kawo matsala wajan

bawa matan hakkinsu na kwana, saboda duk wacce aka fara

da ita, to dayar za ta cutu, saidai idan hakan ta faru, to zai

fara ne da wacce ta fara shigowa gidan, in kuma sun shigo

tare ne sai ya yi musu kuria. Don neman Karin bayani duba :

Al-kafy Na Ibnu Khudaamah shafi na: 981. Allah ne ma fi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa5/10/2015

46. FATAWAR NAN AKWAI GYARAMalam fatawarka da ka yi akan mijin da matarsa ta neme shi

da jima'i, bai amsa mata ba, ba shi da laifi, mun watsa ta a

group da yawa, kuma ta hadu da kalubale, ga abin da wata

take cewa: Nake ganin idan har aka ce namiji kawai ne zai

iya kusantar matarsa duk lokacin da ya so ko tana so ko ba

ta so, ita mace idan ta nemi hakan ko bai biya ma ta

buqatarta ba sai lokacin da ya so, Anya akwai adalci a

hakan? Idan akwai istidlali naqli a taimakamin da su ba aqali

ba. Na ga istidlal din na aqali aka kawo a rubutun.

Ya za'ayi mace ta nemi mijinta ya qi amince ma ta, duk dakasancewar mace tana da kunya. Amma har ta iya nemansaka ga kuwa akwai dalilin da ya sa ta neme shi. Ai shi manamiji ko da bai da sha'awa da an taba shi sha'awarshi za tamotsa. Kenan hakan ba zai zamo dalili da zai sa don mace tanemi mijinta ba ya ki amincewa da dalilin wai baya dasha'awa.Amsa: To abin da zan iya cewa shi ne: saduwar da muke magana

akanta ibada ce, ibada kuma tana bukatar dalili kafin a

tabbatar da ita, babu wani dalili Wanda ya wajabtawa miji

48

Page 49: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

amsa kiran matarsa duk lokacin da ta neme shi, sannan

yanayi da al'ada ya tabbatar da cewa namiji ba zai iya

saduwa da mace ba duk lokacin da ta name shi, saboda

Namiji yana bukatar nashadi kafin saduwa, sabanin mace,

wacce take a matsayin katifa, wannan yasa malamai da

yawa na sharia suka tafi akan cewa ba'a yiwa namiji fyade,

tun da in azzakarinsa bai motsa ba, ba zai sadu da mace ba,

mace kuwa an cimma daidaito za'a iya mata fyade saboda

kamar tirmi take, in har an samu tabarya shike nan, wannan

yasa za'a iya saduwa da mace tana bacci sabanin namiji.

Kasancewar an ce babu la'anta akansa idan matarsa ta

neme shi bai amsa mata ba, ba ya nuna ya halatta ya cutar

da ita, yaki saduwa da ita a lokacin da yake da nishadi. Allah

ne mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa14/10/2015

47. ZAN IYA ZUBAR DA CIKIN DA NA TABBATAR SIKILA NE?

Tambaya:

Salam malam ni AS ce, mijina ma genotype iri daya muke

da shi, yarana biyu babban AA karamar AS, duk sanda na

sami chiki muna zuwa a duba mana genotype din babyn

dake chikin, likitochi suka tabbatar da SS ne sai musa a

chire, amma bai kaiwa 4months muke chirewa, mallam meye

hukunchin yin hakan ?

AMSA: Wa alaikumus salaam warahmatullahi wa

barakaatuhu, To 'yar'uwa

49

Page 50: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an

busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai

watanni hudu, wasu sun haramta, wasu sun halatta wasu

kuma sun karhanta.

Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin

da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin

Sikila ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa

ya rayu, ya bautawa Allah ya amfani al'uma, don haka barin

cikin shi ne ya fi, saidai idan kuka zubar kafin ya cika wata

hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya

fuskanta a rayuwarsa, ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai

zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.

Don neman karin bayani duba Ahkamu al-janin fil-fiqhil

islamy na Umar Ganam Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa18/10/2015

48. IN BA KI DAWO DA ABIN DA KIKA DAUKA BA, NA

SAKE KI

Tambaya: Assalamu alaikum Malam mutum ne matarsa ta

dauki abinsa, sai yace kodai ta dawo da abinda ta dauka ko

kuma ya saketa, ita kuma zafin wannan maganar da yayi, sai

tace ba za ta dawo da abin ba, sai yace ya saketa, sai tace

masa saki nawa, sai yace konawa take so, sai ta yi shiru ba

tace komai ba, sai yayi maza ya shedama mahaifinta abinda

ya faru, da cewa ya sata, ta maido da abin da ta dauka

domin ya warware kalamin da yayi, daga qarshe ta maido da

50

Page 51: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

abin, malam matsalar anan shi ne matar tace ya saketa

amma shi yace bai sake tava , Allah ya san zuciyar shi , idan

harta dawo mashi da wannan abun ,to ya warware kalamin

sakin da yayi, matar ta tsayu akan saki ne amma shi yace ba

sakine va, Mallam don Allah menene gaskiyar wannan lamari

? Allah yasaka da alkhairi amin.

Amsa: Abin da yake daidai shi ne saki ne, saboda niyya ba

ta da tasiri a saki,

ana amfani ne da Abin da miji ya furta. Ya rataya sakin da

wani abu, kuma abin ya tabbata, ya kuma zo ya furta, don

haka ta saku. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa20/10/2015

49. YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA ?Tambaya: Ass. Malam shin mutum ya furta saki ga matarsa ba ta jiba,

shin ta saku ?

Amsa: To dan'uwa matar ta saku, saboda sanin an sake ta, ba shi

daga cikin sharudan saki, mutukar miji ya furta saki, mace ta

saku koda ba ta ji ba, yana daga cikin ka'idoji a wajan

malaman fiqhun musulunci: Duk wanda ba'a damu da

yardarsa ba wajan tabbatuwar abu, ba'a damuwa da

saninsa, yardar mace ba sharadi ba ce wajan zartuwar saki,

haka ma saninta an yi sakın ba sharadi ba ne wajan

tabbatuwarsa.

Allah ne mafi sani.Dr. Jamilu Zarewa

51

Page 52: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

31/10/2015

50. MATAR DA TA GAYYATO JININ HAILA KAFIN LOKACINSA, YAYA SALLARTA?

Tambaya:

Salam malam ina hukunchin macen da in mijinta ya fitine ta

da jima'i take shan magani don jini yazo mata, Yaya

hukuncin jinin yaya kuma maganar sallah, ? tunda gayyato

jinin ta yi.

Amsa:

To 'yar'uwa Allah da manzonsa sun rataya hukunce-

hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, kamar yadda aya ta:

222 a suratul-Bakara take nuni zuwa hakan, duk da cewa

gayyato shi ta yi saidai zai dauki dukkan Hukunce-hukuncen

haila, mutukar ya zo da siffofinsa. Gayyato jini saboda hana

miji jin dadi bai dace ba, saboda duk dabarar da za ta kai

zuwa haramun to ita ma ta zama sabon Allah, Ya wajaba ga

mace ta baiwa miji kanta duk lokacin da yake bukata, in ba

tana da uzurin da sharia ta yarda da shi ba, don haka bai

kamata mace ta hana mijinta saduwa da ita ba ta hanyar

dabara.

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Zarewa

31/10/2015

51. TA AURI WANDA BAYA IYA JIMA'I HAR SUKA RABU,SHIN ZATA YI IDDA?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Malam Wani bawan Allah ne ya Auri

kanwata, sai daga baya muka gane ya ha'incemu sakamakon

52

Page 53: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

rashin mazantaka da baya dashi, daga baya da asirinsa ya

tonu sai ya saketa, shin malam za tayi Idda ne ? don babu

wata mu'amalar Aure da ya taba shiga tsakaninsu.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Mutukar ba su taba kwanciyar aure ba,

ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta : 49 a suratul

ahzaab take nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani. Dr Jamilu Zarewa

21 Muharram, 1437 (03/11/2015)

52. MIJINA MAZINACI NE, ZAN IYA JUYA MASA BAYA?Tambaya:

Assalamu alaikum, Allah ya hadani da miji mazinaci, shin in

na daina hada shinfida dashi dan gudun daukar wani ciwo

innada laifi?

Amsa:

Wa alaikum as salam, abin da ya fi shi ne ki yiwa

magabatansa bayani, don su tsawatar masa ya daina, in

Kuma kin tabbatar ya dau cutar aids kina da damar da za ki

je wajan alkali don ya raba auren, tun da musulunci ya yi

umarni da tunkude cuta gwargwadon iko, in har miji yana

ciyar da matarsa to ya wajaba ta amsa kıransa, wannan

yasa daukar matakin hana shi kanki zai iya jawo muku

rigima, sanya alkali ko magabaci a hukuncin shi ne daidai.

Allah shi ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa21 Muharram, 1437 (03/11/2015).

53

Page 54: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

53. ZAN IYA YIWA MATATA KOME, BAYAN TA FARA JININA UKU?

Tambaya: Malam idan mace tana iddah Har tana Kan jini na uku. miji

zai iya maida ta?

Amsa: To Dan'uwa Allah yana cewa a suratul Bakara aya ta: 228,

"Kuma matan da aka şaki, za su jira (kur'i) uku kafin su gama

idda", saidai Malamai sun yi sabani game da ma'anar (kur'i)

a ayar.

A wajan malaman Malikiyya kur'i a ayar yana nufin tsarki,

don haka duk matar da aka saka in dai ta shiga jini na uku to

miji ba shi da damar yi mata kome, saboda za'a sake ta ne a

tsarki sai ta yi jini sai tsarki, sai jini sai tsarki, daga ta shiga

jini na uku za ta zama ta kammala iddarta.

Malaman Hanafiyya sun fassara (Kur'i) a waccar ayar da jini,

don haka mutukar ba ta kammala jini na uku ba, to miji zai

iya mata kome, Tunda zata fara idda ne da jini, don haka ba

zata kammalaba sai a karshen jini na uku.

Wasu Malaman suna inganta Mazahabar Hanafiyya saboda

Annabi s.a.w ya kira haila da sunan Kur' i a hadisin Imamu

Ahmad mai lamba ta: 25681

Don neman karin bayani duba: Tafsirin Ibnu-Kathir 1/607.

Allah ne mafi Sani.Dr.Jamilu Zarewa

8/11/201554. ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA

CONDOM?Tambaya: Salam. Malam Allah ya karama daukaka da imani.

Shin mutum

54

Page 55: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa

Condom?

Amsa: To dan'uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa

ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai

haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara

da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai

haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın

wanka. Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan

ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai

jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za'a sadu

da mace mai haila ba ko da an sa Condum .

Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Zarewa

28/11/2015

55. JINI YA BARKE MIN, SABODA AN YI MIN WANKIN CIKITambaya :

Assalamu alaikum Dan Allah inada tambaya macen da tayi

bari aka mata wankin ciki bayan nan sai jini yake zuwa mata

yadai baiyana jinin ciwo ne Shin zata dunga wanka ne

lokacin da zatayi kowace sallah?

Ko kuwa tsarki kawai zatayi lokacin sallah? Amsa : To dan'uwa Za ta yi tsarki kuma ta yi alwala ya yın kowaccesallah, saboda hukuncinsu daya da mai istihâlâ, kamaryadda Annabi saw ya umarci Fadimatu 'yar Abi-Hubaish ahadisin Ibnu Hibban mai lamba ta: 1354, da yın alwala yayinkowacce sallah, lokacin da ya tabbatar tana yın jinin cuta.Allah ne mafi sani. Don neman karin bayani duba: Risala Fi Dima'u Addabi'iyya:45.

55

Page 56: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa28/11/2015

56. BABU KOME GA MATAR DA TA FANSHI KANTA

Tambaya:

Salam malam menene sharadin dawo da mata bayan tayi khul'i dan Allah ataimaka? Amsa: To dan'uwa idan mace ta fanshi kanta daga wajan mijinta,

ba zai iya yi mata kome ba, Amma zai iya shiga cikin

manema in ta yarda da shi, sai a sake daura aure ya biya

sadaki

Allah ne mafi sani .Dr. Jamilu Zarewa

30\11\2015

57. LOKACIN YAYE YARO A MUSULUNCI

Tambaya:

Aslm ya Shaikh: Allah yaqara wa Dakta lafia amin. Don Allah

mallam wane lokaci ne mafi inganchi da ya dace a yaye yaro

daga barin shan nono a shariance? Nagode Allah yasaka da

alkhairi amin.

Amsa: To dan'uwa ina rokon Allah ya amsa addu'arka, Lokaci Mafi

çika na yaye yaro shi ne: idan ya kai shekaru biyu, kamar

yadda aya ta: 233 a suratul Bakara ta tabbatar da hakan,

saidai ya halatta a yaye yaro kafin ya cika shekaru biyu,

mutukar ba zai cutu ba, kuma iyaye guda biyu sun cimma

daidaito akan hakan. Don neman karın bayani duba: Tafsirin

Qurdubi 3/162. Allah ne mafi Sani.

56

Page 57: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Dr. Jamilu Zarewa2/12/2015

58. A KWAI GADO GA MATAR DA MIJINTA YA MUTU BATA GAMA IDDA BA?

TAMBAYA:

Assalamu alaikum Mal. mutum ne ya saki matarsa Bai dawo

da ita ba kuma bata gama idda ba sai ya rasu, shin zata ci

gadonsa?. Allah ya kara ma mal imani da ilimi mai amfani

Ameen.

AMSA:Wa alaikumus salaam wa rahmatullahi wa

barakaatuhu, To dan'uwa

Idan miji ya saki matarsa , kuma ya mutu kafin ta gama idda,

to za ta ci gadonsa Mutukar saki daya ne ko biyu, saboda har

a lokaçın tana nan a matarsa, amma in uku ne babu gado a

tsakaninsu, haka nan idan fansar kanta ta yi, saboda ta

nisanta daga gare shi. Allah ne mafi Sani.

Dr Jamilu Zarewa10/12 /2015

59. ZAN IYA SHAN MAGANIN TSAYAR DA HAILA SABODA AIKIN HAJJI?

Tambaya: Garemu kamar haka? Shin ya halatta mace tatsayar da jinin haila saboda aikin hajji?Amsa: To 'yar'uwa ya halatta, mutukar likita ya tabbatar miki ba zai

cutar da ke ba, saidai tsayawa a Dabi'ar da Allah ya halicce

ki akai shi ya fi kyau, saboda shan magunguna irin

wadannan yana birkita kwanakin al'ada, kamar yadda

bincike ya tabbatar Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

57

Page 58: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

21\12\2015

60. RABON GADON MATA-MAZA!

Tambaya: Slm, idan mutum ya mutu ya bar mata-maza da 'yan'uwa,

yaya rabon gadon zai kasance?

Amsa: To dan'uwa mata- maza shi ne wanda yake da al'aurar mace

da ta namiji, kuma ya kasu kashi biyu :

1. Akwai mara rikitarwa, wato wanda aka gane inda ya fi

karfi, kamar ya zama yana haila, kaga za'a riskar da shi da

mace wajan rabon gado, ko ya zama yana fitsari ta al'aurar

namiji, to wannan hukuncinsa hukuncin namiji a wajan rabon

gado, haka nan idan ya zama yana da gemu da gashin baki.

2. Mai rikitarwa, wannan shi ne wanda aka kasa gane inda ya

fi karfi, kamar ya zama yana fitsari ta ala'aura biyu, kuma ba

wanda yafi fitowa da karfi ko da yawa a cikinsu, ko kuma ya

zama yana da gemu, kuma yana haila. Idan har mata maza

ya balaga ba'a gane inda yafi karfi ba, to za'a ba shi rabin

gadon mace ne, da rabin gadon namiji. Duba : Attahkikat

almardhiyya fi-mabahithil-fardhiyya shafi na 206. Allah ne

mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa9/5/2015

61. TA YI BAKANCE, AMMA TA KASA CIKAWA, YAYA ZA TA YI?

Tambaya:

58

Page 59: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Malam wata mace ce ta yi bakance za ta yi azumin Annabi

Dawud, wato yau ta yi azumi gobe ta sha, amma kuma yanzu

ta yi aure ta kasa, ya ya kamata ta yi ? shin akwai mafita ?

Amsa :

To dan'uwa Bakance makaruhi ne, haramun ne a wajan wasu

malaman, saboda Annabi s.aw yana cewa : "Bakance ba ya

zuwa da alkairi" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai

lamba ta : 1639. Saidai ya wajaba a cika bakance idan aka yi.

Wasu daga cikin malaman hadisi sun ta fi akan cewa idan

mutum ya yi bakance ya kasa cikawa zai iya yin kaffarar

rantsuwa, saboda hadisin da aka rawaito daga Muslim a

lamba ta: 1645 a sahihinsa, wanda Annabi s.a.w. yake cewa :

"Kaffarar bakance irin kaffarar rantsuwa ce" . Duba Alminhaaj

na Nawawy 4/269

A bisa abin da ya gabata za ki iya yin kaffarar rantsuwa wato:

ciyar da miskinai goma, ko tufatar da su, ko kuma 'yanta

kuyanga, idan babu hali, sai ayi azumi uku, kamar yadda ya

zo a suratul Ma'idah aya ta : 89 .

Allah ne ma fi saniDr. Jamilu Zarewa

12\7\201562. WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI

SABODA RUWAN SAMA ?Tambaya: Assalamu alaikum. Allah karawa malam ilimi da fahimta.

Shin da Allah malam ko mutum zai iya hada sallah shi kadai

idan ana ruwa bashi da ikon zuwa masallaci? Nagode malam

Amsa:

59

Page 60: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar

zuwa maganganu guda biyu :

1. Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada salloli saboda

ruwan sama, tun da ruhusa ce Allah ya bawa mutane, don

haka ta shafi kowa da kowa, wannan ita ce maganar

Hanabila kamar yadda Mardawy ya ambata a INSAAF 2\340.

2. Bai halatta ga wanda bai je sallar jam'i ba ya hada salloli

saboda ruwan sama, saboda an yi sauki ne ga wadanda za

su je masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa, wannan

wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah a gida, don

haka rahusar ba za ta same shi ba, sannan kuma shari'a ta yi

nufin ta kiyaye sallar jam'i shi ya sa ta saukaka wajan hada

salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse sallar jam'i ta

tozarta, wannan ita ce maganar Imamu shafi'i a littafinsa

Al'umm 1\195 A fahimtata maganar karshe ta fi inganci, don

haka wanda yake gida ba zai hada salloli ba. Allah ne mafi

sani

Dr. Jamilu Zarewa 9/11/2015

63. ZAN IYA AURAN DAN WASAN KWALLON KAFA?

Tambaya:Malam ina tambaya ne akan kwallon qafa, a kwai wanda yake Neman aurena sana'arsa kenan, da ita yake ci yake sha yake

komai, malam ina kokonto akan wannar sana'ar tasa, kada

ya kasance sai anyi auren inji cewa ba halal bane, tunda ana

biyansa idan sukayi wasa, to shine malam ko

a taqaice a sanar dani wani abu akai, saboda musan

makamar mu, nagode•60

Page 61: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Amsa: To 'yar'uwa ına rokon Allah ya baki miji nagari, malamai sunakasa kwallo gıda uku :

1. Kwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyu

su hadu, su yi ball don su tsinka jinin jikinsu, wannan

kam ta hallata mutukar ba ta kautar daga ambaton

Allah ba, ko kuma sallah idan lokacinta ya shiga .2. Kwallon da kungiyoyi biyu ko sama da haka za su hada

kudi su sayı kofi wanda a karshe kungiya daya za ta

dauka, wannan kam bai halatta ba, saboda daidai yake

da CACA, kuma yana sabbaba gaba da kiyayya a

tsakanin 'yan kwallo. 3. Idan ya zama wani ne daban zai sanya Kofin, shi ma

malamai sun ce haramun ne saboda asali musabaka da

wasan tsere haramun ne, in ba abin da dalili na shari'a

ya halatta ba, irin wannan kwallon kuma ba ta cikin

abin da aka togace, sannan akwai barna mai yawa a

cikinta, domin zai yi wuya a tashi irin wannan Kwallon

wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi da

kulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutan

har da doke-doke tsakanin kungiyoyin guda biyu. Idan

ya zama mijin da za ki aura yana yın nau'i na na biyu ko

na uku, to ya wajaba ki yi masa nasiha idan kuma yaki

ji, to auransa akwai hadari saboda zai ciyar dake da

haramun. Don neman karin bayani duba Fataawaa Al-

lajna Adda'imah 3/238 da kuma Fataawaa Muhammad

bn Ibrahim 8/116. Allah ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa12/11/2015

61

Page 62: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

64. INA YAWAN WAYA DA BURDURWATA, KO YA HALATTA A SHARI'ANCE?

Tambaya: Dan Allah ina tambaya, Namiji ne yakeso ya qara

aure to shine bayan ya dawo gida da dare sai budurwar ta

riqa kiran shi ko kuma ta riqa turo txt, shikuma idan matarshi

tana kusa sai ya riqa avoiding amma da ta dan daga sai

shima ya fara responding ko ya kira ta, kuma idan asuba tayi

sai ta kirashi. To shine matar ba taso, dan Allah a Shari'ance

yana da laifi ko ba shi da? sannan matar zata iya neman ya

dena ko kuwa ta shiga rayuwarsa ne a shari'ance?

Amsa: To dan'uwa yana da kyau ka san cewa matar da kake nema

aure ba muharramarka ba ce, don haka bai halatta ka dinga

hira da ita ba, sai gwargwadon bukata.

Yawan hira da budurwa da jin dadin zancenta, yana daga

cikin abubuwan da suke kaiwa zuwa ga fitina, mai AHLARI ya

kirga jin dadin zancen wacce ba muharrama ba daga cikin

ayyukan da Allah ya hana.

Duk wanda yake yawan hira da matar da ba muharramarsa

ba, yana jin dadin zancenta, Allah zai iya haramta masa jin

dadin zancen matarsa ta halal.

Ya wajaba hirarka da buduwarka ta zama gwargwadon

bukata, saboda jin dadin zancenta, zai iya kai ku, ku aikata

katon sabo, yana daga cikin ka'idojin shari'a toshe duk

hanyar da take kaiwa zuwa barna. Zunubi shi ne abin da ya

sosu a ranka kuma ka ji tsoron kar mutane su yi tsinkayo,

kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba

ta: 2553.

62

Page 63: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa4/1/2016.

65. ZAN IYA HUDA HANCI SABODA KWALLIYA GA MIJINA?

Tambaya: Assalamu'alaikum, Malam dan Allah wata ce mijin ta yace

hujin hanci na burge shi. So tana so ta huda sai aka ce mata

babu kyau a musulunci. Shin malam ya abun yake? Haramun

ne,ko kuwa tana iya hudawa tasa dankunne tayi kwalliya da

shi?

Amsa: Wa alaikum assalam, An tambayi sheikh Ibnu

Uthaimin akan Wannan mas'alar ta huda Hancı sai yake

cewa: Huda Hanci zai iya zama canza halittar Allah, amma

idan Garin da matar da ta huda hancin take ana yın ado a

hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi ayi

hakan. Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137. Haka

nan an tambayi Sheikh Abdul Muhsin Al'abbad akan haka a

darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi

akan haka.

Bisa Abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE ta huda

hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun da al'adarsu ce,

saboda ya tabbata sahaban Annabi s.a.w mata suna huda

kunnansu suna sanya 'yan kunnaye Kamar yadda hadisin

Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.Dr. Jamilu Zarewa

4/1/2016

63

Page 64: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

66. ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA?

Tambaya:

Assalam pls. an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba

sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa, tambayata

anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi ?

Amsa: To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure

kafin ya tare da amaryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa

takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi

S.a.w. ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin

da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145,

wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi .

Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

5\1\201667. NA YI WANKAN JANABA, SAI MANIYYI YA SAKE

ZUBO MINI ?Tambaya:

Assalamu Alaikum tambayata itace idan mata ta sadu da

mijinta tayi wanka immidietly bayan ta gama tana zaune sai

taji sperm ya zubo mata shin zata kara yin wani wanka ko

kuma wanda tayi ya isa ?

Amsa:

Wa alaikum assalam, To idan sabuwar Sha'awa ce ta zo

mata, ta zubar da maniyyi, ya wajaba ta sake wanka, amma

idan saboda saduwar da suka yi ne a baya : za ta wanke

wurin ne, ta sake alwala, amma babu bukatar sake wanka,

wanda ta yi na farko ya isa. Duba Bidayatu Almujtahid 1\48

da Insaf 1/232. Allah ne mafi sani

64

Page 65: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Dr. Jamilu Zarewa2/1/2016

68. RASHIN ADALCI TSAKANIN 'YA'YA YANA JAWO FITINTINU

Tambaya: As-salaamu alaykum Malam Allah ya kara maka imani da

fahimta tambayata itace Mahaifinane yake nuna banbanci a

tsakanin mu sannan yana yawan zagin mahaifiyata

musamman in 'kanne na sunyi masa laifi sai ya kama zaginta

Sai na nuna masa rashin jindadina da wannan Al'amari har

ya kai ga mun daga ma juna murya. Karshe sai ya fara yimin

Allah ya isa yana tsine mun.

Amsa:

Ya wajaba uba ya yi adalci a tsakanin 'ya'yansa, Annabi

S.a.w. yana cewa: "Ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin

'ya'ya yanku" Wannan ya sa lokacin da Sahabi Bashir ya yiwa

dansa kyauta, ya nemi Annabi s a w. ya yi shaida akan haka,

ya tambaye shi: shin Duka 'ya'yanka ka yi musu kyauta? sai

ya ce A'a, sai manzon Allah ya ce: Ba ka so su zama daidai

wajan yi maka biyayya? ba zan yi shaida akan zalunci ba".

Bukhari da Muslim sun rawaito wadannan riwayoyi. Yin

adalci a tsakanin iyalai yana inganta tarbiyya, yana sanyawa

su ji tausayin Uba bayan ya girma, yana kara musu hadin kai

da son juna. Ya wajaba mazaje su Sani cewa: zagin

matayansu ya sabawa ka'idojin sharia, kuma hanya ce ta

tabarbarewar tarbiyya, domin Yaran za su rabu biyu, wasu

suna bayan mahaifinsu, wasu kuma Babarsu za su ga ta yi

daidai. Ya wajaba a tausasa harshe lokacin da za'a yi

65

Page 66: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

magana da mahaifi saboda Allah ya hana fadawa Uba kalma

mara kyau ko yaya take, kamar yadda ya zo a Suratul Isra'i.

Ba'a son ana yın muguwar addu'a ga iyalai saboda in aka

dace da lokacin amsar addu'a za ta zamar masa matsala

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa16/1/2016

69. ZANCEN BATSA TSAKANIN MASOYA!

Tambaya:

Wai shin menene hukuncin saurayi idan suna hira da

budurwarsa sai ya dinga yi mata hiran matar aure? yana ce

mata sha'awa tana damunsa, ita kuma budurwar ba

bazawara ba ce, dan Allah mai matsayin hiran a shari'a?

Allah ya kara muku Basira da ikilasi

Amsa:

Bai dace saurayi ya dinga zancen sha'awa ba ga matar da

bai aura ba, tunda Shari'a ta haramta yasashshen zance a

aya ta : 3 a Suratul Muminun, kuma hakan yana iya kaiwa

zuwa ga zina, idan aka samu macen da ba natsatstsiya ba,

ko kuma Shaidan ya ratsa, Yana daga cikin manyan ka'idojin

sharia toshe hanyar da take kaiwa zuwa barna. Allah ne mafi

sani.

Dr. Jamilu Zarewa22/1/2016

70. YAWO BABU DAN-KWALI A TSAKAR GIDA?Tambaya:

66

Page 67: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Assalamu alaikum,Allah gafarta malam shin zan iya yawo

acikin gida ba dan kwali?

Amsa: Mace zata iya yawo babu Dan kwali idan tana tsakanin 'yan

uwanta mata musulmai saboda al'aurar mace ga 'yar uwarta

mace musulma tana kasancewa ne tsakanin gwuiwa zuwa

cibiya, mutukar akwai mazan da ba muharramai ba to bai

halatta ta bude kanta ba, saboda dukkan mace Al'ura ce in

ban da fuska da tafukan hannu. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa24/1/2016

71. HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation)Tambaya:

Assalamu alaikum, Allah ya kara ma malam lapiya da imani,

malam dan Allah menene hukumci masturbation (Istimna'i) a

musulunci

Amsa:

Wa alaikum assalam. To 'yar'uwa Babu nassi ingantacce

bayyananne yankakke da yake haramta wasa da al'aura har

maniyyi ya fito, saidai wasu malaman sun haramta auran

hannu saboda aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan

bukatar sha'awa ta hanyar matar aure ko bayi kawai,

wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba'a iya biyan

bukata ta hanyar su.

Yin wasa da al'aura har maniyyi ya fita yana haddasa

matsaloli a likitance, saidai yana daga cikin ka'idojin shari'a;

idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda za'a yi

67

Page 68: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata,

wannan yasa Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka halatta

auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma ba shi da halin

da zai yi aure.

Idan mu ka ce auran hannu haramun ne, saidai barnar dake

cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki,

sannan tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za'a haifi

'ya'ya gantalallu, marasa asali, wannan ya sa magana ta

biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu sharudan da suka

gabata. Don neman Karin bayani duba: Muhallah 12\407 da

Majmu'ul fataawaa 34/146. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa23\1\2016

72. AL'ADATA TA RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI ?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Malam don Allah ina da tambaya, don

Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyarawa akan

lokaci. Malam matsala ta haihuwa gareni duk haihuwa ta sai

anyi min CS, sai likita ya bani shawarar tsarin iyali don in

huta, sai daga nan al'adata Tarikice sai yazo yau bazan sake

ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to

ni dai wanka na nakeyi na cigaba da ibadata to malam

ibadata tayi ko da gyara. Sai kuma da watan Ramadan yazo

min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai

nayi wanka na cigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai

dauke, don sai da yamin wajen kwana goma sannan ya

68

Page 69: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama wannan

kwanaki goman shima. To malam ya azumin tawa take.

Amsa:

To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki a cikin alqur'ani ya

rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka

mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya

wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai

dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo

miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a

lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah

da azumi ba. Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda

hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo

(zubar da maniyyi a wajen farji yayin saduwa) a lokacin da

Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi

mai lamba ta: 4911, saidai yawancin magungunan tsara iyali

suna birkita al'ada, wannan yasa barin su shi ne ya fi, in ba

likita ne ya tabbatar da lalurar shan ba, ko kuma aka gane

maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa. Allah ne mafi

sa ni

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa22/1/2016

73. KARAWA AMARYA YAWAN KWANAKI, SABODA HONEY MOON

Tambaya:

Meye hukuncin mutumin da yana da mata sai yayi amarya

sai yayi mata visa suka tafi wata kasa wata daya a matsayin

69

Page 70: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

honey moon, to meye hukuncin daya matar, ya zalumceta

kenan?

Amsa:

To dan'uwa Anas RA ya rawaito cewa: "Yana daga cikin sunna

In mutum ya auri budurwa kuma yana da wata matar, ya yi

mata kwana bakwai, in kuma bazawara ce kwana uku"

kamar yadda ya zo a Sunanu Attirmizi a hadisi mai lamba ta:

1139, wannan sai ya nuna kari akan haka ya sabawa sunna.

Amma Idan Uwar gida ta bada izni ya halatta ayi kari akan

haka, tun da ya halatta mace ta sarayar da hakkinta na

kwana, kamar yadda Saudatu ta bawa Nana A'isha

kwananta, lokacin da girma ya zo mata, ta ga Annabi s.a.w.

bai damu da ita ba sosai, kamar yadda Bukhari ya rawaito a

hadisi mai lamba ta: 4914, wannan sai ya nuna halaccin

sarayar da hakkin kwana, da yiwuwar yiwa amarya kari idan

uwar gida ta yarda. Allah mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa31/1/2016.

74. ZAN IYA AURAN WACCE NA YI ZAMAN DADIRO DA ITA?

Tambaya:

As salamu alaikum, Malamai ya halarta musulmi ya

musuluntar da matar da yayi zaman daduro da ita bayan

hakan ya aure ta, limanmin da ya goyi bayan hakan yayi

daide? Please is very important"

Amsa: Wa alaikum as salam, ya halatta sabida babu alaka tsakanin

dadironsu da auransu bayan ta musulunta Mutukar sun tuba,

70

Page 71: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

saboda musulunci yana rusa abin da ya gabace shi na

zunubi kamar yadda ya tabbata a hadisin Amru bn Al'ass.

Idan musulmi ya yi zina ya tuba, to Allah yana gafarta

dükkan zunuban da suke hakkinsa ne, kamar yadda aya

ta:53 a suratu Zumar ta tabbatar hakan Allah ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa1/2/2016

.

75. JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA KAI WATA HUDU?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Dr dan Allah inada tambaya akan matar

da keda ciki yakai wata hudu sai jini ya rinka xubar mata

daga baya kuma sai ya dauke bayan kwana guda ko biyu

yakan iya dawowa ko bayan wasu awowi shin ya hukuncin

sallar ta ? zata jinkirta sallah sai jinin ya dauke ko zata rika

yin wanka duk sanda ya dauke tayi ramakon sallolin baya ne.

Nagode

Amsa:

To 'yar'uwa mutukar cikin ya kai wata hudu kuma jinin da

yake fita yana hade da ciwon haihuwa, to ya zama jinin biki,

kuma zai hana sallah, amma Idan babu ciwon haihuwa to

mutukar ya zo da sifar jinin haila (baki ko karni) to zai zama

haila, tun da a zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila.

In ya fita daga wadannan biyun zai zama jinin cuta ta yadda

ba zai hana sallah ba, in har jinin kusa-kusa yake fita, za ki

iya jinkirta salloli, sai ya dan tsagaita, sai ki rama sallolin da

aka yi su kina da tsarki, saboda addinin musulunci addini ne

71

Page 72: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

mai sauki, babu kunci da damuwa a cikinsa, kamar yadda

aya ta karshe a suratu Al-hajj ta yi bayanin haka.

Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

3\2\2016

76. ZA MU IYA AURAWA KANWARMU DAN SHI'A?Tambaya :

Assalamu'alaikum..da fatan malam yana lafiya.. Malam wata

kanwarmu ce ta kamu da son dan shi'a dake ungurmu kuma

mun yi kokarin rabasu saboda wasu daga cikin munanan

dabi'ar su kamar zagin sahabbai, mutu'a, zagin matan

Annabi da dai sauransu. Amma abin dai ya gagara. Saidai ya

tabbatar mana da cewa shi tinda aka halicce shi bai taba

aikata wadannan laifukan ba. Sannan kuma bai yarda da

hakan azuciya ko a baki ba. Illah iyaka yasan yana bin

zakzaky ne akan yana kiran hadin kai ga musulmi. Shi iya

wannan ne ya amsa amma ya barranta ga duk wani

munmunar akidar shi'a.

A iya zaman da mukayi dai ba muga yana aikata wani

kaba'irar ba dan a masallacin mu yake sallah tin tashin mu

dashi. Shin malam ya halatta mu bashi. Ko kada mu bashi.

Amsa: To dan'uwa tabbas a cikin addinin shi'a akwai manyanabubuwa wadanda suke warware musulunci:

1. Daga ciki akwai zagin mafi yawancin sahabbai, tare da

cewa, Allah ya tabbatar da cewa ya yarda da su a ayoyi

da yawa a cikin alqur'ani, duk wanda ya ce mafi

yawancin sahabban Annabi s.a.w. sun kafirta tabbas ya

72

Page 73: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

karyata Allah, wanda ya karyata Ubangiji hukuncinsa a

fili yake.2. Yana daga cikin akidunsu tabbatar da cewa: Alqur'anin

da yake hannunmu bai cika ba, tare da cewa: Allah ya

tabbatar: zai kiyaye shi, har abada.3. Rafidha 'yan shia sun tafi akan cewa Nana A'isha

Mazinaciya ce, tare da cewa Allah ya kubutar da ita

daga abin da munafukai suka zarge ta da shi a ayoyi

guda goma a suratun Nur.

Duk da cewa da yawa daga cikin 'yan shi'a suna kore

wadannan aqidu, saidai ayyukansu da littatatafansu da

maganganunssu, suna karyata korewarsu. Shugabansu

Zakzaky yace ba ya zagin sahabbai, kawai sai muka gan shi

a zaune a Husainiyyar Zariya yana la'antarsu, Haka Yakubu

Yahya na Katsina shi ma ya yi ikrarin haka, sai ga shi mun ji

shi yana siffanta Sahabbai da 'yan PDP, yana ci musu

mutunci da cewa sun yi juyin mulki. Ya wajaba ka sani yana

daga cikin manyan aqidun 'Yan shi'a TAKIYYA wato yin karya

ga wanda ba dan shi'a ba, kuma duk wanda bai iya wannan

ba, to bai cika dan shi'a ba a wajansu, domin ginshikin

addininsu ce, don haka kar ka dogara da maganarsa.

Annabi s.a.w. yana cewa : "Idan wanda kuka yarda da

addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa" kamar

yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1084, duk

wanda addininsa ya kunshi abin da ya gabata, bai halatta a

aura masa mace ba, tun da Allah bai yarda da hakan ba,

kuma addininsa ba yardajje ba ne, Allah ya ba ta miji nagari

wanda ba dan shi'a ba. Allah ne mafi Sani.

73

Page 74: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa6/2/2016.

77. TAYI WASIYYA DA RABIN DUKIYARTA, SHIN TAINGANTA?

Tambaya:

Assalamu alaikum dan Allah malam tambaya nake yi akan

wasiya, wata tsohowa ce ta rasu ta bar danta guda daya, sai

kuma wani wanda ta rika tun yana jinjiri har ya girma sai

tace: idan allah yayi mata rasuwa a raba gidanta biyu a

bashi rabi shima dan nata ya dauki rabin, hakan ko ya

halatta?

Amsa: Wa alaikum assalam, mutukar ba ta da wani gidan sai wanda

ta yi wasiyya da rabinsa, To wasiyyar ba ta inganta ba,

saboda Annabi s.aw ya hana yın wasiyya da sama da daya

bisa ukun dukiya, Ta bar danta mawadaci, ya fi ta bar shi

yana maula a wajan mutane, kamar yadda hadisi ya

tabbatar, a riwayar bukhari mai lamba ta: 3721. Allah ne

mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa17\2\2016

78. TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE?Tambaya:

Malam wata tayi cikin shege da wani mutum, saita nemi

wani daban ya rufa mata asiri ya aureta. Yanzu sunyi Auren,

yaya hukuncin auren a Shari'a?

Amsa:

74

Page 75: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. Aure

kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai

albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa.

Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar

da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura

mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma

idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba

wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an

daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure

a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce

ne kuma rusasshe. Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam

Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i

kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi

istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma

suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura

mata aure, to auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya

ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta

haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

"Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya

shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud:1847.

Don neman karin bayani duba: AL-MUDAWWANNAH AL-

KUBRAH 2/173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren,

saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma

za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren

to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci

75

Page 76: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba şu nisanci saduwa,

kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata. Allah ne mafi

sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa27\2\2016

79. INA YIN HAILA DUK SATI, MENENE HUKUNCIN

ALLAH?

Tambaya:

Assalamu alaikum. Mal. tambaya nake, mace ce sati-sati

take ganin al'adarta, tun lokacin da tayi fama da rikecewar

al'ada, daga baya zubar jini har na kusan wata daya, ta je

asibiti sun yi bincike da hotona lokuta dabam dabam ba'a

gane komai ba, amma sun bata magani da allura domin

daukewar jinin. Tun daga lokacin da jinin ya dauke sai jinin

Al'ada ya rinka zomata sati-sati, Asibiti suka ce yanzu kam

sai dai ayi Addu'a. tambaya mal. Shin zata bar sallah duk

sati saboda ganin jinin ko mi cece shawara? Nagode

Amsa:

To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki, ya rataya hukuncin jinin

haila ne da samuwarsa a aya ta: 222 a suratul Bakara, don

haka mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni)

to ya wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai

dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, ya zubo

miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a

lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah

da azumi ba. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa28/2/2016

76

Page 77: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

80. BA TA HAILA SAI DUK SHEKARA, YAYA IDDARTA?Tambaya: Assalamu alaikum malam ina da tanbaya: mace aka saketa

saki 3 anma bata yi jinni ba sai bayan shekara 1 yaya iddarta

za ta zama kenan?

Amsa:

Wa alaikum assalam, za ta jira jini uku, ko da kuwa sai ta yi

shekara uku, kafin ta kammala, saboda Allah ya rataye iddar

matar da aka saka, kuma ba ta yanke kauna daga haila ba

da jini uku, kamar yadda aya ta : 228 a suratul Bakara ta

tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa4/3/2016

81. JININ BARI, BA YA HANA SALLAH?Tambaya: Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa, Mal. Ciki ne Na wata

daya sai nake bleeding har ance nayi bedrest shine nace

yaya matsayin Sallah ta? Zanci gaba da yi ne ko zan barta

har se nayi wanka?

Amsa: Malama ya wajaba ki yı sallah, saboda jinin da kike gani jinin

barı ne, Jinin barin cikin da bai kai Wata hudu ba, ba ya

daukar hukuncin jinin haihuwa, saboda ba'a busawa dan

tayin rai ba a lokacin, wannan ya sa ba zai hana sallah ba.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu zarewa5/3/2016

82. ZAN IYA WANKAN JANABA, BA TARE DA ALWALABA?

77

Page 78: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Tambaya:

Assalamu alaikum. tambayata Anan shine: Menene

hukuncin yin wankan janaba ba tare da yin alwala ba?

Amsa:

Ya halatta ayı wankan janaba ba tare da alwala ba, kamar

yadda ya zo a hadisin Ummu-salama, Saboda Annabi S.A.W

ya siffanta mata wankan janaba da cewa: "Ya ishe ki, ki zuba

ruwa sau uku akan kı sannan ki zuba ruwa a duka jikinki, in

kika yi haka, kin tsarkaka" kamar yadda Abu-dawud ya

rawaito, kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta:

251. A cikin wannan hadisin babu alwala, wannan sai ya

nuna wankan ya yi da waccar sifar da kika tambaya. Saidai

sifar da ta zo da alwala a hadisin Nana A'isha ita ce mafi

cika, kamar yadda malamai suka bayyana. Allah ne mafi

sani.

Dr. Jamilu Zarewa6/3/2016

83. MACE, ZA TA IYA YIN FITSARI A TSAYE?Tambaya:

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakaatuhu, Don

Allah malam mene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko

namiji a Musulunci?

Amsa:

Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da

Bukhari ya rawaito cewa: "Annabi S.a.w ya je jujin wasu

mutane sai ya yı fitsari a tsaye"kamar yadda Bukhari ya

rawaito a hadisi na 222. Tare da cewa duk hukuncin da ya zo

78

Page 79: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

dağa Annabi s.a w. yana hada mace da namiji, in ba'a samu

abin da ya kebance shi ba, Tabbas fitsarin mace a tsaye zai

jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda yanayin halittar

da Allah ya yı mata.

Yana daga cikin Ka'idojin sharia gabatar da wajibi akan abin

da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga mace, saidai

zai kai ga kunci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba

ta ingantuwa saida ita. Duk hadisan da suka zo cewa Annabi

ya hana yin fitsari a tsaye ba su inganta ba, sai hadisin Nana

A'isha wanda Hakim ya inganta, in da take cewa : "Duk

wanda ya ce muku Annabi s.a.w ya yi fitsari a tsaye kar ku

gaskata shi" kamar yadda Nasa'i ya rawaito a hadisi mai

lamba ta: 29.

Malamai suna cewa : za'a dau maganarta akan tana bada

labari ne, akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu

wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da ba koyaushe

take zama tare da shi ba, yana daga cikin Ka'idoji a wajan

malaman Usulul-fiqhi : Duk wanda ya tabbatar da abu za'a

gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda wanda

ya tabbatar yana da Karin ilimi na musamman wanda ya

buya ga wanda ya kore. Don neman Karin bayani duba :

Sharhu Assuyudy ala Sunani Annasa'I 1\26.Allah ne mafi

sani.

Dr Jamilu Zarewa8\3\2016

84. INA SON KARIN BAYANI A KAN SALLAR WALHA?Tambaya:

79

Page 80: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Asalamu Alaikum malam ya aiki malam, don Allah ya ka'idar

sallar walaha take ? Allah ya saka da Alheri

Amsa: To 'yar'uwa sallar walaha ba ta da wani adadin raka'o'i na

musamman, Za ki iya yın raka'a biyu ko hudu ko shida da

sallama uku, mafi yawan abin da aka rawaito daga Annabi

s.a.w. a sallar walaha shi ne raka'a takwas, kamar yadda ya

yi ranar bude Makka, Bukhari ya ambaci kissar a hadisi mai

lamba ta: 5806. Lokacin sallar walaha yana farawa daga

sanda rana ta fara zafi, kamar yadda hadisin Muslim mai

lamba ta: 748 ya tabbatar da hakan, har zuwa dab da

karkatar rana daga tsakiyar sama. Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Zarewa

9\3\2016

85. BABU HADISI INGANTACCE AKAN YAWAN KWANAKIN HAILA!

Tambaya:

Na karanta amsar da malam ya bada wadda ban fahimce

taba, Abisa T

tambayar da akayi mashi. Ta zuwan jini duk sati tare da

cewa taje asibiti Amman sunce saidai tayi hakuri in na

fahimci tambayar. Hukuncin matar da take da irin wannan

lalura shine : Zata bar salla a duk lokacin da jini yazo mata in

lokacin yin al'adattane ko da ya doge harfiye da kwanakin da

takeyi mutukar bewoce kwana(15) ba, Amman in ya woce

haka zatayi wanka tayi salla don haila ba ta wuce kwana(15).

Amsa:

80

Page 81: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Abin da abokina ya fada shi ne fatawar Malikiyya da

Shafi'iyya, saidai babu ko hadisi daya da ya tabbata akan

cewa : jinin haila ba ya wuce kwana sha biyar, duk hadisan

da suka zo akan haka ba su inganta ba, daga ciki akwai

hadisin da aka rawaito cewa: "An tambayi Annabi s.a.w

game da tawayar addinin mace, sai ya ce: "Daya daga

cikinsu zata zauna rabin rayuwarta ba ta sallah" Ibnul Jauzu

ya raunana shi a littafinsa Attahkik 1/263 haka Annawawy

shi ma ya ce: hadisin karya ne, kamar yadda ya zo a

AlMajmu''u 2\405, Ibnu Abdulhady shi ma ya raunana shi a

cikin Tankihu attahkiki1\414, Baihaki a cikin Ma'arifatu

assunan wal-athar,2/145 yana cewa: Na nemi hadisin da

sanadi a littattafan hadisi amma ban taba ganinsa ba, Haka

nan Hanafiyya sun tafi akan cewa: Jinin haila ba ya wuce

kwana goma, saidai duk hadisan da suka kafa hujja da su

babu ingantacce a ciki, Duba Al-ilal Al-mutanahiyah na Ibnu

Al-jauzy 2/382.

Zance mafi inganci shi ne haila ba ta da wasu kwanaki na

musamman, kamar yadda sheik Ibnu Uthaimin ya tabbatar

da haka a littafinsa na Dima'uddabi'iyya, tun da Allah da

manzonsa sun rataya hukunce-hukuncenta ne da

samuwarta, don haka duk inda aka samu jinin haila da

sifofinsa (baki, karni) hukuncinta yana tabbata, saidai idan

ya kasance mafi yawan rayuwa ko dukkanta, a lokacin ne zai

zama jinin cuta. Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa11\3\2016

81

Page 82: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

86. MIJINA YA MUTU, TUN KWANA (40), KO ME YA KAMATA NA YI?

Tambaya:

Asalamu Alaikum malam tambayata maitakaba bayan tayi

kwana Arba’in, in tayi wanka zata iya goga shuwa a

hammatarta?

AMSA:

To Yar'uwa ina rokon Allah ya jikan mijinki, akwai hukunce-

hukunce da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki:

1. Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba,

har sai ta gama iddarta, wacce take wata hudu da

kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara

take nuni zuwa hakan. 2. Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji

ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta:

2304, ya yi bayanin hakan. 3. Shari'a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar

yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar

da hakan,4. Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali

ba, kamar yadda hadisin Nasa'i mai lamba ta: 3565 ya

bayyana hakan. 5. An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo

a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304. 6. Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko

da rana ne ko da dare.7. Za ta iya yin Magana da mazan ba muharramanta ba,

idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya

murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul-ahzab ta hana

hakan.

82

Page 83: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

8. Babu wani launi na kaya na musamman da aka

shar'anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba

kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su.9. Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi

ba.10. Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har

ma za ta iya bude gashin kanta, idan duk

muharramanta ne.11. Ya haramta ga mai takaba ta yi aure, har sai ta

kammala iddarta wata hudu da kwana goma, kamar

yadda aya ta: 235 a suratul Bakara take nuni zuwa

hakan. Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa15/03/2016

87. INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINABA LAFIYA ?

Tambaya:

Slm, Dr. macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi,

sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon

tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake?

Amsa: To gaskiya abin yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma

bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin

manufofin aure, katange ma'aurata daga fadawa haramun,

kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.

Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar

da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda

iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma

bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa

83

Page 84: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

falalarsa. Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki

cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar

wannan sababin?

Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya

fita ne ta hanyar jin dadi. Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa.21/03/2016

88. MAI TAKABA, ZA TA IYA FITA AIKIN GWAMNATITambaya: Assalamualaikm mal inada tambaya mace ce mijnta ya

rasu koma ta kasance tana aikin gomnati shin zata iya fita a

lokacin da take takaba?

Amsa: Wa alaikum as salam, a zahirin maganar malamai, mai

takaba ba za ta je aikin gwamnati ba, tun da bai halatta mai

takaba ta fita ba sai lokacin tsananin lalura, aikin gwamnati

ba ko yaushe zai zama lalura ba, tun za'a iya ba ta hutu, in

har ta nema, In tana da yadda za ta cı abinci ya wajaba ta

amshi hutu, ko da babu albashi, saboda bin sharia shi ne

zaman lafiya, duk wanda ya kiyaye Allah, to shi ma zai

kiyaye shi, duk wanda ya yi hakuri Allah hakurkurtar da shi.

Amma idan ta rasa yadda za ta yi ta cı abinci sai ta hanyar

aikinta, to ya halatta ta yi da rana kawai, saboda Annabi

S.a.w ya halattawa matan shahidai a zamaninsa, zama a

gidan daya dağa cikinsu domin hira da debe kewa da rana,

lokacin da suka takuru da zaman kadaici, duk da ya wajabta

musu komawa gidansu in dare ya yi, Kamar yadda Baihaki ya

rawaito, wannan sai ya nuna lalura tana halattawa mai

84

Page 85: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

takaba fita da rana, kamar yadda Ibnu-khudaama ya ambata

a littafinsa na Mugni 8/130. Duk da cewa wasu malaman

Hadisin sun raunana hadisin Baihaki da ya gabata, saidai an

samu kwatankwacinsa daga maganar Abdullahi dan Mas' ud

da Abdullahi dan Umar Allah ya kara musu yarda, maganar

Sahabi hujja ce, in har ba'a samu wani sahabin ya saba maşa

ba, kamar yadda yake a ilimin Usulul-fiqh. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa22/3/2016

89. ZAN IYA KOMAWA WAJAN TSOHON MIJINA, IDANNA BIYU YA SAKE NI, KAFIN MU SADU?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Malamina. Fatan Alkhairi a gareka, da

fatan ka wuni lafiya cikin koshin lafiya. Malam dan ALLAH ina

da tambaya kamar haka: (Mutum ne ya saki matarsa har

saki (3) a lokuta daban-daban, to, sai wani bawan ALLAH

yazo ya aure, bayan ya aureta sai wata matsala ta shiga

tsakaninsu kuma ya saketa amma kuma ko sau daya bai

taba sadu da ita ba, to, yanzu Malam ko wancen tsohon mijin

nata zai iya mayar da ita, tun da gashi tayi aure amma

saduwace kawai ba'a yi da ita ba??? ALLAH ya kara taimakon

ka Malam.

Amsa:

Wa alaikum assalam, ina har ba su sadu ba, to bai halatta ta

auri wani ba, saboda lokacin da matar Rifa'ata ta auri wani

bayan mijinta ya sake ta, ta so ta rabu da mijinta na biyun,

ta koma wajan na farkon, kafin su sadu, Annabi s.a.w. ya

hanata, inda ya ce mata : "Dole sai kin dandana dadinsa, shi

85

Page 86: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ma ya dandana dadinki, kamar yadda Bukhari ya rawaito a

hadisi mai lamba ta:5372, wannan sai ya nuna cewa aya ta :

230 a Suratul Bakara, ba aure kawai take nufi ba, tana nufin

aure hade da saduwa su ne suke halatta mace ga mijinta na

farko, saboda aikin Annabi s.a.w. da maganarsa su ne suke

fassara Alqur'ani. Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa.27/3/2016

90. TA YAYA ZAN IYA GANE MUKTARIN SALLAH DA LALURINTA?

Tambaya: Assalamu alaika mal don Allah amin bayanin yadda ake gàne

yanayin muhktari da lalurin sallan Asuba da Maghrib?

Amsa: Wa alaikum assalam, Muktari da laluri, lokuta ne da Allah ya

rataya hukunce-hukuncen sallah akan şu, a na gane

muktarin sallar asuba idan alfijir na biyu ya keto, ana gane

lalurin sallar asuba idan gari ya yi fayau, ana gane muktarin

sallar azahar idan rana ta karkata daga tsakiyar sama, ana

gane lalurin sallar azahar idan inuwar mutum ta yi daidai da

tsawonsa, ana gane lokacin la'asar zababbe ya shiga idan

inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa, ana gane lalurinta

ya shiga idan inuwar mutum ta ninka tsawonsa, ana gane

muktarin sallar magriba, idan rana ta fadi, Muktarin sallar

Isha yana shiga idan ragowar Jan rana ya buya (shafaki)

Bayan dare ya raba lokaci ne na lalurin magriba da Isha.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

86

Page 87: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

4/04/2016

91. 'YAR KISHIYA ZA TA IYA GADONA ?

Tambaya : Assalam Dr barka da asubah, da fatan kuna lafiya, Allah ya

taimaka. mace ce ta rasu ta bar 'ya'ya maza biyu da mace

daya, da kuma 'yar kishiyar ta, shin 'yar kishiyar tana da

kaso, a cikin gadon? Allah ya saka da alkhairi.

Amsa: Wa alaikum assalam, 'yar kishiya ba ta çıkın magada, don

haka za'a bawa 'ya'yanta ne şu raba a tsakaninsu, duk namiji

ya dauki rabon mata biyu, Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa28/03/2016

92. MACE, ZA TA IYA YIN AURAN KASHEWUTA?

Tambaya:Assalamu Alaikum malam menene hukuncin wadanda sukayi

auran kisan wuta suka maida aurensu,kuma menene

hukuncin auren nasu?

Amsa:Wa alaikum as salam, Auran kisan wuta bai halatta ba.

Saboda Annabi (S.a.w) ya la'anci wanda ya yi da kuma

wanda aka yi saboda shi, kamar yadda Tirmizy ya rawaito

kuma ya inganta shi. Idan miji ya yi aure da niyyar halattawa

mijin baya, auran batacce ne, amma idan mace ce ta yı da

wannan niyyar, kuma mijin da ta aura bai sani ba, to auran

ya yi. Saboda ba dole ba ne mijin ya sake ta. Yana daga cikin

87

Page 88: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Ka'idojin sharia: Duk من ل فرقة بيده ل أثر في نيتتته wanda babu

saki a hannunsa, to niyyarsa ba ta da tasiri.

Allah ne mafi saniDr jamilu Zarewa.

29/3/2016

93. MATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA UNGUWA ?

Tambaya: Assalam malam muna san karin bayani akansa turare ga

mata sufita, wani malami yace wadda ba matar aure ba zata

iya sawa?

Amsa:

Wa alaikum assalam, To'yar'uwa ya haramta ga mace Baliga

ta sanya turare, ta fita unguwaa, saboda fadin Annabi SAW:

"Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to

ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, A

wani hadisin kuma yana cewa: "Duk matar da ta sanya

turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu. Nassoshin da

suka gabata suna haramta sanya turare ga mace

balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin

matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna

gamewarsu ga dukkan mata wadanda sharia ta hau kansu,

tun da ba'a samu abin da ya kebance wasu nau'i ba, sannan

kuma an haramta sanya turaren ne : saboda yana kaiwa

zuwa tada sha'awar Maza, wannan kuma baya bambanta

tsakanin matar aure da wacce ba ta yi ba. Allah ne mafi sani.

Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji

kamshi, in ta yi hakan za ta samu lada. haka ma budurwa, za

88

Page 89: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ta iya sanyawa a tsakanin 'yan'uwanta mata, ko gaban

muharramanta wadanda ta san ba za su yi sha'awarta ba.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa31/03/2016

94. IDAN NA KUSANCI MIJINA, YANA KYAMATATA,MENENE MAFITA ?

Tambaya:

Assalamu alaikum MALAM nice ina da miji a duk lokacin da

zan zo kusa da shi sai yace min barci yake ji, ai sharia ta

hana na dameshi, a haka zamu yi kusan wata ba abin da ya

shiga tsakanina da shi, Allah taimaki MALAM menene mafita?

Amsa: Wa alaikum assalam, Ki tambaye shi dalılin da yasa yake yin

hakan, zai iya yiwuwa kin bata masa rai ko kuma akwai Wata

matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata

lamura za su iya fitowa fili. Sharia bata halattawa namiji yaki

saduwa da matarsa ba da gangan, saboda nau'ine na

cutarwa, yana dağa cikin manufofin aure katange ma'aurata

daga kallon haram.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa26/03/2016

95. MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN KISHIYATA ?

Tambaya:

Assalamu alaikum Mun kasance mu biyu awajen mijinmu,

Sai ya kasance yar'uwata bata iya gamsar dashi, to ko ranar

girkinta yakan shigo ya tara dani da rana ko da daddare,

tambaya anan shi ne malam shi hakan ya halasta? Kuma

89

Page 90: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

idan na mishi magana ya daina zuwa baya ji, ba gidan mu

daya ba, Dan Allah hukuncin hakan da mafita?

Amsa: Wa alaikum assalam, Ya wajaba ya nemi izininta, tun da

hakkinta ne, in har ta sarayar ya halatta ya sadu da ke a

ranar kwananki da kwananta. Saboda lokacin da Nana

Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi S.a.w. ya sake ta, ta

dauki kwananta ta bawa Nana A'isha, kamar yadda Bukhari

ya rawaito. Bayan haka Annabi S.a.w. yana yin kwana dai-dai

a dakunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana Aisha yana

mata kwana biyu, Saudat kuwa ba ya kwana da ita, saboda

ta sarayar da hakkınta. Ya wajaba mai gida ya guji dukkan

abin da zai kawo matsala da fitintinu a tsakanin iyalansa,

adalci yana tabbatar da zaman lafiya. Allah ne mafi sani.

Dr jamilu zarewa.15\4\2016

96. ANA BINA RAMAKON AZUMI, AMMA INAKOKONTON YAWANSU ?

Tambaya:

Assalamu alaikum Mal. Mace ce ta sha Rabin azumi kuma

bayan azumin Ya wuce ta ranka Saidai ba duka ba yanzu

Tana so ta ida amma ta manta azumin Nawa tayi a baya

Tana ganin batayi rabi ba kuma tana ganin kamar tayi rabi

Amma ita ta manta DAN ALLAH MAL YA ZA TA YI??

Amsa: Wa alaikum assalam, za ta yi gini ne akan tabbas wajan

ramako, misali idan kına zaton ashirin suka rage miki ko

kuma ashirin da biyar, to sai ki rama ashirin da biyar (25),

90

Page 91: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

saboda in kin yi haka za ki fita daga kokwanto, kuma zai

zama tabbas kin rama abin da ake binki, ki rama abin da za

ki nutsu a zuciyarki kin rama. Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa.18/04/2016

97. INA SO NA SAN YADDA AKE ISTIBRA'I?Tambaya: Assalamu ahlaikum Don girman Allah ina da

Tambaya ina so na

san yadda ake istibra'i da kuma dokokin su? Nagode

Amsa: Wa alaikum assalam, ana yin istibra'i ne da jini daya a zance

mafi inganci, yana kasancewa ne ga matar da ta yi zina take

so ta tabbatar ciki bai shiga ba, kafin ta yi aure, kamar yadda

yake wajaba ga baiwar da mai gidanta ya sayar da ita bayan

ya take ta, kafin ubangidan ta na biyu ya fara saduwa da ita,

saboda kada a samu cakuduwar nasaba, matar da aka yi

mata fyade za ta yi istibra'i kafin ta yi aure. Allah ne mafi

sani

Dr Jamilu Zarewa.20/04/2016

98. BA'A IDDAR SAKI DA WATA UKU!Tambaya:

Assalamu Alaikum Malam ina da tambaya don Allah mace

ce tana shayarwa amma bata jini, sai mijinta ya sake ta, to

wai za ta kirga watannin ne na iddanta ko ya zata yi?

Amsa: Wa alaikum assalam, Idan aka saki mace tana shayarwa, ya

wajaba ta jira tsarki uku, ko da kuwa za ta yi shekara uku

91

Page 92: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

kafin ta gama, Ba'a idda da watanni uku sai ga wacce ba ta

fara haila ba, ko kuma wacce ta yanke kauna daga haila

saboda tsufa, kamar yadda aya ta: 4 a suratu Addalak ta

tabbatar da hakan. Allah ne mafi Sani.

Dr Jamilu Zarewa22/04/2016

99. MIJINA ZAI IYA SIYAN KWANAN KISHIYATA, DON YA KWANTA DA NI?

Tambaya:

Slm, ya halasta miji yasai kwanan kishiyanki ya biyata, don

ya kwana dake?

Amsa: Wa alaikum as salam, ban San dalilin da ya nuna ana

sayen kwana

ba, amma za'a iya nema mace ta sarayar da hakkinta na

kwanan,in har ta bayar ya bayu, tun da hakkinta ne, kamar

yadda Nana Sauda ta bawa Nana A'isha kwananta, saboda

tsananin son da ta ga Annabi s.a.w. yana Mata. Wannan yasa

Annabi s.a.w. yake kwana biyu a dakin Nana Aisha kamar

yadda ya tabbata a Bukhari, ragowar matansa bakwai kuma

yana musu kwana dai-dai, Nana Saudat kuwa ba ya kwana a

dakinta, bayan ta bawa Nana Aisha kwananta. Allah ne mafi

sani

Dr jamilu Zarewa23/4/2016

100. DUK MINTI BIYU SAI NA YI TUSA, YAYA SALLATA??

Tambaya:

92

Page 93: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Salamun'alaikum Malam Wai akwai sallah ga wanda in yana

sallah sai ya fitar da iskar tusa kuma duk sallah yake hakan

koda ace yayi kashi kafin yayi sallar, amma in har ya zo

sallah sai ta futo koda ace zayyi alwala sama da 10?

Amsa:

Wa alaikum assalam, akwai sallah akan shi, ba za ta taba

faduwa ba akansa, ya wajaba a gare shi ya yi alwala yayin

kowacce sallah, dağa nan duk abin da ya fito yana sallah ba

zai cutar da shi ba, tun da in aka ce ya sake alwala yayin

fitowar kowacce tusa ba zai iya ba, zai kuma shiga cikin

wahala, Sharia ba ta dorawa rai sai abin da za ta iya, kamar

yadda ayoyi da hadisai da yawa suka tabbatar da haka. Babu

takurawa da kunci a cikin Addinin musulunci kamar yadda

ayar karshe a suratul Hajji ta tabbatar da hakan. Don neman

Karin bayani duba: Alfawakihuddawany na Annafraawy

1\340.

Amma idan tusar ba'a mafi yawan lokuta take fitowa ba ya

wajaba ya sake alwala duk sanda ta fito, saboda sallah ba ta

ingantuwa saida alwala. Kula da wasuwasin abu ne mai

muhimmancin gaske, saboda da yawa Shaidan yake busa a

duburar dan'adam amma ba tusa ba ce, wanda ya ji haka, to

kar ya fita daga sallarsa, har sai ya ji iska ko kara ta fita,

kamar yada hadisin Bukhari ya tabbatar da hakan.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa24/04/2016

101. MACE ZATA IYA YANKE KITSONTA BAYANKAMMALA UMRA?

Tambaya:

93

Page 94: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Assalamu alaikum mlm inada tambaya don Allah in mutum

yayi umarah sai ya yanke gashinsa, amma na mace nake

nufi. Idan ta yi kitso zata iya kama jelar kitson daya ta yanke,

kuma kamar yaya za'a yanke gashin don Allah ina son

amsar dawuri Allah yataimaki mlm, yakara ma imani

Allahumma Ameeen.

Amsa: Wa alaikum assalam, za ta iya kama gargawadon gabar dan

yatsa sai ta yanke daga dukkan kitsonta. Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa28/04/2016

102. ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI?Tambaya:

Assalamu alaikum wa rahmatullah, Malam Barka da dare,

Malam ina tambaya ne dangane da wakilci a aikin hajji

(Anniyaabatu anil mayyit), mahaifina yana son yiwa wani

daga cikin makusantan shi da ya rasu; sai wani mutum

(malami) yake ce masa ai akwai addu'ar da ake yi (qul huwal

laahu sau wani adadi dss) wadda tafi wannan aikin hajjin da

za ai masa!! To dan Allah Malam yana so ne yaji shin hakan

ya tabbata, kuma dai-dai ne? ko akwai wani Malami da ya

fadi hakan?

Amsa: Wa alaikum assalam, Ba haka ba ne, wannan

maganar ba ta da asali,

Yiwa wani hajji ya tabbata a hadisai, wani mutum ya tambayi

Annabi (s.a.w) cewa: "Babana ya mutu bai yi hajj ba, zan iya

yi masa? sai Annabi (s.a.w) ya ce yaya kake gani Idan da

94

Page 95: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

bashi ya bari za ka biya masa? sai yace E,sai Annabi (s.a.w)

yace to ai bashin Allah shi ya fi cancanta a biya, don haka ka

yi masa hajj, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya rawaito a

Muntaka hadisi mai lamba ta:1797, da kuma Darakudni.

Sannan Kathamiyya ta tambayi a Annabi (s.a.w) cewa: Hajji

ya riski babanta ya tsufa zata iyayi masa? sai Yace E, kamar

yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta;1756.

Malaman fiqhu sun kafa hujja da Wadannan hadisan

tabbatattu kan halacci ko wajabcin yiwa mamaci ko Wanda

bazai iya ba aikin hajji Idan yana da halı. Hajji ibada ce mai

zaman kanta,kuma daya daga cikin ginshikan musulunci

babu yadda za'a yi wata addu'a ta zauna a makwafinta.

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu Zarewa.

29\4\2016

103. ABUBUWAN DA ZA'A IYA FASA AURE SABODA SU

Tambaya: Assalamu alaikum, da fatan mallamai da dukkan 'yan uwa

sun tashi lafiya, Ina rokon Mallam bayani kan hukuncin

Wanda aka sanyama ranar aure kafin lokacin yace ya fasa.

Allah ya karama mallam lafiya da basira. Ameen

Amsa: Wa alaikum assalam,in har akwai hujjar da sharia ta yadda

da ita, ba shi da laifi in ya fasa,kamar ya bayyana budurwar

ta sa ba ta da tarbiyya ko mazinaciya ce, ko kuma ba ta son

shi, ko tana da cutar da za ta hana a sadu da ita,kamar

toshewar farji ko hadewarsa da dubura, ko ya zama şu duka

suna da jinin da in sun hadu za su haifi sikila, yana iya fasa

95

Page 96: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

auren idan ya zama ba shi da halin da zai iya ciyar da ita,ko

kuma likita ya tabbatar maşa ba shi da mazakutar da zai iya

saduwa da mace,haka ma idan ya ji ya tsaneta.

Dukkan abin da ake iya saki saboda shi, ana iya fasa aure ın

aka same shi, an shar'anta saki ne saboda tunkude cuta

daga ma'aurata ko daya daga cikinsu, yana daga cikin

ka'idojin sharia da kuma masu hankali: Tunkude cuta kafin ta

auku ya fi sauki fiye da kokarin kautar da ita bayan ta faru.

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu Zarewa

3/5/2016

104. ZAN IYA RIKE HANNUN BUDURWATA?Tambaya:

Malam Ya Hukunchin Wanda ya rike Hannun wata mace

Kuma ba matarsa ba ce, amma Budurwarsa ce?

Amsa: Wa alaikumus salam, Bai hallata mutum ya rike hannun

wacce ba muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya

kasance ba ya Musafaha (hada hannu) da mata yayin da zai

musu mubaya'a, yana yi musu mubaya'a ne da Magana,

kamar yadda ya tabbata a hadisi.

Taba hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga Zina

saboda yana tayar da sha'awa, Allah Madaukaki ya haramta

kusantar zina a aya ta 32 a suratul Isra'i, Zina tana daga

cikin manyan zunuban da babu kamar su bayan shirka da

Allah. Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai kiyaye

96

Page 97: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

shi, wanda ya bı son zuciyarsa, to Allah yana nan a

madakata.

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu Zarewa

05/05/2016.

105. YAUSHE ZAN FARA SADUWA DA AMARYAR DA NA AURETA TANA KARAMA?

Tambaya: Assalamu alaikum, Ina fatar Allah ya kara ma

malam Ikhlasi.

Ya halatta idan mutum ya auri mace karama wadda bata fara

jini ba ya sadu da ita? Kokuwa rainonta zaiyi?

Amsa: Wa alaikum assalam, Malamai sun cimma daidaito game da

halaccin aurar 'yar karamar yarinya, saboda aya ta hudu a

suratu Addalak ta bada labarin yadda karamar yarınya za ta

yi idda, hakan sai ya nuna ingancin yi mata aure kafin ta

balaga, sannan Annabi (s.a.w) ya auri nana Aisha tana 'yar

shekara shida.

Malamai sun yi sabani game da lokacin da za'a fara saduwa

da ita, bayan an yi auren,akwai wadanda suka tafi akan

cewa dole sai ta balaga za'a mikata ga mijinta. Wasu

malaman sun kayyade shi da shekara (9) saboda Annabi

(s.a.w) ya tare da nana A'isha ne bayan ta kai shekaru tara.

Zancen da ya fi zama daidai shi ne: za'a duba yanayin jikin

yarinyar, in har za'a iya jima'i da ita ba ta cutu ba,za'a iya

mikata ga mijinta, ko da shekarunta kadan ne, saboda mata

suna bambanta wajan girman jiki gwargwadon wurin da suke

rayuwa, da kuma irin abincin da suke ci, sannan sharia ba ta

97

Page 98: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

iyakance lokacin da ake fara jima'i da mace ba. Don neman

karin bayani duba: AlMugni 27/77 da kuma Alminhaj na

Nawawy 9/206.

Allah ne mafi saniDr Jamilu Zarewa.

09\5\2016

106. TA YI AURE RANAR DA TA GAMA TAKABA?Tambaya:

Assalamualaikum malam meye matsayin auren da aka daura

randa mace tagama takaba ?

Amsa:-

Wa alaikum assalam, in har kwanakin iddar sun cika auran

ya yi, saidai Allah ya haramta neman aure cikin idda, in har

ya zama an fara neman auran ne tun kafin ta kammala

takaba, to tabbas an sabawa aya ta (235) a suratul Bakara,

saba dokar Allah yana jawo matsaloli. Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa16/05/2016

107. YA NEMI AURE A CIKIN IDDA?Tambaya:

Assalamu Alaikum, Malam tambaya ne nakeso a taimaka a

amsa mun akan sha'anin aure. Malam mace ne tana zaune

da mijinta sae ya kasance zaman sun babu dadi, kullum a

cikin matsaloli iri-iri har ya kai ga takoma gidan iyayenta.

Iyayenta sun matsa mata se da ta tilasta mijinta ya saketa,

saboda suna da wani manufa akan idon ya saketa tsohon

saurayinta se ya aureta. Bayan ta matsawa mijinta akan lalle

98

Page 99: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ya saketa se mijin nata ya amince akan zai kawo mata

takardan sakin. Mallam a ranan da sukayi zai kawo mata

takardan sakin, kawai sae ta samu tsohon saurayinta akan ta

naso da zaran ta gama idda se ya aureta. Mallam menene

hukuncin wannan auren idon tagama idda ya aureta?

Na taba ji ance duk wanda ya nemi mace tana idda babu

aure a tsakanin su har abada, Mallam don Allah ka taimaka

mana da Karin bayani ?.

Amsa:Wa alaikum assalam, in mutum ya nemi mace tana idda ya

aikata haramun, kamar yadda aya ta: (235) a suratul Bakara

ta tabbatar da hakan,saidai in an yi auran bayan ta gama

idda auran ya inganta, amma an aikata zunubin nema.

Malikiyya suna haramta mace ga mutum har abada in ya

aure ta cikin idda, ba in ya neme ta ba. Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa.19/5/2016.

108. ZAN IYA AURAN 'YAR KANWAR MATATA?Tambaya:

Assalamu alaikum Malam, Ya halatta mutum ya auri yar

qanwar matarsa?

Amsa: Wa alaikum assalam, ya halatta ya aure ta, bayan ya saki

matarsa, amma bai halatta ya hada su ba saboda innarta ce,

Annabi s.a.w. yana cewa: "Ba'a a hada mace da goggonta,

ba'a hada mace da innarta a auratayya, saboda in kuka yi

haka, za ku lallata zumunci ku" kamar yadda ibnu Hibban ya

rawaito.Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

99

Page 100: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

20\5\2016

109. NA YIWA MIJINA KUL'I, KO AKWAI DAMAR KOME?

Tambaya:

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, Dr muna

maka fatan alkhairi, tambayata ita ce auren da akai hul'i

yana halatta mijin ya maida matan, in kuma zai maidata,

shin zai sake biyan sadaki koko har abada ba suda aure?

Amsa:

Wa alaikum assalam, auran da mace ta fanshi kanta, daga

wajan mijinta yana halatta ta koma wajan shi bayan an sake

sabon aure da sadaki, ba sharadi ba ne sai ta auri wani kafin

a sake daura aure. Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa23/05/2016.

110. DAN ZINA ZAI GAJI MAHAIFIYARSA?Tambaya:

Assalamu alaykum. Malam don Allah Malam in nada

tanbaya, Malam mace ce tayi ciki ba tare da aure ba, ta

haihu kuma tana da kudi sai Allah ya mata rasuwa toh

malam yaron zai ci gadonta?

Amsa:

Wa alaikum assalam, idan mace ta yi cikin shege kuma ta

haifi Da, daga baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta,

saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta :

10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado, Dan zina kuma yana

cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.

100

Page 101: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi yawancin

malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne.Don neman karin

bayani duba : Sunanu Attirmizy hadisi mai lamba ta: 2113 da

kuma Tabyinul haka'ik 6\214.

Allah ne mafi saniDr. Jamilu Yusuf Zarewa

25\5\2016

111. IDDA TANA FARAWA NE, BAYAN AN YI SAKI!Tambaya: Aslm alkm, malam Mace ce ta samu matsala da mijinta har

sukayi shekara daya bata gidansa sai daga baya yace ya

saketa, shin zatayi iddah ne ko kuma a'a?

Amsa: Wa alaikum assalam, matar da aka saki bayan jimawa da

samun matsalar aure, iddarta za ta fara ne daga lokacin da

aka sake ta, Allah yana cewa a cikin suratul Bakara " Kuma

matan da aka saka za su zauna tsawon tsarki uku, kubutar

mahaifa ba ita ce manufar idda ba kawai, tunanin yiwuwar

daidaitawa yana daga cikin hikimomin idda, idan saki daya

ne ko biyu, kamar yadda aya ta farko a suratu Addalak ta yi

nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu Zarewa.

27/5/2016

112. ZA KA IYA AURAN MACE BAYAN KA SAKI BABARTA! Tambaya:

Malam mutun ne ya auri mace yana tsammanin budurwace

mai kananan shekaru, bayan sun tare sai ya gane cewa ba

101

Page 102: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

karamar yarinya bace tana da shekaru masu yawa, Don haka

ba tare da sun yi saduwa na aure oay a saketa. Bayan haka

tafiya ta oay aoi zuwa wani gari inda acan yasami yarinya

mai irin shekarun da yakeso sai sukayi aure. Bayan auren sai

ya zaman wacce ya auran ‘ yar wancan mata oay a sakane.

To anan Auren ya halatta ko kuma bai halatta ba a bisa ayoyi

ko kuma Hadisai na Annabi (S.A.W)?

Amsa:

Wa alaikum assalam, idan mutum ya auri mace sai ya sake

ta kafin su sadu, ya halatta ya auri ‘yarta kamar yadda aya

ta: 23 a suratun Nisa’I da kuma hadisin da Tirmizi ya rawaito

suka tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa.5/6/2016

113. INA SO NA SAN SIFFOFIN JININ HAILA?Tambaya: Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don

Allah Tambaya gare ni Kan wani ruwa ke fitomin amma

kuma ba jini bane ina ganinsa kasa kasa babu wari ko qarni

tare dashi ina ganinsa idan nayi Azumi ko nayi aiki sosaise

marata tayi ciwo shine yake fitomin. Yaya Azumina da

sallahta take, shin zan cigaba da yinsu? sannan yana fitomin

wajan qarfe 3 na rana ne.

Amsa:Wa alaikum assalam, mutukar ba jini bane, kuma ba baki ba

ne, ba shi da karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi

kyau ki je wajan likita don ya duba lafiyarki, saboda abin da

102

Page 103: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da ya rasa daya

daga cikin siffofinsa. Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa7 Ramadan, 1437H (12/06/2016).

114. MACE ZA TA IYA YIN I'ITIKAFI?Tambaya:

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh, malam

menene hukuncin ittikafin mata a musulunchi?

Amsa: Wa alaikum asssalam, ya halatta mace ta yi i'itikafi, saboda

matayan Annabi s.a.w sun yi I'itikafi kamar yadda ya zo a

sahihil Bukhari. Yana daga cikin ka'idoji a usulul fiqhi duk

hukuncin da ya zo a sharia yana hade mata da maza, sai

idan an samu dalilin da ya kebance maza kawai. I'itikafi

ibada ce tabbatacciya a musulunci wacce Annabi s.a.w. ya

aikata ta saboda neman kusanci da Allah a watan

Ramdhana, babu banbanci tsakanin mace da namiji wajan

koyi da Annabi s.a.w a wannan ibadar, saidai kar matar aure

ta fita sai ta nemi iznin mijinta. Allah ne mafi sani.

Dr jamilu Zarewa

115.ZAN IYA BIYAYYA GA MIJINA WAJAN YIN

KULUMBOTO?

Tambaya: Assalamu alaikum, Mallam mijina ne ya bani nama in dafa

masa amma ko wani yanka akwai alura a jiki sannan da

ruwan rubutu na dafa masa. Mallam naji tsoro kuma in banyi

103

Page 104: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ba zai kawo matsala tsakanin mu. Toh mallam yaya hukuncin

wannan abun?

AMSA: Wa alaikum assalam, ina ba ki shawara ki tambaye

shi, In har kin gano sihiri ne aka yi ya halatta ki ki dafawa, ko

da kuwa zai sake ki, saboda sihiri kafurci ne. Biyayya ga miji

dole ce kamar yadda hadisai da ayoyi suka tabbatar, saidai

babu biyayya ga abin halitta wajan sabawa mahalicci, kamar

yadda ayoyi a suratul Ankabuti da Lukman suka tabbatar da

hakan.

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu Yusuf Zarewa.

26 Ramadan, 1437H

116. YA YI BUDA BAKI DA JIMA'I DA MATARSA?Tambaya:

Aslaam alaykum malam barka da warhaka da fatar kana

lapia. Malam

minene hukuncin Wanda yayi azumi amma bai yi buda baki

ba, ma'ana bai sha ruwa bayan ladan ya kira sallah. Sai yayi

jima'i da matarsa, Ya azuminsa?

Amsa:Wa alaikum assalam, Azuminsa ya yi daidai, mutukar ya

sadu da ita ne bayan rana ta fadi. Annabi s.a.w ya yi umarni

ayi buda baki da dabino ga wanda ya samu dama, in ba hali

kuma ayi da ruwa kamar yadda ya tabbata a hadisai, Yin

buda baki da dabino ko ruwa shi ne sunna, saidai wanda ya

fara da jima'i azuminsa ya inganta, tun da Allah ya halatta

masa jima'i a daidai wannan lokacin kamar yadda aya ta:

187 a suratul Bakara ta nuna hakan.

104

Page 105: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Allah ne mafi saniDr Jamilu Zarewa.

117. ALAMOMIN DAUKEWAR JININ HAILA!Tambaya:Assalamu alaikum. Allah ya kara Ma Mallam Basira. Malam

Tambaya ta akan jinin haila ne. Malam an ce alaman da ake

gane karshen haila shi ne idan jinin ya canza kala zuwa

ruwan kasa. Na ga alaman hakan Se nayi wankan tsarki

Bayan haka Se kuma ya cigaba da zuba na kwana biyu

Malam tsarkin nawa yayi? Yaya matsayin sallah da azumi?

Nagode.

Amsa:

To 'yar'uwa abin da na sani daga malaman fiqhu shi ne: Ana

gane daukewar jinin haila ne ta hanyoyi guda biyu:

1- Kekasar kasanki ; Ta yadda mace za ta ga gabanta ya

bushe ko kuma tsumma ko always din da ta tare jinin

da shi.2- Fitowar farin ruwa bayan daukar lokaci ana haila.

Idan jininki ya koma ruwan kasa kafin ki ga daya daga cikin

wadannan alamomi guda biyu, to ba ki gama haila ba, kuma

ba za ki dauki hukuncin masu tsarki ba, don haka azuminki

da sallarki ba su yi ba. Idan kika ga ruwa mai kama da kasa

bayan daukewar jinin haila, to ba zai cutar da tsarkin da kika

samu ba, kamar yadda hadisin Bukhari daga Ummu Addiya

ya tabbatar da hakan. Don neman karin bayani duba:

Addima'uddabi'iyya shafi na: 14.

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu zarewa.

105

Page 106: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

10/7/2016

118. YADDA AKE SADUWA DA MAI CIKI?Tambaya:

Malam na kan ji wasu mutane na fadar cewa ba ya halatta

idan matar mutum tana da juna biyu ya yi jima'i da ita har

sai ta haihu meye gaskiyar maganar?

Amsa:To dan'uwa ya halatta a sadu damace lokacin da take da ciki,

saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada

ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud : 1847

Ibnul kayim yana cewa :"Wannan hadisi yana nuna cewa ciki

yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi

tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi

da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta

ruwa" Tahzibussunan 1\193 .

Masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga hawa kan

matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho

yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda

kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron .

Sannan yawanci mata ba su cika son yawan saduwa ba idan

cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a

karanta saduwa a wadannan lokutan.

Allah ne ma fi sani .Dr. Jamilu Zarewa

13-7-2017

106

Page 107: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

119. MACE ZA TA IYA YIN ALKALANCI?Tanbaya:Assalamun alaykum Warahmatullahi wabarakatuhu bayan

sallama irin ta musulunci malam inayi maka fatan alheri

Allah yasa kana cikin koshin lafiya. Tanbayata malam ya

halatta mace ta yi alkalanci a musulunci, Allah yakarawa

malam lafiya.

Amsa:Wa alaikum assalam, a wajan mafi yawan malamai mace bai

halatta ta yi alkalanci ba, saboda hadisin Abu-bakrata wanda

Annabi (s.aw) yake cewa: "Duk mutanen da suka jibintawa

mace lamuransu ba za su rabauta ba" kamar yanda Bukhari

ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4425.

Alkalanci yana bukatar nutsuwa da daidaiton yanayi, wannan

yasa Annabi (s.a.w) ya hana wanda yake cikin fushi ya yi

alkalanci, kamar yadda Muslum ya rawaito, mace kuma idan

ta fara jinin haila takan fita daga daidaito, ta yi abin da bai

dace ba, wannan yake nuna rashin dacewarta da wannan

aiki na Annabawa da manzanni.

Allah ne mafi sani.Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

13/07/2016120. MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE?

Tambaya:

Assalamu alaikum wa rahamatullahi wabarakaatuhu: Miji ne

ya je saduwa da matar sa sai ya kuskure ya saka mata a

dubura shin mene ne hukuncinsa?

Amsa:

107

Page 108: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Wa alaikumus salam wa rahamatullahi wa barakaatuhu, In

har da kuskure ya saka mata a dubura, sai ya yi maza ya

zare, mutukar ya cire daga zarar ya ji ba wurin ba ne Allah

ba zai kama shi da laifin hakan ba.

A karshen suratul Bakara "Ya ubangijinmu karka ka kamamu

in mun manta ko munyi kuskure" Muslim ya rawaito hadisi

cewa: Allah ya zartarda hakan. Ibnu-majah ya rawaito hadisi,

Annabi s.a.w. yana cewa: "Allah ya yafewa al'umata abin da

suka aikata cikin kuskure". Cigaba da jin dadi a wurin bayan

gano kuskuren, yana daga cikin zunubai. Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa11 Shawwal, 1437 (16/07/2016).

121.MA'AURATA ZASU IYA KALLON TSIRAICIN JUNANSU?

Tambaya:

Assalamu alaikum mallam menene matsayin kallon tsaraicin

ma’aurata?

Amsa:

Wa'alaykumussalam. Ya halatta ma'aurata su kalli tsaraicinjunansu, Saboda Annabi s.a.w. yana wankan janaba damatansa, kamar yadda hadisai suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa26/09 /2016

108

Page 109: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

122. MEYASA AKA BAMBANTA NAMIJI DA MACE A WAJAN RABON GADO?

Tambaya: Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke

kokarin ganin an baiwa mace kason da aka bawa namiji

wajen rabon gado?

Amsa:

Wa'alaikum assalam, Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya

fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin haka,

saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar.

Allah da kansa ya raba gado bai wakilta wani don ya raba ba,

ya bawa kowa hakkinsa gwargwadon kusancinsa da mamaci

da kuma masalahar da Allah ya duba, wacce ya fi kowa

saninta.

Daga cikin hikimomin da suka sanya shariar Musulunci ta

bambanta tsakanin mace da namiji a rabon gado shi ne:

kasancewar hidimar namiji ta fi ta mace, yawanci mace idan

tana karama tana karkashin kulawar mahaifinta, idan kuma

ta yi aure tana komawa cikin kulawar mijinta.

Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya

sabawa ayoyin rabon gado a cikin suratun Nisa'i aya:14,

kamar yadda ya yi alkawarin Aljanna mai koramu ga wanda

ya bi rabon da ya yi a cikin aya ta:13 a waccar Surat. Duk

Wanda ya kiyaye dokokin Allah tabbas zai kiyaye shi, Wanda

ya sabawa Allah, to yana nan a madakata, kuma mabuwayi

ne mai tsananin karfi kamar yadda ayoyin Alqur'ani masu

yawa suka tabbatar. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

109

Page 110: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

05/10/2016

123. SHIN SUNAN RUMAISA'U YANA DA ASALI?Tambaya:

Assalamu alaykum Malam menene asalin sunan Rumaisa ko

Rumassa'u kuma a zamanin Annabi akwai mai sunan in

akwai a bani tarihin ta?

Amsa: Wa alaikum assalam, Rumaisa'u suna ne na daya daga cikin

sahabbai mata, ita ce ta haifi Anas Dan Malik hadimin Annabi

(S.A.W) ita ce ta kai shi wajan Manzon Allah don ya dinga

masa hidima, ta auri Abu-Dalha, sahararren sahabi mutumin

Madina, an fi saninta da sunan Ummu-sulaim. Tana daga

cikin mataye masu hikima, akwai mahaddatan Alqu'ani da

yawa da suka fito daga tsatsonta. Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Zarewa 11/10/2016

124. ZAN IYA AURAN WANDA YAKE DAUKE DA KWAYAR SIKILA?

Tambaya: Assalamu Alaykum, don Allah ya halatta yahukuncin auran mace da genotype dinku daya da ita, AS AS,ya halatta; sannan yana da fa'ida ko babu? Don Allah atambaya min malamai, na gode.

Amsa: Wa alaikum Assalam,Yana daga cikin ka'idojin sharia

tunkude cuta gwargwadon iko. Ilimin likitanci na zamani ya

tabbatar da cewa: idan AS da AS suka hadu za su iya haifar

Sikila (1) a cikin duk yara hudu ko biyar da za su Haifa.

A mafi yawan lokuta musamman a kasashen da talauci ya yi

musu katuutu, Sikila yana rayuwa ne cikin wahala, kuma

110

Page 111: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

iyayansa ma a wahalce, Saboda raunin jininsu Wanda yake

haddasa musu ciwon wasu daga cikin gabobinsu.

Zai yi kyau ma'aurata su yi gwaji kafin aure, in har dukkansu

suna dauke da kwayar Sikila (AS) su hakura da yin aure tare,

tun da za su haifi yaron da zai rayu a wahale, da rashin

Walwala gashi kuma addinin musulunci ya yi nufin sauki da

jin dadi ga al'uma. Dukkan wani abu ba ya faruwa sai da

kaddara, saidai riko da sababi abu ne da sharia ta tabbatar,

kuma ayoyi da yawa suka yi bayaninsa. Wanda yake (AS)

idan ya auri (AA) za su haifi 'ya'ya lafiyayyu da iznin Allah,

wannan sai ya nuna abin yana da yalwa.

Allah ne mafi SaniDr. Jamilu Zarewa

12/10/2016

125. MIJINA YA SADU DA NI, KAFIN NA YI WANKANHAILA?

Tambaya: Assalamu alaykum, Malam inada tambaya, malam mi ar hukuncin mace taqare haila ba tayi wanka ba mijin ta ya sadu da ita? Amsa: Wa alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shi ne:

ta jira sai ta yi wanka kafin su sadu, kamar yadda suka

fahimta a aya ta 222 suratul Bakara, amma Abu-hanifa yana

ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar da

yankewar jinin haila kawai. Riko da mazhabar farko shi ne ya

fi saboda Allah ya kira haila da kazanta. Babu wata kaffara

ga wanda ya sadu da matarsa kafin ta yi wanka bayan

yankewar jinin haila. Allah ne mafi sani:

Dr Jamilu Zarewa

111

Page 112: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

2/11/2016

126. HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA

NI.

Tambaya:

Assalamu alaykum, Malam ina da tambaya,mace ce bayan

mijinta ya sadu da ita, kafin ta yi wanka Sai jini ya xo mata

ya xa ta yi wanka, shin gabadai zatayi niyya ko kuma

wannan na biyun xa tayi?

Amsa: Wa alaikum assalam, za ta jira in ta samu tsarkin haila sai ta

yi wanka daya kawai. Yana daga cikin ka'idojin SHARIA Idan

ibadoji guda biyu suka hadu, kuma manufarsu ta zama guda

daya, sannan za'a iya hada su a lokaci guda, to sai daya ta

shiga cikin dayar. Wannan yasa mai janabar da jinin haila ya

same ta kafin ta yi wanka, za ta wadatu da wankan karshe,

saboda saukin musulunci da kuma daukewa jama'a abin da

zai kuntata musu, kamar yadda aya ta karshe a suratul Hajj

ta tabbatar. Allah ne mafi Sani

Dr Jamilu Zarewa11/09/2016

127.TARON SUNA GA MATA HALAL NE? Tambaya:

Assalamu Alaikum, Malam don Allah menene hukuncin taron

bikin suna a Musulunci ?

Amsa: Wa alaikum assalam, A zahiri taron sunan da mata suke yi

al'ada ne, tun da mata ba sa yinsa da nufin samun lada ko

112

Page 113: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

karawa abin da aka haifa albarka. Mata suna yinsa ne don

taya juna farin ciki, da kuma nuna annashuwa saboda

karuwar da aka samu, wannan yasa haramta shi yake

bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amalolin mutane a

bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wadda take

taron suna ba tare da ta riya cewa ibada ba ce hana ta ko

bidi'antar da taron yana da wuya, tunda bamu da dalilin

SHARIA daya haramta. Idan a cikin taron aka samu bidi'o'i ko

kuma ayyukan da Allah ya haramta kamar fito da tsaraici, ko

zancen da Allah ya hana, hakan zai iya zamar da shi

haramun, saboda yana daga cikin sharudan lura da al'ada

kar ta zama da sabawa nassoshin SHARIA, ko kuma ka'idojin

da malaman musulunci suka cimma daidaito akan su, kamar

yadda malaman Usul da na Kawa'idul Fiqhiyya suka ambata.

Allah ne mafi sani Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

7/11/2016

128. ZAN IYA AURAN WANDA IYAYANSA BA MUSULMI BA?Tambaya:

Assalamu alaikum, Dr ya halatta mace ta auri wani wanda

Baban shi ba musulmi ba ne?, amma Mahaifiyar shi musulma

ce?

Amsa:

Wa alaikumus salam, Ya hallata mana ko da kuwa duka

iyayansa arna ne. Babban abin lura a wajan aure shi ne

addinin Wanda ya zo neman aure, saboda fadin Annabi,

sallallahu alaihi wa sallama: "Idan Wanda kuka yarda da

addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa". Tirmizi113

Page 114: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1084, kuma Albani ya

kyautata.

In kika lura za ki ga hadisin ya yi magana ne akan mutumin

ba iyayansa ba. Akwai sahabban Annabi, sallallahu alaihi wa

sallama, da yawa wadanda iyayensu ba musulmai ba ne,

amma wannan bai hana a aura musu 'ya'ya ba, irinsu

Sayyadina Aliyu dan Abu-Dalib da Abu-Ubaidah da saurasu.

Mahaifin sayyidina Aliyu Abu-dalib bai musulunta ba, Amma

kuma an aura masa shugaban Matan Aljanna Nana Fadima,

Allah ya kara yarda ga mata da mijin. Allah ne mafi Sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa12/11/2016

129. KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA!Tambaya: Assalamu alaikum Mal dan Allah ga tambaya nan Nice nai

aure na rabu da mijina, wato ya bani takardan saki, kafin ya

bani wannan takardar,mun samu matsala na bar gidanshi

tsawon shekara daya da wata tara,kuma Daman tsawon

zaman mu tare shekara bakwai ban taba samun ciki ba, yaya

iddata zata kasance?

Amsa: Wa alaikum assalam, Za ki jira tsarki uku, tun da kun taba

kwanciyar aure kamar yadda aya ta 228 a Suratul Bakara ta

tabbatar da hakan.

Hukunce-hukuncen Saki suna farawa ne daga lokacin da aka

yi saki, ba daga sanda aka samu hatsaniya ba. Allah ya

shar'anta idda saboda manufofi da yawa daga ciki akwai:

bawa miji damar kome Idan saki daya ne ko biyu, ta yiwu

wani daga cikin ma'aurata ya yi nadama, Tare da cewa

114

Page 115: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

babban makasudin shi ne tabbatar da kubutar mahaifa,

Amma ba shi kadai ba ne.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa25/11/2016

130. HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA

Tambaya: Assalamu Alaikum! Mallam ina tambaya idan mutum yasadu da matarsa tana haila me ya kamata yayi? kuma inaneman cikekken bayani mallam.Amsa: Wa alaikum assalam, Wanda ya sadu da matarsa tana haila,

ya wajaba ya yi istigfari saboda ya aikata abin da Allah ya

hana a aya ta: 222 a suratul Bakara, Wannan ita ce maganar

mafi yawan malamai kamar yadda Ibnu Rushd ya fada a

Bidayatul mujtahid. Hadisin da ya zo na cewa: (Wanda ya

sadu da matarsa tana haila ya yi sadaka da rabin dinare) bai

inganta ba, wannan yasa ba za'a iya gina hukunci akansa ba.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa27/11/2016

131.MAGANIN ZAFIN NAKUDA?

Tambaya: Assalamu alaikum, Don Allah Malam a taimaka mana da

addu'ar nakuda Don muna hanya ko yau ko gobe Allahu a

'alam. Allah yasa kawa Malam da gidan aljannatul firdausi.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Ban san wata addu'a ta musamman ba

wacce Mai nakuda za ta karanta, amma za ta iya karanta

addu'o'in da suka tabbata a Sharia ana karantawa saboda

tunkude tsanani kamar:

115

Page 116: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

اللهم ل سهل إل ما جعلته سهل وأنت -1

.تجعل الحزن إذا شئت سهل

ل إله إل أنت سبحانك إني كنت من .2

.الظالمين

.حسبنا الله ونعم الوكيل .3

Allah ne mafi sani. Dr Jamilu Yusuf Zarewa

4/12/2016.

132. YA TSOTSI NONON BUDUWARSA, KO ZASU IYA AURE?

Tambaya: Assalamu alaykum. tambaya malam saurayi da

budurwane shaidan ya shiga tsakaninsu har ya kai ga

saurayin ya tsotsi qirjin budirwan har saida ruwa ya fito.

Hakan yafaru ba so dayaba ba biyu ba amma bata taba

ganin ruwanba sai ranar. To mallam yaya hukuncin aurensu,

ya halatta suyi auren? Kuma minene hukuncin shan Ruwan

da yayi

Amsa:

Wa'alaykumussalam, To dan'uwa wannan abin da suka aikata

mummuna ne, Tun da Allah ya haramta taba jikin matar da

ba ka aura ba, kuma kofa ce da za ta kai zuwa zina, idan

mutum ya tsotsi nonan mace bayan ya girma Amma babu

ruwa a ciki, wannan ba zai haramta musu aure ba, amma

idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan hakan

zuwa maganganu guda biyu :

1. Ya halatta su angunce, saboda kasancewar nonon da yake

haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika

shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da take

116

Page 117: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa” ,

Bukhari lamba ta : 5102, ma’ana lokacin da ba zai iya

wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma

wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi

tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi

yawan malamai.

2. Yana haramta aure, saboda ko da yaushe mutum ya sha

nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.a.w.

ya umarci matar Abu- huzaifa da ta shayar da Salim, don ta

haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi

mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya

girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono

to zai yi tasiri wajan haramcin aure.

Zancen da ya fi karfi shi ne nonon da mutum ya sha bayan

ya girma ba ya haramta aure a tsakaninsa da matar da ta ba

shi.

Don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67.

Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas zai kiyaye shi,

Wanda ya saba masa zai same shi a madakata.

Allah ne mafi sani.Dr Jamilu Zarewa

26/12/2016

133. INA DA SHEKARU (28), WACCE MACE YA KAMATA

NA AURA?

Tambaya: Assalamu alaikum, dafatan Malam yana cikin

qoshin lfy Allah sa haka amin. Malam inaneman shawara,

Wace mace yakamata na aura amatsayina na dan shekara

117

Page 118: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ashirin da takwas 28-29. yar shekara nawa tafi dacewa dani

a yanzu? Allah sa mudace amin .

Amsa: Wa alaikum assalam, ka auri mai addini, wacce Idan ka

kalleta za ta burge ka, mai sonka, mai nutsuwa da sanin ya

kamata, yana da kyau ka Sami matar da ka fi ta kudi da ilimi,

ta fi sonka, ta kuma fika kananan shekaru, Ka tsaya ka

kalleta da kyau, kafın ka aure ta, kada ka yi gaggawa. Allah

ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa. 16/03/2016

134.MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWABAYAN ASUBA, A WATAN RAMADANA?

Tambaya: Assalmu alaikum, malam ina da Tambaya shin

meye hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin

azumi, amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito, shin

yaya matsayin azumin su yake? Nagode

Amsa: Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da

mijinta su jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan

Ramadhana, Azuminsu kuma ya inganta, saboda Annabi

(S.A.W) yakan yi haka da matansa, kamar yadda iyalansa

A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma Muslim

ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 1874.

Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa21/05/2016

118

Page 119: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

135. MAI HAILA ZA TA IYA TABA IZU GOMA?

Tambaya:Assalamu Alaikum, Malam. Wai gaskia ne mace

mai haila (period) zata iya rike Alqur'ani izu gima?

Amsa:

Wa alaikum assalam, Abin da yafi zama daidai Shi ne: kar

mai haila ta taba ko da wani bangare ne na Alqur’ani, saboda

hadisin Amru Bn Hazm, wanda wasu malaman hadisin suka

inganta, Inda Annabi S.a.w. Yake cewa: (Kar Wanda ya taba

Alqur'ani sai mai tsarki), kamar Albani a Sahihi wa dha'ifil

Jami'I hadisi mai lamba ta: 13738. Amma ya halatta ta

karanta ta hanyar kallo, saboda duk hadisan da suka hana

mai haila karatun Alqur'ani ba su inganta ba.

Allah ne mafi saniDr Jamilu Zarewa

4/01/2017

136. NA KASA BAMBANCE TSAKANIN JININ BARI DANA HAIHUWA, YAYA ZAN YI?

Tambaya: Assalamu alaikum. mallan nice nake yawan yin

bari( misscariage) sai wata ya kama nayi al'ada anma ba

kaman yanda na saba ganin jinin al'adar ba domin kuwa bai

zuwa da dan yawa kaman yanda nasaba ganin jinin al'ada

bai wuce naganshi dis dis ba a wano toh mallam bayan

kwana uku sai ya tsaya anma tundaga wan nan bansake

ganin jinin ba kuma nayi gwajin ciki wanda akeyi na fitsari

anma bai nunamin akwai ciki na bayan wani watan ya tsaya

saina fara ganin jini shima ba yanda na saba ganin jinin

al'ada ba sai ciwon ciki da mara qarni sosai gashi jajawur ga

119

Page 120: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

wani dan kitse da wani zare zare da yake fitowa:shin dan

Allah mallam ya zanyi na banbance jinin bari dana haila

kasancewar nayi bari akai akai harsau 5 haihuwa 1.

Amsa:

Wa'alaykumussalam, Duk jinin da kika gani a BARIN da kika yi bayan ciki ya kai wata hudu, sunansa jinin haihuwa, in kuma bai kai ba sunansa jinin bari wanda baya hana sallah.

Dr Jamilu Zarewa21/01/2017

137. SHIN WATANNI NAWA MIJI ZAI IYA KAURACEWA MATARSA TA SUNNA?

Tambaya؛ shin Tsawon wani lokaci ne ya halatta miji ya

kaurace wa matar shi ta sunna kuma wani Mataki ya dace ta

dauka in har ya wuce period din da sharia ta halatta?

Amsa:

Wa'alaykumussalam, Ya halatta ya kaurace mata tsawon

watanni hudu kamar yadda Allah ya fadi a suratul Bakara

aya ta: 226. Bai halatta ya wuce hakan ba, in ya koma da

kansa ya cigaba da saduwa da ita to Allah mai gafara ne

game da abin da ya wuce, in har ba zai koma ba bayan

watanni hudu sai ya sake ta kamar yadda aya ta 227 a cikin

surar ta nuna hakan.

In ya ki komawa ya sadu da ita kuma ya ki saki sai taje wurin

Alkali don ya bashi zabi tunda wata hudu ya cika ko ya dawo

mata ko kuma ya sake.

Allah ne mafi Sani.Dr Jamilu Yusuf Zarewa

10/02/2017

120

Page 121: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

138. MIJINA YANA CHARTING DA TSOHUWAR BUDUWARSA,BAYAN TA YI AURE

Tambaya:

Assalamu alaikum, Allah ya taimaki Dr, mijina ne suke chat

da wata matar aure, wadda tsohuwar budurwarsa ce a baya

sama da shekara 20 da wani abu ta yi aure, suna turawa

juna hotuna, shin malam wata shawara da nasiha ya kamata

na yi masa? Saboda kubutar da su ga fadawa halaka. Allah

ya taimaki mallam ya kara fahimta.

Amsa: Wa alaikum assalam, Ki yi masa nasiha da tsoran Allah,

sannan kuma ki nuna masa cewa: Inda matarsa ce ba zai so

ayi irin wannan mua'malar da ita ba. Yin charting irin

wannan da matar aure yana iya kaiwa zuwa zina,

musamman da alama har yanzu suna son juna, Allah ya

hana duk abin da zai kusantar zuwa Zina a suratul Isra'a'i.

Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi kuma ka ji tsoran kar

mutane su yi tsinkayo akai.

Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye Shi, wanda ya saba masa

zai hadu da Shi a madakata. Dayanku ba zai yi cikakken

imani ba har sai ya sowa dan'uwansa abin da yake soma

kansa. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa4/4/2017

139. SHEKARA DAYA MIJINA BAI SADU DA NI BA, MENENE SHAWARATambaya:

121

Page 122: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah ya samu dace.

Malam don Allah ina son nasan matsayin aurena shekara

daya mijina be kusanceni ba alhalin muna tare kuma

dukkanin mu muna lafiya. Nagode .

Amsa:

Wa alaikum assalam, Auranku ingantacce ne,, amma zai yi

kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da

saduwar ma'aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure,

wanda rashinsa yana kai ma'aurata zuwa saɓon Allah. In har

ba ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya

kai shi Kotu alkali ya muku hukunci, Saboda a musulunci bai

Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da wata (4)

kamar yadda aya ta (226) a suratul

Bakara ta tabbatar da haka. Allah ne mafi sani Dr. Jamilu Yusuf Zarewa 08/06/2017

140. INA SON CIKAKKEN BAYANI AKAN KUL'I?Tambaya: Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Malam ina so amin cikakken bayani akan kul'I?

Amsa:Wa alaikum assalam, Khul'i shi ne mace ta fanshi

kanta daga wajan

mijinta ta hanyar ba shi sadakin da ya ba ta lokacin auranta

kamar yadda matar Thabit Bn Kais bn Shammas ta yiwa

mijinta à hadisin da ya tabbata a manyan Kundayan

musulunci. Ya halatta à shariar Allah mace ta yiwa miijnta

Kul'i in har ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokinsa na aure

122

Page 123: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

ba, kamar yadda aya ta (229)a suratul BAKARA ta tabbatar

da hakan.

À zance mafi inganci Kul'i yana saukar da saki daya, saidai

yana nisanta mace da mijinta ta yadda ba zai iya saké zama

da matar ba, sai in ya bayar da SADAKI sannan an kara

daura sabon aure.Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA20/06/2017

141.WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU?

Tambaya: Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji

ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa

ku?

Amsa:

Wa alaikum assalam, ta saku mana, saboda rubutu yana

daidai da furuci a musulunci, Annabi s. a. W. yana cewa

"Allah ya yiwa Al'uma rangwame akan abin da ta riya a

zuciyarta, mutukar ba ta furta ba ko ta aikata. Hadisin da ya

gabata yana nuna cewa: idan ya Saki matarsa a rubutu ta

saku, saboda duk masu hankali sun cimma daidaiton cewa

rubutu aiki NE, shi kuma ya yi aiki. Yana daga cikin Ka'idojin

Shariar da malamai fada a littattafan fiqhu:الكتاب كالخطتتاب

Rubutu kamar magana NE.

Allah ne mafi saniDR. JAMILU YUSUF ZAREWA

24/06/2017

123

Page 124: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

142.TA HAIHU KAFIN TA CIKA WATA BAKWAI DA AURE?

Tambaya: Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar

da ita ba tayi

wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara

(9) to malam

meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a

musulunci?

Amsa: Wa'alaikum salam,In har an San tana da ciki aka yi

auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai

inganta ba a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi

Kafin ta cika wata bakwai, kuma ba'a santa da ciki ba to

dansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi

sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida.Auran dá

aka yi dá cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai

ba zá'à danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba.

In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya

take ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi s.a.w. "Duk

wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar

da ruwansa ga shukar waninsa" kamar yadda Abu-dawud ya

rawaito. In ta haihu za su iya cigaba dá mu'amalarsu ta aure,

musamman in bai sani ba saí dá aka daura.Allah ne mafi

sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

07/08/2017

143. WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE, BA TA SAKU BA

124

Page 125: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Tambaya:

Assalamu alaikum malam, tambaya ce dani. Mijina ne

yasake ni sau biyu, sai yasha abin maye yace na zo

nasameshi, nii kuma banzoba saboda bana son abin da

yakesha na maye, shine yace idan banzoba a bakin aure na.

Shin yaya auren mu? Allah ya saka da alheri.

Amsa:

Wa alaikumus salam, Malamai sun yi sabani game da

aukuwar sakin wanda yake cikin maye: akwai maganganu

guda biyu:

1. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan ya saki

matarsa, tabbas sakin ya auku, saboda shan giya sabon

Allah né, kuma shi ya jawowa kansa, don haka ba za'à

yi masa uzuri ba, wannan ita ce maganar Abu-hanifa da

Malik da Shafii a daya daga cikin zantukansu.2. Sakinsa bai auku ba, saboda lokacin dá Má'iz ya zo ya

tabbatarwa Annabi S. A. W. ya yi zina saidá ya tambaye

shi ko ka sha giya né, kamar yadda Baihaki ya rawaito a

Sunanul-kubrah, hakan saí ya nuna mashayin giya ba'a

amsar maganarsa. Sannan an rawaito daga sayyadina

Usman da Ibnu Abbas cewa : sakin mashayin giya ba ya

aukuwa, kuma ba'a san wanda ya Sabá musu ba a cikin

Sahabbai.wannan ita ce maganar Imamu Ahmad da

Zahiriyya da Ibnu Taimiyya.

Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik

Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da

magana ta biyu saboda mashayin giya bai san abin da

yake fada ba, hakan sai ya sa ya yi kama da Mahaukaci

125

Page 126: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

wanda Alkalami ya saraya daga kan shi, kai har sallah

ma an hana mashayin giya ya yi saboda ba ya cikin

hayyacinsa, kamar yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'í

ta tabbatar da hakan. Don neman karin bayani duba :

Al-Mugni 7/289 dá kuma Sharhul Munti'i 10/233.

Allah ne mafi sani.DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

9/08/2017

144. ZA MU IYA SANA'A DA WUTAR LANTARKI A GIDAJAN GWAMNATI ?Tambaya:

Assalamu alaikum malam, Tare da fatan Allah Ya karbi

ibadun mu da ku Alhazai baki daya. Malam ina hukunchin

wanda suke zaune a gidan hukuma, kudin wuta da ruwa duk

hukuma ke biya. Ya halatta suyi harkan kasuwanchi da ruwa

da wuta, kamar niqa gari, ko yin qanqara suna chin kudin da

suka samu. Ina matsayin wannan a Shari'a?

Amsa:

Wa alaikum assalam, In har a cikin albashinsa ake dauka

babu laifi in ya yi sana'a kamar yadda hakan yake faruwa a

cikin albashinmu na malaman jami'o'i, tun da hakkinsa ne

kuma in da ba ya shan wutar da ba'a cira a albashinsa.Misali

a A. B. U. Zaria hukuma tana cirar min dubunanai daga

Albashina duk wata, saboda wutar lantarkin GIDANA, kin ga

babu laifi in na yi Sana'a da wutar saboda na riga na biya.

Amma idan akwai sharadin da hukuma ta sanya na hana

amfani da wutar a wasu halaye da kuma lokuta ko wasu

kayan lantarki saboda kar asha ta wuce ka'ida ko gudun

126

Page 127: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

fadawa hadari ya wajaba a kula da su, mutukar bai sabawa

sharia ba, tun da musulamai suna kan sharudansu ne kamar

yadda hadisi ya tabbatar.

Allah ne mafi sani DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

28/08/2017

145.MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?Tambaya: Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka, Don

Allah ya halatta me takaba ta je sallar Eid?

Amsa:Wa alaikum assalam, Bai halatta ga mai takaba ba ta fita

zuwa Idi, saboda Hadisin Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031)

inda Annabi SAW yake cewa da Furaia lokacin da mijinta ya

Rasu: (Ki zauna a cikin gidan da kika samu labarin mutuwar

mijinki har zuwa Ki kammala iddarki"

Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba ba za ta

fita ba sai in akwai lalura, sallar idi kuma ba ta cikin lalorori a

sharia. Imamu Ashshaukani a cikin Nailul Audaar 3/343 ya yi

bayani cewa "Dukkan Mata ana fitar da su daga gidanjansu

Don su halarci idi, in ban da wacce take iddar mutuwa".

Allah ne mafi SaniDr Jamilu Zarewa

03/09/2017146.HUKUNCIN RATAYA LAYA DA GURU

Tambaya:

Assalam Alaikum.Malam, menene hukuncin amfani da LAYA

KO GURU a musulunci? Allah yasa mu dace.

Amsa:

127

Page 128: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

Wa alaikum assalam,To dan'uwa Layu da guru sun kasu

kashi biyu:

1. Layun da aka yi su da Sakandami ko Hatimi ko sunayan

aljanu ko wani abu na daban wanda ba Qur'ani ba,

wannnan malamai sun cimma daidaito game da

haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna

Adda'imah 1/212 saboda fadin Annabi S.A.W. (LAYU da

kuma abin da ake daurawa mace don miji ya sota shirka

ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai

lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da

hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito mai lamba ta:

(16969), inda Annabi S.A.W. yake cewa: (Wanda ya rataya

laya to ya yi shirka), shima wannnan hadisin Albani ya

inganta shi a Silsila Sahiha. Hadisan da suka gabata suna

nuna haramcin daura Laya saboda Manzon tsira ya kira ta

da shirka, shirka kuma tana fitar da mutum daga

musulunci.2. LAYUN da aka yi su daga Alqur'ani ko hadisai ingantattu,

wadannan na'u'i malamai sun yi sabani akansu:

A. Sun halatta saboda sun kunshi sunan Allah da kuma

karatun alqur'ani wanda sifar Allah ce, wanda ya dogara da

su ya dogara ga Allah, wannan ita ce maganar Amru bn Al-

ass da Aisha da wasu daga cikin magabata.

B. Ba su halatta ba saboda Ba'a samu Annabi S.A.W. ya yi

ba, da hakan sharia ne da an gan shi ya yi ko da sau daya ne

a rayuwarshi, sannan rataya layun da suke dauke da

Alqur'ani zai jawo a wulakanta su tun da za'a shiga wurare

128

Page 129: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

marasa tsarki da su lokacin biyan bukata, kiyaye hakan

kuma yana da kamar wuya.

Zance mafi inganci shi ne haramcin amfani da Layun da suke

daga Alqur'ani saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya ga

manzon Allah S.A.W, sannan shariar musulunci ta halatta

mana addu'o'i da yawa na neman kariya wadanda suka

wadatar da mu daga layu. Don neman karin bayani duba:

Taisirul Azizil Hamid shafi na : (136) da kuma Ma'arijul Kabul

2/510

Allah ne mafi sani.DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

4/10/2017

147.SAURAYINA YANA LUWADI MENENE SHAWARA?Tambaya:

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Malam Barka Da Asuba.

malam wata 'yar'uwammuce take tambayata tana da saurayi

suna soyayya har an sa musu ranar aurensu amma yarinyar

sai ta gano saurayin aikinsa neman maza yan uwansa shine

take tambayata ta rufa masa asiri suyi aure ya halatta??.

Ahuta lafiya bissalam

Amsa:

Wa alaikum assalam, Ta sanya a yi masa nasiha ko ita ta yi

masa, in har ya tuba, tuba ingantacce za su iya yin aure,

saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taba

aikatawa ba ne. In bai tuba ba ana iya fasa auran saboda

mai wannan aikin FASIKI ne, Annabi S.A.W. yana cewa: (Idan

wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku to

ku aura masa) kamar yadda Tirmizi ya rawaito. Mai neman

129

Page 130: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

maza dabi'unsa ba yardaddu ba ne, wannan ya sa za'a iya

hana shi aure. Sannan bai kamata a rufa masa asiri ba,

musamman idan aka masa nasiha a asirce ya ki tuba saboda

Mabarnaci ne. In har za su yi aure ya kamata ayi gwajin jini

saboda yiwuwar ya kwashi wata lalurar ta hanyar masha'ar

da ya aikata a baya.

Allah ne mafi saniDR. JAMILU YUSUF ZAREWA

28/10/2017148.MACE ZA TA IYA BAWA MIJINTA ZAKKA?Tambaya: Assalamu alaikum, Malam Menene sahihi kan mace tabawa

mijnta zakkah ?

Amsa: Wa alaikum assalam, ya halatta a zancen mafi yawan

malamai saboda hadisin Zainab matar Abdullahi Dan Mas'ud

wanda Bukhari ya rawaito a sahihinsa a lamba ta:(1462) da

kuma Muslim a hadisi mai lamba ta: (1000) lokacin da ta

nemi fatwa akan bawa mijinta sadaka kuma Annabi S A W. ya

halatta mata hakan. Malaman sun kafa hujja da wannan

hadisin saboda kalmar sadaka ta kunshi farilla da sunna. Aya

ta (60) a suratu Attaubah ta yi bayanin nau'o'i takwas na

mutanen da ake bawa zakka, daga ciki akwai talaka, hakan

sai ya nuna mutukar miji talaka ne matarsa za ta iya ba shi

zakka, tun da ba'a samu dalilin da ya fitar da shi ba. Saidai

Ibnul Munzir ya hakaito ijma'i cewa: "Bai halatta miji ya bawa

matarsa zakka ba idan tana fama da talauci, tun da zai iya

wadatata ta hanyar ciyarwar da Allah ya wajabta masa. Don

neman karin bayani duba: Sharhul Mumti'i (6/168) da kuma

Fataawa Allajnah Adda'imah (10/62) Allah ne mafi sani.

130

Page 131: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA21/11 /2017

149. YA YI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFINYA YI KAFFARA?Tambaya:

Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne ya yi

wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya

sake wani auren. Malam ya matsayin wannan sakin da

matsayin auren? Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga

Malam.

Amsa:Wa alaikum assalam, Auransa na biyun ya inganta saboda ba

su da alaka da juna.Wasu Malaman sun tafi akan cewa

mutukar saki uku ne, to wancan ziharin ya warware, amma

in saki daya ne kuma ya yi kome, to bai halatta ya taba ta

har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudaamah

ya fada a cikin Al-Mugni.Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 01/06/2017.

150.AURAN KAFURAI KAFIN SU MUSULUNTA INGANTACCE NE!

Tambaya: Assalamu alaykum, don Allah ina son a tambaya min

malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya

musulunta shi da iyalan sa ta dalili na, kuma ni na basu

kalmar shahada. Suna da yara manya da kanana, sai suka

tambayeni ya ya matsayin auren su nace auren suna nan

kamar yadda shariar musuluncinta tsara, sai yace min to

yaya matsayin ‘ya’yan su? To gaskiya wannan ne ban sani ba

131

Page 132: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman

Allah yataimaka amen.

Amsa: Wa alaikum assalam, To ɗan'uwa auran da kafurai suka yi

kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan

ƙa'idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu,

saboda Annabi S. A. W bai canza auran kafiran da suka

musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda

da 'ya'yansu da suka haifa ta hanyar wancan aure.

Sahabban Annabi S. A. W. da yawa an haife su ne ta hanyar

auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da

dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da

kafurai suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa

iyayansa bayan sun musulunta. In kafirai suka yi zina suka

haifi Ɗa ba za'a danganta shi zuwa babansa ba bayan ya

musulunta. Don neman karin bayani duba:

Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kumasharhulMumti'i12/239.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa13-09-1438/ 08-06-2017

151. TA KI YARDA DA MIJINTA SABODA TANA AZUMIN NAFILA!

Tambaya: AssalamuAlaikum.Mallam ina da tambaya? Yaya

hukuncin Matar da miji ya bukacheta tana Azumin sunna. Taki

ta aminche mishi

Amsa: Wa alaikumus salam, ta yi kuskure ya kamata ta amsa

kiran mijinta, saboda azumin sunna ya halatta a karya shi ko

da babu dalili, Annabi (SAW) yana cewa"Mai azumin nafila

sarkin kansa ne ina ya Ga dama ya cigaba da azumin, in

132

Page 133: AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA - WordPress.com · biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen

kuma ya so ya karya " kamar yadda Tirmizi ya rawaito a

Sunan.

Allah ne mafi sani.DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

30/1/2018

152. MIJINA YA SAKE NI INA SHAYARWA, KO ZAN IYA IDDA DA WATA UKU?Tambaya:

Assalamu alaikum, Malam ga tambayata kamar haka watace

aka saketa tana shayarwa kuma ba ta yin al'ada to shin xa ta

iya yin aure bayan wata uku ko kuma sai tajira ta yaye

yaronta har taga al'adanta Kafin tayi auren nagode.

Amsa: Wa alaikum assalam, za ta jira jini uku, ko da kuwa sai ta yi

shekara uku, kafin ta kammala iddar, saboda Allah ya rataye

iddar matar da aka saka, kuma ba ta yanke kauna daga haila

ba da jini uku, kamar yadda aya ta : 228 a suratul Bakara ta

tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA18/02/2018

153. MIJINA YA SAKE NI DA DANYAN GOYO, YAYA IDDATATambaya: Assalamu Alaikum, Dr. macece mijinta ya saketa

bayan ta haihu da danyen goyo. Ya iddarta zata kasance?

Allah ya karawa Dr. Ikhlasi

Amsa: Wa alaikum assalam. Za ta jira jini uku Kamar yadda

aya ta (228) a Suratul Bakara ta tabbatar da hakan, ba za ta

yi aure ba har sai ta kammala su, Allah ya kara mana iklasi a

duka lamuranmu. Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA25/06/2018

133