11
Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 1 Facebook: https://facebook.com/journalistsharfadi Instagram: https://instagram.com/journalist55 Twitter: https://twitter.com/bjournalist55 Email: [email protected] Call & WhatsApp: +2349035830253 MU KOYI COMPUTER A SAUKAKE (Takarda ta Biyu 002) Rubutawa/Tsarawa: Basheer Journalist Sharfadi #BasheerSharfadi #BasheerSharfadi

Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

  • Upload
    others

  • View
    150

  • Download
    21

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 1

Facebook: https://facebook.com/journalistsharfadi

Instagram: https://instagram.com/journalist55

Twitter: https://twitter.com/bjournalist55

Email: [email protected]

Call & WhatsApp: +2349035830253

MU KOYI COMPUTER A SAUKAKE (Takarda ta Biyu 002)

Rubutawa/Tsarawa: Basheer Journalist Sharfadi

#BasheerSharfadi #BasheerSharfadi

Page 2: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2

GABATARWA:

Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, wannan takardar ce da zata kunshi

muhimman bayanai dangane da Ilmin Computer tun daga ma’anar ta, tarihin ta, da kuma

yadda ake amfai da ita.

Cibiyar wayar da kan al’umma ta Sharfadi.com itace ta shirya wannan takarda domin

amfanar al’umma baki daya.

.

SHARADI:

Ba’a yarda wani ko wata tayi amfani da wannan takarda ko tayi kwafi dinta ba tare da iznin

marubucin ba.

MECECE COMPUTER (NA’URA MAI KWAKWALWA) ?

Computer na’ura ce da ake amfani da ita wajen ajiye bayanai sannan zaka iya neman abinda ka ajiye

a duk sanda kake bukata, ana iya bata umarni kuma tana bi, sannan ana adana ko shirya bayanai ta

tsarin rubutu ko hotuna ko video acikin ta, kuma ana saka mata manhajoji (software) sannan ana iya

tura sakon email, ko yin games (wasanni) ko shiga shafukan yanar gizo-gizo, (wannan a takaice

kenan)

TARIHIN COMPUTER:

Wani Professor na turanci da lissafi mai suna Charles Babbage shine ya fara kirkiro na’urar computer

sai dai a wancan lokacin tana da bam-bamci da computer da ake amfani da ita a wannan lokaci,

Computer ta farko da ta fara fitowa a duniya itace wadda Dr. John V. Atanasoff da Clifford Berry

suka kera kuma a shekarar 1937 zuwa 1946 a lokacin girman computer ya kai girman daki ko kuma

muce dakuna jibgegiya ce sosai, a haka aka cigaba da samun cigaba lokaci bayan lokaci sannan ana

dada rage girman ta a shekarun 1947 zuwa 1963 shima an samu gagarumin cigaba a wancan lokacin,

a yanzu computer ta zamo gidan kowa da akwai domin kuwa zaka ga ko ina ana yin amfani da ita

sannan duka guraren ayyuka a yanzu yanayi na kara bayyana da yake tilasta yin amfani da ita, domin

a yanzu ma ana sa ran nan da yan shekaru hatta masu sana’o’in gargajiya na malam bahaushe za’a

samu cigaban da zasu dinga amfani da computer, daman ba’a maganar kamfanunuwa ko kantuna da

kuma makarantu,

Page 3: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 3

BANGARORIN COMPUTER:

Computer tana da bangarori amma mafi muhimmanci da ya kamata ka sani a wannan lokaci sune:

Monitor: Wanda ake kallon abinda kake yi a computer (mai kama da talabijin)

Mouse: a laptop kuma ana kiransa touchpad ko trackpad: wanda ake amfani dashi wajen sarrafa

computer

Keybord: madannan da ake amfani dasu wajen yin rubutu, ko bada umarni.

C.P.U (Central Processing Unit): a hausance muna cewa dashi (kwakwalwar computer) a nan take

adana dukkan bayanai sannan duk wani umarni da zaka bata acan ne take karba, amman ita laptop

da ake kira tafi da gidanka tana dauke da nata ne acikin ta, (wannan a takaice kenan)

Ga misali a hoton dake kasa, dama sauran bangarorin nata,

IRE-IREN COMPUTER:

Anan zamu yi magana ne akan dangin computer guda biyu duk da akwai tarin ire-iren ta daban-

daban amman zamu dauki wadannan guda biyun kacal muyi magana akan su domin sune wadanda

akafi amfani dasu, sune Desktop da kuma Laptop, Desktop itace wadda kuka ga hoton ta a sama

tana rabe da sauran bangarorin computer sabanin laptop wadda ake kira da tafi da gidanka domin

tana dauke da komai nata a tare da ita.

BAM-BAMCIN DESKTOP DA KUMA LAPTOP:

Desktop: tana rabe da C.P.U, Mouse, Monitor da kuma keybord da sauransu duka daban daban ne,

sannan bata aiki sai da wuta, dukda akwai batirin da ake saka mata amman shima bai taka kara ya

karya ba kuma bayanin sa shima zai zo ga yan diploma,

Laptop: tana dauke da dukkan abubuwanta a tattare da ita sannan tana da batir don haka tana aiki

ba tare da wutar lantarki ba, (wannan a takaice kenan)

Page 4: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 4

YAYA AKE KUNNA COMPUTER?

A desktop ajikin C.P.U akwai wani madanni wani ajikinsa an rubuta “on” kamar dai madanni irin na

talabijin to da zarar ka jona wayoyin ta ka dannan zata kawo haske, haka a Laptop tana zuwa da

makunnin ta a samman Keybord zaka ga madanni shima kana dannan shi zata kawo haske, akwai

wadansu kananun computer wadanda ake kira da Mini su kuma wasu sukan zo da wannan

madannin a gefe, bayan ka danna ta kawo haske zata danyi loading idan da akwai password (kalmar

sirri) zata kawo sai ka saka idan babu kuma zata bude ma ka, zaka ga ta saka user wata tana budewa

kai tsaye wata kuma sai ka danna wajen daka saka user din, a computocin da suke dauke da windows

8 idan ta bude zata baka alamomi kamar yan hotuna sai ka nemi wanda aka saka desktop sai ka

danna shine zata bude maka,

YAYA AKE KASHE COMPUTER?

Computer ba kamar talabijin ba wadda ta inda aka hawo ta nan ake sauka ma’ana ta inda aka kunna

ta tanan ne za’a kashe ta, a’a idan ka kammala amfani da computer kana son ka kasheta abinda zaka

yi na farko shine ka rufe dukkan ayyukan da ka bude tukunna, sanna sai ka kai kibiyar ka can kasa

daga bangaren dama zaka ga Start sai ka shiga zaka ga shutdown, restart, hibernating da sleep sai

ka danna shutdown idan kuma a windows 8 ne sai ka dannan can gefen ka na bangaren hagu zaka ga

ya bude maka da su search start dasauransu a can kasa zaka ga setting sai ka shiga shima zaka ga

shut dow nan ne zaka shiga kamar wancan,

Ga misalin su nan a hoton dake kasa:

Zaka Iya amfani da Shut cut ta hanyar danna “Alt” da “F4” shima zai kawo maka zabi sai ka zaba

“shut down” “restart” sleeping” “hibernating”.

Idan ka shiga wannan start da nayi magana a sama zaka ga wani guri da aka saka My Computer to

nanne zaka shiga domin ganin cikin computer ka ma’ana ko wani abu daka ajiye akanta, anan zaka

foldojin da kake dasu irin su my document, music, video , da pictures da kuma sauransu, ko kuma

kayi amfani da shut cut ka danne alamar windows + E ma’ana Idan ka danne shi ba zaka daga ba sai

ka danna harafin “E”

Page 5: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 5

MADANNAI MASU MATUKAR AMFANI DA YA KAMATA KA SANSU SANNAN KA KIYAYE SU:

1. Ctrl: da shine ake amfani wajen baiwa computer umarni,

2. Shift: ajikin keybord akwai alamomin da suke kasan madannai misali ajikin lamba 5 akwai

alamar % to ina son na dannan alamar % amman idan na danna sai naga lamba biyar ta fito,

amfanin shift anan shine zaka danne shi sai kadanna lamba biyar zai baka wannan abin dake

kan wannan madannin wanda yaki fitowa,

3. Caps lock: idan ka danna shi kana cewa computer duk abinda ka rubuta to ya fito maka da

babban baki sannan idan ka kara danna shi kana nunfin ya fito da karamin baki,

4. Esc: ana danna shine domin fita daga wani guri gaba daya kana ganin computer dinka ta

shiga wani gurin da baka gane masa ba cikin hanzari ka danna escape zai fito da kai,

5. Space bar: shine madannin da yafi ko wanne girma a computer ana dana shi ne domin bada

space acikin rubutu, ko kuma in kana kallo ko sauraran abu ka dannan domin tsayarwa ko

cigaba.

6. Backspace: ana dana shi domin goge rubutu ko komawa baya,

7. Enter: ana danna shi domin shiga waje tamkar “ok” a waya

8. Right click:- domin bada option ko shiga guri

9. Left click:- domin yin selecting highlighting

START MENU:

Na danyi bayanin a sama da yadda ake shigar sa, shi start menu anan ne zaka ga dukkan program din

da kake dasu da mahajojin da kake dasu akan computer ka acikin sa zaka ga All Program shima idan

ka shiga zaka gan su, abinda ake cewa manhaja shine software ga masu amfani da wayoyi zasu fi

ganewa in ance application to kamar yadda waya take da application to itama computer tana da

nata shina ake kira software,

INA SO ZANYI RUBUTU A COMPUTER:

Microsoft office suit: sune dangin kamfani da suka samar da manhajoji na computer wanda ake

amfani dasu wajen rubutu da kuma na abubuwa da daman a computer daga ciki akwai Word shine

zaku gani a computer da tambarin “W”

Zaka iya shiga cikin start menu ko All Program ka nemo Word kana shiga zai kawo maka new

document guri rubuta wanda babu komai kamar haka:

Ga Hoto Nan A Kasa

Page 6: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 6

Wannan Menu da akayi magana anan shine nace dukkan abubuwan da zakuyi amfani dasu, suna ciki

gasu nan zan jerosu a kasa,

1. Cut, 8. Italic

2. Copy, 9. Underline

3. Past, 10. Maida rubutu zuwa babban baki ko karamin baki

4. Insert:- Table, Pictures, Page Number 11. Sanya Kala a rubutu

5. Salon rubutu (font) 12. Dai-dai ta rubutu (dama, hagu, da tsakiya)

6. Girman rubutu (size) 13. Sanya Boder

7. Kumbura rubutu (Bold) 14. Tazara tsakanin layuka

SHORTCUT KEYS NA MICROSOFT WORD:

1. CTRL and A :- Kayi Selects na gaba ki dayan document din da kake kai (misali in kayi rubutu

ka danna hakan zai yi maka selecting gabaki daya,)

2. CTRL and B :- Kumbura Rubutu

3. CTRL and C:- domin kwafar rubutu ko wani abu amman bayan anyi hylighting (select) sannan

yi amfani da CTRL and V domin yin paste ma’ana dawo da rubutun a inda kake so,

4. CTRL and E :- domin dai dai ta rubutu zuwa tsakiya,

5. CTRL and I :- domin mai da rubutu italic a karkace,

6. CTRL and J :-domin dai dai ta rubutu,

7. CTRL and L :- domin maida rubutu bangaren hagu

8. CTRL and N :- domin bude sabon document (new)

9. CTRL and O :- domin bude wani document din,

10. CTRL and P :- domin yin printing

11. CTRL and R :- domin maida rubutu bangaren dama

12. CTRL and S :- domin yin saving din document

Page 7: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 7

13. CTRL and U :- domin jan layi a kasan rubutu

14. CTRL and V :- domin ajiye abinda ka kwafo a inda kake so

15. CTRL and X :- domin yanke abu ko kuma rubutun da akayi selecting

16. CTRL and Y :- idan ina yin aiki sai na goge shi to zan danna CTRL and Z domin nayi undo

wannan abin ya dawo to idan nayi hakan sai kuma nake son abinda nayi na gaba ya dawo

(redo) shine zan danna CTRL and Y sai ya dawo

17. CTRL and Z :- undo domin dawo da abinda aka goge ko kana yin aiki kawai sai ka neme shi ka

rasa to sai ka danna CTRL and Z zai dawo,

18. Tab: idan kana cikin table kana so ka kara yawan table sai kayi ta danna tab zai kara maka

yawan table din, sannan idan ana bada space misali wajen tsara wasika dasauransu

19. Enter: domin bada sakin layi,

20. CTRL and Enter: shine idan kana rubutu ka kammala wanda kake so ya zama a iya page din

kana so ka tafi page na gaba, mai makon kayi ta bada sakin layi sai ka danna CTRL and Enter

zai bude maka sabon page,

YAYA AKE YIN SELECTING KO HIGHLIGHTING A COMPUTER?

CTRL and A nace shine highlighting na gabaki dayan document to idan kana son yin highlighting na

wani bangare sai ka kai tsinkenka farkon wannan abun da kake son yi sai ka danna sau biyu kada ka

daga hannun ka a na biyun sai ka jawo shi, zai yi maka select din ko kuma in ka kai tsinken ka farko

saika danne madannin hagu “left click” ko madannin “shift” sai ka ja shi zai yi ma highlighting shima,

YAYA AKE SAKA TABLE A WORD:

Idan ka shiga insert zaka ga table nan zaka shiga akwai automatic table wanda zaka janyo shi kawai

yayi maka iya adadin da kake so, ko kuma kayi kasa kadan zaka ga inda zaka zabi colum da row nawa

kake so yayi maka, Row shine layi na kwance. Colum kuma layi na tsaye, misali a kasa ga table nan

mai row 2 culum 3

Shima wannan abune da zaku haddace domin duk inda zaka shiga acomputer kana tare dasu Karin

bayani shine idan ka yi minimizing kuma kana so ka dawo dashi zaka duba can kasa zaka ga alamar

wannan abin da kayi minimizing kawai sai ka danna zai dawo,

Cancel / Rufe abu (clothing) Kara girma ko ragewa Minimizing ko dawo wa da shi

Page 8: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 8

MICROSOFT EXCEL:

Shi Excel daya ne daga cikin manhajoji wadanda a Computer ana iya cewa mutum sai dai yayi iya

kokarin sa amman ba dai yaga karshen sa ba, domin ko yaushe zuaka dinga ganin sa da sababbin

abubuwa acikin sa ne ma’aikatu kan tsara biyan albashi da sauran abubuwa na lissafi sannan a shine

ake tsara sakamakon jarrabawa na makaranta wato Exam Result,

A mataki na farko zamu koyar da yadda ake tsara Exam Result ne kawai sai dai a gaba zamu fadada,

Wannan hoton dake sama shine yadda tsarin excel yake kuma shima ana bude shi ne kamar yadda

ake bude Word sannan shi cikin sa kamar yadda kuke gani gida-gida ne, Colum yana tafiya da harufa

(Alphabetically A-Z) row kuma yana tafiya da lamba sai ka rike wannan ka idar, ga misalin

sakamakon jarabawar wasu dalibai a kasa

Bayan na gama shigar da makin kowa sai naje gidan total sai na saka =sum( sai na duba gida na farko

da na saka maki gida na biyu a excel banda gida na farko da na saka S/N Suna d.s inda sunan dalibi na

farko Bashir Sani yake gida na biyu (row na biyu 2) ne a excel sannan a colum “B” ne, don haka na

fara saka maki ne daga gidan column a C a bangaren row kuma na fara saka sunan dalibin ne a row 2,

don haka sai na saka C2 acikin bracket dinka zanga gidan ya kewaye sai na saka wannan alamar : a

gaban kuma sai na duba naga wane gida ne maki na ya kare? Kunga ya kare a gidan J2 zaka ga gidan

ya kewaye gaba daya makin wannan dalibar, anan nace dashi ne ina so yayi min total na dukkan

makin wannnan dalibin, daga nan sai na rufe bracket dina wato nayi haka =sum(c2:j2) sannan na

danna Enter ina dannawa zata yimin total ta fadamin adadin wannan makin, a kasan akwai wani dan

tsinke sai na ja shi yayi kasa gabaki daya zai yi min total din na sauran daliban shine sai na saka grade

da position shikenan, ga misalin wannan daliban bayan na gama, ga shi nan a kasa,

Page 9: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 9

MICROSOFT POWER POINT:

Daya daga cikin manhajoji dangin Microsoft suits da mukayi bayani a baya, kuma yana da matukar

muhimman ci sosai ana yin amfani dashi wajen tsara Presentation na wajen taro da kuma hada slide

show,

Da farko ana bude shi ne kamar yadda ake bude word da sauran software da mukayi a baya, bayan

an bude yana da abubuwa da dama akan sa amman a wannan mataki na certificate zamu dauki

abubuwa guda biyar (5) ne kacal sai a biyo mu,

1. Home:- anan ne zaka ga alamomin rubutu kamar yadda suke a Microsoft word

2. Insert:- a nan ne idan zaka sanya wani abu kamar hoto ko sound ko video da sauran su

3. Design:- anan zaka dauki wane irin salo kake so tsarin aikin da kake yi ya kasance, tsarin kala

da kuma design

4. Transitions:- anan zaka zabi yadda kake so design dinka ya fito, misali kana so ya wul-wula

ko ya bullo ko ya tarwaste

5. Aminations:- anan zaka zabi yadda kake so design dinka ya fito, misali kana so ya wul-wula

ko ya bullo ko ya tarwaste, a yaya kake so abinka yazo? amma akan iya abinda kayi hylighting

kamar rubutu ko wani hoton shi kadai

COREL DRAW:

Daya ne daga cikin manhajoji masu matukar muhimmanci a computer anan ne ake yin zane kamar

bajo, logo, da sauran zane kala-kala kuma yana da abubuwa masu muhimmanci da ya kamata dalibi

ya lura dasu misali:

Wurin daukan abu, Wurin ajiyewa, Alamar shape, Kala, wurin rubutu dasauransu amman zamu dauki

iya wadannan amatakin farko.

RIBAR KAFA:

I. YADDA ZAKA YI FLASHING DIN WAYAR KA DA KANKA

Duba da yadda wayoyin Yan uwa zasu samu yar qaramar mastala Amman in sun kai gayara

kawai se a raba kudin wayar biyu ace su biya kudin gyara wanda kuma ani gyaran ba wai

wani gyaran kirki bane,

Yanzu dai zamuyi bayanin yadda zaka yiwa wayarka Flashing da kanka ba se ka kaiwa wani

ba,

Ba idan wayarka tana dan qamewa kadan shikenan ai se an kaxa ta ciyo kaxa ba a'a kaima

Page 10: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 10

jarraba Amman ka tabbata ka zare sim da memory sannan kana da Isashshen chaji,

II. YADDA ZAKA YI FLASHING A WAYA QIRAR SAMSUNG

Idan kana son yiwa Samsung dinka Flashing to ka tabbata ka cire layinka da memory card

dinka kafin kayi,

A samsung zaka yi Amfani da daya daga cikin wadannan lambobin:-

*#2767*2878#

*#2767*7377#

Idan daya lambar bata yi maka ba to ka gwada dayar InshaAllahu zataa yi maka.

Yadda zaka yi shine: Bayan ka zare layinka da memory card se ka danna wadancan lambobin

sannan ka kula Idan kasa lambobi 4 na farko to ragowar baza su dinga fitowa ba se dai su

dinga saka maka **** kana gama sanya lambobin zaka ga tayi restart in ta gama zata kawo

maka ka sanya password To Pasword din Samsung shine: 12345 ka na sawa shikenan

wayarka tayi Free se kaje ka sake saita duk abinda kake so don ta dawo kamar sanda kasiyo

ta,

III. YADDA ZAKA YI FLASHING A WAYA QIRAR NOKIA

Ga masu Amfani da Nokia kuma ku tabbata kun zare Sim Card da Memory Card sannan se ka

danna wadannan lambobin

*#7780#

Zaka ga ta baka za6i shin kanaso kayi Restory se kayi 'Ok' to zaka ga ta dauke sannan ta kawo

zata ce ka samata password kuma koda ka manta password dinka in kaimata haka inshaAllah

zata dawo.

In kaga ta nuno maka kasa password to wanda zaka saka shine:-

Idan Nokia Original ce =12345

Nokia China = 1234

Shi kenan

IV. YADDA ZAKA YI FLASHING A WAYA QIRAR ANDROID

Ga masu Amfani da waya Qirar Android Abin nasu mai sauqi ne kawai ka danne Gurin

kashewa 'swich off' da kuma wajen qaro magana 'Volume shikenan,

Amman kaima ka tabbata kabi waccan qa'idar ka zare layi da memory kuma kana da chaji

sosai,

V. AN SACE MUN WAYA TA KUMA NA FIDDA RAI DA SAMUN TA shin yaya zanyi??

Abin lura bawai mun kawo wannan maganar bane don aje a cuci wani ba,

To Abinda zakayi shine zaka Iya qona wayar matuqar ka dauki 'IME number' din wayar Ime

number wadan su numbobi ne guda 15,

Da farko yadda zaka dauki 'IME numba dinka shine ka danna:

*#06# zaka ga lambobin guda goma 15,

Idan kayi copy din su ka ajiye to duk sanda irin wannan ta faru kawai samo wata wayar ka

shiga wajen tura msg ka rubuta wadannan lambobin guda 15 sannan ka tura su zuwa ga

Page 11: Facebook: ... · Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com ©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 2 GABATARWA: Assalamu Alaikum warahmatullahi

Mu Koyi Computer A Saukake – Basheer Journalist Sharfadi Sharfadi.com

©Basheer Journalist Sharfadi, Sharfadi.com Page 11

wannan lambobin 15,

To ko an zare batir ko ba'a zare ba kwanan waya ya qare Amman ina ganin Haquri shine yafi,

VI. YADDA ZAKA SAMU SAQIN KIRA

Ka qara #555 bayan lambar da zaka kira misali 070...............#555

Ga masu Amfani da Mtn kuma ga wata hanya Idan kai kana zone kana so ka kira wanda ba a

zone ya ke ba se ka qara 0000 guda 4 misali 081.........0000 InshaAllah za'a samu saqin

farashi,

VII. YADDA ZAKA SAMU NETWORK

Ka qara 000 guda 3 ko 111 guda 3 koa 180 bayan lambar da zaka kira misali:-

080..............000

081..............111

070..............180

Insha Allah zaka samu Network Sosai,

InshaAllahu zamu cigaba,

Anan zan gimtse wannan rubutu nawa tare da fatan Alkhairi da fatan samun nasara da kwarewa ga

dukkan yan uwa na dalibai:

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),

Phone No: 09035830253

www.sharfadi.com

Email: [email protected]

Facebook:

www.facebook.com/journalistsharfadi

Instagram: www.instagram.com/journalist55

Twitter: www.twitter.com/bjournalist55

#BasheerSharfadi #BasheerSharfadi