77

Mujallar FIM

  • Upload
    vukiet

  • View
    1.395

  • Download
    76

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Page 2: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Advert:

Larura

1

Page 3: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Juyin Mulki 2

2

Page 4: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001 3

Ci gaba daga watan jiya

Ba za a yi da Iyan-Tama ba!

ADO Ahmad Gidan Dabino ya burgeni da ya yarda da shawarar da nakawo ta a kafa sabuwar mujalla

wadda za ta bambanta da Tauraruwa. Toamma sai ya dube ni ya ce, “Shi Iyan-Tamada kake so ka shigo da shi ciki, ka san shine?”

A cikin mamaki, na ce, “Haba na san shimana! Ba wanda ya fita ]azu...”

“A’a, ina nufin ka san halinsa sosai? Kunta~a yin wata hul]a ta kasuwanci da shi?”ya katse mani hanzari.

Na ce, “A’a. Amma ni nakan gan shikamar kamilin mutum. Yana da fara’a dasaurin }ulla abota. Ba ka yarda da shi ba ne?”

“Ba wai ban yarda da shi ba. Kai dai kabari zan yi maka bayani.”

Na ce, “To.” Daga nan na shiga tunaninme Ado yake nufi.

A daidai lokacin sai aka bugo masa waya.Yarinya ce. Da ma da wuya ka yi minti biyarda Ado wata mace ba ta bugo masa waya ba, su shiga tsarance.Shi kansa yakan bugi }irji a kan yawan tarho da yake samu, haryakan ce mani a duk masu yin fim a Kano, da wuya in akwaiwanda ya fi shi samun waya daga gun ’yan mata; wasu ’ya’yanmanya, wasu kuma ga su nan dai. Wannan ya faru ne tun dagalokacin da ya yi tashe a fagen rubuta littattafai, musamman bayanfitowar In Da So Da {auna. Har nakan ce masa, “Ya kamata inzo in ri}a ]aukar darasi a gun ka na iya zance da ’yan mata.”

Shi kuma yakan yi dariya, ya ce, “To sai ka zo.”A lokacin da yake wayar nan kuma sai ga wasu ’yan matan

sun tsaya a bakin }ofa, suna jiransa. Ni kuma sai na shiga tunaninabin da ya ce mani game da Hamisu Iyan-Tama. A raina na ceIyan-Tama ya yi kama da mutanen kirki ... yana da yawan haba-haba da jama’a. Allah sa dai ba ]an ‘419’ ba ne kawai!

Da Ado ya }are, sai ya kar~i ba}insa hannu bibiyu. To, donkada in tsare masu wuri (don babu isasshen wurin zama a gabanteburinsa) sai na fita waje. Akwai wani mai saida rake a bakintiti; na saya na fara sha. Na dubi agogo, a raina na yi fatan sugama da wuri kada dare ya yi mani a hanya.

Can sai gogan nawa ya fito.“Af, Ibirahim fitowa ka yi?” inji shi.“E mana, ai na ga ka yi ba}i,” na amsa masa.Ya ce, “To ashe ba makarantar za ka yi ba.”“Ta me?”Ya yi dariya. “Ta soyayya mana.”Muka yi dariya tare.Sai na ce, “Ado, gara mu yi maganar nan mu gama. Ka san

garinmu da nisa!”Sai ya ce, “To mu koma ciki mana.”A nan sai na ce masa, “Wai babu wani wuri ne da za mu shiga

mu tattauna? Kai ofishinka mutane sun yi yawa; wannan ya zowaccan ta zo.”

Akwai ]an ]aki kusa da ]akin ofis ]in, wanda Ado ya mayar

FIM: ASALINTA, TASIRINTA

DA MATSALOLINTA (II)

sito ]insa inda yake aje takardu da saurankayan ]ab’i (wanda ya yi amfani da shi ya}ara wa ofishinsa fa]i a yanzu). Ya ce ko zamu shiga ciki mu gama ganawa? Na yarda.Kafin haka, sai na ce, “Don Allah bari in yiamfani da wayarka in buga wa Yusuf Adamuwaya a gidansu, don ya san ina gari. Kadaya fita.”

“Bismilla mana,” inji Ado.Na shiga ofis na buga wa Yusuf waya.

Na yi sa’a yana gida, aka kira shi mukagaisa. Na ce masa, “Ina nan wurin GidanDabino. In na }are zan zo.”

Yusuf ya ce, “Me zai hana ka jira ni a nantunda ga ni nan fitowa?”

Na yarda, domin ko banza ya hutasshe nizuwa Tarauni. Yusuf abokina ne matu}a.Malami ne a Jami’ar Bayero, Kano, indayake koyar da Nazarin Halayyar {asa (Ge-ography). Ba Ado ne ya ha]a ni da shi ba.Mun san juna ne ta hanyar wani abokina

mai suna Ibrahim Malumfashi. A gidan Ibrahim ]in muka faraha]uwa. Shi kuma sun san juna a Jami’ar Sakkwato inda Yusufya yi ]alibta, shi kuma Ibrahim yake malami. Zancen rubutu dafasaha ya ha]a mu, muka yi }awance; da ma Hausawa sun ceabokin damo guza. Shi ya sa mukan ziyarci juna, har ta kai makusan a ce abotarmu ta yi }arfi fiye da wadda ke tsakaninmu daAdo ko kuma shi Ibrahim Malumfashi.

Ni da Ado muka shiga sito, muka ci gaba da tattaunawa. Dayake abin da tsawo, bari in ta}aita. Da farko ba ya da ra’ayin mukafa mujalla domin a cewarsa ba ya da ku]i. Har ya kada bakiya ce, “Bayan Tauraruwa ta fito, mun lura ta wani ~angare ce.Mun so mu kafa tamu, to amma rashin ku]i ya hana. Kuma agaskiya a yanzu ]in ma ba ni da ku]i.” Ya ci gaba ya bayyanamani jin haushinsa da masu Tauraruwa, wa]anda ya ce ba su bashi wani muhimmanci ba a cikin shafukansu, wai sai kawai suka]an ambace shi a lokacin da suka yi wata magana ’yar }yas akan jarumin fim ]in nan Sanusi Burhan Daneji (Elbis).

A nan, sai na ce masa ni a shirye nake in zuba ku]ina a yimujallar.

Ado ya ce, “Af to, ai ban hana ka ba. Ni dai na ce maka ba nida ku]i. Amma duk goyon baya zan iya bayarwa.”

Na ce masa na gode. To amma sai na ba shi wani shara]i: inaso ya zuba ko da nawa ne mu yi tare. Na lura yana hangenyawan ku]in da za a kashe, don haka na ce ko ku]i ka]an ne yazuba.

Ya ce, “Kamar nawa?”Na ce, “Ya danganta kan ko nawa za a kashe a yi ta.” Na ce

masa mu lissafa mana. Kafin ya ce wani abu na je wurin motatana bu]e wata }aramar jaka, na kawo fararen takardu na rubutuda al}alami. Ina da wata dabara. Zan so in yi mujalla, amma zanfi son mu yi ha]in gwiwa da wani mazaunin Kano inda harkarfim ta fi }arfi. Sannan ina son mu yi tare da wani wanda yakecikin harkar fim, domin za mu ri}a jin labarai daga tushe sahihi.

Ibrahim Sheme

Daga

Page 5: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 20014

A raina, na tuno da wani shirin talbijin da ake gabatarwa a watatashar TV a Amerika mai suna Hard Copy, wanda ya dogara akan rahotanni daga ’yan sanda a kan aikata laifuka, ko kumalabaran fitattun masu sana’ar nisha]antarwa irin su mawa}a da’yan fim. Kamar yadda na ce, Ado abokina ne, kuma ]an fimne. Don haka zai iya samar mana labarai da ]umi-]uminsu. Buguda }ari, akwai yarda a tsakaninmu.

Da na kawo kayan rubutu, sai muka shiga lissafi: nawa za akashe wajen tsara shafuka a komfuta; nawa za a kashe wajensayen takardun ]ab’imasu inganci; nawakwanon ]ab’i yake, dasauransu. Ba mu gamaba, sai ga Yusuf ya iso.Ya ]an le}o, sai zaikoma tare da cewa, “Af,kuna ganawa ne?”

Ado ya ce, “E.”Sai na ce, “Shigo

mana. Ai ba wani sirriba ne. Mujalla za mukafa.”

Ya shigo, ya ce,“Mujalla? Ta me?”

Sai na yi masabayani.

Sai Yusuf ya ce, “Toyaya muna ciki?”

Ado ya yi farat ya ce,“Ba mu fara lissafamutanen da za a sa ba.”

Na ce, “Ai harkarku]i ce; in kana da su shigo mana!”

Yusuf ya nemi wuri ya zauna. Muka ci gaba da lissafi ni daAdo, shi kuma yana kallo. Inda ya ga yana da wata lura, sai yafa]a mana. Har dai muka }are. Da muka samu jimilla, sai na ce,“To nawa za ka iya bayarwa a ciki?”

Ado ya ]an yi tunani, ya ce, “Dubu biyar.”Na yi tsaki, na ce, “Don Allah ka yi magana kamar namiji

mana. Menene naira dubu biyar?”A ta}aice, da }yar ya kai dubu goma, ya ce ya kamata a kira

wasu mutane daban su zuba jari don kada nauyin ya yi manayawa.

Na dubi Yusuf na ce, “Kai kuma fa Malam, miliyan nawa zaka zuba?”

A cikin barkwanci, Yusuf ya ce, “Mu malamai ne, talakawa,ba irinku ba ’yan business. Dubu biyu zan sa.”

A nan, sai na cije, na ce ku]in sun yi ka]an. Shi ma da }yarya kai dubu uku, ya tsaya a nan.

A gaskiya, na fi su samun ku]i su duka. Kuma niyyata ita cein zuba sauran ni ka]ai – wajen dubu saba’in. To amma na yardada shawarar Ado ta a shigo da wasu. Mutum na farko da Ado yaambata shi ne [an’azimi Baba. Babu mamaki, domin kowa yasan su tare; kamar [anjuma ne da [anjummai. Daga nan sai nace, “A sa mace.”

Suka ce, “Don me?”Na ce, “Domin a surka. Kun san da yawa labaran da za mu

ri}a bayarwa sun shafi mata. Kuma abin zai }ayatar in akwaimace, su ma su sami wakiliya.”

“Ka ji masu kare ha}}in mata – feminists!” inji Yusuf.A }arshe aka amince da shawarar da na kawo cewa a sa sunan

Hajiya Balaraba Ramat Yakubu. Dalili shi ne ita ma fitacciyarmarubuciya ce wadda ke tashe, musamman tun bayan fitowarlittafinta Budurwar Zuciya, wanda na karanta a lokacin da nake]alibi a Jami’ar Bayero, Kano. Aka ce Ado ya fa]a mata, domin

ya fi mu kusa da ita. Daga nan Ado ya kawo sunan wani mutumwanda na sani – Bashir Mudi Yakasai, wanda }wararrenma’aikacin talbijin ne wanda ya zama ma’aikacin shirya fim aKano.

Na ce, “Hamisu Iyan-Tama fa? Da shi muka fara maganar.”“Rabu da shi kawai,” inji Ado. “Kai na gaya maka mu muka

san shi.”Sai Yusuf ya nemi ya ji me ya faru. Ado ya da}ile zancen.

Kuma ya }ara da cewa, “A yanzu haka rigima suke da[an’azimi. Kuma a kanku]i ne. Shi ya sa ma kaga ya zo nan. Sai kumamu sake jawo shi ajika?”

Na ce, “To ai ni na yimasa al}awari. Yanzu inya ga...”

“Ibrahim! Ibrahim!”inji Ado. “In da Hamisuza ku yi mujalla ku je kuyi. Ni zan fita!”

Na yi dariya, na ce,“Ba komai. Mu cigaba.”

Daga nan dai Ado yakashe maganar Hamisu.

Mu kenan mu shidaya zuwa lokacin.

A daidai wannanlokacin sai Yusuf ya ce,“Kada fa a yi riga-Malam-masallaci. Ba a

ra]a wa mujallar suna ba.”“Haka ne fa. To me za a kira ta?”“Jagora,” inji Ado, ba tare da ~ata lokaci ba.Na ce, “Haba, sai ka ce da makafi za mu ri}a hul]a?”Aka kawo wani sunan. Bai yi ba. Aka kawo wani. Shi ma.Sai na ce, “Mu kira ta Fim mana. Fim kawai!”“Saboda me?” inji Yusuf, ya ~ata rai.Na ce, “Saboda wannan kalma ita aka fi amfani da ita a wannan

harkar. Kowa cewa yake fim, fim, fim.”Yusuf ya ce, “Kalmar Turanci ce ai. A fassara ta da Hausa

mana!”Ado ya ce, “A kira ta Majigi.”Na yi dariya na ce, “Af, ba a rabu da Bukar ba kenan an haifi

Habu. Ai ita ma majigin kalmar Turanci ce, daga magic aka sameta, wato sihiri!”

Kowa ya ]an yi tunani. A }arshe aka amince za a kira mujallaFim. Na rubuta. Duk abin nan da ake yi ina ta rubutawa; shi akekira minutes in an yi wani muhimmin taro, wato gundarinabubuwan da aka tattauna a tsanake. A nan na rubuta sunayenmuda ku]in da kowa zai bayar. Abin da zan bayar shi ne N20,000,tunda sauran kowa zai ba da N10,000, in ban da Yusuf da zai bada N3,000, sai Bashir Mudi wanda Ado ya ce yana binsa N3,000don haka zai saya masa hannun jari da ku]in.

A wajen rubuta sunaye, sai na ce sunan matata zan rubuta.Suka ce, “Saboda me?”Na ce, “Saboda ni ma’aikacin Gwamnatrin Tarayya ne, ko

kun mance? Ba a yarda ma’aikaci ya yi kasuwanci na }ashinkansa ba a bayyane. Don haka zan zuba jari da sunan HajiyaMaryam Yakubu.”

Jin haka sai Yusuf ya ce shi ma a sa sunan ]ansa. Ado mahaka.

“To wa za a na]a edita?” inji Yusuf.Na ce, “Kai za mu sa.”Ya girgiza kai, ya ce, “Tunda ba za a sa sunana kai tsaye

Ado Ahmad Gidan Dabino Yusuf Muhammad Adamu

Page 6: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

ba ai bai kamata in yi editan ba. Ni ma ma’aikaci ne.”Ado ya ce, “To dole ne sai da edita?”Na ce, “E mana. Duk jaridar kirki tana da edita, ko da na ri}o

ne. Abin ya zama al’ada a aikin jarida.”Ado ya ce me zai hana mu sa wani suna kawai na iska? Na }i.

A nan, sai na ce a sa sunan Ado. Yusuf ya girgiza kai, ya ce,“Kada mu sa Ado. Domin Ado yana rigima da mutane da yawa acikin ’yan fim. Da zarar mujallar ta fito da sunansa cewa za a yi‘ta Gidan Dabino ce.’ Ka ga an yi mata lamba kenan. Kumawasu za su guje ta.”

Ni ko sai na tsaya kai da fata sai an sa Ado. Dalilina: Adofitaccen marubuci ne, kuma masu karatu ba za su san rigimarsada ’yan’uwansa furodusoshi ba.

Yusuf ya ce za a gane. Ya ce, “Ka ga, ni fa ni na san siyasarmatasan garin nan irin su Bala Anas. Kai dai a bar maganar saimun sake zama, in ka dawo daga Isra’ila.”

Shi ma Ado sai na ga ya amince kada a sa sunansa a matsayinedita, a kan dai wa]ancan dalilai na Yusuf.

Na ce, “To, ku dai kuka sani!”Kafin a watse, muka tattauna irin labaran da za mu ri}a bugawa.

A gaskiya, ni na kawo sama da kashi 90 cikin ]ari na irin labaran.Ina da masaniya kan irin labaran da jaridun harkokin sha}atawake bugawa, wato jaridu irin The Sun ta London da kuma Na-tional Enquirer ta Amerika. Labarai ne na ’yan }ananan al’amurra

ake mayar da su manya da }arfi da yaji. Na ce masu, “Idan wani]an wasa ya yi fa]a da wani, labari ne. Idan wata ta yi aure, kowani ya mutu, ko wani ya sami }aruwar haihuwa, duk labari ne.In Ciroki ya tafi Nijar...”

A nan take na rubuta irin wa]annan al’amura na mi}a wa Ado,na ce, “A nemo irin wa]annan labaran.”

Yusuf ya yi murmushi ya ce, “Ni da za ku bar ni, da ba irinwannan mujallar ma za mu yi ba. Mu yi mujalla wadda za taha]a abubuwa da yawa mana, kamar rubuce-rubuce da sauransu.Ta arts in general dai, ba fim kawai ba. Kuma labaran fim ]inguda nawa ne?”

Na ce, “Haba Yusuf, kada ka mai da mu baya mana! Ai akwailabarai! Kai dai bari mu fara ka gani!”

Kafin mu watse, mun yanke wasu shawarwari. Na farko anamince Ado ya nemo labarai a Kano. Na biyu, Ibrahim Shemeya nemo na ~angaren Kaduna. Yusuf zai yi rubutu kan marubutalittattafai, kamar yadda yake so. Burinmu ne Fim ta ri}a ba dalabaran shirin fim a ko’ina a Nijeriya; kai, in ta kama ma a ta~o}asashen waje. Tauraruwa ba ta yi haka ba, sai ta tsaya ga labaranKano kawai. An kuma ]ora mani alhakin tsara shafukan mujallarda komfuta – tunda na }ware a nan – yadda idan ta fito a gan tada kyau, har a ]aga ta a ce, “Kai, a nan }asar aka yi wannanmujallar kuwa?”

Za mu ci gaba a watan gobe.

Abin da sa nake karanta mujallar FIM

Hajiya Hajara Usman

Shehu Hassan Kano

SHEHU HASSAN KANO, Shugaban Majalisar ’Yan Wasa ta Jihar Kano“ALLAH Ya sani, kuma ina da shaidun da in suka karanta wannan maganar za

su ga abin da na fa]a masu watanni hu]u da suka wuce, shi ne ’yan wasa sun shakaranta mujallu wa]anda ba mujallar Fim ba, sai su ga wa]ansu labararrukawa]anda suka sosa masu zuciya ko suka ba}anta masu rayuwa. A matsayina nashugaba sai su zo su same ni suna fa]a: yaya aka yi kaza aka yi kaza? In na tambayesu ya aka yi? sai su ce ai sun gani ne a wata mujalla (ba Fim ba). Ni kuma abin danake fa]a masu shi ne a ra’ayina ba ni da wata mujalla da nake karantawa kumanake sha’awar mallakarta a kowane lokaci sai mujallar Fim. Don haka duk tambayarda za ku yi mani kan wata mujalla da ba Fim ba, ba zan iya cewa komai a kai ba. Atawa fahimtar da hankalin, ban ga wata mujalla da take burge ni saboda iya aiki babaya ga mujallar Fim. Ga shi bugunta da tsare-tsaren shafukanta suna da matu}arkyau. Kai, ko Turai aka kai mujallar Fim, Bature zai yaba kan cewa an samu

gagarumin ci-gaba a }asar Hausa wajen bugamujalla da Hausa. Abin da kawai zan ce gamujallar Fim (shi ne) Allah Ya yi taimako, Ya}ara basirar aiki. Ina taya ku addu’ar bana kusamu ci-gaba na yi wa mujallar Fim kala cikida waje. Don na lura cewa a bangon baya nekawai yawancin mujallunmu suke fitowa dakala, sa~anin na }asashen waje; kodayake nasan akwai matsalar ku]i, amma duk da hakaina ba ku shawarar ku ri}a fitowa kala a ciki,ko da shafukan (masu kalar) ba yawa!”

HAJARA USMAN, fitacciyar ’yar wasa“INA yi wa mujallar Fim fatar alheri da har ta kai shekaru biyu tana fitowa

cikin aiki mai kyau wajen }ara mana ilimi da kuma sada mu da masoyanmu tahanyar wasi}a da kuma shawarwari da suke ba mu ta cikin mujallar. Kuma ara’ayina duk da cewa ana zargin yawancin ’yan jarida da tayar da husuma, ni atawa fahimtar, ina karanta mujallar Fim ne saboda ni ban ga wasu abubuwan datake yi na aibu cikin ayyukanta ba. Shawarata ita ce ku ci gaba da }o}ari kamaryadda kuka saba yi tun farkon fitowar mujallar.”

5

Page 7: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 20016

kaset yana cewa a ba shi Nagari. Maijiran gurin ya gaya masa wai an riga anara sai an dawo da shi. A nan, ina ganinbabban nauyi ne ba a kan masu shiryafinafinan Hausa kawai ba, har ma da mu’yan kallo. Don zai zama rashin adalci agare mu muna su ku]inmu muna sayenkaset amma wasu na ara su gani a kannaira ashirin. Wannan dalili ya sa na fara

Tuya babu albasaDaga

MUHAMMED SALISU ABDUL

A HALIN da ake ciki a }asarnan, an samu kakkafuwar}ungiyoyi iri daban-daban.Kowace irin }ungiya tana damanufofi da buri ammayawancinsu a kan manufa daburi ]aya suke, wato ha]akan ’ya’yanta da kuma binal}ibla ]aya.

Duk da cewa a harkar shirinfim, musamman a Arewacin}asar nan, akwai }ungiyoyi iridaban-daban kama daga nafurodusoshi, da ’yan wasa, harzuwa kan dillalan kasa-kasai.Sau da yawa akan samumatsaloli saboda rashin ha]akai da kuma gasa. Koda yakeharkar shirin fim aba ce dadole a samu gasa a cikinta, toamma irin halin nan na wane-ya-yi-ni-ma-sai-na-yi ko kumawane-ya-sa-wane-a-wasa-ni-wane-zan-sa ko kuma ni-kamfanina-bazai-sa-wane-a-wasa-ba, irin wa]annanabubuwa sun jima sunadakushe wannan harka.

Sai dai kafa ha]a]]iyar}ungiyar masu shirya finafinaita Arewa da aka yi zai haifar

tunanin tuntu~ar masu irin wannan}orafi nawa don mu kafa wata }ungiyata masu kallon finafinan Hausa donmagance wannan ta’asar.

A nan ina kira ga shugabannin}ungiyar shirya finafinai ta Arewa da susaka ’yan kallo a cikin kwamitinsu naya}i da ~arayin zaune, kuma su dingashirya bitoci a kan shirin fim don }arawayar da kan ’ya’yan wannan }ungiyarda horar da su a kan su dinga shiryafinafinan da za su sa gwamnati ta rin}aba su gudunmawa. Misali, idan za sushirya fim a kan hannun jari, ya}i datalauci, ya}i da cin hanci da rashawa dasauransu, babu abin da zai hanagwamnati ba da nata tallafin.

Malam Muhammed Salisu Abdul yarubuto ne daga Babbar Kotun Shari’a taJihar Kano (High Court of Justice), P.M. B. 3019, Kano.

Nura Imam, Abida Mohammed da Hussaini Najiddah a cikin shirin Ikirari

irin kalaman da wasu masu wannanharka suka ri}ayi a kan aiwatar daShari’ar, za mu yarda cewa wannanhasashen ba shi da wani tushe ballemakama.

Tabbas, daga kan furodusoshi,darektoci masu ]aukar hoto, ’yan wasa,maka]a da mawa}a, dillalai, har zuwakan ’yan kallo, ba za a ta~a mantawa dairin namijin }o}arin da HonourableAlhaji Abdu Haro Mashi (SardaunanFurodusoshin Arewa) ya yi ba. Bashakka wannan gwarzon namiji yacancanci jinjina.

To amma fa akwai wani hanzari bagudu ba; akwai babban }alubale gawannan }ungiya, baya ga }o}arin zamatsintsiya-ma]aurinki-]aya akwai ya}ida ~arayin zaune. Wani abin takaici aranar da fim ]in Nagari ya fito, na jekantin Alhaji Musa na Mallam {ato zansaya, sai aka ce ya }are sai dai in komawashegari. Abin mamaki, a wannanrana da magariba na raka wani abokinawajen yin photostat, ashe gurin bidiyo-kulob ne, sai na ji wani ya zo kar~ar

da babban ci-gaba da kawar dabambance-bambancen da ke tsakaninmasu wannan harkar duk da kasancewaran kafa ta a makare idan muka yila’akari da da]ewar da aka yi ana shiryafinafinan Hausa. Ha}i}a, goyon bayanda aka samu daga masu wannan harkarya nuna cewa sun tasar wa ]inke~arakokin da suka jima suna addabarsu.To amma rashin gayyatar wakilai dagacikin masu kallon finafinan Hausa yatabbatar da cewa masu shirya wannantaro sun yi tuya sun manta da albasa.Don kuwa su ma ’yan kallon suna dagagarumar rawar da suke takawa donbun}asa wannan harkar.

Wasu na ganin kafa wannan }ungiyaba zai rasa nasaba da tsoron da masushirya finafinai ke ji na ko Shari’arMusulunci za ta hana su gudanar daharkokinsu ba. Idan muka yi la’akari da

Page 8: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Page 9: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

7

ME YA SA BA KU BUGA WASIKUNA?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN da ya sa har nadaure na sake rubuto maku wata

wasi}ar shi ne domin jin dalilin da yasa ni ba a ma kulawa da dukkanwasi}una; domin a gasarku ta Kacici-Kacici inda kuka ba da tambayarShehu Hassan Kano da ta YusufBarau duk na rubuto maku, to ammashiru ban ga sunana ba. Ko kuwaakwai wasu ku]i da ake biyankukafin ku buga sunan mutum ne? Suhotuna, na aiko da kwafe biyu ammaduk a banza. Na rubuto game daHalima Adam da tsohon mijinta banga komai ba. Amma duk da haka, gawannan amsar nan zan rubuto, saurankuma ita ma ku }i bugawa!

Sani Jaja,Ruwan Dare Video Club,Anka Road, G/Kwala, Gusau,Jihar Zamfara.

Haj Sani, a gaskiya ba da gangan aka }i buga wasi}arka ba. Ko daiba ta zo ba, ko kuma ta makara har muka buga amsar Kacici-Kacici. Kayi ha}uri!

A RAGE TSAWON TALLA A KASETZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA fatan za ku taimake ni da fili a cikin mujallar tamu mai farin jinnid o n

in shaida maku cewa ku sanar da masu fim na Hausa wani kaset ]intalla yana yin yawa. Idan kun duba Madauri ko Sai A Lahira za ku gaban da talla ba komai. Haba furodusoshin finafinan Hausa! Za ku farakashe kasuwar finafinanku fa! Shi fim komai kyawunsa, yawan tallace-tallace yana ~ata shi. Ya kamata kada talla ta wuce biyu zuwa uku. Nanma ya zama ko dai farkon fim ko kuma }arshen fim. Mu ma ma’abotakallon finafinan Hausa muna son mu ga talla, amma ’yar ka]an, ba

Muna maraba da wasi}unmasu karatu. A tabbatar an sacikakken suna da adireshi,kuma a yi rubutu mai kyau. Ata}aita bayani. A aiko da saurizuwa ga Edita, FIM, P.O. Box2678, Kano, ko kuma P.O.Box 3585, Kaduna. Tel.: 062-243112, 417347; 065-433005E-mail: [email protected]

Wasi}u

immediatepast

edition

MAWALLAFIIbrahim Sheme

*DARAKTA

Alh. Garba Dangida*

EDITAN RIKOShafi’u Magaji Usman

*MATAIMAKIN EDITA

Ashafa Murnai Barkiya*

WAKILAIKano: Kallamu Shu’aibu, Yakubu IbrahimYakasai;Wudil: Auwal Idris; Kaduna: Iro

Mamman, Aliyu Abdullahi Gora; Jos: SaniM. Sani; Katsina: Bashir Yahuza; Zariya:Galin Money; Sokoto: Bashir Abusabe

*MARUBUCI NA MUSAMMAN

Danjuma Katsina*

KASUWANCIMukhtar Musa Dikwa

*GUDANARWA

Sadiya Abdu Rano*

HOTOBala Mohammed

*KOMFUTA

Mary Isa Chonoko*

MASHAWARTAAlh. Kasimu Yero, Dr. Abubakar A.

Rasheed, Alh. Yusuf Barau, Haj. BalarabaRamat Yakubu, Alh. Sa’idu M. Sanusi, Alh.

A. Maikano Usman,Alh. Habibu Sani Kofar-Soro

*LAUYOYI

Mamman Nasir & Co., Kaduna, SadauGarba & Co., Kaduna

Mujallar FIM tana fitowa ne a kowane watadaga kamfanin Fim Publications, No. 22,Zaria Road, Gya]i-Gya]i, by Fly-over,Kano, Nijeriya. Ofishinmu a Kaduna: S. 11,Ibrahim Taiwo Road, saman asibitin ‘Ya’uMemorial,’ gefen Kasuwar Barci, TudunWada, Kaduna. A aiko da dukkan wasi}uzuwa ga Mujallar FIM, P.O. Box 2678, Kano,ko P.O. Box 3585, Kaduna. Tel.: 062-243112; 065-433005.Adireshinmu na E-mail:[email protected]. Ba a yarda a sarrafakowane ~angare na wannan mujalla ba tareda izini a rubuce daga mawallafanta ba. Maisha’awa zai iya karanta Fim kyauta a ko’inaa duniya ta hanyar Internet ta wannanadireshin: www.kanoonline.comHa}}in mallaka (m) Fim Publications

Mujallar FIM a ‘Internet’Shin ko ka san cewa daga wannan fitowar za ka iyakaranta mujallar Fim kyauta a ko’ina kake a duniya?Masu karatu za su iya karanta mujallar a Amerika da}asashen Turai da Indiya da China da }asashen Afrika(kai, ko ma ina a duniya) ta hanyar zamani ta ‘Internet.’Kawai ka duba wannan adireshin a na’urar komfuta]in ka, za ka mujallar baki ]ayanta, kuma kyauta –maganin mai wayo!

www.kanoonline.com/mujallarfim

WWW.KANOONLINE.COM/MUJALLARFIM

Page 10: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 20018

masu yawa ba.Bala Idris Bara,c/o K.A. Dalladi (Walin Bara)P.O. Box 50, Kir, Jihar Bauchi.

HAR YANZU BABU KAMAR BIBAZUWA GA MUJALLAR FIM,

A GASKIYA wannan mujallar tana matu}ar burge ni, don inajin da]inta }warai da gaske. Saboda haka na yanke shawararrubuta wannan ta}aitacciyar wasi}ar tawa. Na rubuto wasi}ardon in yaba ma Hauwa Ali Dodo (Biba) tare da jinjina mata donirin namijin }o}arin da take yi wurin shirya fim. A gaskiya idanka duba mata masu shirya fim gaba ]aya da wuya ka sami kamarHauwa a cikinsu. A gaskiya ni dai ina son ta matu}a har cikinraina.

Zulaihat Lawal Ahmed,No. 21B, Tafoki Road, Funtuwa,Jihar Katsina.

INA YABA AIKINKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA fatan masu karanta mujallar Fim suna lafiya. Mujallarmumai farin jini! Ban ta~a yo muku wasi}a ba, amma ni ba ba}o bane wajen karatun mujallar. Saboda Antina takan sai mun duklokacin da ta fito. Ni ]an makaranta ne. Ina yabawa da aikinku.Allah Ya saka maku da alheri. Bayan haka ina son in isar dasa}on gaisuwata ga wa]anda nake son finafinansu, kamar FatiMohammed, Sani Musa (Danja), Hajara Usman, Amina Garba(‘Sweet Mummy’), Hajara Abubakar (Dum~aru) da kuma IbrahimMandawari.

Umar Suleiman Mulumfashi,Sheikh Abubakar Gumi College, T/Wadac/o Hajiya Ladidi Yusuf,No. A.K. 1, Sallau Road, Badikko, Kaduna.

FATI CE KE DA MAGANIN CIWONAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai farin cikin rubuto maku wannan wasi}a. Wannan shin e

karo na farko da na rubuto maku wasi}a, don haka ina fatanza ta samu shiga wurinku. Ina neman ku share mani hawayenaku isar mani da sa}ona wajen Fati Mohammed; sa}on kuma bawani ba ne illa ku ce mata ina da wani ciwo, ba ya da magani saiwurinta. Bu}atata kuwa ita ce hotonta nake so ta ba ni.

Sannan kuma ina so ku mi}a sa}on gaisuwata zuwa gaMandawari, Aminu Shehu Dambazau, Ali Nuhu, Ishaq Sidi Ishaq,Zik, Hajara Usman (Hajjo) da sauransu.

Hajara Sabi’uSaulawa Quaters, c/o Amasad Video Link, General Hos-

pital Road, P.O. Box 130, Katsina.

INA ’YAN FIM SUKA SA GABA?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuto maku wannan takarda tawa shi ne don in ba’yan fim shawara. A gaskiya in Shari’a ta hana su fim, to

wallahi ta yi daidai. Ni ban ga laifinta ba domin abin nasu ya farawuce maka]i da rawa domin da yawansu sun shiga harkar fim alokacin da take da darajarta ba kamar iyayenmu na baya bawa]anda suka bayar da kansu don wayar da kai da ci gabanal’adunmu da addini. Don haka ya kamata su tashi su san gari yawaye; in suna fim ne na ilimantarwa mu sani, in kuma ki]a dawa}a ne, to mu sani don mu san inda suka sa gaba.

Usman (Theatre Staff),NNPC Housing Complex Hospital,PMB 2285, Kachia Road, Kaduna.Tel: 062-515645, 511527

SHAWARA KAN YAWAN WASIKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in ba da wata shawara a kan yadda na fuskacin cewawasi}un da ake aiko maku suna da yawa }warai da gaske duk

da cewa wasu daga cikinsu ba masu ma’ana ba ne. Sannan kumakowa so yake ya ga cewa an rubuta sunansa a cikin kowacefitowa ta mujallar Fim. To a bisa wa]annan dalilai ne nake so inba ku shawara da ku ware lokuta ko wata na kowace wasi}a daaka aiko maku. Abin da nake nufi shi ne duk wasi}ar da akakaranta aka ga cewa tana da muhimmanci to a ware }arni-}arni,ba a ce dole sai a watan da aka aiko za a sako ta ba; a}allamutum ya sa rai ta yi wata biyu kafin ya ga

Wasi}u

Duk wani wanda yake so yafa]i wani abu muhimmi a kanharkar finafinan Hausa,to a Mujallar FIM zai so ya fa]imaganarsa...

* an fi karanta ta* ga kyan tsari da yawan shafuka* ga hikimar lafazi* ga kamanta gaskiya* ga isa kowace jiha* ga fitowa a kowane wataShirya fim ba tare da tallata shi ba kamar harara a duhu ne. Me zai hana ka sa tallarka a cikin FIM?

Jagorar Mujallun Hausa

Page 11: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001 9

cewa an saka wasi}arsa. Ko kuma a ware shafi ko shafuka kamarbiyu a yi jerin sunayen wa]anda wasi}unsu suka zo kusan iri]aya, sai a za~i guda daga cikinsu a buga. Da fatan za a dubawannan shawarar.

Abba Atiku,Tsamiyar Boka Bus Stop, Hotoro North, Kano.

ALLAH YA SAUKI HALIMA LAFIYAZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan Allah Ya yi muku jagora a kan wannan aiki, amin.Sai kuma gaisuwata ga Halima Adamu Yahaya da kuma taya

ta ba}in ciki a a kan abin da ya faru. To Halima kada ki manta da}addara wadda ta riga fata. Don haka ki mi}a al’amuranki wurinUbangiji; haka Ya so a gare ki. Allah Ya sauke ki lafiya kuma Yaba ki mai biyayya ga Ubangijinsa amin.

Shawara ga Biba da Fati: tunda kun yi fice a duniya to donAllah ku mutunta kai ku yi rige-rigen yin aure don shi ya kamataku sa a gaba ba fa]a ba, don na yi mamakin ganin wani labariinda aka ce kun yi fa]a. Da fatan Allah Ya kiyaye gaba amin.

Mariya Aliyu,c/o Muhammed Kabir Jumare,N.B.T.E., Kaduna.

ISHAQ NE LAMBAWANZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN wannan wasi}a shi ne don ni jinjina wa shahararre,gogagge kuma }wararren ]an wasa kuma darakta, Ishaq

Sidi Ishaq (Yaro ]an }walisa) bisa ga nuna baiwa da basira danatsuwa da Allah Ya yi masa wajen shirya fim. A wajena shi nelambawan a daraktoci.

A gaskiya Ishaq ya yi darakta a finafinai da yawa kuma kowaya so su saboda tsabar ha]uwa da kuma }warewa wajen ba ’yanwasa umarni. A dalilin haka ya sa nake kira ga sauran daraktocida su yi koyi da natsuwa irin na Ishaq. Sannan kuma ina so sukasance masu kishin Arewa kamar yadda shi yake yi ba tare danuna bambanci ba.

Ina son sauran daraktocin su sun cewa Allah Ya yi wa Ishaqbaiwa ta ilimi, tunani, natsuwa da tsabar basira. Shi ya sa har agama kallon fim ]in sa ba za ka ga wata mashkila ba. Ku dubimisali da finafinan Aljannar Mace, Wuya, Sakayya, Juyin Mulkida Wasila.

Shehu Hassan Suleja,c/o Yusuf Aminu Ras,U/Kuren-ki Suleja, Jihar Neja.

INA SON KALADAR MA’AIKATAN FIMZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ina son kalandar ma’aikatan wannan mujallarsaboda ba mu san ku ba sai sunayenku da muke gani. Shi

ya sa nake son hotunanku cikin kalanda. Da fatan za ku aikomani da ita.

Sisinaho Umar Kafar Bai,C/o Salama Video Centre Opp. Sabon-LayiMagana Hotel, Katsina.

NI ZAN AURI FATI MOHAMMEDZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan alheri ga mujallar Fim da ma’aikatanta gaba ]aya.Allah Ya ja zamanin mujallar farin wata sha kallo!

Mahassadanki fadawanki! kin yi taki kin yi ta raggo! Wuyar aikiba a fara ba! Sama da ikon Allah mujallar Fim!

Bayan haka ina son ku isar min da wani sa}o nawa ga watayarinya wadda ban san yadda zan kwatanta irin son da nake yimata ba. Wannan ko ita ce Fati Mohammed. Wannan sa}o bawani sa}o ba ne illa a shaida mata cikin wannan mujallar cewarni Ubale Lawal ina }aunarta da aure tsakani da Allah.

Na ji Fati tana cewa wai za ta yi aure. To ni na san kawai tanafa]a ne. Amma in ta amince man, in Allah Ya so zan aure ta.

Kuma in na aure ta zan iya barinta ta yi fim in tana bu}ata sabodahanya ce ta neman abinci kuma duk mata ga su nan a ofis-ofisda makarantu suna aiki don neman abinci. To fim ma makarantace ta ilimantar da jama’a.

Ubale Lawal Buns,Bakin Kasuwa Daura,Jihar Katsina.

MATA KU YI TAKA-TSANTSANZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan alheri a gare ku baki ]aya nake son ku ]an ba ni filia cikin mujallar mai farin jini domin in isar da sa}ona ko

kuma garga]i ga ’yan wasa, musasmman mata wa]anda ke daniyyar yin aure. Garga]in shi ne ya kamata yanzu ku yi hankalikuma ku yi taka-tsantsan da duk namijin da ya zo ya ce wai yanason ku da aure ba tare da sanin halinsa da asalinsa ba. Ku yinazari ku ga cewa wasu mayaudara ne sai sun ci moriyar gangasu yada kwaurenta, musamman kamar yadda ta kasance a kanJamila Haruna da kuma Halima Adamu Yahaya.

Abubakar Jabbi (Lucky Boy),c/o Abubakar Bawa Aliyu,Education Department, C.S.T., The PolythechnicPMB 1034 Birnin Kebbi.

MANDAWARI BAI FADI GASKIYA BAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA karanta jawabin da Ibrahim Mandawari ya yi lokacin aurenHalima Adamu Yahaya, inda ya ce shi a kasuwa yake. To a

gaskiya ku mazan nan kuna fa]in wannan kalma ce wadda kunsan ba zai yiwu a ce mata za su taya ba, domin wannan harka ceta aure; maza aka sani da tayi. Shi ya sa ma Allah (SWT) Ya cemaza su ba da sadaki. Saboda haka idan Mandawari da gaskeyake yi, to lallai ya furta wadda yake so a cikin ’yan fim ya ganiko ba za a yi da shi ba. Ai ka ga Ciroki shi ma ya ce a kasuwayake amma har sai da ya taya sannan aka yi da shi. Kuma wannanba kalami ne na gaskiya ba, tunda neman aure wajen ku mazayake. Da fatan wannan shawara tawa za a dube ta da tunani a yiamfani da ita.

Mrs. Jamila Deeni,c/o Deeni Suleiman Adamu,Bauchi Emirate Council, Bauchi.

AURE? KADA BIBA TA DAMU!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA ]aya daga cikin wa]anda mujalla ba ta wuce su kuma inason in yi amfani da wannan dama domin mi}a ta’aziyyata ga

Hauwa Ali Dodo saboda rasuwar mahaifiyarta. Allah Ya ji}antada rahama, Ya ba ta aljannarsa firdausi, Ya kuma ba zuri’artaha}urin jure wannan rashi.

Kuma ina son in sanar da Hauwa cewa gaskiya duk wandayake da ]iya, to babu abinda yake fata illa ya ga ranar aurenta.To amma ni na san cewa aure, mutuwa, da haihuwa duk suna dalokacinsu, kuma duk wanda ya yi }o}arin kawo ]aya daga cikinwa]annan lokacisa bai yi ba, to wallahi wahala zai yi kawai.Saboda haka kada ki damu kanki. Idan lokaci ya yi za a yi.

Aminu Ibrahim Lere,14, Kashim Ibrahim Road, Kaduna.

MUNA GAMSUWA DA AIKINKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuto maku wannan wasi}ar shi ne don in nunanawa farin cikin da fitowar wannan mujallar taku mai daraja . . Agaskiya muna gamsuwa da duk irin bayanan da kuke bayarwada kuma irin ra’ayoyin jama’a da kuke bugawa a mujallar. Inamaku fatan alheri. Ubangiji Ya }ara maku fahimta, amin summaamin.

Wasi}u

Page 12: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Wasi}u

10

Bayan haka, ina so a mi}a mani gaisuwata ga jarumaina AliNuhu, Rabi Mustapha, Fati Mohammed, Maijidda Abdul}adir,Wasila Isma’il, Hauwa Ali Dodo, da kuma Galin Money.

Binta Lawal Bakori (Ladidi),KWND 32, Dutsinma Street, Opp. Kasuwar Barci,Kaduna.

BURINA IN KARANTA FIM,ZUWA GA MUJALLAR FIM,

GAISUWA irin ta addinin Musulunci. Ina fatan duk kuna lafiyaamin. Bayan haka, a kullum burina bai wuce in karanta

mujallar Fim ba. Ina kuma jin da]in karanta ta daga farko har}arshe. Don haka ina taya ku addu’ar Allah Ya taimaka maku akan mujallar Fim, Allah kuma Ya ba ku sa’a, amin.

Daga }arshe nake son ku mi}a gaisuwata ga Hindatu Bashirda kuma Tahir Fagge da Wasila Isma’il da duk sauran ’yan wasamaza da mata. Allah Ya taimaki mujallar Fim!

A’ishatu Umar,T/Wada U/BajogaGombe.

KUMURCI, DAINA WUCE GONA...ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN wannan wasi}a tawa shi ne in gaya ma Shu’aibuLawan (Kumurci) cewa ya daina over-acting (wato wuce

maka]i da rawa a wasa). Shi a zatonsa yana burge mutane, ammabai san duk a banza yake ba. Kamar a Jumur]a, ya dinga sambatuyana ihu kamar wani sabon mahaukaci.

Ina ro}on furodusoshi da daraktoci a kan su daina bai waKumurci irin wannan matsayin, don sam ba ya burge mu.

Godiyata ta musamman ga Maijidda da Abida da furodusa SirHafizu Bello.Mariah Ujudud ShariffNo. 634 Sabuwar Kofa,Kano.

A DAINA SA BOKAYEZUWA GA MUJALLAR FIM,

HABA ’yan’uwa Hausawa! Yaya muke haka? Sanin kowa necewar a al’adar Hausawa babu boka sai malamai. Mun san

cewa ba a }asarmu ka]ai fim ]in Hausa ke tsayawa ba. Sabodahaka don Allah a daina amfani da bokaye.

Sannan kuma, daraktoci da editoci a ri}a kula wajen koya wa’yan wasa fa]ar kalmomi sosai. Kamar a Uwargida, Shu’aibuLawan Boss yana cewa, “Muna importing da exporting ]in kayane daga Paris, Japan, etc.” Saboda haka ana cin su gyara wurinfa]ar kalmomin Turanci.

A }arshe ina mi}a gaisuwata ta musamman ga Fati Ibrahim(Tasalla), Ali Nuhu, Sir Hafizu Bello da Ibrahim Maishinku ([an{aruna).Barira Ujudud Shariff,F.G.G.C. Minjibir,P.M.B. 3414, Kano.

JINJINA GA ’YAN WASAZUWA GA MUJALLAR FIM,

YAYI! A gaskiya babu abin da zan ce wa ’yan wasa wurin}o}arinsu na yin finafinai sai Allah Ya sanya alheri. Jinjinata

ta musamman ga Sir Hafizu Bello, Ali Nuhu, Alhassan Kwalle,Fatima Ibrahim (Tasalla), Abida Mohammed da Sani S.K.Kuma shawarata ga Shu’aibu Kumurci ita ce ya daina wuce gonada iri a wasa, ya san me yake yi tun kafin ya kashe wa kansakasuwa.Ainal Hayat,Fed. Govt. Girls College,

Kazaure, Jihar Jigawa.

A DAINA ARO DAGA WAJEZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai ba da shawara ga furodusoshi da daraktoci a kan donAllah su dinga amfani da komai namu na Hausa. A gaskiya

akwai aro da yawa; za ka ji wa}ar Hausa tamkar ta Indiya; baabin da ya raba in ban da kalmomin da ake fa]i. Misali, wa}arAlaqa, kowa ya ji ta ya san wa}ar Indiya ce. Don Allah a dingakoyi da ‘Sarauniya Production.’

Haka kuma wajen are-aren kalmomi, don Allah a dinga furtasu daidai, don guje wa kunya, domin kuwa finafinan Hausa bainda ba sa shiga a fa]in duniyar nan. Ina fata za a gyara.

A }arshe nake cewa Allah Ya }ara wa Sir Hafizu Bello basiraamin. Gaisuwa ta musamman ga Hafizu, Rufa’i Nasidi (maiBadali), Nura [anfillo, Fatima Ibrahim (Tasalla), Alasan Kwalle,da Sani S.K.A’ishatu S. Baffa,No. 634 Sabuwar Kofa,Kano.

INA TAYA KU MURNA,ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan duk ma’aikatan mujallar Fim suna nan lafiya. Inamai matu}ar farin ciki da annashuwa domin in taya mujallar Fimmurnar cika shekara 2 da kafuwa. Ina fatan wannan mujalla baza ta gushe ba har har }arshen rayuwarmu.

Kuma ba zan manta da shugabanin wannan mujallar ba tundaga kan mawallafi Ibrahim Sheme da Edita Shafi’u M. Usmanda Wakilai Kano da na Kaduna, Katsina da marubuta namusamman da mai ]aukar hoto da lauyoyin wannan mujalla dadaraktoci ina taya su murnar cikar mujallar Fim shekara biyukafuwa. Da fatan duk kun yi Babbar Sallah lafiya. Allah Ya nunamana na ba]I ba]a]a amin.

Abdulkarim M. Bashir Al’Arabi,No. K11, Saminaka Road, U/Kanawa, Kaduna.

LALLAI KU NE JAGORAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto ne domin in yi maku murnar cika shekara biyu da}ayatar da mu masu karatun mujallar Fim. Ha}i}a kun ci

sunanku na Jagorar Mujallun Hausa kai ba ma Hausa ba har masauran harsunan Nijeriya ba su da mujalla irin wannan (Fim).Don haka na yi muku suna Jagoran Dukkan Mujallu. Allah Ya}ara maku }warin gwiwa, amin.

Shehu Mohammed,No. Y5, Aliyu Gidado Road,Sabon Gari, Kaduna.

HAFIZU BELLO YA CE WANI ABUZUWA GA MUJALLAR FIM,

MUNA taya Fim murnar cika shekara biyu da kafuwa. AllahYa }ara mata farin jini da ]aukaka.

Na rubuto wannan wasi}ar domin irin rawan da Hauwa AliDodo (Biba) ta taka a cikin fim ]in Jumur]a. Ina nuna farin cikinada furodusa mai hangen nesa ya taka, wato Hafizu Bello. AllahYa }ara masa basira, amin.

A }arshe ina mi}a gaisuwata ga Hauwa Ali Dodo, Shu’aibuLawan (Kumurci) da Hafizu Bello.

Ahmad S. Umar (Imam),Block N, No 134 Ph. I Kundila,Maiduguri Road, Kano.

TAMBAYA GA IYAN-TAMAZUWA GA MUJALLAR FIM,

SA{ON gaisuwata ta musamman ga mashahurin ]an wasannan Hamisu Lami]o Iyan-Tama. Sannan a tambaye shi me

ya sa finafinan kamfaninsu ba sa fitowa a kan lokaci? Bayanhaka muna jin

Page 13: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Wasi}uda]in finafinan su kamar Ha}uri, Gashin {uma da dai sauransudomin finafinan suna ilimantarwa, musamman ma a kanauratayya

Habibu Ibrahim Obo, Govt. Day Sec School, P.M.B 17,Gashu’a, Jihar Yobe.

FATI DA ALI SU YAKI MAHASSADAZUWA GA MUJALLAR FIM,

GODIYA ta tabbata ga Allah Ma]aukakin Sarki tare dashugabanmu Annabi Muhammad (SAW). Dalilin wannan

wasi}a shi ne ha}i}a idan Allah (SWA) Ya yi maka baiwa, ban gamai maka }wace ba. Abin nufi a nan shi ne shahararrun ’yanwasan nan Fati Mohammed da Ali Nuhu sun cancanci yabo.Shakka babu, ko ba ka son matasan biyu, dole ne ka bayyanabaiwar da Jallah Ya yi masu, musamman idan ka yi la’akari darawar da suke takawa a fagen wasan kwaikwayo. Bayan hakakuma yaran ’yan baiwa ne, domin duk abin da darakta ya ba suumarni yanzu ne za su haddace shi ba tare da ~ata lokaci ba,wasu lokutan ma har sukan ci gyaran mai ba da umarnin. Irinwannan baiwar tasu ce ta sa duk irin matsayin da aka ba su suketakawa.

Ale-Isya Mohammed Sadi (AIMS),No. 268, Yaginil Islam, Layin Mangwaro, Kabuga, Kano.

INA JINJINA WA MAIJIDDAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NI ma ina so in tofa albarkacin bakina a harkar fim, kodayake na sha rubuto wasi}a amma ba ku ta~a bugawa ba; ko

laifin me na yi maku, oho! Don haka ina fatan za ku buga wannanwasi}ar. Bayan haka kuma ina son in yi gaisuwa da jinjina tamusamman ga Maijidda Abdul}adir saboda irin kama kanta datake yi a fim, ba kamar yadda wasu suke yi ba. Kuma ga shiAllah Ya yi mata kyakkyawar sura. A gaskiya, Maijidda tana burgeni!

Don Allah idan ta karanta wannan wasi}ar kar ta ba ni kunyata yi }o}ari ta aiko mani da hotonta ta adireshina; ni ma ishaAllahu za ta ga nawa hoton kwanan nan. Kuma ina so in yigaisuwa ta musamman zuwa ga dukkan ’yan wasa.

Sa’adatu Ishaq Wafa,Abubakar Gumi College, P.O. Box 679, Kankara Road,

Zango Tudun Wada, Kaduna. Tel: 062-411770

INA FARIN CIKI DA AIKINKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto maku wannan wasi}a domin in nuna maku farincikina dangane da aikin, da kuke gudanarwa a wannan

mujallar mai albarka da fatan Allah Ya taimake ku, amin. Sannankuma gaisuwa ta musamman zuwa ga mawallafi da edita da kumaIbrahim Mohammed Mandawari, Tahir Fagge, HalisaMohammed, da fatan suna lafiya, Allah Ya sa haka, amin.

Ibrahim Mai Laida,Kasuwar T/Wada Gusau, Jihar Zamfara.

HATTARA DAI IBRO!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

BA tare da wani ~ata lokaci ba ka sama min wani ]an filidomin in yi dirar mikiya a kan [an Ibro, kai har ma da Tsigai.

Tsokacin da zan yi kuwa shi ne irin yadda suke rantsuwa daayoyin Allah a wuraren da ba muhallinsu ba ko kuma sai bayanIbro ya gama jawo ayoyi kuma sai ka ga an nuna shi yana wanishirme, kamar irin kokawar da yake yi da Tsigai. To tambaya anan ita ce: idan ya ce wasan kwaikwayo ne, to su wa kakekwaikwayo? Ina ya ta~a gani a }asar Hausa Bakwai Hausawanda ke yankunan Banza Bakwai inda malami sai bayan ya jawoayoyi da hadisai kuma ya tashi yana ti}ar rawa? Shawara gareshi dai ita ce ya daina yin “Zulwajahaimi.” Idan zai fito a malami

ya tsaya a malaminsa, idan kuma tantirinsa zai ci gaba da fitowa(da ma shi ya fi dacewa da shi), to ya ci gaba. Ya daina yi waaddini hawan }awara. Idan bai canza ba kuwa to tabbas shi ne]an wasan farko da Shari’ar Musulunci za ta hau kansa.

Nasir Muhammed Mamman,Musa Muduru, mai kaset, Kasuwar Kofar Wambai, Kano.

FATI JARUMAR GASKE CE!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan wannan wasi}a za ta samu shiga. Ina ro}on arzikidon Allah mujallar Fim ta mi}a sa}on gaisuwata ga Fati

Mohammed. Bayan haka, ina sha’awar kallon finafinanta sabodaita jaruma ce wajen fim kowane iri ne kuwa, komai wahalarsa.Allah Ya }ara ba ku jaruntaka wajen shirya finafinan Hausa, amin.

Sulaiman Umar,c/o Mohammed Abdullahi, Ministry of Justice, P.M.B

1074, Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

BIBA BA TA WULAKANTA JAMA’AZUWA GA MUJALLAR FIM,

A GASKIYA ina jin da]in wannan mujalla mai farin jini. Donhaka ne nake so in yi wa masu zargin Hauwa Ali Dodo (Biba)

cewa tana yi ma mutane wula}anci martani. Sam ba haka halinHauwa yake ba. A gaskiya mutane sun yi mata mummunarfahimta, don ni a iya sanina da Hauwa, tana da matu}ar sonmutane. Don haka duk wanda ya ce ya ga Hauwa Ali ta yi masawula}anci, to bai yi mata magana yadda ya dace ba.

Kun san ji-ta-ji-ta ba ta da amfani. Haka aka yi ta ya]a ji-ta-ji-ta a kan Saima Mohammed cewa tana da wula}anci, amma dana gan ta sai na ga abin ba haka yake ba. Saboda mutuncinta harmun }ulla abota tsakanina da ita.

Jamila Suleiman,Abubakar Gumi College, Kankara Road, Kaduna.

NI FIM KADAI TA ISHE NIZUWA GA MUJALLAR FIM,

BAYAN fatan alheri ga wannan mujalla mai farin jini, ina mi}agaisuwata ga duk wani mai yi wa wannan mujallar hidima

tare da murnar shiga sabuwar shekara lafiya (2001). Tuni na shareduk wata mujalla na tsaya ga mujallar Fim domin ita ce mai bamu sahihan labaran ’yan fim ]in Hausa, ka ji tamkar gidanku]aya. Ina so in yi amfani da wannan dama domin ku ba nicikakken tarihin wa]annan ’yan wasa biyu: wato Momo, jaruminU}uba da Ibrahim Mai Shunku (Mega), jarumin Hujja.

A }arshe ina gaida Ibrahim Mandawari, Ali Nuhu, Ahmed S.Nuhu, Aminu S. Dambazau, Hauwa Ali Dodo, Abida Mohammed,sai uwar kowa, Hajara Usman.

Rabi’u A. Sani Maiduguri,c/o Alhaji Sani Mai Fata, Talba Ahmed Street, Gwange

Ward, P.O. Box 2471, Maiduguri, Jihar Borno.

Malam Rabi’u, mun ba da tarihin Aminu Shariff (Momo). Shikuwa Ibrahim Mai Shunku, sai ka biyo mu bashi.

YA ZAN SAMI FIM A MAKURDI?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN wannan wasi}a tawa a gare ku shi ne: na sayimujallarku a lokacin da na zo gida Kano a cikin azumin nan

da ya wuce. Na ji da]in karanta wannan mujalla. To amma babbanabin ba}in cikina da mujallar shi ne ba a sayar da ita a garin danake aiki, Makur]i. Don haka nake son edita ya sanar da ni hanyarda zan bi domin in ri}a samun mujallar a duk lokacin da ta fitoko da kuma nawa zan kashe.

Trooper Ibrahim YakubuAlfha Company, 72 Para. Battalion, Nigerian Army,

Makurdi, Jihar Binuwai.

11

Page 14: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Wasi}uBa mu kai mujallar Fim Makur]i a yanzu. Me zai hana ka cikafom ]inmu na ‘subscription,’ a ri}a aiko maka da ita kai tsaye?

SHAWARA KAN MASU KASHE AUREZUWA GA FURODUSOSHI DA DARAKTOCI,

ALLAH Ya }ara wa mujallar Fim farin jini kamar watan Sallah,amin! Dalilin rubuta wasi}ata shi ne domin in ba ku shawara

cewar ya kamata ku ri}a shawartar ’yan wasa mata da su yi auretun lokaci bai }ure masu ba, su bar na }asa da su su mayegurbinsu. Su ]in ma idan zamaninsu ya wuce sai a kawo wasu.Idan kun yi haka kuma kun huta da zargin da ake maku cewamatan shirin fim karuwai ne. Bayan haka duk wacce ta kasheaurenta kada ku ]auke ta a fim; ku ce mata zamaninta ya wuce.Allah Ya ba ta mijin aure ta koma gidan miji.

A }arshe ina mi}a gaisuwata ga shugaba Shehu Hassan Kanoda Sarki Ibrahim Mandawari da Auwalu Sabo da Hamisu Lami]oIyan-Tama da Tahir Fagge.

Shafi’u Alhaji Musa Aliyu Mai ShagoBakin Kasuwa, Tafida Street, P.O.Box 5, Ibi, Jihar Taraba.

ABIN KUNYA, TOZARTA ’YAN WASAZUWA GA MUJALLAR FIM,

KASANCEWATA mai }aunar finafinan Hausa, ban so ganinirin halin da bikin Gala ya shiga a Kaduna ba. Ni dai na ga

rashin kishin Arewa daga gun ’yan’uwa matasan Kaduna. Agaskiya an tozarta dukkan wa]anda muke alfahari da su kamaryadda ’yan Kudu ke yi (Nigerian Films) in an lura, makaminmukenan na ya]a al’adunmu na Hausawa. Amma sai ga shi munmanta mun tsara cin mutuncin ’yan’uwanmu masu shirya manafinafinai masu ma’ana gami da wayar da kai. To a nan ina kiranmatasa da mu guji wula}anta ’yan wasa, don bai kamata ba.Wannan abin kunya ne a gare mu.

Ina aka ta~a jin ’yan Kudu masu Nigerian films sun aikatawani abu irin haka, wato na wula}anta ’yan wasansu? Domin susun san abin da suke yi, ba sa yarda su muzguna wa kowa, saidai su }ara daraja su ’yan wasan. Ga shi dai sun fi mu aikatakura-kurai a cikin shirye-shiryensu, amma ba sa tozatarwa, saimu Hausawa. Haba Bahaushe! Ba ka jin kunya ne? Ko kai ba kason ci-gaban ]an’uwanka ne?

Abdullahi Isa Lanko,No. V.33, Kawo Road Kawo, Kaduna.

WAKAR WASILA TA JAWO FITINAZUWA GA MUJALLAR FIM,

ALLAH Ya kara wa mujallar Fim ya]uwa a fa]in }asar nanda }asashen waje. Ni ma’abociyar kallon fim ce, amma a

gaskiya ban ji da]in abin da aka fa]a a a kan Kanawa a cikinwa}ar fim ]in Wasila ba. Domin neman fitina ne. Allah (SWT)Yana cewa fitina a kwace take; Ya la’anci mai tada ita. Sani Danjaya mai da martani. Ga shi a Wasila 2 an sake. Don Allah donAnnabi su daina. Da Kano da Zariya duk ]aya ne; ba wanda yafi wani sai mai tsoron Allah.

Hajiya Hajjaju Alh. Barau Potiskum,Miss Baka Pot Low-Cost, Potiskum, Jihar Yobe.

BURHAN YA AURI FATI SULAIMANZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai farin cikin ci gaban fitowa wannan mujalar ta Fimdomin kuwa tana sa mu san komai game da ’yan wasa da

furodusoshin fim ta hanya mai sau}i. Bayan haka, ina son a isarmin da sa}ona wajen Fati Suleiman da Sunusi Burhan. Wallahisun dace da juna. Ina ma a ce su yi aure! Don Allah ina ro}onsuda su yi aure; kuma da fatan Allah Ya albarkaci auren, amin.

Kuma ni Nafisat ina matu}ar son A’ishat Dauda sosai. Tanaburge ni. Kuma ina fatan Allah Ya za~a mata miji nagari ta yiaure.

Nafisatu T. Abare,Salamatu Instute, P.O.Box 237, A/Ma’azu, Kaduna.

MUNA BUKATAR HOTUNANSUZUWA GA MUJALLAR FIM,

MU masu karanta mujallar Fim ne a kowane wata. Munami}a gaisuwarmu ga Ali Nuhu, Fati Mohammed, Maijidda

Abdul}adir, Aminu Shariff, Hamisu Iyan-Tama, IbrahimMandawari, Ahmed S. Nuhu, Tahir Fagge da kuma AbidaMohammed. Allah Ya }ara ]auka su, amin. Bayan haka munamasu bu}atar mallakar hoton Maijidda, Fati Mohammed, daAbida, tare da fatan za mu same su.

Umma, Asiya, Fatima da Hauwa’u Alh. Jibrin Haruna,FB3, Ibrahim Taiwo Road, Tudun Wada, Kaduna.

ALLAH SA A YI AUREN SU HAJJOZUWA GA MUJALLAR FIM,

GODIYA ta tabbata ga Allah Ma]aukakin Sarki, mai kowamai komai. Na yi farin ciki }warai da gaske ga mujallar da

na gani ta watan Nuwamba mai cewa Hajara Usman da KabiruMaikaba (takwarana) za su yi aure. Don wallahi sun dace }waraida gaske; ga shi kowannensu yana da ha}uri. Ubagiji Allah Yaba su damar yin auren, kuma in an yi Ya ba su zaman lafiya dazuri’a tagari. Ina mi}a gaisuwa ta musamman a gare su.

Kabiru AliyuNo. 6, Kangiwa Road, Runjin Sambo, Sokoto.

NA YI TAKAICIN HAKA!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan Allah Ya }ara wa wannan mujallar farin jini. Ina sonna yi amfani da wannan dama domin in nuna takaicina game

da wasu abubuwa da suka faru. Da farko dai takaicin nawa shine game da mutuwar auren Jamila Haruna da kuma HalimaAdamu Yahaya. Da fatan Allah Ya ba su mazaje nagari, amin.

Bayan haka, a ra’ayina game da kyautar Arewa Films Awardswacce aka ba Mandawari kyautar Gwarzon Shekara. A ganina,babu wanda ya cancanta a bai wa kyautar illa namijin duniya,wato Tahir M. Fagge. Daga }arshe ina mai mi}a gaisuwa ga Tahir,Halima Halisa, Jamila da Saima.

Abdulkarim M. Abdulkarim (Abuya),No. 065, Race Course Qts., Nassarawa, Kano.

KU SA WASA KWAKWALWAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mi}a gaisuwa ta musamman ga ma’aikatan wannanmujallar mai kwarjini da farin jini. Domin ni mai son karanta

mujallar ne; a kowane wata sai na saya domin kuna burge nimatu}a. Kuma ina son in ba ku wata shawara. Ina ganin zai yikyau ku saka (wordsearch puzzle), wato irin kalma da akagarwaya ko da sunan gari ko na mutane a cikin mujallarku. Gamisali nan na ha]o maku.

Wannan wasan zai sa mutane su }ara son mujallarku mai farinjini. Ina fatan za ku kar~i shawarata da hannu biyu-biyu.

Fati Muhammed,No. 9, Mohammed Monguno Road. Old GRA Maiduguri,

Jihar Borno, Tel: 076-231137, 342155.

Malama Fati, mun gode }warai da shawararki, kuma in AllahYa yarda za mu shigo da irin wannan gasar. Ki tarbe mu a gabaki gani!

GAISUWA GA ’YAN WASAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son in mi}a gaisuwa ga wa]annan ’yan wasa domin nunaso da }auna a gare su, wato Fati Mohammed da Abida

Mohammed. Allah Ya }ara masu baiwar fahimta, amin.A }arshe ina mi}a gaisuwa ga Ali Nuhu, Wasila Isma’il, A’isha

12

Page 15: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001 13

Ibrahim, Galin Money, Halima Adamu Yahaya, da Sani Musa.Ina fatan alkhairi a gare su gaba ]aya.

Habib idris,No. 42, Abba Gana Street, Fagge, Kano.

TSAKANINMU DA LERE BA FA]AZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in sanar da Kanawa cewa akwai da]a]]en wasatsakaninsu da Zage-zagi tun kaka da kakanni. Domin haka na

ji furodusan Wasila, Yakubu Lere, sau biyu yana cewa kadaKanawa su wuce gona da iri wajen yin wasa. Ai ya kamata Lereya gane cewa ba wuce gona da iri ba ne, duk wasa wasa ne.Kawai dai Kanawa suna nuna

Mun sami wa]annan wasi}un ne ta hanyar ‘E-mail.’

Wasi}u

TUBARKALLA DA ‘E-MAIL’!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

BAYAN gaisuwa irin ta addini Musulunci, tare da fatan kunanan lafiya, Allah Ya sa haka, amin. Dalilin rubuto maku

wannan wasi}a tawa shi ne da farko dai ina taya ku murnar bu]ehanyar isar da sa}o ta zamani ta hanyar ‘E-mail,’ tare da fatanAllah Ya kare ku, amin.

Mohammed Rajavi,Gidan Sarikin Fawa, Anguwan Mai Gwado, Sabon Garin

Zariya, Jihar Kaduna.

AN YI WA RADIO AMFANI BUTULCIZUWA GA ’YAN FIM NA KANO,

BAYAN gaisuwa mai tarin yawa a gare ku, muna fatan kunalafiya kamar yadda muke a nan gidan Radio Amfani FM da

ke birnin Yamai lafiya. Dalilin rubuto maku wannan wasi}ar shine domin in bayyana maku rashin jin da]inmu na dangane dawani labari na zuwan su Hindatu Bashir da Ibrahim Mandawarinan Nijar, wanda aka buga a cikin mujallar Fim guda biyu da nakaranta bayan na dawo daga Jamus inda na yi aiki a sashen Hausana Muryar Jama’ar Jamus. Gaskiya ku su Ibrahim Mandawarikuna da butulci. Abin da ya sa na ce haka kuwa shi ne in da daiku ’ya’ya ne, to da ko wani kuka ji zai soki ko }ulla wa gidanRadio Amfani sharri to za ku garga]e shi da kar ya aikata. Ammaabin mamaki ku da kanku ne za ku ce wai shugaban gidan Ra-dio Amfani ya yi }o}arin ]ana maku bom lokacin zuwanku ashekarar 1999 saboda tsakaninku ba kwa shiri da juna. RadioAmfani ta gayyato su [an Ibro, ku kuma su Mandawari da ShehuKano wani daban ya gayyato ku. To don Allah don Annabi karku zamo kamar sunan wani fim ]in ku mai suna An ci MoriyarGanga.

Abu na biyu kuma, ni lokacin da na dawo daga Turai da kwana]aya sai mutane suka soma tambayata wai an ce su FatiMohammed sun yi ha]arin mota har ta mutu. Duk garin birninYamai ya ]auki wannan ji-ta-ji-tar wadda aka ce wani gidan radiyomai zaman kasa ne ya ba da labarin kuma gidan talbijin na }asashi ma ya ba da labarin a cikin shirin su na “Taurarin Maka]a”.Domin samun gaskiyar wannan labari, ni da kaina ne na bugawaya ofishin Ado Ahmed Gidan Dabino wanda ya ce }arya newannan labarin, babu wani ]an wasa ko guda da ya ta~a samunha]ari. Kuma muka watsa labarin a gidan Radio Amfani dominkowa da kowa ya ji. Amma sai na ga mujallar Fim ta yi hira daFati Mohammed inda ta ce wai gidan Radio Amfani ne ya ba dalabarin aukuwar ha]arin. To don Allah in dai za ku fa]i magana,to ku tabbatar da sahihancinta kafin ku fa]a. Kuma kar ku mantada cewa duk wata }arya da ku ’yan wasa za ku zo da ita }asarnan, dalilin gidan Radio Amfani ne, domin ni ]in nan, ni ne nakegabatar da wani shiri da na la}aba wa sunan “Dandalin Soyayya;”tun kafin na je Jamus nake gabatar da shi a gidan Radio Amfanikuma Amfani ce ta fara gayyato ku a }asar Nijar; amman kumayanzu ita ce abin ~ata wa suna! To mu ba za mu ta~a yafe makuba, musamman ma shi Mandawari da Shehu Kano wa]anda sukace shugaban Radio Amfani, Gremah Bukar, ]an ta’adda ne, ya]ana masu bom lokacin zuwan nasu wanda suka yi wasansu agidan Sinema Vox saboda a lokacin gwamnatin wannan }asa takama hayar dukkanin gidajen wasa saboda wasannin }asashemasu magana da harshen Faransanci da ke taro a lokacin.

Wannan duk }azafi ne kuka yiwa wannan gidan rediyo na

Amfani, kuma kun ga shi rrdiyon ya ci gaba, sai ku ne ke bayakuna tsintar huluna da takalma.

Yusuf Mamman,Radio Amfani FM, BP 2096, Niamey, Niger.

AUREN DAYYABA ISYAKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN da ya sa na rubuto maku wannan wasi}a shi ne donin bayyana maku matu}ar jin da]ina da fitowar wannan ta

Fim da ke fayyace mana abin da ke gudana a rayuwar ’yan wasana Hausa, da na Turai da na Indiya. Na da]e a nan Saudiyya.Tun farkon fitowar finafinan Hausa na ji ina sha’awar kallonsu,a lokaci guda kuma sai zuciyata ce ta cika ma}il da tambayoyigame da rayuwar wa]annan bayin Allah (’yan wasa) da nakekallo. Allah cikin ikonsa sai na ga mujallar Fim a hannun wani.Sai na tambaye shi a ina ya samo ta? Sai ya ce a Nijeriya ya sayota. A ta}aice dai na samu waraka domin yanzu ba ta wuce ni akowane wata. A }arshe ina so in san shin da gaske ’yar wasannan ta Kaduna [ayyaba Isyaku ba da sanin mahaifinta take shirinfim ba sai bayan ta yi aure ya sani? Kuma ko wannan shi neaurenta na farko ko ta ta~a yi?

Nasir Hutu Na Fatsima,Buzzaqat Alqamar St., Al Hindaweyyah, Jeddah, Saudi.

Haj. Nasir, muna jin a hirar da muka yi da mahaifin [ayyabane ka samo bayaninsa. Don haka gaskiya ne. Abu na biyu da zamu iya tabbatar maka shi ne wannan ne auren [ayyaba na farko.

YA BATUN AUREN MASHAHAMA?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto maku wannan wasi}ar ne don in tambaye ku gameda wani labari da kuka buga (Fim ta 12) cewa kyakyawar

furodusar nan kuma ’yar wasa, Maryam Mohammed [anfulani(Mashahama), za ta yi aure bayan Sallah. Amma shiru muke ji.Shin ta yi auren ne ba a gayyace ku ba ne, ko a’a? A }arshe, inagaida A’isha Hamza ta Kogin Bagaja. Sai an jima.

Alhaji Laminou Gonda,Al Hindaweyyah, Jeddah, Saudi Arabia.

Alhaji Laminou, Maryam ba ta yi auren ba; in da ta yi ]in, toda ka karanta labarin a mujallar Fim ko da ba a gayyace mu ba!

FIM DIN A’ISHA YA SA NI KUKAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA da]e ina kallon finafinan Hausa masu ban al’ajabi, mamakida kuma tausayi, amma ban ta~a ganin fim da ya girgiza

tunanina, har a }arshe ya sa ni kuka irin fim ]in A’isha ba. Aha}i}anin gaskiya fim ]in ya ha]u, domin kuwa ya ha]ashahararrun ’yan wasa irin su Zik da Salaha da Mandawari daTahir Fagge. Har ila yau fim ]in yana }unshe da da]a]an wa}o}i,musamman wadda ita A’isha ]in take rerawa. Da za a ri}a shiryafinafinai masu ta~o halayen da zamantakewar jama’a kamarshida ba haka ba, koda yake Alhamdulillahi an fara samun ci-gabaa harkar.

Alhaji Laminou Gonda,Ibn Al Arzey Street, Al Hindaweyyah,Jeddah, Saudi Arabia.

Page 16: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Ina masu kukan ba su samun Mujallar Fim saboda suna nesa ko kuma ba su san inda za su same ta ba? Gamaganin matsalar ya zo. Idan ka cika wannan fom, ka ha]o da ku]in tsawon lokacin da kake bu}ata, to za muri}a aiko maka da mujallar a kowane wata. Ba za ka rasa ta ba ko da ka yi balaguro zuwa wata }asa, ko kumain ka manta ba ka saya ba! Za a ri}a kawo maka ita har gida ko ofis a kowane wata kuma a kan lokaci. Kuma baruwanka da ’yan sari da suke }ara farashi ba bisa }a’ida ba. Ka cike fom ]in nan, ka yanke da reza, ka ha]o daku]in, ka biya a ofishinmu da ke Kano ko Kaduna, a ba ka rasi]i. In kuma aikowa za ka yi sai ka aiko da cek nabanki, ka biya ku]in da sunan FIM PUBLICATIONS. Da zarar mun kar~a a banki sai mu ci gaba da aiko makada mujalla. Da]i bisa da]i, duk wanda ya biya ku]i ta wannan hanyar yana da ragi da aka yi masa. Don hakasai ka za~a – ku]in wata 6 za ka biya ko na shekara ]aya.

LOKACI KU[I RAGI ZA|I

Wata shidda N700 N80

Wata 12 N1,400 N160

SUNA............................................................................................................................................ADIRESHI...................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................................SA HANNU..................................................................................................................................TARHO (In akwai).........................................................................................................................KWANAN WATA..........................................................................................................................

*Mutum ya tabbatar duk bayanin da ya bayar game da kansa daidai ne, musamman suna da adireshi su zama wa]andaza a iya aiko wa mutum da wasi}a ne ko kuma za a same shi in an je wurin. Da zarar mutum ya ga an samu kuskure

(misali in bai ga mujalla ba bayan ya biya ku]i, to ya sanar da mu da wuri. Kuma mutum zai iya fasawa ko da ya biya,mu kuma za mu mayar masa da ku]insa cif cif a cikin ruwan sanyi.

A aiko ga: Fim Publications, No. 22, Zaria Road, Gyadi-Gyadi by Fly-over, P.O. Box 2678, Kano, ko kuma FimPublications, S. 11, Ibrahim Taiwo Road, Tudun Wada, Kaduna, P.O. Box 3585, Kaduna.

15

su, wasu kuma ake ba ta a wajen shirin.Hakan duk ana yi masu su ’yan wasan ne domin a inganta

wannan shirin a kuma isar da sa}on da ake so a isar ga jama’a.To amma duk sai ka ga sun manta, sai kawai abin ya sa zukatansumutuwa, tunaninsu ya nisanta daga gare su, rayuwarsu ta canzamatu}a. Don haka za ka ga duk wanda ya aure su zai yi wuyargaske su canza wata rayuwa wacce ta yi daidai da ta ma’auratana al’ada da addinmu saboda kawai sun saba yawace-yawacelungu-lungu,.

Bugu da }ari, ga shi kuma duk suna ji kuma suna ganin sauran}awayensu wa]anda ba su yi auren ba suna ta harkarsu, ga kumaabin duniya suna ta samu ba a wajen mutum ]aya ba, wandadole a jira shi kamar yadda suke takure.

Mutuwar auren Halima bai kamata a yanzu. Wannan ya nunamana }arara cewa ilimin da Halima ta koya wa sauran mata acikin finafinai kamar su Kara Da Kiyashi, Aljannar Mace,[an’uwa da sauransu, ba ta yi aiki da shi ba a ita tata rayuwar tazahiri. Don haka wannan ya zama gani ga wane... Kuma su masushiri ko kuma son su auri ’yar wasan fim, su yi hattara, don an ceidan gemun ]an’uwanka ya kama da wuta, to ka shafa ma nakaruwa, in kuma kunne ya ji to jiki ya tsira.

Najamuddeen Hali Ahmed,Dept. of Rural Development, Fed. Min. of Agric. & Rural

Development, PMB 2162, Katsina.

YADDA ZA KU RARRABA WASIKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA farko ina yi wa ma’aikatan wannan mujallar fatan AllahYa }ara masu haza}a da basira. Bayan haka ina so in yi

amfani da wannan dama in ba mujallar shawara a kan wasi}unda ake rubuto maku daga jama’a. Ina so ku raba shafukan dakuke buga wasi}un jama’a gida uku, kamar haka:

1. Filin wasi}un tambaya da amsa. A wannan filin za a bugawasi}ar da take bu}atar amsa dangane da mujallar Fim ko ]anwasa ko furodusa ko wata tambayar da ta shafi harkar fim.

2. Filin wasi}un shawara ko suka mai ma’ana. A wannan filinza a buga wasi}ar da take ]auke da shawara ko suka mai ma’anaga mujallar Fim ko ]an wasa ko ’yar wasa ko furodusa.

3. Filin wasi}un bayyana ra’ayoyin masu karatu. Wannan filinzai }unshi wasi}u da suke ]auke da bayyana ra’ayin mutumdangane da irin so ko }aunar da yake yi wa ]an wasa ko ’yarwasa ko furodusa ko mujallar Fim.

Farouk Mohammed Bachirawa,Kano State Primary Education Board, Ungogo L.G.A.,

P.M.B 3449 Kano.

Wasi}u

Page 17: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Advert

Zumunci

16

Page 18: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

ABOKANMU

Jibril Umar Jibril,P.O. Box 2576 Maiduguri,Jihar Borno

Mohammed A. Sa’idu,No. 245 Lagos Line, IBBMain Market, SulejaJihar Neja

Mohammed Sabi’u,No. 25, Katagum Road,Tudun Wada,Kaduna

Hajiya Zainab Sanata-One,Unguwar Kamfala Street,P.O. Box 276 Potiskum,Jihar Yobe

Al-Husain Iliyas Mai FetaNo. 64 Galadima Sallau Rd.,P.O. Box 202 Malumfashi,Jihar Katsina

Salisu Audee Elzo,Basira Film Production,Bakin Kasuwa, HausawaWard, Gashu’a, Jihar Yobe

Ayuba A. Imam Fari G/Liman,c/o Sa’idu Musa Fari,Seven-Up Bottling Co. Plc.,P.O. Box 5173, Kano

Yarima Abubakar Sadiq,c/o Garba IbrahimSaminaka, No. KJ 4, ZariaRd., Nassarawa, Kaduna

Wasu masu karatu suna aiko da hotuna marasa kyau: ko sun yi duhu, kowanda ke ciki ya yi nisa. Ba za a iya amfani da irin wa]annan ba! A tabbatarhoto ya fito ra]au, kuma a sa cikakken adireshi.

Fatima Sani Ibrahim Khalil,Ramin Hudu, P.O. Box 28Hadejia, Jihar Jigawa

Furodusoshi da darektoci da ’yan kasuwa masu dabara dahangen nesa ne suke saka tallarsu a cikin mujallar FIM

17

Mohammed LammaMaimai, Bakin Kasuwa,Jajere, Fune LGA,Jihar Yobe

Atiku Muh’d Rijau,Dept. of Mass Comm.,Sokoto Polytechnic,Sokoto.

Bala Abubakar Shiri,Dept. of Agriculture,(Vet. Section), Shira LGA,Bauchi.

Page 19: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Uwani Aliyu, Barade Road,Unguwar Sarki, Kaduna.*Maryam Mohammed Aminu Ya’u Memorial Hospital & Ma-ternity, S11 Ibrahim TaiwoRoad, Tudun Wada, Kaduna.*A’isha Falalun Katsayal, No. 2Boko Road, Katsayal,Sandamu LGA, Jihar Katsina.*Hajiya Ladidi Yusuf (Mrs.Abdulwahab), No. A.K. 1,Sallau Road, Badikko,Kaduna.*Yarleda Muntari, TsohonSarkin Kasuwar KwanarGafan, Chiromawa, GarunMallam L.G.A., Jihar Kano.*Ibrahim Abdullahi Wali (Tata),No. 520, Modibbo AdamaRoad, Adarawa Area, PO Box4143, Sokoto.*Ahmad S. Umar (Imam), BlockN, No. 134 PH I, Kundila,Maiduguri Road, Kano.*Hajiya Jamila Abdullahi, KI10, Gangara Road, Sabon Gari,Kaduna.*Hauwa Yunusa Abba, c/oAlhaji Yunusa A. Kambai, A.U.Motors Nig. Ltd., P.O. Box10770, Ahmadu Bello Way,Kaduna.*Amina Ibrahim Ozoza daHajiya Harira Haruna, SheikhGumi College, P.O. Box 679,Kaduna.*A’isha Ahmed Ladan, No 2BSafana Road, U/Sarki,Kaduna.*Amir da Walid Imam, No. KF

AMSAR GASA TA 7

Sunayen wa]anda suka gane

ISA BELLO (JA)A gasa ta 7, mun buga hoton fitaccen ]an wasa ISABELLO (JA), muka ce ku gane shi. Gasar ta fito a FIM tawatan jiya, Maris. Mutane da dama sun aiko da amsa. Munkawo sunayen wasunsu. Mun gode wa dukkan wanda yayi }o}arin aiko da amsa ko da bai ga sunansa a nan ba. Ashafi na gaba, mun sa gasa ta 8.

18

Malam Isa Bello (Ja)

4, Rock Road, K/Costain,Kaduna.*Sa’adatu Ishaq Wafa (Mrs.A.S.I.D.), No. R13 [anladiYunusa Road, U/Sunusi,Kaduna. Tel: 062-411770.*Hafseeyat Ahmed Yabano, c/oAlh. Ahmed Ganga, P.O. Box36, Gombe, Jihar Gombe.*Kabiru, Iyan-Tama Multime-dia,44, Sabon Titi, Kano.*Abubakar Muhammad, Block11, No. 9, Central Market,Bauchi, Tel.: 077-541305*Nasiru Muhammad, Block 7,No. 1, Central Market, Bauchi,Tel.: 077-541562*Zainab Baita Moh’d Kankarofi,Hospital Road, P.O. Box 36,Gya]i-Gya]i, Kano.*Abubakar Aminu, Iyan-TamaMultimedia, No. 44, SabonTitin Mandawari, Kano.*Iliya Dream Photos, Iyan-TamaMultimedia, Sabon Titi, Kano.*Nasiru Haruna, An-NaseerVideo Investment, Gusau, c/oMamman Baba UnguwarToka, P.O. Box 737 Gusau,Jihar Zamfara.*Nasir Muhammed Mahuta,Dausayin Matasa Writers, c/oIdris Hassan, Information Of-ficer, Fakai L.G.A., Mahuta,Jihar Kebbi.*Salamatu U.D., No. 1A, IdomaRoad, U/Rimi, (GRA), Kaduna.*Aiyushat Umar Faruk, Kafin

*Lawali Na Alh. MohammedMaigando, c/o Mohammed G.Lawal, Dept. of Public Admin-istration, Kaduna State Poly-technic, P.M.B. 1061 Zaria,Kaduna.*Hajiya Rabi MuhammedMaye,T32, Dogon Bauchi, SabonGari,Kaduna.*Salisu Magaji Dogarawa, P.O.Box 1036, Sabon Garin Zaria,Jihar Kaduna.*Muhammed Rajavi, GidanSarkin Fawa A/Mai Gwado,

Sabon Garin Zaria, P.O. Box14 Zaria, Jihar Kaduna.*Maryam da Ibrahim AbubakarZamzam, A.G. College, ZangoRoad, T/Wada, Kaduna.*Ahmad Saleh Bebeji, No. 6,Zaria Road, Last Bus-stop,Rigasa, Kaduna.*Maimuna Ibrahim Yarima(Mrs. Basiru), Dokaji Street,Nassarawa, Kaduna.*Umaru Mohammed KakuGashu’a, c/o Alh. Bukar Adam(Matawalin Bade), Bade LocalGovt. Area, Gashu’a, JiharYobe.

Wasu amsoshinAmsa: Zilkiflu Muhammad(Zik)A’isha Adamu,Kaduna Capital School,(Department of Commerce),P.M.B. 2039, Kaduna.*Amsa: Zilkiflu MuhammadAdamu Garba,L 47, [antajo Avenue, NnamdiAzikiwe Way, Opp. WhanuGas, Nassarawa, Kaduna.*Amsa: Zilkiflu MuhammadAbdulkarim M. BashirAl’Arabi,No. K11, Saminaka Road,U/Kanawa, Kaduna.*

Amsa: Zilkifli MuhammadShehu Mohammed Haruna,Y. 54, Gidado Road,Sabon Gari, Kaduna.*Amsa: Zilkifli MuhammadHabiba Mahmud Alhassan,Y. 59, Charanchi Road,T/Wada, Kaduna.*Amsa: Zilkifli MuhammadMusa Halidu,Sunrise International School Is-lamic Education Trust, 37,Thomas Sankara Street,Asokoro,P.O. Box 3801, Garki, Abuja.

Hausa Line, No.110, Gadon {aya,Kano.

Page 20: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001 19

Wace ’yar wasa ce wannan?Wa]anda ba su ci gasar Kacici-Kacici ta 7 ba, da wa]anda suka ci ]in,suna da damar sake kwafsawa a gasa ta 8 wadda ta fito a yau. Dubi hotunannan guda biyu. Wata shahararriyar ’yar wasan fim ]in Hausa ce lokacintana }arama, wadda sunanta ya kasance ruwan-dare-game-duniya. Waceceita? An ]auki hoto na farko inda yarinyar take ta-ta-ta a cikin 1980. A hotona biyu kuma, ’yar wasan ce ta farko a hannun dama tare da wasu’yan’uwanta a }asar Amerika a cikin 1985.

Hoto na 1

Ga satar amsa:Tana dagacikin manyan’yan wasan fima Kaduna.Ku yi maza kurubuto kafin}arshen wataku gaya manako wacece, muga wanenezakara a gasar!

Hoto na 2

*Amsa: Zilkifli MuhammadAlh. Sabi’u K.K., NagwamatseCrescent, Sabon Gari, PO Box160, Kontagora, Jihar Neja.*Amsa: Zilkifli MuhammadUmaru Haruna WadaBabayani, c/o Alh. ManniruAdamu, PO Box 126, BolariWest, Gombe.*Amsa: Zilkifli MuhammadMalam Kawu Jalingo, TudunWada, Jalingo, Jihar Taraba.*Amsa: Isa A. Isa (Halifa)Zakariyya Muhammed Umar,c/o Alhaji AbubakarMuhammed,Islamic Bookshop, BakinMasallacin Sultan Bello, P.O.Box 9730, Unguwar SarkinMusulmi, Kaduna.*Amsa: Sani Musa (Danja)A’isha Ja’afar,E6, Kabuga Housing Estate,RedBricks, Kano.*Amsa: Sani Musa (Danja)Salisu Ibrahim Kafinta KakumiBakori Local Govt., JiharKatsina.*Amsa: Auwalu Mashal

Muntari [an Santsi,Garun Malam L.G.A., Kano.*Amsa: Tahir FaggeMohammed Kabir Abdullahi,Dogarawa S/Gari L.G.A.,P.O. Box 1036, Zaria,Jihar Kaduna.*Amsa: Tahir FaggeKabir Nanaye,Dollars Man Barbing Saloon,Muh’d Wili Road, U/Sunusi,Kaduna.*Amsa: Tahir FaggeSharfaddeen Sidi Umar(Sidex), No. 1, GuiwaLowcost, opp. Custom Bar-racks, PMB 2398, Sokoto.*Amsa: Tahir FaggeNuhu Umar Kankurmi,NBY 14, Kankurmi, Turunku,Igabi L.G.A., Jihar Kaduna.*Amsa: Tahir FaggeLawali Tambai Kurba,GSS, K/Kusar, PMB 1541,Kwaya Kusar LGA, JiharBorno.*Amsa: Shehu KanoIsyaku Tanko Zakari,Nigeria Customs Service, AreaOne, Port-Harcourt,Jihar Rivers.

*Amsa: Kabiru MaikabaMurtala Mahamman,No. BB 12, Kankurmi, Igabi Lo-cal Govt., Jihar Kaduna.*Amsa: Kabiru MaikabaUsman Sambo (Osima), Chair-man, Bagaja Film Prod., BolariWest, Gombe.*Amsa: Kabiru MaikabaAlhaji Sabo A. B. Bako,No. 158, Ahmadu Bello Way,Saminaka, Jihar Kaduna.*Amsa: Kabiru MaikabaHamisu [an Hayis,Layin Tafasa, [ambatta,Jihar Kano.*Amsa: Aminu S. DambazauZainab Ashara, H. B. KogomoRoad, U/Sanusi, Kaduna.*Amsa: Aminu S. DambazauBaba Gana (Yanziye), BakinKasuwan Cross, Tashan ModuDijami, Bama LGA, Jihar Borno.*Amsa: Hamisu Iyan-TamaShehu Bakari, c/o Umaru Bakari,N.T.A., PO Box 181, Jalingo,Jihar Taraba.*Amsa: Hamisu Iyan-TamaAliyu Matazu,

Nass Agrovet & Chemicals,IT 3031, Ibrahim Taiwo Road byCentral Market, Kaduna.Tel 062-411253*Amsa: Hamisu Iyan-TamaAliyu Abdullahi Abubakar,c/o Muh’d K. Babandi Ent. M. 19, Ibrahim Taiwo Road,T/Wada, Kaduna.*Amsa: Hamisu Iyan-TamaHabu Hamidu Kurba,Primary Healthcare Dept.,Kwaya Kusar LGA,Jihar Borno.*Amsa: Hamisu Iyan-TamaJamila Jibril,c/o Lawal Usman, DambunGawo Film Production,Katsina.*Amsa: Hamisu Iyan-TamaZulaihat Mohammed, c/oZakari D. Mohammed, Govt.Sec. School, PMB 72, Kuje,Abuja.*Amsa: Ali NuhuMaryam Ibrahim,AF 16, Rigachikun Road,S/Gari, T/Wada, Kaduna.*Amsa: Ishaq Sidi IshaqBaballe [an Alhaji, ImanVideo & Audio Centre,Zonkwa, Jihar Kaduna.

Kacici-Kacici na 8

Page 21: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 200120

Taho ’Yar Halak,” sunakaranto wa}ar daga cikin}asidar da Lere ya ba su.

Fasihin mawa}in nanMudassiru {asim ma yahallara a wurin. Yana sanye da}aramar riga da wando ]inkinsafari, ya sa gilas a idonsa. Alokacin da Alee Baba yaketa~e-ta~ensa, Mudassiru yari}a yin atisayen wa}ar“She]an Yai Mani Laya Na SaNa Gaza Kwancewa,” waddaake so Sani Idris Kauru(Mo]a) ya rera a fim ]in.

Daga inda suke, suna jin maiwurin, Hamisu Lami]o Iyan-Tama, yana yi wa yaransa fa]aa kan yadda suke kar~ar wayartarho in wani ya bugo. Yanacan falo, tare da sauran jama’arda ke taruwa a wurin. Sabodayadda suke ]aga murya sunahira, sai da Lere ya ]aga tasamuryar, ya ce wa Hamisu,“Kuna damunmu fa!” Daganan suka rage sauti.

Daga bisani, an sauya FatiB. Muhammad da Zuwaira,zabiyar da ke tashe a yanzu. Daita aka sake ]aukar tsofaffinwa}o}in Wasila 1&2,wa]anda aka jera a zubinwa}a ]aya. Mudassiru ke bada umarni wajen ]aukar. Lereya sa ido, abin ya burge shi.Da ma burinsa shi ne Sharu daZuwaira su yi muryoyi irin naGalin Money da FatiAbubakar, wa]anda su sukafara yin wa}o}in; shi Gali, yasami matsala da Lere, ita kumaFati ta yi aure. Sai aka yi sa’a,Sharu gwanin sauya murya ne,don haka wa}ar ta yi daidai dawadda Gali ya yi. Haka ita maZuwaira. Da aka }are, sabodamurna sai da Lere ya ]an yijuyin rawa yana shewa donda]i.

Wa}a ta biyu ita ce “KiTaho ’Yar Halak Ki BarMuzanta Ni,” wadda ita cejagorar wa}o}in da ke cikinfaifan. Sharu da Zuwaira sukayi atisaye tare da ki]an da AleeBaba yake jefo masu ta cikinlasifika. Ainihin ki]an, Inusa

A FARKON watan Fabrairu na bana, El-SaeedYakubu Lere, furodusan fim ]in Wasila 1&2, yabayyana a ]akin ]aukar sauti na ‘Iyan-TamaMultimedia’ da ke Sabon Titin Mandawari,Kano. Daga Kaduna ya zo. Sun aje lokaci za a

]aukar masa wa}o}in da zai sa a kashi na 3 na Wasila. Idan anayi wa Lere aiki, ba a wasa. Shi a kullum cikin sauri yake, dominya tsara abubuwan da yake so ya yi. Kuma akwai shi da sonlallai abubuwansa su tafi kamar yadda ya tsara.

A wannan rana, kamar kullum, da shi ake tsara wa}o}in Wasila3. Musamman ma dai yana da sha’awar yadda ki]an wa}ar “KiTaho ’Yar Halak Ki Bar Muzanta Ni” zai kasance. Lere yana sowa}ar ta yi zarra, domin tana daga cikin abubuwan da yakeganin za su sa a sayi fim ]in.

Ma’aikatan ]aukar sauti sun hallara. Maka]i Alee BabaYakasai, sanye da guntuwar riga, yana zaune a cikin ]an guntunofis ]insa na ki]a, yana ta gwada kayan ki]ansa don ya samisautin da ya dace. Mawa}i Sharu Sidi Sharifai da zabiyoyi FatiB. Muhammad da Zuwaira kuma tuni suka gama gyaran murya,suna kallon Alee ta cikin madubin ’yar tagar da ta raba nasu]akin da na maka]in. Sharu yana sanye da kaftani, ma~allinwuyanta a ~alle, kansa ba hula. Fati kuma ta yi kyau a cikin jaratamfa da farin hijabi. Ita da Sharu suka ri}a gwada wa}ar “Ki

Daga IRO MAMMAN

Page 22: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Gumel Mai Gurmi ne ya yi shi,Lere ya yi dabara ya ba AleeBaba shi ya sake yinsa tare dasanya zamananci a cikinsa.Tuwon wa}ar, tare da miyarki]an Alee Baba, ya yi da]i.Da aka gama ]aukar wannanwa}a, sai murna ta lullu~ekowa, har duk suka mi}e sukayi rawa da juyi.

An ]an jima ana atisaye, saiHamisu ya ]aga murya, ya ceda su Alee Baba, “Alee Babakuna using janareto ne! Haryanzu a wa}a ]aya kuke?”

Jin haka, Alee Baba ya ceya shirya. Daga nan suka]auki wa}a ta gaba...

Duk wanda ke wurin yasan lallai wa]annan

wa}o}i za su yi kasuwa. Lallaitana kai wa Lere. Ko lokacinda ya kar~i wa}o}insa ya nufiKaduna, shi ma yana da fatankomai ya tafi daidai. Ya zuwayanzu dai shi ne furodusa maitashe. Fim ]insa na Wasila yazama ja-gaban duk wani fim akasuwa, har ana ganin ya fiSangaya samun ciniki. Asanadiyyarsa, Lere yaku]ance. Wata majiya maitushe ta ce Lere ya sami abinda ya kai naira miliyan biyardaga fim ]in Wasila.Ya sayimota samfurin ‘Toyota FirstLady,’ ya sayi filin da zai ginagida a Kaduna, ya yi ofis nasana kansa wanda ya }awata dakujeru da talbijin da tarho, dasauransu. Bugu da }ari, yabiya wa matarsa Makka. Gasuna ya yi. Ga auren budurwayana nema. Ga tarho na hannu,wato selula. Ga...

Abin da Lere ya sa a gabashi ne fitar da Wasila 3. Yashirya Adali, to amma Wasila3 ne ya tsone wa kowa ido, harda shi kansa. Mutane sun za}usu ga yadda labarin zaikasance, tunda an nuna angama shi a kashi na 2. Shi koLere, ya }udiri aniyar zai nunamasu irin fasahar da Allah Yaba shi. Shi ya tabbatar zai ha]afim ]in, har ya burge. Bamatsala!

Matsalar Lere guda ]aya ce.Amma bai san ta ba tukuna.Sunan matsalar Wasila Isma’ilIbrahim, jarumar fim ]inwadda ta yi tashe tun bayanfitowar Wasila 1 a cikinshekarar 2000. A gaskiya, ba

a san Wasila ba sai bayan dafim ]in ya fito. [an wasan nanYusuf Barau da furodusaMaikano ne }ashin bayanshigarta harkar fim. Ta ]an fitoa fim ]in Jinin Masoya (amatsayin Bilkisu), da Ma}iyi

suna. A harkar fim, suna kawai]an wasa yake bu}ata ya je yazama abin da zai zama. Shi kofurodusa a bar shi da ku]insa.Ita ko Wasila, ta yi tunanin yakamata ita ma ta ]ana arzikinda aka samu ta hanyar yin

gun Galin Money don surubuta wa}o}in Wasila 2), tafa]a masa an wula}anta ta aofishinsa. Har ta yi barazanarba za ta yi Wasila 2 ba wandaLeren ya sa a gaba a lokacin.Ya ce ta yi ha}uri, amma ya ce

farko, Salaha?, ya jawo masasurutu da suka. Tilas ya yi taka-tsantsan a na biyun. Wata ranaSani Mo]a ya zo ya tseguntamasa wai furodusan da Wasilatake kewayawa a gun sa,Abdullahi Maikano Usman,ya wula}anta yarinyar, abinya dame ta. Lere, wanda suketakun-sa}a da Maikano alokacin (kan batun }ungiyarfurodusoshin Kaduna), ya cea kawo ta. Ya yi mataal}awarin zai shirya fim, ya fitoda ita. Daga nan ta zama}awarsa, kullum suna tare, harwasu na cewa nemanta yakeyi.

Ya shirya Wasila. Wannanne karo na farko da wani fimya fito da sunan ainihinjarumar da ke cikinsa. Wasilata ta~a fitowa da sunanta acikin Baban Mulika, amma baita ce jarumar shirin ba. Abinmamaki, Lere bai sa A’ishaIbrahim (Salaha) a matsayinjaruma ba, duk da yake kowaya san yana tare da ita akoyaushe. Allah Ya taimake shidai, fim ]in ya kar~u, ya ratsa}asar nan kamar wutar bazara.Daga nan ne fa sai matsala takunno kai.

Da farko dai, Lere yaku]ance, ita kuma Wasila ta yi

amfani da fasaharta. Ya zuwalokacin, tana kallon Lere amatsayin aboki, ba ubangidaba. Don haka tana ganin tundaHausawa sun ce da abokindaka akan sha gari, to tilas Lereya tafi tare da ita duk inda yasa gaba. Kash! abin da ba tasani ba shi ne gogan naka yayi gaba, ya bar yarinya datsintar takalmi.

Wasila ba ta san haka ba harsai da ta je sabon ofis ]insa dake Badarawa, Kaduna. Wani~angare na ofis ]in, shagonsayar da kasakasai ne. Ba tasame shi ba, amma ta samisakatarorinsa Ijeoma daAbdullahi {waya. A cewarwata majiya, su ba su sanWasila ba. In ma sun san ta, baabin da ya dame su. Ita kotashen da take yi yana ]ibarta.Don haka tana shiga sai ta shigata~e-ta~en kayan da ke wurin.An sa faifai a rikoda, ana ji. Saita kashe rikodar, ta ]aukokaset ]in wa}o}in Wasila, tasa. Ganin haka, sai sakatarorinsuka ja kunnenta, suka kore ta.

Abin ya yi mata zafi, har taje gidan Lere ta gaya wamatarsa. Ita kuma ta ba taha}uri. Da suka ha]u da Lerea Zariya (ta je yin wani fim naUmar Mamaya, shi kuma ya je

don me ta je ofishin tana bu]e-bu]e (domin an gaya masa)?Suka dai yi ’yar hayaniyarsu anan, abin ya wuce bayansaurayinta Yakubu Nuhu[anja (jarumin Dare [aya) yasa baki.

Bayan fitowar Wasila 1,jarumar ta mayar da akalartaKano, domin ba a yin finafinaida yawa a Kaduna, ga shi tanaso ta ci nata rabon a fagen fim.Kano ce ka]ai ta ishe ta rigada wando. A can, ta }ullazumunci da jarumi ZilkifliMuhammad (Zik), har anaganin saurayinta ne domin shika]ai take saurare a birnin naDabo. Tana zaune a gidanyarta. Daga can ta zo aka yiWasila 2. Shi ]in ma ba da sonranta ta yi shi ba. Dalili shi neya zuwa lokacin, mutane dayawa sun yi mata magana kanWasila 1, ana cewa, “NawaLere ya ba ki tunda yaku]ance da fim ]in?”

Mujallar Fim ta tabbatar dacewa N5,000 Lere ya biya tata yi shirin Wasila 1. Dalilin daya sa wa]annan ku]i sukeka]an shi ne a lokacin ita bafitacciyar ’yar wasa ba ce. Dama }ananan ’yan wasa, ba suda farashi, sai abin da aka basu. Irin su Hauwa Ali Dodo

A’isha Ibrahim (Salaha) da Wasila Isma’il

21

(Zainab), da BabanMulika (Wasila), dawasu ’yan wasannintalbijin, duk a Kaduna.Amma sai bayan ta yiWasila ne, a cikin}an}anen lokaci,sunanta ya ya]uko’ina. Duk inda tagitta ana kallonta, haryara suna maimaitawa}arta, “Kin CiAmanata Wasila...”

Mujallar Fim ta yibincike, inda ta ganocewa Wasila ta da]etana jin haushin Lere.Ga shi dai shi ya fitoda ita. Sun ha]u acikin 1999, lokacinyana so ya yi fim ]insana biyu. Fim ]insa na

Page 23: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

da farashi, sai abin da aka basu. Irin su Hauwa Ali Dodo daFati Mohammed ne (wato su-perstars) ake ba naira dubu]aya a duk fitowa ]aya awasa. Shi ya sa da Wasila tazo yin Wasila 2, N7,000 akabiya ta. Wasu masu nazarinal’amarin sun ce yarinyar tanahushi da cewa Lere bai ba taku]i sosai ba bayan yaku]ance. Mun ji an ce har mamahaifiyarta Hajiya Umma tata~a ce masa, “Tun da ka sayimota, ai sai ka saya ma Wasilagida, ko?” Wato tana nufin haryanzu akwai ha}}in ’yarta akan furodusan.

Shi ko Lere, yakan gaya waabokansa cewa shi babu waniha}}in Wasila a kansa, tundaaiki ta yi masa kuma ya biyata. Abin da bai sani ba shi nezugar da ake yi wa jarumar agida da kuma a Kano, ta ratsata. Ita kanta ta ri}a nuna wa}awayenta cewa an zalince ta,musamman da yake N5,000kacal aka ba ta aka yi fim ]in.Wani furodusa a Kano ya yitsokaci a kan haka, ya ce:“Maganar banza ce da mutaneke yi cewa wai ya kamata Lereya }ara mata ku]i. Ai ya biyata adadin yarjejeniyar da sukayi. To, in da fa]uwa ya yi fa afim ]in, zai zo ne ya ce ta ragomasa ku]in da ya ba ta?”

Wani kuma cewa ya yi, “Aimu Musulmi ne. Yana da kyaua ce Yakubu Lere ya kawowani tukwici ya yi wa Wasila,tunda ya san hotonta ne yasayar a kaset ya yi ku]i. Kumarole ]in da ta yi na ~atanci ne– wato kwartanci. Ya ba ta koda atamfa ce, in ba zai ba taku]i masu kauri ba. Manta dacewa wai ya biya ta ha}}inta!”

Wata ’yar fim a Kaduna tata~o wani ~angare na matsalarwanda ba a cika kulawa da shiba. Cewa ta yi wai akwai kishia tsakanin Wasila da Salaha(A’isha Ibrahim). Ta ce wai alokacin da Wasila 1 ya fito,Lere ya yi watsi da Wasila, yakoma hul]arsa da A’isha,wadda aka ce ya ]an watsar alokacin da suke ]asawa daWasila. Da ma ita A’isha, tanabin Lere kamar bante tun dagalokacin da ya }wato ta dagawajen su Architect AbdullahiSa’idu Bello, furodusan nan

kafa.Mai ba mu labarin ta ce

wannan bai yi wa Wasila da]iba, tana ganin wato an cimoriyar ganga an yadakwaurenta kenan. Ta cewannan ya taimaka wajenhushin da Wasila ta yi da Lere.Ko Lere ya san da haka ko baisani ba, ya dai ci gaba daaiwatar da shirye-shiryensa nayin fim ]in Wasila 3. Kumaduk abin da yake ciki, bai sanarda ita ba, har ya bayyana}udirinsa a cikin mujallar Fim.

Wata majiya ta daban ta ceba laifin Lere ba ne rashin cigaba da hul]a da Wasila,domin “ai bayan an yi fim ]inita Kano ta koma ta tare. To,zai bi ta can ne yana ro}ontata zo gunsa?” A cikin Fabrairu2001 Lere ya yi kici~is dajarumar a harabar KasuwarDuniya (‘Trade Fair’) taKaduna. Suna tare da SaniMo]a. A nan, ta nemi ta jizgashi, ta nuna ba ta san shi ba.Sai da ya ha]iye alfaharinsa yayi mata magana da kansa. Anan ya yi mata bayanin zai yikashi na 3, kuma ya ]auko

za a yi ba, wai sau uku ka]aiza ta fito a cikinsa, wai A’ishaIbrahim ce jarumar! Wani yace, “Wasila ta nuna mani cewashi Lere yana ta}ama da ku]ine, ita ko ba zai burge ta daku]i ba. Don haka ta ce ba zata yi fim ]in ba ma.”

Wani ~angare na wannanrigima shi ne yadda ’yan gidansu Wasila suka shiga cikinrigimar. A da, yawancinrigingimu tsakanin furodusoshida ’yan wasa akan yi su ne cana wurin wasa. Ba sai an zo gidaba. Ita ko Wasila, yayyentaHassana da Abdullahi da Fatisun shiga cikin al’amarin, sukazama mashawartanta. Su masuna da tunanin cewa Lere baikyauta wa }anwarsu ba, harsuna duban dangantakar da ta}ullu tsakaninsa da jaruminfim ]in, Ali Nuhu. A gaskiya,Ali da Lere suna ]asawa, toamma wannan bai rasa nasabada neman aure da suke yi agida ]aya, Ali na son ya, Lerena son }anwa. An ce’yan’uwan Wasila suna zatonLere yana ba Ali ku]a]e datufafi saboda rawar da ya takaa fim ]in Wasila. Su ma sungoyi bayan kada Wasila ta yiwasan. Sun san cewa idanWasila ta }i yin fim ]in, to tazama bom kenan, ta tarwatsa}udirin yinsa. Tilas kowa yawatse.

Don haka babu mamaki, akashegarin ranar da su AliNuhu da Ishaq Sidi Ishaq daHajara Usman da Ahmed S.Nuhu suka zo daga Kano,suka ha]u da ’yan wasa naKaduna don ]aukar fim ]in,sai aka tura Wasila Kano. Saibayan ta tafi, an jira ta a wurin]aukar fim ]in, sannan ’yanfim ]in suka fara fahimtarcewa lallai akwai rikici a }asa.Ga dara ga dare ya yi! Nan danan Lere ya buga wayakamfanin ‘Mu’azzat’ a Kano,inda ake aikin tace fim, don yayi magana da Zilkifli. Ya sanyana can yana aikin tace fim]insa. Kuma ya san Zik neka]ai zai iya sa baki har Wasilata ji.

Ya yi sa’a ko, ya same shi.Lere ya yi wa Zik bayani.

Sai Zik ya kada baki ya ce, “E,ga ta nan ma muna tare da ita.”Daga nan ya ci gaba ya gaya

Zik: ya sa baki, amma abanza

wanda ya fara sa ta a fim ]inTaskira, inda ta fito da sunanMufida. Majiyarmu ta ceA’isha, wadda ]aliba ce aJami’ar Ahmadu Bello ayanzu, ta ba da gagarumargudunmawa ta ku]i wajen yinWasila 1. Ko saurayinta ya bata ku]i, sai ta ba Lere “sabodatana sonsa, so na hakika,” injimajiyarmu. To, da fim ]insaya kar~u, sai ya ]inke~arakarsa da A’isha, har yana]a ta manaja a sabonkamfanin ‘Lerawa Films’ da ya

kaset ]inwa}o}infim ]in yaba ta donta je ta ji tahaddace.Ya gayamata ranarda ake sota zo don] a u k a rfim ]in.

D a g ab a y a ,Wasila tace in daiLere bazai jeg i d a n s usu yimaganarfim ]inba, ba zata ofis]insa ba.Abin daya }ara bata haushishi ne daaka ce waiba ita cej a r u m a rfim ]in da

DUK wani ]an wasa yana yaba wa YakubuLere wajen ba da ha}}i da ya dace ga duk

wanda ya yi masa wasa. Amma abin mamaki,lokacin da yake shirya fim ]in Adali wanda yafito kwanan nan, Abida Mohammed ce ya za~aa matsayin jarumar fim ]in. Har ya buga hotontaa bayan kaset ]in wa}o}in fim ]in kuma yashigar da shi kasuwa. Kuma Fati Mohammedma tana daga cikin wa]anda ya gayyata su zoyin fim ]in, amma dukkansu sai da suka barian fara shirya fim ]in suka yi wa Lere tawaye,suka }i zuwa, ba tare da wani bayani ko sa}oba. Sai kuma ga Wasila ita ma ta }i.

Kuma ina Galin Money, wanda ya yi wa}o}inWasila 1&2? kuma ya fito a matsayin Auwalua fim ]in? Babu shi a Wasila 3, kuma wa}o}inma Sharu ne ya yi su, tare da muryar Gali. Munada tabbacin sun raba hanya da Lere. Da za a yiWasila 3, Gali ya ce sai Lere ya same shi a gidaZariya, shi ko ya }i. Kuma Gali ya sauya she}a,ya }ulla dangantaka da wani sabon furodusa aKaduna wanda ba sa ]asawa da Lere, har anna]a shi manaja a kamfanin furodusan. Shi yasa Lere ya ‘share’ shi. A madadin Gali, ya ]aukoAhmed S. Nuhu daga Kano ya fito a matsayinabokin Jamilu a cikin Wasila 3. Wato an nunako ba Gali za a yi wa}a da fim, kuma shi maGali ya nuna ko ba Lere Gali zai iya yin aikinfim. Ba a san maci tuwo ba...

Ina Galin Money?

22

Page 24: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

SANI IDRIS KAURU(Mo]a) ]an wasa ne a fim ]inWasila. Har wa yau shi neManajan Shirye-Shirye (Pro-duction Manager) a kamfanin‘Lerawa Films.’ Ya fa]a wawakilinmu ALIYUABDULLAHI GORA II yaddaya ji lokacin da Wasila Isma’ilta juya masu baya:

Fim: Menene matsayinshirin Wasila 3 tunda itataurarruwar wasan ta yi tawayecewa ba za ta yi ba?

Mo]a: To ai mu ba mu masan ko wacece Wasila ba balleta tsone mana ido. Ban dawula}anci, lokacin da aka yishirin yin Wasila na 3 mun kiraWasila mun yi mata maganakuma na je gidansu da kaina,Yakubu Lere ya je gidansu,kuma an ba ta kaset nawa}o}in fim ]in, amma sai daya rage saura kwana uku mufara sai ta bar garin zuwa Kano.Da muka buga waya sai ta cewai ita ba ta ma san za a yiWasila na 3 ba. Ka ga wannanai wula}anci ne. To ina }aragaya ma Wasila cewa ko da itako ba ta fim ]in zai yi kyau. Inkuma malaminta ya gaya matacewa ba za mu iya yi ba sai daita, to ta sake malami, wannanya yi }arya.

Fim: Me kake ganin shi nesanadin tawayen da ta yimaku?

Mo]a: A dalilin tawayentashi ne shi ]an banzan gashi koka dun}ule shi watsewa yake

yi. Saboda haka Allah Shi Yasan ingo zoman }arya da harda za ta bu]e baki ta ce manashi furodusa ya yi ku]i da ita,saboda haka tana bu}atarabubuwa da yawa bai yi mataba, wai ya yi watsi da ita, dadai sauransu.

Fim: Shin babu wani alherida shi Yakubu Lere ya yi makada Ali Nuhu da kuma Salahawanda bai yi wa Wasila ba harya sa ta yi maku tawayen?

Mo]a: Ba dole ba ne Yakubuya yi mana alheri. Aikin ku]imuka yi mashi, kuma ya biyamu. In har wani alheri ne itaaka yi ma wa domin ai a nancikin Kaduna wani furodusaya yi mata wula}anci. Ni na zona shaida wa Lere, shi kumaya ce insha Allahu zai hucemata haushi. Ya shirya fim yakuma ba fim ]in sunanta na

asali. Ta yi tunani mana, dukwanda ya san ta sabodawannan fim ]in ne ya san ta.

Fim: A matsayinka namanajan shirin Lerawa akwaiwani }o}ari da ka yi don ganincewa an sasanta tsakaninku daWasila?

Mo]a: Lokacin da ta tafiKano mun yi mata waya ta ceza ta dawo, amma ita ba za tazo wajenmu ba sai dai mu jemu ]auko ta. Da ta dawo ranarLahadi na tura Salaha cewa taje ta ]auko ta, sai ta gaya wasu Salaha cewa su gaya maniin ni ba zan zo da kaina ba kokuma Lere, to ita ba za ta zoba. Na tashi da kaina na jegidan su Wasila. Maimakon tashirya mu tafi sai suka kirataron gaggawa na dangi. Nazauna ina jira har tsawon mintitalatin. Zuwa can sai ga ta tafito. Tana fitowa sai ta dube nita ce, “Mo]a, ku tashi ku tafi.Ba zan yi ba.”

Fim: Ko akwai matakin dakuke shirin ]auka kan abin data yi maku?

Mo]a: Mu ba wani mataki daza mu ]auka, domin aikin ku]ine. “Wasila zo ki yi,” ta ce baza ta yi ba. Sai kuma in ]aukimataki a kanta?

Fim: Ko kana da watashawara da za ka iya ba ta akan abin da ta yi?

Mo]a: Ba wata shawara illacewa idan Wasila tana ganinyau tauraruwarta na haske, tota tabbatar da cewa wata ranasai dai ta ga ana yi.

Wasila ta wula}anta mu – Sani Mo]a

Sani Idris Kauru (Moda)

wa Lere cewa shi ma bai jida]in abin da Wasila ta yi ba,amma in Allah Ya yarda zaituro ta da safe ta dawo Kaduna.Ya ce kada ya damu.

Da gari ya waye, Wasila tadawo. To amma idan Zik yasan wata bai san wata ba. Saita }i zuwa gun su Ishaq, ta yizamanta a gida. Da su Mo]ada A’isha Salaha suka je gunta a gida, sai ta ce in dai Lereba zai zo da kansa ba, to itakuma ba za ta je wurin wasanba.

Ji da kai ya ha]u da ji da kaikenan. Lere ya }i zuwa.Wasila ta }i zuwa. Ishaq da Alida wani Alhaji Rufa’i suka jegidan don su zo da ita, ’yangidan suka kafe a kan ba za taba. Ko ganin Wasilar ma ba suyi ba. A }arshe aka yi fim baWasila.

Abin da ya faru ya barmutane da yawa a cikin ru]u.Tilas aka sauya labarin, akanuna cewa Wasila ta mutu aha]arin jirgin sama a kanhanyarsu ta dawowa dagaSaudiyya tare da mijinta. Saiaka nuna cewa Jamilu (AliNuhu) ya ji nasihar wanimalami a kan alfanun yin aure,kuma ya ha]u da watayarinyar daban (Fati Ibrahim,}anwar A’isha Ibrahim, wadda]aliba ce a Jami’ar Fasaha dake Minna). Sai soyayya ta}ullu a tsakaninsu. Sunanyarinyar a fim ]in: Wasila.Wato an yi Wasila biyu kenan:Wasila matar Jamilu ta farko (akashi na 1 da na 2) da Wasilata biyu wadda Jamilu ya auraa aurensa na biyu (a kashi na 3na fim ]in). Ita Wasila Isma’il,ba za a ga fuskarta ko ka]anba a Wasila 3. Darakta IshaqSidi Ishaq da furodusa Leresun kashe ta a ha]arin jirgi.

Abin da ya biyo baya shi ne]aukacin wa]anda suka yiaikin shirya Wasila 3 sun jihaushin Wasila Isma’ilmatu}a. Wasu da suka tattaunada Fim sun yi zage-zage tayadda ba za a iya buga hirarsuba. A tsakanin furodusoshitakwarorin Lere kuwa, akwaiwa]anda suka ji haushinWasila, to amma akwaiwa]anda suka yi murna.Wasu sun ce Wasila ta yi rashinmutunci, kuma su ba za su sa

ta a fim ]in su ba ko da akyauta. Suka ce abin da ta yiwa Lere za ta iya yi wa kowa.

Akwai wanda ya ce yakamata {ungiyarFurodusoshin Arewa koMajalisar ’Yan Wasa tahukunta jarumar. “In da aAmerika ne, da sai an sa waWasila takunkumin shekarabiyu,” inji shi. “A cikinwannan lokacin, ba wanda zai]auke ta ko da aikin rabaabinci a location. Ai ka gahukumar wasan }wallon }afahaka take yi.”

Su kuwa masu murna, cewa

suka yi maganin Lere kenan.Wani ya ce, “In ma ba donzarinsa ba, menene na yinWasila part 3 tunda Allah Yasa ya sami abin da zai samu akashi na 1 da na 2?” Ya }arada cewa da ma Lere ya raina’yan wasa, yana yin yadda yaga dama. “To yau ya gamu dagamonsa!”

Wani ya ce Lere ba ya dakimtsuwa. “Ka duba, ko wurin]aukar fim Lere ba zai yidukkan shirin da ya kamata yayi ba sai abu ya zo dab. A ranarda za a ]au wani scene fa yakeneman inda za a je a yi wasan!

23

To, in da yana da tsari maikyau da kimtsuwa, ai da yafahimci wula}ancin da Wasilaza ta yi masa tun ma kafin a zoyin fim ]in. Ka ga da ya yimaganin abin, kuma ya kawarda jin kunya.”

A yanzu dai an yi fim babuWasila. Zai fito a ran 5 gawatan gobe (Mayu). Daraktada furodusan shirin sun ba databbacin zai yi kyau duk dayake babu Wasila Isma’il acikinsa.

To, ya rage ruwan masukallo su yarda ko a’a bayansun kalli fim ]in.

Page 25: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Ali Nuhu ne jarumin shirinWasila. Ya fito a matsayinJamilu mijin Wasila ta farko.Ya tattauna da IBRAHIMSHEME:

Fim: Daga daidai ina ne kakeganin an fara samun matsala daWasila Isma’il a wannan fim?

Ali: A ha}i}anin gaskiyainda nake ganin an fara samunmatsala, sai da muka zoKaduna. Da za mu zo ma da nida Ahmed da Wasila akwaitsiya ma da take yi mani tarin}a cewa ai Ahmed ya aureta, Ahmed ya aure ta, har yakecewa zai je za ya ga darling]insa. Sai ni kuma nake cewa,“Wannan karon kar matar takata guje ka ta dawo hannunJamilu.”

Muka zo garin nan dai lami-lafiya. Mun yi wa shi furodusaLere bayanai kan wasufinafinai da ke gabanmu, mukafahimci juna, don haka mumuka tsai da lokacin da za afara ]aukar wannan fim naWasila 3 gaba ]aya ba tare datunanin akwai wata matsala daza ta biyo baya ba. Amma abinmamaki, ranar da za a farashooting sai aka ce Wasila taje Kano.

Yakubu ya ce, “Lafiya ta jeKano?”

Ni kuma na ce, “Maiyiwuwa wani muhimminal’amari ne ta je yi ta dawo,”tunda ta san za mu kwanaa}alla 4 zuwa 5 a Kaduna.

Har dare Wasila ba ta dawoba. Lere ya yi waya Kano, harZik ya ce zai yi mata maganata dawo. Da ta dawo, da ta zogarin nan, A’isha Ibrahim ta jewajenta, ta }i ta biyo A’isha.Aka tura Mo]a saboda shi ne‘Poduction Manager.’ Wasila ta}i zuwa.

A lokacin ne muka ce, “Tolafiya?”

Muna tare da darakta a lo-cation (Unguwar Rimi) babuYakubu Lere a wurin. Sai mukasamu wani labarin cewa saiLere ya je da kan shi. Lokacinba ya wurin.

Na ce ma darakta, “Tun daba Yakubu Lere, ya kamata mu

’yan’uwanta – Wasila ba ta nan– suka ce mana suna }o}arinsu kare mutuncin }anwarsu ne.

Fim: Su waye ’yan’uwannata?

Ali: Akwai wata yarta maisuna Hassana da kuma waniwanta da ban san sunansa ba.Sai suka ce akwai fom nayarjejeniyar aiki da ya kamatata sa hannu, (Lere) bai kawomata ta sa hannu ba, kuma aimu zuwa ya yi Kano ya ]aukomu; don me shi Lere ba zai zoya ]auko ita Wasila ba?

A gaskiya, ban ji da]i dawannan magana da suka yi ba.Mu dai muka yi ro}on suamince wa Wasila ta je tundaaikin nan sai an ha]u akecimma kowace irin nasara. Inma akwai wata matsala su barisai an natsa tukuna. Suka cesam sai in Yakubu Lere ya jeda kan shi. Muka koma mukafa]a wa Yakubu Lere yaddaaka yi.

Fim: Kai a ganinka me kakeganin ya jawo wannan abugaba ]aya?

Ali: A gaskiya ni ina ganinwannan abu ba wani abu yajawo shi ba illa yawan sauraron

Zuga ta aka yi – Ali Nuhu

Sabuwar ‘Wasila’: Fatima Ibrahim (kanwarSalaha). Ita Jamilu zai aura

mu je.”Sai ga

Y a k u b u .Muka fa]am a s a :“Wasila tace ba za tazo ba sai kaje dakanka.”

Shi kumac i k i nmamaki yace wanedalili yasanya sai yaje da kanshi? Donhaka in baza ta zo bashi ba zai bita ba.

Ni daIshaq munz a m a’ y a n ’ u w asaboda munyi aiki dayawa tare.Sai mumuka jemuka tarard a

Sabuwar Wasila (Fati Ibrahim) da Jamilu (Ali Nuhu) da kuma Ahmed S. Nuhu(wanda ya fito a matsayin abokin Jamilu a Wasila 3) a wurin walimar bikinauren Jamilu da Wasila

24

Page 26: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

}ananan maganganu najama’a. Yau duk mutumin dakuka ha]u kuka yi wani abuna arziki, sai ka ji wasu}ananan maganganu sunatasowa. Wani ba ka san shi bazai zo ya same ka ya ce,“Wane, fim kaza da ka yi ka-ji-ka-ji. Me furodusan ya yimaka?”

In an zo an same ka da irinwannan magana sai ka nunawa mutum cewa wannan fa aikine na kwangila da aka yiyarjejeniya a kan ta. Yau inasara furodusa ya yi ba zai cemu biya shi ku]inshi ba. Insuna da ra’ayin su kyautatamana bayan sun ci ribar fim,suna iya kyautata mana.

Fim: Kana ganin irinwa]annan magangun su nesuka shiga zuciyar ita Wasilakenan?

Ali: Ni dai abin da nake ganikenan. Kuma a sanin da na yiwa Wasila, ba ta yin mani com-plain (kuka) a kan Lere.

Fim: Cikin hul]arka da ita bata ta~a gaya maka akwai waniabu a tsakaninsu ba?

Ali: A gaskiya ba ta yi manikuka da shi; hana rantsuwa,akwai lokaci da ta ce mani taje ofishinshi, ko an matawula}anci? Daga baya na sameshi, ya ce ba wula}anci aka yimata ba, ta je ofishin ne tanata~e-ta~e, ma’aikatanshi sukahana ta.

Fim: A matsayinka nafitaccen ]an wasa, akwai indairin wannan matsalar ta ta~afaruwa?

Ali: A gaskiya ni ban saninda irin wannan ya faru ba,artist wanda yake damuhimmanci ya ce ba zai yi fimba a lokacin da za a fara ]auka.

Fim: Yanzu in ka ga Wasilame za ka ce mata?

Ali: Zan shawarce ta: duk]an sunan da ta yi wannan faba dama ba ce da za ta iya yiwa kowa abin ta ga dama.

Fim: Kana ganin wannan zaishafi rayuwarta ne da sauranfurodusoshi?

Ali: Ai dole ya shafe ta.Wani abin ko an ~ata maka raisai ka yi ha}uri sabodamutuncin rayuwarka.

Fim: Yanzu kai ma furodusane; za ka iya sa ta a fim ]in ka?

Ali: E, in ta dace, amma saimun yi ta da wajewa!

muna fim ]in Ba’asi na Ziktare da ita a Kano, kuma ba tanuna mani ko akwai watamatsala ba, har muke sallamada ita sai mun ha]u a Wasila3.

Duk ’yan wasa sun ha]u saini da Ali Nuhu da ya ]aukomu daga Kano. Su HajaraUsman suka yi nasu suka tafi.Ana ta kashe ku]i a otal ammawata mace guda ]aya tananeman dukkan aikin ya rushebisa dalilin da ba mu sani ba.Dalilinmu kenan na zuwagidan su Wasila ni da Ali Nuhuda wani Alhaji Rufa’i. Damuka je ba mu same ta ba sai’yan’uwanta wa]anda suke ta}o}arin kare ta tare daambaton sai Lere ya je. Tosaboda me sai Lere ya je? Abinmamaki, yadda muka je hakamuka fito.

Fim: Yaya ka ji bayan kunbar gidan?

Ishaq: A gaskiya ban ji da]iba. Saboda muna ganin kamarmun isa mu je mu nemi wataalfarma a yi mana. Har na fitofili na ce (wa ’yan’uwanta) inwata matsala ce ta ku]i kowata yarjejeniya ba su yi ba,to ni zan tsaya wa Wasila a yiwannan yarjejeniya. Amma akan wannan magana sai suka

waske wai dole sai Lere ya je.Fim: To a baya ba ka

tunanin ko an samu watamatsala a lokacing ]aukarWasila 1&2 wacce ta haifar dawannan?

Ishaq: Akwai matsalarkamar yadda na fa]a maka, atsakanin furodusa da ]an wasada darakta duk akan samukuma a daidaita. Zan iyatunawa, akwai wani lokaci damuka je gyaran wata mota alokacin ]aukar sin na }arshe aWasila 1. muna sauri musallami Ali Nuhu sabodaayyukan da ke gabansa. Hakaita ma Wasilar tana da shoot-ing a Zariya. To (ita Wasila)sun yi wata magana da Lere,ko me ya faru? Ina jin ku]i tatambaye shi. To wannan abinshi ya harzu}a Lere. Ita kumasai ta yi fushi; ka san sha’aninraunin mace! Ina tsammaninwannan zai iya zama farkonmatsalarsu.

Fim: Kuma ko ka san anbiya ta dukkan ha}}o}inta?

Ishaq: To wannan da yakesuna tare, ban sani ba.

Fim: Ba ka zaton zuga nedaga ’yan’uwanta daabokanta?

Ishaq: Kowannensu inakwai wani abu a tsakaninsu

ya je ya fa]a wa ’yan’uwansako abokansa da shi za su iyaamfani. Amma su in sun sanhalinta ba su san halin harkarba.

Fim: Tana da fitowa uku nea wasan. Yanzu da ba ta yayaka yi?

Ishaq: Gaba ]aya na gyaralabarin na juya shi. Da ita daba ita, labarin ya yi kyau. Abinda muka shi ne abin da ake sodai shi ne Jamilu ya yi aure.Don haka in ka kashe mijinWasila, ko bayan shekaranawa ne za ta dawo su sake yinaure da Jamilu. Abin da mukayi shi ne shi Jamilu da ya}udurta ba zai yi aure basaboda yana ganin mata dukamayaudara ne, sai malami yayi masa nasiha sosai ta addinikan maganganun da Manzo yayi kan muhimmancin aure.Duk wanda ya }yamaci aurekuwa ya }yamace shi (AnnabiSAW). Akwai hadisai da yawakan haka. Sai ya yarda. Ammawacece zai aura? A ]aya~angaren kuma akwai watamace da take mamakin me yasa maza suka ]auki matatamkar dabbobi? Saboda hakada ta samu labarin Jamilu saita sha alwashin kallon da yakewa

Abin da Wasila ta yi zai shafisana’arta ta fim – IshaqIshaq Sidi Ishaq ne daraktan shirin Wasila.Ya fa]a wa Mawallafin Fim, IBRAHIMSHEME, nasa ~angaren a kan rikicin Wasila.

Fim: Darakta Ishaq, a daidai wane lokacine ka fahimci cewa akwai matsala tsakaninWasila Isma’il da Yakubu Lere?

Ishaq: Lokacin da na fara fahimtar akwaimatsala shi ne bayan su Mo]a sun yi maganasu da Wasila aka ce ga ta nan zuwa, sai mukasamu labarin ta tafi Kano. Kuma sai aka cemana za ta taho daga Kanon da safiyar ranata gaba. Mun ta jiranta amma ba ta zo ba. SuMo]a suka sake zuwa da kansu, ba a yinasara ba, suka dawo suka fa]a mana. Mumuna ganin muna da ta-cewa. Ali ya cemani, “Ishaq, ka je wajen nan.” Ni kuma nace ba za ni ba saboda tana jin nauyina kumain har na je gidansu ban iya warware wannanmatsalar ba, a gaskiya ba zan ji da]i ba.Kuma da hannuna na ]au script ]in nan(rubutaccen labarin) na Wasila 3 na ba ta, Ishaq: ‘Ba Wasila ake so ba, labarin...’

25

Page 27: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

mata to ba haka suke ba. Itama wannan matar sunantaWasila. A ta}aice dai Wasila ta~ata masa, Wasila ta gyaramasa.

Fim: To ita kuma Wasila tafarko, matar Jamilu da ya saki,yaya kuka yi da ita?

Ishaq: Ta mutu! Sun taso ajirgi za su zo ganin gida jirgiya yi ha]ari ta mutu.

Fim: ’Yan kallo ba za su ganta ba ko ka]an?

Ishaq: Wallahi babu.Fim: Me za ka ce ga

wa]anda suke tunanin in baWasila Isma’il fim ]in ba zaiyi armashi ba?

Ishaq: Abin da zan ce masushi ne labari don su ake yi, saisu tsaya su kalli labarin. Shi dailabarin, ni a tunanina, don basu ga Wasila a kashi na 3 naWasila ba, gaskiya ba watamatsala, don ai ba Wasilar akeso ba, a’a fim ]in ko labarinake so.

Fim: A matsayinka na ]ayadaga cikin shugabanninwannan harka, ya kake ganinwannan abu da Wasila Isma’ilta yi zai iya shafar rayuwartata wasa?

Ishaq: Ka san mufurodusoshi da daraktoci dukmuna da ha]in kai, koda yakea matsayina na furodusa zaniya cewa abin da ya faru atsakanin wani da wata baruwana, don ban san abin daya ha]a su ba ko ya ha]a waneda wane. In na tashi yin fim

]ina zan ]auko shi.Fim: Ba ka tunanin

furodusoshi da daraktoci za su

iya ha]a kai wajen}yamatarta?

Ishaq: Ko da wasu ba su yi

ba wasu za su yi. Ina databbacin haka.

Fim: Kai a matsayinka za kaiya sa ta a fim ]in da kake dahannu ciki?

Ishaq: Zan iya sa ta. Ammaakwai wani abu da nake sonartistes (ba Wasila kawai ba) susani: kowane abu da aka yi, tobiyu aka yi; akwai wuta akwairuwa, akwai dama akwaihagu, akwai gabas akwaiyamma, akwai sama da }asa.Don haka in akwai matsayinda ya kamaci Wasila Isma’il,zan iya ]auko sabuwar ’yarwasa in gina ta ta zama yaddanake son ta a matsayina nadarakta.

Fim: In kuka ha]u da ita meza ka ce mata?

Ishaq: Ba wani abutsakanina da ita illa in ce matako menene (ya faru), ya kamatasu sasanta da Lere, don (abinda ta yi) zai iya shafar dukkanrayuwarta.

mani fim ba.Fim: Ba ka tunanin ko cikin

mahassadanka wani ya zuge tada cewa kada ta yi makawasan?

Yakubu Lere ya bayyanawa wakilinmu ALIYUABDULLAHI GORA II~acin ransa a kan abin daWasila Isma’il ta yi masa:

Fim: Yakubu Lere, kakammala duk wasu shirye-shirye da suka kamata a yi don]aukar shirin Wasila kashi na3, to sai ga shi Wasila Isma’ilta yi maka tawaye. Menenedalili?

Lere: Wallahi ban sani ba.Fim: Ko tawayen ba ya da

nasaba da ko akwai ha}}in daba ka fitar mata ba a shirye-shiryen da suka gabata?

Lere: Ni dai ban gan ta bahar yanzu, amma wa]andasuka dace a yi wa wannantambaya su ne wa]anda sukaje wajenta don jin dalilin da yahana ta zuwa yi mani wasa: AliNuhu, Ishaq Sidi Ishaq, SaniMo]a da kuma Salaha. Susuka je wajen Wasila. Ammani har yanzu ba su zo sun gayamani abin da ta gaya masu ba.Mai yiwuwa ta gaya masuhujjarta, amma ni ba su gayamani ba. Abin da na sani kawaishi ne Wasila ta ce ba za ta yi

Lere: A’a, na tabbatar yinkanta ne, tunda ai lokacin dana ce ta yi na ]aya da na biyuba wanda ya sa ta, ita ta yi donkanta. Wannan karon kuma saida muka fara shirin na 3 kawaisai ta bar garin ta tafi Kano.

Fim: Ko akwai wani }o}arida ka yi don ganin kun sasantasaboda gudun kada ka yiasarar dukiyar da ka narkacikin shirin?

Lere: Ai lokacin da muka yiWasila na 1 da na 2 ban jegidanta ba. Saboda haka banga dalilin da zai sa in je gidansudon za mu yi Wasila na 3 ba.Abin da ma yake ~ata mani raishi ne zuwan da su Ali Nuhu,Ishaq Sidi Ishaq, da kumaMo]a suka yi. Saboda ko daWasila ko ba Wasila fim ]inWasila na 3 zai yi kyau. Hasalima da ma fita uku kawai gareta cikin shirin.

Amma ban ji da]in zuwanda su Mo]a suka yi gidan suWasila ba. Umurnin da na barikawai shi ne Wasila ta zo,saboda ni ke sama da ita, aikiza ta yi mani in biya ta. Idan tace ba za ta zo ba ni ba zan jegidansu ba saboda ba ta da

Wasila 3 zai yi kyau duk dayake ba Wasila Isma’il – Lere

Ishaq yana ba Ali Nuhu umurni a lokacin daukar sashen bikin auren Jamilu dasabuwar Wasila a shirin Wasila 3

“Ita ta yiasara tundabiyanta zan

yi”26

Page 28: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

ladabi kenan, ba ta da ]a’a, nikuma ba ni mu’amala da marar]a’a.

Fim: Kana ganin fim ]in zai}ayatar da masu kallo duk dacewa Wasila ba ta cikinsa?

Lere: To wannan kuma ikone na Allah. Shi fim kamarmace ce da ciki; ba a san abinda za ta haifa ba. Amma abinda na sani shi ne mun yi iya}o}arinmu don mu ga ya}ayatar kamar yadda. N naukun ya }ayatar. Kuma sumasu kallo insha Allahu zai}ayatar da su.

Fim: Menene zurfin ba}incikin da Wasila ta guma makaa cikin zuciyarka game datawayen da ta yi maka?

Lere: Wallahi ba wani ba}inciki. Amma ta ba ni mamaki ne,saboda abin dariya ne; ai ba tada hujja kuma cutar kanta ta yi.Ni na riga na ]aukaka, AllahYa ]aukake ni. Saboda hakaita ta yi asara tunda biyanta zanyi. Wallahi na ce maka abin daya yi mani ba}in ciki shi nezuwan da su Ali Nuhu suka yigidan, amma su kansu ai ka gata guma masu ba}in ciki, donna ce masu kada su je suka cesu sai sun je. Ni kuma tunfarko da ma ban yi wani tsarida ita ba; fitowa uku kawaigare ta a cikin wasan. Ita kantata sani ta kuma san cewa koda ita ko ba ta wasan yana nanyanda aka tsara shi, kuma zaifi na 1 da na 2 kyau.

Fim: To yanzu ko akwaiwani mataki da kake shirin]auka a kan Wasila don ganinka rama wula}ancin da ta yimaka?

Lere: Ba ta yi mani laifi baai. Don me zan yi ramuwa? Aiba dole ba ne. Kiranta na yi,ita kuma ta ce ba ta yi. Yau kaida ka zo hira da ni sai na ce bani yi; sai ka ]auki mataki a kaina?

Fim: Yanzu duk dakasancewar abin da ya farutsakaninka da Wasila, nan gabaza ka iya }ara kiranta ta yimaka wani wasa?

Lere: In ya zama dole sai itaza ta iya yin abin da nike so,zan iya kiranta, ai aikin ku]ine.

Fim: Kana ganin tawayenWasila ba ya da nasaba da koakwai kyautar da ka yi mawasu ’yan wasan ita kuma baka yi mata ba?

Furodusa Yakubu Lere da Manajan Tsara Shiri, Sani Idris Kauru (Moda), alokacin daukar shirin Wasila 2

Lere: Ba wanda na ta~a yiwa wani abu. Ban ta~a yi wawani kyauta ko ta kwabo badaga cikinsu.

Fim: To ba ka ganin kokishin yadda ka ]auki Salahakuna tare ko da yaushe ana cinribar Wasila tare da ita Salahamaimakon ita Wasila ]in shi yajawo tawayen?

Lere: Tun kafin in sanWasila muke tare da Salaha.Saboda haka in ma ta yi hushida Salaha ta yi aikin banza. ItaSalaha yanzu mun zama

kamar ’yan’uwa da ita, ita koWasila kiranta na yi kawai tayi mani aikin ku]i in biya ta.Saboda haka a cikin harkar fimba wata mace kamar Salaha awurina.

Fim: Lokacin da kake shiryafim ]in Adali irin wannan tata~a faruwa da kai inda ka kiraAbida da Fati Mohammedamma suka }i zuwa. Yanzukuma ga shi Wasila ta bisahunsu. Shin halinsu kenanko ko kai ka]ai suke yi wahaka?

Lere: To ’yan jarida ku yakamata ku san irin wannan.Amma na san cewa yanzuidan Abida ta gan ni gudu takeyi. Ka ga kenan ita ma ta sanba ta kyauta ba. Fati kuma taha]u da matata ta fara yi matabayanin cewa za ta zo ta ba niha}uri. Ka ga kenan dukkansusun gane kuskurensu. Kumako’ina ana iya samun irinwannan matsalar – ka samutum wasa ya ce ba zai yi ba.

A daidai lokacin da ake }i}i-}a}a daWasila Isma’il Ibrahim,jarumar shirin Wasila 1&2,kuma komai ya tsaya, wakilinmujallar Fim SHAFI’UMAGAJI USMAN yagarzaya gidansu don jinmatsayinta a kan rikicin Wasila3. Duk da yake ta }i yincikakken bayani, jarumar (’yarshekara 22) ta ba da haske kandalilin tawayenta:

Fim: Labari ya ishe mucewar a ranar da za a fara]aukar shirin Wasila 3 sai kika}i halartar wurin ]aukar shirinkamar yadda aka yi al}awari.Me ya faru har haka yakasance?

Wasila: Babu abin da yafaru.

Fim: Mun ji cewa a ranarfara ]aukar shirin ne kika barKaduna zuwa Kano, awashegarin ranar bayan kindawo aka biyo sawunki hargida amma sai kika ce ke fim]in ne ma gaba ]aya ba za kiyi ba. Menene dalilin haka?

Wasila: Ni dalilina na rashinyin Wasila 3 shi ne: ni ba nama mutum fim don ku]i. Ni bawani abu ba ne, mutunci ne,ya sa nake ma mutum fim. Fimba don ku]i

Ko miliyan za a ba ni ba zan yiWasila 3 ba, tunda ba mutunci

– inji Wasila

27

Page 29: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

nake yin shi ba, mutunci yasa nake yin fim. Kuma idanku]i sun kai miliyan ammababu mutunci a cikinshi, towallahi ba zan yi ba. Don hakani ba abin da zan ce illa kawaimutunci ya fi ku]i.

Fim: An ce kun yiyarjejeniyar za ki yi wannanfim amma sai a ranar fara]aukar shirin kika yi tutsu,wanda haka kamar sa~aal}awari ne da kuma tozarta

yarjejeniyar. Ina gaskiyarwannan zargi da ake yi makina sa~a al}awari?

Wasila: Ni ba ni da watamagana a kan wannan. Ni fana riga na fa]a maka mutunciya fi ku]i a ko’ina.

Fim: A matsayinki nafitacciyar ’yar wasa in akanemi shawararki yadda za ainganta dangantakar ’yan wasada furodusoshi don a samunasarar shirya wasa, me za ki

Lokacin da komai yana tafiya daidai: A’isha Ibrahim (Salaha), Dayyaba Isyaku,da Wasila Isma’il, a lokacin daukar shirin Wasila 2

ce?Wasila: Wane wasan kake

nufi?Fim: Wasa kowane iri.Wasila: I, ni ’yar wasa ce,

wannan kuma kana iyatambayar furodusoshi.

Fim: Shin gaskiya ne da akeya]a ra]e-ra]in cewa kin }izuwa ne saboda kina }yashi daalherin da Yakubu Lere yasamu a kan fim ]in Wasila

wanda ke ce jarumar fim ]inkuma kina ganin ke baikyautata maki sosai ba?

Wasila: Ni duk wani abin dawani mutum zai ce ba ruwanada wani zancen jama’a; ni daina riga na fa]a maka ni bannemi komai a wurin kowa bakuma ai na fa]a maka cewamutunci ya fi ku]i, ko bai fiba?

Fim: A fahimtarmu dai,akwai wata ~araka atsakaninki da shi Lere. In akanemi a sulhunta tsakaninku zaki ba da ha]in kai har a yiwannan fim na Wasila 3?

Wasila: Kai kana janwannan magana! Na riga nafa]a maka ko miliyan za a bani in ba mutunci a cikin harkarba zan yi shi ba. Kuma bagirman kai nake yi ba, ba donwani abu ba. Mutunci ya fiku]i shi ne nawa. Ni ban ]aukiLere a matsayin furodusakawai a wajena ba; a matsayin]an’uwana na ]auke shi.

Fim: Ko ke ma kina da burinshirya fim naki na kanki kamaryadda wasu suka fara yaddawannan maganar?

Wasila: Wannan kuma idanlokacin ya yi ai kwa ji; in magaskiya ne, in ma }arya nedole za ku ji, tunda abin duniyaba mai ~oyuwa ba ne.

Hajiya Binta Abubakar (Makwasa)

Allah Ya yi wa uwarmu kuma kakarmu rasuwa, watoHAJIYA BINTA ABUBAKAR SHEME (wadda aka fisani da sunan HAJIYA MAKWASA).

Ta rasu a gida a Kano a ranar Lahadi, 25 ga Maris,2001.

Ta rasu tana da shekara 92 da haihuwa.

Hajiya ta rasu ta bar ’ya’ya da jikoki da tatta~a-kunne, cikinsu har da jikanta Malam Musa GamboSheme, ma’aikaci a kamfanin mujallar NigerianOutlook da ke Kano.

Allah Ya ji}anta, Ya sa ta huta, amin.

28

Page 30: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

IBRO: Na gaido Ubangiji,kuma na yi mugun gani!

Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA

AIKIN Hajji na bana ya samihalartar wasu manyan ’yanwasan fim na Hausa. Cikinsu

har da Ibrahim Mandawari, HamisuIyan-Tama, Rabilu Musa (Ibro), AuwaluMohammed Sabo, Hussaina Gombe(Tsigai), da Mansur A. Shariff.

Ya zuwa lokacin da za mu buga

mujalla, mutum biyu ne muka samilabarin sun dira a Kano – Ibro daMandawari. Don haka Fim ta zanta daHaj Ibro a ran 25 ga Maris, kuma ta zantada Alh. Mandawari.

Ibro dai bai yi wata-wata ba sai yafara da shaida wa wakilinmu irin abintakaicin da ya gano a {asa Mai Tsarkiwanda ’yan Nijeriya ke tafkawa a can.Har ma ya sami labarai da zai shiryafinafinai a kansu na daga abin da yagani. To fa!

Da Fim ta tambaye shi ko ya shiryofim ]insa a can wanda ya sa wa sunaIbro A Makka tun kafin ya tafi, sai yace, “Ai ni da ma ba shooting ne ya kaini {asa Mai Tsarki ba. Na je ne dominin gaida Ubangijina.”

Duk da haka, Ibro ya ce sai da ya]auko rahotannin irin masha’ar datakari (’yan Nijeriya da ke zaune a can)suke yi. “Kuma duk na na]o su zanwarware cikin fim ]ina mai suna Ibro AMakka,” inji jarumin sarkin barkwanci.

Da aka tambaye shi irin mugun ganinda ya yi a Saudiyya, Assheikh Ibro yakada baki ya ce ai suna da yawa. Wasudaga cikinsu, inji ]an wasan, su ne yagano yadda mata ke yin ~ad-da-kamasu ri}a yin bara ko wata muguwarsana’a. “Idan sun dawo gida kuma suyi ta }aryar cewa wai su Hajiyoyi ne,”inji shi.

Ibro ya }ara da cewa ya kuma ganoirin matan da ke barin mazan aurensu aNijeriya amma abin mamaki sai su yiwani aure a can wai shi “auren ha]uwarJidda.” Su kuwa maza tikari, Ibro ya“le}o” irin sana’o’in da suke yi na zubarda mutunci da wa]ansu “iskanci daban-daban da suke yi.” A nan dai Alhajin yanuna matu}ar ~acin ransa kan zubar damutuncin sauran Musulmin Nijeriya dawasu ke yi a Saudiyya. Gaba ]aya daisai ya ce ba zai fa]e su a mujalla ba, saidai a saurari shirin Ibro A Makka.

Da ya koma kan aikin Hajjin bana,Ibro, wanda ya diro daga jirgi sanye daha}orin Makka fari }al, ya nemi ’yan

Alh. Ibro ya wangale baki don ku ga hakorin Makka dinsa ... a cikin wani wasandabe da aka yi a gidan sinima na Lale da ke Kano a ran 24 ga Maris, 2001

Nijeriya su fahimci cewa mafi yawanabin kunyar da ’yan }asar nan ke yilokacin Hajji duk tikari ne ke ]ibga su.“Ba ruwan mahajjata!” inji shi.

A }arshe ya gode wa ]imbinjama’ar da suka nuna masa }auna tundaga wurin tashin alhazai, da filinjirgi da kuma a can {asa Mai Tsarki.Ya ce, “Wallahi ni a can sai na jikamar a gida nake saboda }aunar dajama’a suka nuna mani.”

Ban da ha}orin Makka da ]an wasanya ma}alo kuwa, dirowarsa ke da wuyasai ya yi sabuwar amarya, ’yar Kwatano,wato Marsandi }irar 190.

Shi ma wani ]an wasa da ya dawodaga aikin Hajji, watau Muntari Nuhu,wanda aka fi sani da sunan [angata, yashaida wa Fim cewa ai shi mugun ganinda ya yi a Saudiyya har da na mazaje’yan luwa]i, “duk kuma ’yan Nijeriyatikari.”

[angata ya ce duk she]anar da sukagano sun na]o labaran sun kawo Kano,za su warware su a cikin fim ]in Ibro AMakka. Lallai gobe da kallo jibi dalabari kenan!

29

Page 31: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Wakilinmu ya tuntu~i ALH.IBRAHIM MANDAWARI jim ka]anbayan dawowarsa daga Saudiyya donjin yadda ya sami kansa a can.

Fim: Alhaji, ko za mu iya sanin yaddaka sami kanka cikin jama’a a Saudiyyakasancewar kai ]an wasa ne?

Mandawari: Gaskiya babu abin dazan ce wa wannan sana’a tamu ta shirya

finafinai sai godiya. Tun daga filin jirgin sama naKano aka fara nuna min gata ta sanayya. Tun aJidda kuma, kafin in yi wata tambaya mutanenmusun ilimintar da ni kan komai, da yake ni a jirginyawo na tafi. Lokacin da muka isa Makka da }arfe2 na dare na can }asar, na }ara ha]uwa da jama’afiye da yadda kake tsammani. A ta}aice dai tun dana je garin Makka, in ban da lemon gwangwani,ban sayi abinci da ku]ina ba. Kuma ban kamamasauki ba. Masoyana ne suka ba ni masauki,abinci da kyaututtuka da dama.

Fim: Kamar su wanene suka yi maka haka?Mandawari: Suna da yawa, amma ina so in yi

amfani da wannan damar don in gode wa wata}ungiya, watau {ungiyar Masu Kallon FinafinanIbrahim Mandawari, wa]anda suka kai min ziyara

harkar fim a nan Kano tana cikinmawuyacin hali. Shin wace irin addu’aka yi wa wannan harkar a can?

Mandawari: Da farko, na yi wa }asaaddu’a, kuma na yi wa wannan sana’atamu addu’a. Ba don komai ba kuwasai saboda na san na bar baya da }ura.Matsalar }asar nan, da sana’armu, daita kanta Shari’a, duk suna bu}ataraddu’a ganin yadda take langa. Gaskiyaduk na yi addu’a kan wannan.

Fim: Shin maganganun da ake yigame da munanan halayen wasu ’yanNijeriya mazauna Saudiyya gaskiyane? Ka ci karo da masu irin wa]annanhalayen?

Mandawari: Gaskiya na gani,

musamman mata. Mata, ku gafarce ni!Amma irin ]abi’un da na gani wasumata ’yan Nijeriya suna nunawa a can,abin takaici ne matu}a. Wannan makenan, ban da masu zuwa can kumasuna yin sace-sace da sauran abubuwana rashin ]a’a.

Fim: Yaya labarin jarumar nan HalisaMohammed wadda ta yi aure a can? KoAllah Ya sa kun ha]u da ka je?

Mandawari: Gaskiya, wallahial’amarin Halisa sai sam-barka. Ta zotare da mijinta sun kai min ziyara, sungaishe ni, har mijinta ya ba ni kyautarwani dan}areren agogo wanda ma niba zan iya saye da ku]ina ba. Har mashi Talal, watau mijin Halisa, yai minial}awarin cewa duk inda nake sonzuwa to in buga masa waya a ba da motaa kai ni. Ka san ma’aikacin security(tsaro) ne a can. Ban yi masa wayar ba,amma dai ina gode masa kuma ina yimasu fatan zaman lafiya.

Fim: Mun gode.Mandawari: Ni ma na gode.

Mandawari: Na ha]u da Halisa aJidda har mijinta ya ba ni kyautar agogo

Alh. Ibrahim Mandawari (na biyu daga dama) a cikin harami tare dasauran alhazai

a Mina, kuma suka yi minkyaututtuka, da sauranjama’a da dama. Ba ni ka]aiaka yi wa haka ba; na samilabarin Ibro saboda yawanjama’a sai da ya ~uya aMakka!

Kuma idan ka je wataunguwa mai suna ‘Tala’arMai Gammo’ a cikin birninMakka, za ka yi mamakiidan ka ga Hausawa a can –tamkar kana Kano. Unguwace ta Hausawa zunzurutu.Can na ji yara suna tsallesuna wa}ar “Wasila Kin CiAmanata.” Kai, har tallar]anwake da taushe da }osaida yaji za ka ji ana yi, kamarcikin garin Kano, ko Zariyako Katsina! To wallahi ni maa can sai da aka ri}a ~oye nisaboda maziyarta maza damata.

Fim: Kafin ka tafi, ka barAlh. Ibrahim Mandawari a cikin harami30

Page 32: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

L A B A R A I

Sun }ulla zumunci da mujallar Fim

Daliban GGASS, Dambatta, a harabar ofishin Fim a Kano

Daga ASHAFA MURNAIBARKIYA, a Kano

A RANAR Asabar, 23 gaFabrairu, 2001, wata

tawagar ]alibai mata dagamakarantar sakandarenArabiyya ta ’yan mata (Gov-ernment Girls Arabic Sec-ondary School) da ke garin[ambatta cikin Jihar Kanota kawo ziyara a ofishinmujallar Fim da ke kan TitinZariya, Kano. Tawagar ta}unshi ]alibai 20 da kumajagoransu, Malam AbdullahiAbubakar.

Malam Abdullahi, wandashi ne malaminsu naTuranci, ya yi jawabi gama’aikaan mujallar inda yace ya jagoranci ]aliban nedomin kawo ziyarar bu]e idozuwa mujallar Fim da kuma]laburare na cibiyar }asarBirtaniya (British CouncilLibrary) da ke Kano.

Ya ce, “Yau mun kawomaku wannan ziyara ta farkodomin }arfafa zumunci dawannan mujalla. Gaskiyairin yadda wannan mujallata kar~u a hannun jama’amasu sha’awar sanin rayuwar’yan wasan Hausa,musamman ]alibaina, shi yasa har suka yanke shawararyin tattaki domin }ulla}awance da ita.”

Malamin ya yaba da irinjuriya da kuma yaddamawallafin mujallar, MalamIbrahim Sheme, ke tantancelabarai kafin ya buga, dukkuwa da cewa sana’ar fimwani dandali ne wanda akeyawan samun gulmace-gulmace da tsegunguma.Kuma ya yi ro}o ga wakilaida sauran ma’aikatanmujallar da su }ara zagedamtse domin }ara ]aukakamujallar.

Da yake gabatar dajawabin maraba a madadinmawallafin, ]aya daga cikinwakilin mujallar na Kano,Ashafa Murnai Barkiya, yanuna farin cikin ]aukacinma’aikatan domin ganin su

ne na farkon ]alibai dasuka fara yin tattaki sukakai irin wannan ziyara a}ungiyance. Ashafa yakuma bayyana wa ’yantawagar cewa sun yi rashinkatarin yin tozali damawallafin mujallar domina lokacin ziyara tasu,Ibrahim Sheme yana can ababban ofishin mujallar dake Kaduna. Sai dai ya yial}awarin isar da sa}onziyarar tasu a wurin shimawallafin. Ya kuma yimasu bayanin irin dajin damujallar Fim ta keto cikinshekaru biyu kafin ta samikanta a matsayinta nayanzu.

Da take tofa albarkacinbakinta, jami’ar gudanarwarmujallar da ke Kano, SadiyaAbdu Rano, ta nuna matu}arfarin cikin ganin yadda]aliban ke sadaukar dalokacinsu suke biye damujallar Fim a kowane wata.Ta }ara da cewa, “Wannan yanuna irin kar~uwar damujallar ta yi a cikin zukatan’yan mata matasa.”

Ita kuwa shugabar tawagar,

wata ]aliba mai sunaRashida Isa GamboBachirawa, ta bayyana cewawasu daga cikin abubuwanda suka sa har suka }ullawannan }awance da mujallarFim, shi ne irin abubuwan daake bugawa na ban sha’awamusamman wasi}un da masukaratu ke aikowa. Wannan,inji Rashida, ya nunamujallar tana kula da masukaratu, ta ce su ]alibai sunamatu}ar nuna }auna gawannan mujalla. Ta kuma bada shawarar cewa kadayawan kushe ya sare wama’aikatan gwiwa. Sai ta yikira a gare su da su kalli dukwani }alubale a matsayinwani abin }warin gwiwa dabasira.

Ita kuwa Umma AdamuBrigade, cewa ta yi suna jinda]in karanta Fim domin sundaina kallon ‘Nigerian Film’,ko da sun gaji da kallon naHausar kuwa to sai su ]aukomujallar }awarsu ta ri}a ]ebemasu kewa. Zabiya UmmaBrigade dai ta rera wamujallar wa}ar bege.

Shahararren ]an wasan

nan mai suna Bashir Nayaya([an Magori), wanda yaziyarci ofishin domin }ullazumunci da ]aliban, ya nunajin da]in zuwan nasu. Jinda]in ganin wannan ]anwasa ido da ido ya sa ]alibansun yi ta she}a masa ruwantambayoyi musamman kanirin finafinan da ya fitocikinsu, irin su Sai A Lahira,[an Halak, da kuma AbinSirri Ne.

[aliban dai wa]andadukkansu ’yan aji biyu ne ababban aji (S.S. II), sun yiamfani da mujallar fim indasuka ba ’yan wasa matashawarwari daban-daban.Wasila Abdullahi Kadunacewa ta yi ’yan wasa mata suri}a jure ji-ta-ji-tar da akeya]awa dangane da su. Takuma ce aure nufin Allah ne;idan Allah Ya ba su miji saisu yi aure.

Su ma MaryamAbdulhamid da Amina WadaIsmael ro}o suka yi ga ’yanwasa mata da cewa “don Al-lah idan suka yi aure to suri}a daurewa suna zaunawaa gidan miji.” Sai dai ita

31

Page 33: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

L A B A R A I

kuma shugabar tawagar,watau Rashida IsaBachirawa, ta jawo hankalin’yan wasa mata da cewawa]anda ba su yi karatu badaga cikinsu to su daure sukama hanyar aji, domin zaifi kyau suna “ta~a ki]a suna

ta~a karatu.”[aliban da suka kai

wannan ziyarar sun ha]ada: Nafisa Lawan,Zulaihatu Salisu, FauziyyaMu’azu, MaryamAbdulhamid Adam dakuma Umma Adamu.

Akwai kuma WasilaAbdullahi Idris, Badi’aAdamu Salisu, Amina Bello,Aina’u Mahadi Ahmed,Shafa’atu Ado Shitu,Naja’atu Alto Isah da kumaRashida Isa Gambo.

Sauran su ne Amina

Mukhtar, Amina Wada,Bilkisu [ahir Mohammed,Aishat Ubah Abubakar,Sakina Rabi’u Malam,Maryam Abubakar Sadiq,Fatima AbdulsalamAbdullahi da HajarahMohammed Suleman.

A }arshe dai Umma Adamuta rera wa}ar yabo da kumabegen mujallar Fim.

Daga ALIYU ABDULLAHIGORA II, a Kaduna

KAMAR yadda aka sani,Kaduna ta yi suna ainun

wajen harkar shirya finafinanHausa. Daga baya aka samujuyin juya hali Kano ta ]agatuta. A halin da ake cikiyanzu, Kaduna tana dafurodushoshi da yawa, ammakash, dukkansu sukantsallake Kaduna su je neman’yan wasa a Kano. Shin meya sa ba su ]aukar nasu naKaduna? Ko ko ’yan wasanne ba }wararru ba?

Wasu daga cikin ’yanwasan Kaduna sun tofaalbarkacin bakinsu a kanwannan al’amari.

Wani ]an wasa mai sunaLawan Idris Kauru cewa yayi shi kam a saninsa duk wani]an wasa da ake nema akwaishi a Kaduna, saboda hakaba wani dalili da zai safurodusa ya tsallake Kadunaya je Kano neman ’yan wasa,in dai ba son rai ba.

Shi ko Abdullahi

Furodushoshi ba su kyauta manaa Kaduna, inji ’yan wasa

Muhammad {waya, wandaya ta~a fitowa a cikin Isharada Wasila , da kuma AnaBikin Duniya…, cewa ya yisu kansu furodushoshin naKaduna ba su yarda da kansuba balle su yarda da ’yanwasan. Amma shi yana kiraga furodusoshin da su dauresu ba ’yan wasan Kaduna filisu ga abin mamaki.

Lawan Idris Kauru

shi duk a cikin }ungiyarsune kawai. Inda kumamalamin ya nuna cewa yatabbata wasu }ungiyoyin dadama sun aurar da nasu ’yanwasan mata da yawa.

Ya yi ro}on cewa ya dacea ri}a yabonsu idan sun yiabin }warai, kuma a ri}a basu shawara idan sun yi badaidai ba, maimakon a ri}azaginsu.

MA’AJIN }ungiyar‘Tauraruwa Drama’ da

ke unguwar Limanci GadarSalga cikin birnin Kano, yanemi jama’a da su ri}a yi wa’yan wasa mata adalci.Malam Umar MuhammadLimanci ya yi wannan janhankali ne musamman kanirin kallon da jama’a ke yiwa ’yan wasa mata amatsayin wasu gungunmarasa zaman aure.

Umar ya shaida wamujallar Fim cewa, “Jama’asu fahimta cewa akwai ’yanmata da dama wa]anda sukayi aure kuma suka zauna.” Anan sai ya tambayi jama’a:“To me ya sa ba a yabonwa]ancan ’yan matanwa]anda suka daure sukazauna, sai dai a yi ta damunguda ]aya wadda ta fito?”

Ma’ajin ya yi amfani dawannan dama ya ce, “Jama’asu fahimci cewa yawancin’yan matan nan fa yaudararsuake yi. Wasu kumamakauniyar fahimta ake yimusu. Watau idan aka gawata yarinya ta yi wani abinburgewa a cikin fim, sai suaure su da nufin lallai sai sunyi irin waccan rayuwa da su.”Wasu kuwa inji shi idan akaaure su aka biya bu}ata, saikawai a kore su.

Malamin ya buga misalinwasu daga cikin ’yan wasamatan da suka yi aure harsuka daure suka zauna. “Kaga dai akwai Salamatu Umarta cikin Wata Shari’ar, akwaiHadiza Kura ta cikin In DaSo Da {auna, sai kumaHajiya Uwani Alasan ta cikinKaren Bana. Wa]annan inji

Ma’ajin Tauraruwa na so ayi wa mata adalci

FurodusoshinJihar Sokoto

suna sogwamnati taagaza masu

Daga BASHIR ABUSABEa Sokoto

AN yi kira ga GwamnatinJihar Sokoto da ta

taimaka kuma ta tallafa wamasu shirya finafinan Hausaa jihar. Wannan kiran ya fitone daga bakin Alhaji SharifUsman Baban Umma,shugaban }ungiyarfurodusoshi na jihar(‘Sokoto State Films MakersAssociation,’ SSFMA). Ya yikira ga gwamnatin ta taimakamasu kamar yadda wasujihohin suke tallafa wa masushiryawa a jihohinsu.

Ya }ara da cewa, “Yana dakyau mai girma Gwamna yatallafa ma Jihar Sokotodomin ci gaban jihar.” Hakazalika ya yi irin wannan kiranga masu hannu da shuni najihar da su taimaka su ga anci gaba a wannan harkar ajihar.

Alhaji Usman, wandakuma shi ne shugaban‘Shurafa’u FilmsProduciton,’ ya yi kira gamutane da babbar murya dasu daina yi wa fimmummunar fahimta. “Yakamata a bincika a kumatsaya a yi nazari kafin ayanke hukunci,” inji shi.

Kamfani Shurafa’u dai ayanzun haka yana dafinafinai guda uku da ke gabda fitowa; sun ha]a da HaramKo Halak?, Ina Hujja? dakuma Sa’adatu.

Umar M. Limanci

32

Page 34: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

L A B A R A I

Da yake }arin haskegame da abin da suka}unsa, furodusan ya ce,“Finafinanmu sun shafimatsaloli na auratayya aaddinance, sai ka ga ga abinda addini ya amince da shigame da aure amma al’ada naneman ta haramta shi.Wannan kusan shi ne jigonfinafinan ‘Shurafa’u FilmsProduction’.”

Furodusan ya yi godiya ga’yan wasa sabodamuhimmiyar rawar da sukataka da wata godiyar tamusamman ga mutanen da yace sun ara masu motoci dawasu wurare yayin ]aukarfinafinansu. Daga }arshe yace finafinansa za su fito ]ayabayan ]aya insha Allahu, ya}ara da cewa, “Ina sa ranmuddin wa]annan finafinansuka fito, to lallai idan mutumbai yaba ba, to, ba ya kushesu ba in Allah Ya so.”

Shi ma da muke hira da shia ofishinsa, M.Z. Faru,shugaban ‘Faru Films Pro-duction’ wa]anda sukashirya finafinan Bari… dakuma Salma 1&2, ya yi kiraga gwamnati da ta taima}awa masu shirya finafinai aJihar Sokoto domin kuwawannan ma wani ci-gaba nena musamman. AlhajiZubairu ya ce yayin da sukashirya finafinnsu wa]andasuka fiddo sun fuskacinmatsaloli musaman na ku]i.”

M.Z. Faru, wanda shi neaka za~a mai binciken ku]ina 2 a taron da aka yi aKatsina na {ungiyarFurodusoshin Arewa, ya yi}orafin cewa sun fuskancirashin ha]in kai daga jama’adomin mutane sai su dingayi wa ’yan fim mummunarfahimta alhali kuma harkarba harka ce ta iskanci ba,harka ce ta isar da sa}o gajama’a. Ya kuma yi kira ga’yan’uwansa furodusoshi dasu zo a ba da ha]in kai a}ungiyar da aka kafa aKatsina, “ya zamo komaiyana tafiya yadda yakamata.”

Ya yi fatan Allah Ya saalbarkaci }ungiyar kuma yasa a cimma manufofin da akazartar. Furodusan ya yi

WANI sabon furodusada ke garin Suleja

cikin Jihar Neja, Alhaji IdrisTanko Na Baraka, yabayyana cewa duk dakasancewar su ba}i ne awannan sana’a, za su iyakarawa da kowa a filinshirya finafinai masuinganci da ma’ana, wa]andaza su dace da zamani.

Furodusan shi ke dakamfanin shirya finafinaimai suna ‘Zuma FilmsPriductions,’ Suleja, wandaa halin yanzu suke cikinshirin fim ]insu na farko mai

jinjina da mi}a godiya gaSardaunan FurodusoshinA r e w a ,Alhaji Abdu Haro Mashi,

wanda shi ne ya ]aukinauyi da ]awainiyar taronna Katsina. Ya kuma yiro}on Allah Ya ba shi

ha}urin jure ma wasuabubuwa. Daga }arshe ya yifatan alheri ga ]aukacinshuwagabannin da akaza~a a taron na Katsina.

Suleja za ta ba da mamaki a filin shirya fim,inji furodusa

suna Firdausi.Idris Tanko ya }ara da

cewa, “Ina kira ga duk wani]an wasa ko furodusa, cewa}ofa a bu]e take, duk wandaya hango wani kuskure akamfaninmu, don Allah yataimaka mana da shawararyadda za mu yi mu gyara.”

Haka kuma furodusan yayi kira ga masu hannu dashuni cewa su ri}a taimakawa furodushosi masu ]an}arfi don inganta sana’ar, tayadda marasa aikin yi za susamu abin yi, “maimakonzaman banza da nemanmaula.”Idris Tanko Na Baraka

Daga ALIYU A. GORA II

WANI kansila a JiharKaduna, Hon.

Mohammed Adamu, ya yikira ga gwamnatin JiharKaduna da ta tallafa wamasu shirya finafinan Hausaa jihar da duk abin dakamata. Kansilan ya yibayani cewa shiryawa]annan finafinai da ake yia halin yanzu abu ne maiamfani ga gwamnati dakuma sauran jama’a,musamman ma idan aka yila’akari da irin darussan daake ]auka daga finafinan.

A hirar da ya yi da wakilinmujallar Fim a kwanakinbaya, kansilan wandatsohon ]an wasankwaikwayo ne a tashartalbijin ta NTA Kadunakuma kansilan maza~arBabadora Malali da ke{aramar Hukumar Kadunata Arewa, Hon. Mohammedya yi nuni da cewa ba}aramin arziki ba ne gaal’umma baki ]aya yaddawasu jama’a suka }ir}iro wakansu hanyar cin abinci, batare da dogaro da gwamnatiba. Ya ba da haske da cewa

Allah ka]ai Ya san yawanmutanen da suke cin abincia cikin wannan sana’a.Saboda haka maimakon azura masu ido kawai, kamataya yi gwamnati ta tallafamasu mutu}ar suna bindokokin da gwamnati tashimfi]a masu.

Tsohon ]an wasan ya yikira ga furodusoshi da su ri}ayin taka-tsantsan wajenshirya finafinansu dongudun yi wa addinikatsalandan. Yana kuma bada shawara da a ri}a baaddinin Musuluncimuhimmanci a finafinanHausa da ake shiryawa fiyeda komai.

Kansila na son gwamnati ta tallafa wa ’yan wasa

Alh. Mohammed Adamu

Daga ASHAFA M. BARKIYA

FURODUSAN sabon fim]in Alaqa, Alh. Sani

Abdurrashid, ya kare dalilanda ya sa ya cusa wa}a maisigar wa}o}in Indiya a cikinfim ]in. Ya bayyana wa

Furodusa ya kare Indiyancida ke cikin wa}ar Alaqa

mujallar Fim cewa irinwa}o}in da suke sanyawa akamfaninsa na ‘Sarari Ven-tures’ ba wa]anda za sugur~ata al’ada ba ne.

Ya yi wannan bayani nesakamakon }orafin da wasuke yi a kan salon wa}ar

33

Page 35: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

L A B A R A I

Indiya a cikin fim ]in naAlaqa. Alh. Sani, wanda shine furodusan Tsumagiya, ya}ara yin nuni da cewa ba laifiba ne idan an kwaikwayiwa}ar Indiya ta wata sigadaban cikin wa}ar Hausa,muddin dai babu wani aibiga wa]ar ko kuma yayin da

‘U.K. Soro’ ya sama wa Katsinawahanyar nisha]i da aikin yiDaga BASHIR YAHUZAa Katsina

S H A H A R A R R E Nkamfanin nan na shirya

finafinai, wato ‘U.K. SoroProduction,’ ya bu]e ofis]insa na farko a Katsina. Ada ba ya da ofis a garin dukkuwa da cewa shugabankamfanin, Alhaji HabibuSani {ofar Soro, mutuminKatsina ne. An bu]e ofis ]inne a watan Fabrairu na bana.

Da yake zantawa dawakilin Fim a ofis ]in wandake kusa da Filin Kangiwa dabda babban MasallacinJumma’a na Katsina, AlhajiHabibu ya ce ya bu]e ofis]in ne domin bun}asasana’ar fim a birnin naDikko, kuma domin ya ba dagudunmawar sama wa matasaaikin yi ganin cewa sana’artana bun}asa da amsuwa gaal’umma.

Domin neman }arinbayani kan harkokinkamfanin, wakilinmu yagana da furodusa MalamMuhammed Mukhtar

Muhammed M. Inwala

Inwala, wanda ya ce,“Kamfanin U.K. Soro Pro-duction mun raba shi zuwakashi-kashi. Akwai fanninsayar da kaset-kaset indamuke ba da sari ga ’yankasuwa, ]aukar fim sashenda ke ]aukar biki ko suna kotaro ga duk mai bu}ata, gasashen shirya finafinai.Sannan kuma akwai sashenediting da recording inda

muka tanadi ingantattunna’urorin aiki”.

Ya ci gaba da cewa za sutaimaka sosai wajen fito da’yan wasan Katsina ta hanyarsaka su cikin finafinan da zasu ri}a shiryawa. Kuma za sutaimaka wa gwamnati wajenwayar da kan al’umma.

A yanzu haka dai harkokincinikayya sai bun}asa sukeyi a kamfanin.

ake yin ta – kamar kamahannuwa tsakanin maza damata da caku]ewa junansu.

Alhaji Sani ya nuna irinbambancin wa}ar cikin fim]in sa da kuma ta Indiya, yace, “Ki]an wa}ar cikin fim]ina ba ki]an wa}ar Indiyaba ne.” Ya yi i}irarin cewashi nasa ki]an rubutaccenki]a ne na wa}ar Indiya yasamo a rubuce ya bayar akabuga masa ki]an a nan Kanoinda aka kwaikwayi karinharshen wa}ar Indiya ammada sigar wa}ar Hausa.

A }arshe dai ya nuna cewayanzu saboda finafinanIndiya da shi kansa na Hausasuna tafiya da zamani to dukda cewa al’adun }abilun sunsha bamban wa}a ta sanyasuna ha]uwa su yi harshe]aya.

Alh. Sani Abdurrashid

Alh. Habibu Sani KofarSoro

A KARO na biyu cikin watahu]u, mujallar Fim ta sake

samun takardar shaidar yabo. Awannan karon, wata }ungiya maisuna ‘H.M.K. Organisation ofSports and Hausa Club’ da keKaduna ce ta ba da kyautaryabon.

Mujallar ta samu wannanyabon ne a ranar Asabar, 24/3/01 tare da wasu makarantu, ’yanwasa, furodusoshin finafinanHausa da kuma wasu ma’aikatada hukumomin gidajen RediyonJihar Kaduna (KSMC) da naTarayya na Kaduna (FRCN).

In a manta ba, a cikin }arshenbara ma wata }ungiyar mai suna‘Farin Wata’ da ke Kaduna ta baiwa mujallar irin wannan takardarshaidar ta yabo.

Cikin ’yan wasa da

furodusoshi da suka samuwa]annan lambobin yabon}ar}arshin ‘H.M.K.’ akwai SaniMo]a, Galin Money, AbdullahiMaikano Usman, da Yakubu Lereta hannun wakilinsa AbdullahiMohammed (manajan ‘LerawaFilms,’ Kaduna). Duk sun samudamar halartar bikin kuma sunkar~i lambobin yabon nasu dakansu.

Shi kuwa Alhaji IbrahimMusa Gashash, SardaunanMatasan Nijeriya, wanda yake]aya daga cikin masu amsarlambobin yabon, ya yi jawabi mairatsa jiki dangane da irinmuhimmmiyar rawar da matasaza su iya takawa wajen ciyar da}asar nan gaba, musamman tafuskar wasannin kwaikwayo daaiki tu}uru. Don haka sai ya yi

kira ga attajirai da malamanaddini kan su shigo cikingwagwarmayar da matasa ke yiyanzu wajen shirya finafinai.Kuma ya bai wa }ungiyar da tashirya bikin }ar}ashinjagorancin wani ]alibinSakandare Gwamnati taUnguwar Sarki, Kaduna,Hamisu Mohammed, ku]ingudunmuwa N10,000. FurodusaAlhaji Nata’ala Aliyu Zariya shima ya bai wa }ungiyar N500.

A lokacin bikin an yi jawabaimasu dama kan muhimmancinilimi ga matasa, don haka aka yikira ga iyayen yara da su dainawasa da ilimantar da da ’ya’yansua kowane lokaci.

[aliban makarantun da sukahalarci bikin sun taya mahalartahira da ka]e-kade, wa}e-wa}eda kuma wasannin kwaikwayo.

Fim ta }ara samun lambar yabo

HARARA A DUHU:shi ne

Shirya fim ba tareda yin tallarsa ba!

34

Page 36: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

L A B A R A I

Tubarkalla, bikin baje kolin fasaha na ArewaTubarkalla, bikin baje kolin fasaha na Arewa

Alh. Adamu Halilu (a tsakiya) yana karbar lambar yabo daga gun Janar Buhari

Daga SHAFI’U MAGAJIUSMAN, a Kaduna

MAHALARTA bikin bajekolin finafinai, da

littattafai, da kayan komfuta,da sauran kayayyakinal’adun gargajiya da fasahana al’ummar ArewacinNijeriya wanda aka yikwanan nan a Kaduna sun gaabin juyayi a lokacin datsohon shugaban HukumarFinafinai ta Nijeriya (NFC),Alhaji Adamu Halilu, yazubar da hawaye yanagodiya kan karrama shi daaka yi a wurin taron. AlhajiAdamu dai }wararrenmarubucin wasanninfinafinan Hausa da Turancine kuma gogaggen furodusa,sa’annan shahararrendaraktan finafinai sama da70 da aka shirya a }ar}ashingwamnatocin ArewancinNijeriya. Shi ne ]an Arewana farko da ya je Ingila dominkarantar aikin fim (1959-1961).

Sauran mazan jiya ]in yazubar da hawaye yanaambaton, “Na gode! Nagode!! Na gode!!!” a yayinda tsohon shugaban }asaJanar Muhammadu Buhariyake mi}a masa takardarshaidar yabo da kyautar ku]ihar Naira dubu 60 sabodagagarumar gudunmawar daya ba da a harkokin ya]alabarai da ayyukan fim natsawon shekaru 40,musamman a Arewa.

A ranar Asabar, 18 gaMaris, 2001 al’amarin yagudana a ]akin taro na‘Arewa House’ da keKaduna, lokacin rufe bajekolin wanda Cibiyar AdanaKayan Tarihi ta Arewa(‘Arewa House’) ta Jami’arAhmadu Bello, Zariya tareda gudunmawarHukumomin Al’adunGargajiya da Fasaha daTarihi na jihohin Arewa 19suka shirya na kwanaki biyardaga ranar 14 ga Maris, 2001

a Kaduna.A lokacin da Alhaji Adamu

yake zubar da hawaye donmurna, da dama cikinmahalarta taron su ma sunzubar da nasu hawayensaboda tausayin halin dasamu kansa a yanzu na rashinlafiya (mutuwar sashe gudana jikinsa). Domin kuwa baya iya tashi daga zaune saida taimakawar wani. Sabodawannan dalili ne ma yasanya shi kansa Janar Buhariya taso daga tasa kujerar amatsayin babban ba}o ataron ya je inda shi AlhajiAdamu yake zaune sannanya mi}a masa kyaututtukannasa.

[an shekara 65 dahaihuwa a bana, mun ba dacikakken tarihin rayuwarsaa mujallar fim ta 8 (Agusta2000). Wannan ba shi nekaro na farko da ya samu irinwannan lambar yabo ba,domin kuwa ita wannanlambar ma ita ce ta takwastun daga 1955 zuwa yau.

Wakilinmu ya so jin abinda ya sanya shi zubar dahawaye, amma sabodayawan jama’ar da ke mi}agaisuwarsu gare shi a wannanlokacin har zuwa lokacin

shigarsa mota don komawagida abin ya faskara.

A lokacin wannan bajekolin an nuna wa ’yan kallo

na wasu jihohin Arewa tareda dukkan kamfanoni damutane masu zaman kansuda suka shiga baje kolin.Kuma kasancewar wannanshi ne na farko, ya yi fatanhakan ya ]ore.

Shi kuwa daraktan cibiyar,Dokta Hamid Bobboyi, anasa jawabin godiyar ya yiyabo da godiya ga jihohi,hukumomi, kamfanoni da’yan kasuwar da suka shigabikin a karo na farko, kumaya ce suna tunani tare da}o}arin ganin wannan bajekoli ya gudana a }ar}ashincibiyar a duk shekara cikinyardar Allah.

Da yake amsa watatambaya daga mujallar Fima ofishinsa bayan ankammala bikin, Daraktan na‘Arewa House’ ya ce a yanzuhaka cibiyar tasa tana da}udurin shirya finafinai kanal’adu da fasaha da tarihinshugabanninmu na baya. Yafa]a tare da nanatawa cewasam finafinan ba za su yikama da irin finafinan Hausada ake shiryawa a yanzu ba.

Taron dai ya yi armashi,har ba abin da kowa ke cewasai sambarka da Allah-maimaita-mana.

Abu ya yi kyau, har dattijo Adamu Halilu ya zubar da hawaye

Dr. Hamid Bobboyifinafinan Turanci da naHausa da dama, musammanwa]anda suka shafi tarihinshugabanninmu na baya irinsu Sir Ahmadu Bello(Sardaunan Sakkwato), SirAbubakar Tafawa Balewa daMalam Aminu Kano. Ajawabinsa na rufe taron, JanarBuhari ya yi yabo ga ‘ArewaHouse’, da HukumominAl’adun Gargajiya da Fasaha

HO

TO

: Fim

35

Page 37: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 200136

Advert

Mujadala 2

Page 38: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

K A S U W A N C I

37

A LOKUTA da dama,dangantaka tsakanindillalan kaset da

furodusoshi takan yi tsami,musamman idan wani dagacikin ~angarorin biyu ya yi}o}arin kare ra’ayinsa – koya-Allah ra’ayin na ]an}ungiyarsa ne ko kuma tafannin kasuwa. Irin wannansa~ani ya auku kwanan bayatsakanin shahararrenfurodusa IbrahimMandawari da ’yan }ungiyardillalan. Amma tuni ansasanta. Wannan ba abinmamaki ba ne, domin ko datsakanin harshe da ha}oriwani sa’ilin dangantakatakan samu tangar]a. Idanaka yi rashin sa’a hakan tafaru, to kuwa harshe yakan]an]ana kaifin ha}ori.

Ga alama shigen irinwannan al’amari yana nemanya kunno kai tsakaninwa]annan abokan ci-gabaguda biyu. Dalili kuwa shine }arin ku]in kwali da sufurodusoshi suka yi kwanannan daga N40 zuwa N50.

Bincikenmu ya nunawannan wata yarjejeniya ceda aka }ulla tsakanin}ungiyoyin biyu a lokacintaron ha]in kan da akagudanar a Katsina a }arshenbara wanda dilallan sun yii}irarin ba a tuntu~e su bakafin a yanke hukuncin}arin. Saboda haka sunabu}atar a yi taro tsakaninsuda furodusoshi kafinwata}ila su amince da }arin.Binciken da mujallar Fim tayi ya nuna daga kowane~angare na }ungiyoyin biyuakwai masu goyon baya damarasa goyon bayan }udurin}arin farashin kwalin.

A ra’ayin Aminu A. Shariff(Momo), furodusan U}uba,lokacin }arin ku]in kwalibai zo ba. Dalilin Aminu shine ’yan kwamitin shari’a daza su fara duba finafinai susa haraji ba su zauna sun faraaiki ba. Idan har za a yi }ari,inji shi, to da sai a bari harsai sun saka harajinsutukuna. Domin a ganinsasannan ne za a san ma shinnawa ya kamata a }ara ]in?Ya yi suka a kan yaddashugabannin suka yankeshawarar }arin ba tare da

tuntu~ar yawancinfurodusoshi ba. Saboda hakasai ya yi kira da a janye }arinhar sai an ga abin da ’yankwamitin suka yi tukuna.

Shi kuwa furodusan sabonfim Izaya, Musa Jalingo,shawara ya bayar da a jiradawowar shugabanninsu nafurodusoshi da suka je aikinhajji, sannan a zauna dashugabannin dillalan kaset]in domin fahimtar juna,don a cewarsa ’yan kasuwarba abokan gabarsu ba ne,’yan’uwa ne.

A ganin darakta Bala Anaskuwa, rashin amincewa da}arin ya zama dole ne domindillalan ba za su iya biya basaboda cinkoson finafinai akasuwa. “Idan har anabu}atar yin }arin,” inji Bala,wanda shi ne furodusanKallo Ya Koma Sama, to tilasne a kafa wata hukuma da zata kula ta kuma ta}aitayawan fitar finafinai akasuwa.

Ra’ayin Ahmed El-Kanawy, furodusan Fallasa,ya sha bamban da na sauranfurodusoshi. Shi ya goyibayan }arin ]ari bisa ]arisaboda shawarar uwar}ungiyarsa ce “kuma ma aidillalan suna bin umurnin}ungiyarsu.” El-Kanawy yakawo shawarar furodusoshi

Ga matsaloli guda biyu: Na ]aya, ana }i}i-}a}a a kan farashinkwalin kaset tsakanin dillalai da furodusoshi. Na biyu, dillalaisuna riki]a, suna shirya fim da kansu. Yaya za a yi? KALLAMUSHU’AIBU ya binciki al’amarin

Aminu A. Shariff Bala Anas

Ahmad Al-Kanawy Bala Ahmed

Page 39: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

su ri}e finafinansu dominidan suka yi hakan to lallaidillalan dole su karyo dominsun dogara ne kacokam akan furodusoshi.

Bala Ahmed, furodusanRagayar Dutse kuma maikamfanin ‘Sarauniya Films’da ke Sabon Titi kuwa yadanganta rashin amincewarda dillalan suka yi ne garashin ha]in kan sufurodusoshin. A ganinsa,babu wata }ungiyarfurodusoshi. “Munamunafintar juna ne kurum,saboda fa]in rai da girmankai da hassada da muguntasun yi katutu a zuciyoyinfurodusoshi,” inji shi.Wannan, a cewarsa, shi kekawo tarna}i ga ci-gabanfurodusoshi kuma shi kesanya dillalan ke jan akalarfurodusoshin yadda ransu keso. Saboda wannan matsalar,inji Bala Ahmed, har dillalansun samu damar tacefinafinai baya ga tacewar daake yi ta }asa a Abujasannan suke }ayyade farashi.“Ko ka yarda ko kuma kaji}a kaset ]in ka sha abinka,”in ji Bala.

Daga ~angaren dillallankaset kuwa, Alhaji Musa NaMalam Sale cewa ya yi afahimtarsa game da maganar}arin farashin, akwai rashinsanin yadda al’amarin yakea yanzu daga ~angarenfurodusoshi. Saboda haka aganinsa idan ba a gode masuba, to bai kuma kamata a yimasu bi-ta-da-}ulli da }arinku]in kwali a yanzu ba.Domin a ganinsafurodusoshi suna samunma}udan ku]i a farashinyanzu sai dai rashin godeAllah.

Alh. Musa Na Malam Sale,wanda ya yi yabo sosai gaIbrahim Mandawari,mutumin da suka samutangar]a a baya, ya ce yabongwani ya zama dole dominshi ne ya }ir}iro masuwannan sana’a ta sayar dakasakasan bidiyo na Hausa.Alh. Musa ya ce tun ma kafinfurodusoshin su ambata}arin, wa]ansu daga cikinsu,musamman }anananfurodusoshi, sun same su“sun nuna adawarsu da

K A S U W A N C I}udurin }arin domin tsarin}arin zai karya }anananfurodusoshi ne ya ginamanyan.”

Shi kuwa JibrinMohammed, mai saida kaseta El-Duniya, cewa ya yi}ungiyarsu ta dillalai ba tace ta }i }arin ba ne sai dailokaci ne bai yi ba. “Kamataya yi a bari sai an ga abin da’yan kwamitin Shari’a za suyi tukuna.

Duk }o}arin dawakilinmu ya yi na tuntu~arsakataren }ungiyar dillalan,Alh. Ahmed Mohammed

aka zanta da su sun nunacewa ba wata barazana dashigowarsu za ta kawo ga suforudusoshi. Sai dai abin daAminu Shariff ke gani shi neba za su yarda wani ]an saidakaset ya zauna a taronsu nafurodusoshi ba. Kuma ba zasu yarda da shisshigi ba,domin suna sane cewa wanihamsha}in dillalin kaset nanan yana shirin shigowacikin harkarsu, wai har maana ra]e-ra]in zai nemishugabancin }ungiyar dukda cewa shi sakataren watsalabarai ne a }ungiyarsu ta

Jibrin Mohammed na El-duniya ya ce sun shigaharkar samar da kasa-kasaine domin wanda ya san sirrinabu shi ya kamata ya yi shi.Ya ce, “Sau da dama akanbugo mana waya anatambayarmu, ana tsammaninmu ke yin fim. Saboda hakamuka yanke hukuncin shigamu ma a yi da mu tunda munsan harkar. Dalilin da ya samuka fara jarabawa kenandomin mu }ara dan}onzumuncin da ke tsakaninmuda furodusoshi da ’yanwasa.” Ya zuwa yanzu su El-Duniya sun samar dafinafinai wajen gudabakwai; daga cikinsu akwaiGani Ga Wane, Dadiron Ibro,Ba a Ba Ka Labari, RashinSani, da sauransu. Ya kumace suna }o}arin shiga}ungiyar furodusoshi. Yakuma kawar da tsoron saninsirrin furodusoshi domin acewarsa ai membobi za suzama amma ba shugabanniba idan sun shiga }ungiyar.“Kuma ma ai ba wani abu sufurodusoshi suke yi a ~oyeda ba su so jama’a su saniba.”

A kan cewa yawancinfinafinansu chamama ne, yace a duk fim, daraja daraja cekamar yadda man fetur yakea kasuwar duniya. IbrahimHassan Na Sale ya musantazargin cewa ba su yi fim ko]aya ba ya zuwa yanzu ammasuna da niyyar yi a shekaramai zuwa. Shi Alhaji MusaNa Sale ya musanta zargincewa yana fim, ya ce ya daisha taimaka wa masu yi daku]i da goyon baya.

Duk }o}arinmu na ganinAlh. Ahmed MohammedAmge ya ci tura domintsokaci a kan wannanal’amari tunda kwanan nanya fitar da fim ]insa naTangaran.

Yawancin jama’ar damuka zanta da su sunha}}a}e cewa mafi yawancinfinafinan da dillalan sukafitar ba su da wani inganci.Amma su dillalan, suna ganinba abin da za a nuna masu aharkar fim. Don haka rikicinbai }are ba. Hausawa dai sunce ba a san maci tuwo ba saimiya ta }are.

Musa Na Malam Sale Sanusi A. Limanchi

Amge, ya ci tura har yazuwa lokacin da aka rubutawannan labari.

Wani bincikekwatankwancin wanda yagudana a sama game dadangatakar }ungiyoyin biyuita ce yadda ake samunambaliyar shiga harkarsamar da fim da dillalan keyi. Ma’ana, suna riki]ewazuwa furodusoshi.Tambayoyi a nan su ne:wane dalili ya sa sukeriki]ewa suna zamafurodusoshi? Shin kuma zasu iya zama ’yan }ungiyarmasu shirya finafinan su sansirrinsu? Sannan shinfinafinan da suke shiryawasuna da inganci ko kuwa“chamama” ne, wato kwashi-kwaraf? Kuma wace barazanashigowar tasu ke yi ga sufurodusoshi?

A kan hakan mafiyawancin furodusoshi da

masu kaset.Shi kuwa furodusan Juyin

Mulki, Alh. Sanusi A.Limanchi, maraba ya yi dashigowar dillalan domin zaiinganta sana’ar saboda za susan irin wahalar abin kumasu ma in sun zuba jarinsu zasu fi kulawa da karemutuncin furodusoshi.

Amma Bala Ahmed shigani ya yi shigar tasu za ta yibarazana ga sana’arsu,“kuma kamar cin mutuncinwannan sana’a ne.” Amma yadanganta laifin ga rashinha]in kan }ungiyarfurodusoshi.

Musa Jalingo kuwa cewaya yi tunda harkar kasuwancice, zai yi wuya a ce ga wandazai yi kaza ga wanda zai yikaza. “Saboda duk wanda zaishigo, ga fili ga doki nan.”Sai dai ya ce ba za su aminceda dillalan a }ungiyarsu tamasu shirya finafinai ba.

38

Page 40: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Fati Mohammed tana gwatso a gidan sinima na Lale a Kanolokacin bikin Gala

Maijidda Abdulkadir tana rawar fim din ’Yanci lokacin bikinGala na Babbar Sallah a Kano

Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA, a Kano

ANYA bikin kalankuwa na ’yan fim ]in Hausabai fara zama shirme ba? Wannan ita ce tambayarda wakilan Fim suka yi bayan sun kallibukukuwan ‘Gala’ da aka yi a Kano da Kadunalokacin Babbar Sallah da ta wuce. A lurarsu,

bikin Gala ya zama na kowa da kowa, babu wata hukuma kocibiya da ke da alhakin shirya shi. Sannan ana yinsa barkatai.Bugu da }ari, a duk lokacin da aka yi bikin, ba a wanyewalafiya; ko dai a tashi da jefe-jefe, ko kuma ’yan sanda sutarwatsa wasan da barkonon tsohuwa. Wakilanmu sun luracewa in ba a yi sannu ba, to wata rana fitsararrun matasa zasu iya danne wata ’yar wasa su yi mata fya]e, ko su sace ta sugudu da ita, ko su raunata wani ]an wasa, da dai sauransu.An tuno da Galar Bauchi? Allah Ya kiyaye!

Bari mu dubi yadda aka yi Gala a Kano da Kaduna. AKano, an ]an cimma nasara saboda wasu dalilai. A Kaduna

ko, wasa ya yi }asa, domin da }yar jami’an tsaro sukaceci ’yan fim.

A ranar Babbar Sallah ]in, 4 ga Maris, 2001 aka yi ]an}warya-}waryan bikin Gala a Kano. Bikin, wanda HukumarAdana Tarihi da A’adu ta Jihar Kano ta shirya, an gudanar dashi ne a gidan sinima na ‘Lale’ da ke kan Titin Malam AminuKano.

Tun kafin }arfe 4:30 na yamma gidan ya cika ma}il da’yan kallo, wa]anda suka yi tururuwa zuwa wurin dominganin ’yan wasan da suke kallo a cikin akwatunan talbijin.

Yadda dandazon jama’a suka ri}a zaro naira hamsin-hamsin daga cikin aljifansu suna sayen tikitin shiga ya nunairin farin jinin da Allah Ya bai wa ’yan wasan da kuma yaddaake sha’awar ganinsu a fili. Koda yake dai yawancin ’yanwasa ba su je wurin ba, ’yan kalilan ]in da suka halarta sun]ebe wa ’yan kallo kewa kuma sun burge sosai. Wani abinsha’awa da za a iya cewa shi ne ya kawo nasarar yin wannanbiki shi ne irin yadda maka]an wasan fim suka ri}a nuna

39

Page 41: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

basirarsu ta ki]a tare da kayan ki]an da suka girke adandalin bikin. Lallai Alee Baba Yakasai, MuntariKwanzuma da Sama’ila sun yi matu}ar }o}arin ganin anburge ’yan kallo. Sa’annan kuma ganin cewa a }araminwuri ne aka yi bikin, wannan ya sa ba a yi masa shelargama-gari ba. Hakan ya sa jama’a da dama ba su san anyi bikin ba. Da kuwa sun sani to yawan jama’a ka]ai zaiiya wargaza tsarin. Haka kuma rashin zuwan ’yan wasada yawa shi ma ya sa abin ya yi armashi bakingwargwado. Domin rashin zuwan nasu ya sa an ]an samisau}in tafiyar da al’amurra, musamman ta fannin tsaro.

Duk da haka, akwai masu ganin cewa yin irin wannanbiki ba shi da amfani, ko da yake dai wani wanda ya bayyanawa mujallar Fim sunansa Muntari ya ce abin ya burge shidomin ko ba komai “ai ta Kaduna da Bauchi duk ba su biyabu}ata ba.” Muntari ya ce shi kuwa yau ga shi ya zo har yaga Alee Baba, Fati Mohammed da Maijidda ido da ido. Ammada wakilin Fim ya tuntu~i wani ]an wasa bayan an tashibikin sai ya ce yin Gala ba shi da wani amfani a Kano.Dalilin da shi Awwalu Yakubu [ankano ya bayar kuwa shine masu shirya bikin suna yi ne kawai don neman ku]i, badomin inganta martabar fim ko al’adun Hausa ba.

A wani jawo hankali da [ankano ya yi, ya ce, “To gwamnati

ta soke wa]ansu finafinan daga nuna su a sinima bayanda can ta hana mu yin fim, to me zai sa ita gwamnatin tashirya wannan biki da kan ta?” [an wasan ya nuna rashin

Auwalu Yakubu Dankano

gamsuwarsa darashin wadataccentsaro ga ’yan wasa ainda aka yi wasan.“Ni dai a iya sanina,Gala sai wane dawane. To yaya za abar kowa ya shigakai har ma da}wanyamin }anananyara?”

An dai tashi bikinlafiya duk da cewa bada shirin aka tashi bako da yake dai bayanan tashi sai da aka]auki tsawon lokacikafin jami’an tsaro sukori gungun mutanenda suka yi }ememesuka tsaya jiran sai’yan wasa sun fito anyi musabaha da su.

*Shahararren]an wasa AliNuhu da Fati

Mohammed ne suka faracashewa da wa}ar “RuwaNa Malale.” Rawar taburge ’yan kallo ganinyadda ’yan rawa mutumhu]u suka yi shiga iri ]ayata jajayen kaya. An dai yita she}a wa Ali da Fatiruwan ku]i. * Sani Musa (Mai Iska) daIdris Lilisco sun yi rawar“’Yar Gudalle” tare da RabiMustapha da kuma FatiMohammed. Wannan wa}ace kusan a ce ta fi ]aukarhankalin ’yan kallo.

* Bayan wa}ar “’YarGudalle,” an gabatar damayan basawa masu cin zali- Shu’aibu Lawan (Kumurci)da Ibrahim Y. Ibrahim(Sinana). Wa]annan basawasun nuna wa ’yan kallo irinbasirar da Allah Ya ba su - kodai ta iya nuna kamannunmasu cin zalin ko kuma ta}warewa wajen kwaikwayon’yan kokawar Amerika(wrestlemania).

* “Ni ban gane wannanirin abu ba. An ce wasanHausa ake so a ri}aha~akawa amma su Kumurcisun zo suna yi mana }arajida hargowa irin ta su (]ankokawar nan na Amerika,)‘Undertaker.’” Haka dai wani

...Yadda bikin Gala ya kasance A Kano dalla-dalla

Ali Nuhu da Fati Mohammed suna wakar “Ruwa Na Malale”

mutum ya furta lokacin da ya ga abin ya yi yawa har yakai su ga yin Turanci bayan kuma irin shigar ’yankokawar suka yi. “Hmm! Idan za a tsaya gida a tsaya, adaina kame-kame. Kuma gyara kayan ka…”

* Wani kurtun ]an sanda ya yi ta tsala wa wani saurayibulala lokacin da ya yi }o}arin yin “kallon kurar {osau”sa’ad da Maijidda da su Lilisco ke ti}ar rawar ’Yanci. Abinya yi }amari har ’yan kallo suka nemi shiga su rama wayaron. Koda yake dai shi ma yaron ya yi }arfin hali ya]auko wani }aton burguje ya nemi ya }wa]a wa ]an sandan.Ba don Allah Ya sa jama’a sun shiga tsakani ba, da an yi wa]an sandan nan tauraro a gaban goshi. Hmm, Allah dai yakiyashe mu da mugun gani, amin.

* Ciri ya ~arke sosai a cikin ’yan kallo wa]anda ke zaunedaga gaba daidai lokacin da Rabi Mustapha da Lilisco sukeyin wa}ar nan ta “Soyayya.” Kowa tsammani ya yi wanimaciji ne ya shigo cikin ’yan kallo, ashe wani }adangarene. Wani aiki sai fasa taro!

* Shin ko Ali Nuhu ya san zun]ensa da aka yi a wannanbikin? Wani ]an kallo ya ce, “Ni ma ban sani ba sai da na ji

taguwa fan-]arinka-tsirara.Ni kuma da na }ara dubawasai na ga taguwar ma kamarta mata ce. Haka dai jaruminya sanyo abinsa ya yi ta rawatare da Fati lokacin da suAlee Baba da Kwanzumasuka buga masu tamburanwa}ar Tawakkali.

* Wallahi malam sai ka jeirin wannan taron za ka sanba kowane ]an wasa ne kowake so ba duk kuwa dashahararsa. Ashe da ma kowada gwaninsa? Yayin da wanike rawa ana yi masa li}i daku]i, wasu kuwa hargowakawai ake yi masu, ana cewa,“Ba ma so! Ba ma so!”

* [an Yarabawa da Baban

wani ]an kalloyana cewa waimaimakon ’yanwasanmu su ri}akashe ku]i suna]inka kayanHausawa sai suri}a yin shigar’yan ‘Holly-wood.’” To da Aliyake, ganinjarumin na sanyeda kwafcecentakalmin nan ba}imai nauyi irinwanda a }auye akece wa ‘}ato-]auki-da-nishi’ kuma yasa ba}in wandojeans da wata ’yar

HO

TO

: Fim

40

Page 42: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Gaje sun yi kokawar cinnasarar auren Hadiza Fijo,‘]iyar’ Malam Haruna Aliyuda kuma Ladi Mutu-ka-Rabaa wani wasan kwaikwayo. Anyi wannan ne sanadiyyarkasa tantance wanda yariyake so da aure.

* Wani ya nemi ya zuga suKumurci su kece rainitsakaninsu a lokacin da yagaji da }arajin da suke yi wajama’a da kuma cika-baki.Zugar dai duk ba ta shigakunnensu ba domin kuwasun mayar masa da amsa wai“kura ba ta cin kura sai dai taci akuya.” A yi hankali,kuraye dai gabanku masuawaki!

* Abin takaici da kuma banhaushi, sha’awa ta ru]i wanisaurayi lokacin da ya je yanayi wa Rabi Mustapha li}isa’ad da take rera wa}ar“Sa’a” tare da Sani Mai Iska.Saurayin dai ba a goshi yali}a mata ku]in ba… Ankuma yi rashin sa’awakilinmu bai ga inda yaronya li}a ku]in ba sai dai yaga lokacin da Rabi ta li}amasa mari ta baya a lokacinda ya yi }o}arin barindakalin filin rawar. Kash!naka shi ke ba da kai!

* Su kuma wasu samari(nigogi) sun nemi jinmujallar da wakilinmu yakewakilta. Dalili kuwa shi newai wani ]an… ya yi masu}arya. Allah Ya kiyaye dagamujallar Fim ya fito, da anhuce haushi a kansa.“Mujallar Fim ai tamu ce,”matasan suka fa]a masa,kuma suka gaisa.

* A }arshe kuma ’yan kalloda suka shigo cikin dandalinsun ~ata tsari daidai lokacinda Fati da Ali da Maijiddasuka fara ka]a }ugu za su yirawar “Sangaya.” Ai fara ki]ake da wuya sai ’yan kallosuka ce ai su ma an yi masumaraba lale. Kuma ko dai bakomai ai su ma Ali da Fatiduk “sangayarsu” ne. Wa}ardai ba ta yiwu ba. Da mawa]anda suka shirya abinsun fara fahimtar cewa ’yankallo dai sun gane ’yan wasaba su je ba, sun kuma faragajiya da ganin wa]anda keta }o}arin ganin sun farantawa ’yan kallo rai. Ganin hakasai aka na]e kaya aka tashidaga wasan.

Bayan kwana takwaskuma, a ran 12 ga Maris, saiaka sake shirya wata Galar asinima ta Lale. Aka ce da mawaccan ta ran 4 ga wata tabu]ewa ce. Kamar dai yaddaake gudanar da kowace, itama wannan Gala ta bayanSallah ba a fara ta a kanlokaci ba, sai dai masu shiryata sun ]auke hankalin ’yankallo ne da suka ri}a sawa]ansu wa}o}in finafinanHausa.

“Ko dai ku fara ko kuma kuci duka!” Haka ’yan kallosuka fara furtawa cikin fushi.Abin kuwa har ya kai wasuga fara watsa zagi. “Kai, kunci ganyen gujiyar …ku!”Wani irin zagi kenan da akari}a yi lokacin da ’yan kallosuka gaji da sauraren wa}ar“Ganyen Gujiya” wadda akasanya don ]ebe masu kewarjinkirin da aka samu kafinfara wasan. Kamar dai irin naranar Babbar Sallah, shi mawannan ga dalla-dallaryadda aka gudanar da shi.Shi ma Hukumar AdanaTarihi da Al’adu ta JiharKano ce ta ]auki nauyinshirya shi.

* Daidai lokacin da akezaman jimamin rashin farawasan da wuri, wani rincimiya tashi sa’ad da wanigungun ’yan mata sukashigo cikin gidan sinima ]in.’Yan matan, wa]anda mafiyawansu duk sabbin-yanka-rake ne a harkar fim, sun zokallo ne, amma sai cunkoson’yan kallo suka mi}e tsayesuna kallonsu. Allah Ya sa angaggauta yi masu hijabidaga ’yan kallo amma da saizaratan yara matasa sunwuce gona da iri.

* Aminu Shehu IluDambazau da kuma FatiMohammed su ne suka farayin wasa. Su biyu sun yiwa}ar “Naja’atu” ta cikinfim ]in Al’ajabi. Abin ya yiarmashi. Sai kuma wata rawada kusan a ce ta fi burge ’yankallo; ita ce wadda SaniDanja ya fito ya yi a cikinwata wa}ar ta fim ]in Imani.Ita ma dai wannan rawa tareda Fati aka taka ta.

* Daga nan kuma sai akaba malaman abin fili sukafara cashewa, watau IdrisLilisco da da Sani Mai Iska.Suka taka rawar ’Yanci tareda Abida. Af, shin Abida takwanta dama ne ko kuwasanyi ta yi? Wallahi duk dakurin da masoyanta ke yi nacewa ai rawa sai Abida, to data shigo kasa takawa ta yi; aida dai ta fara ta ga abin bazai yiwu ba sai ta yi tsayewuri ]aya tana kwa~in }asa.Amma ni dai tsammanina shine takalman nan “taya-ni-tanta]o” da ta sanyo su nesuka hana ta. To Abida ai baa neman ku]i da takalminado. Sai dai kuma ko bakomai, takalmin ya }aramata tsawo. Shin ko ta kaitsawon Fati?

*Shi ma dai [an Yarabawaya fito ya nuna basirarsa tagwaranci, ya kuma bai wa’yan kallo dariya. Har ma yashaida wa ]imbin ’yan kalloinda [an Ibro yake a lokacin.“Mu Ibro muna can Manka!”Haka dai ya shaida masucewa Ibro na can }asarMakka lokacin da wasu sukatambaye shi.

* Farin yaro, dogo, saurayiIsa A. Isah (Khalifa) ya fitoya yi wata rawar cikin wanisabon fim da bai shigakasuwa ba, watau Khalas. Yakuma taka rawar ne tare daRabi Mustapha, zabiyarzabiyoyi.

* ’Yan kallo sun yi ta~arka ihu kamar gidan zaitsage lokacin da mai gabatarda ’yan wasa ya ce, “Nan da]an lokaci ka]an za agabatar da Dum~aru.” Kash!har aka tashi ba a gabatar daita ba!

* Gwanin rawa Lilisco dayaransa su Lilo sun fito sunnuna iya }warewarsu lokacinda Rabi Mustapha ke rerawa}ar “Ruwan Zuma.” Babuirin gwanintar da malaminrawa bai nuna ba (watoLilisco); su kuma ]alibansasun nuna wa ’yan kallo cewawallahi sun karantu.

*Na ji tausayin MuntariKwanzuma lokacin da yakewa Rabi Mustapha ki]a tanawa}ar “An Cuce Ni Wallahi

An Cuce Ni.” Malam, in baka labari sai da aka zo kanga~ar da]in wa}a sai hikimada basira duk suka su~ucewa Kwanzuma. Ya yi takame-kame, hankalinsa yatashi. Kai da ganinsa ka sanba cikin hayyacinsa yake ba.Gumi ya karyo masa, gafuskar nan buzu-buzu dasaje, duk ya fita dagakamannunsa. Duk da}o}arin da ya yi sai da akagane halin da yake ciki. Doleya ha}ura ya daina ki]an.Wani abin tausayi kuma shine Alee Baba yana tsaye kusada shi. Bai taimake shi ba,kuma bai kar~e shi ba.

*Shi kuwa “kyakkyawan”yaro mai rubuta wa}o}i,watau Yakubu Muhammad,fitowa ya yi suka yi wa}arU}uba tare da Abida. Bayangama wa}ar ne kuma sai akagabatar da shi, ’yan kallosuka san ko shi wanene. AsheYakubu lallai ya nuna wa’yan kallo cewa shimarubucin wa}o}i ne? Ainan take sai ga Sani Musa(Danja) ya she}o da gudu yasame shi sun yi wata wa}amai sar}a}iya. Ban iya rerawa}ar ba. Amma dai yarinyace ake wa wa}ar har a cikisuna cewa, “Hotonki ki bani taho ki ho”. Abin daigwanin sha’awa, yadda sukeyin karin sautin wa}arkamar numfashi ya ]aukemasu ne in sun kai }arshenbaitin wa}ar tasu mai }arewada “ho.” Ho ]an nema}erarre!

*Wani abin da ke ]auremin kai shi ne irinmummunar fahimtar damatasa suke yi wa Shu’aibuLawan (Kumurci). A gaskiyaduk tsammani suke ]an dabane har a zahiri. Idan ka gairin gaisuwar da suke masa awurin bikin Gala, abin zai baka al’ajabi; sun kewaye shi,duk wanda ya je sai ya yimasa irin gaisuwar }auraye(wai su ga }aura): “Sai oga!Wallahi tallahi can can canwallahi tallahi sai fa kai fa!”To irin wannan kirarin za kaji matasa masu irin siga,kamannu da kuma halayenda Kumurci ke nunawa a

Gala: Fitowa ta Biyu, A Kano

41

Page 43: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

cikin fim suke zuwa sunajinjina wa gwarzon nasu.

To ni dai ban ga yadda zaa yi a ce wai Gala za ta yiarmashi sosai ba. Na farko daian maida abin kamar ajo,ko’ina ana yi. Yayin da wasuke yin tasu a Kano ranarSallah wasu kuwa Kadunasuka tafi, wasu kuwa Ha]eja.Ban da wannan kuma, maitar

son ku]in da masu shiryaabin ke nunawa duk tadagula al’amari, wataukamfanin ‘Handsome CikoProduction and Matasa Film’tare da ha]in kan HukumarAdana Tarihi da Al’adu taJihar Kano.

Su dai masu shirya Galasuna so a ri}a li}a wa ’yan

wasa ku]i, su kuwawa]anda suka zomusamman domin kallonsuna suna yin li}in sunatare wasu ’yan wasa yaddaba a ganin abin da ake yi.

Wani abin takaici kuma shine wasu daga cikin masuzuwa yin li}i suna zuwa nedon }o}arin ha]a jiki da’yan wasa mata, ko }o}arin

ta~a masu nono ko kuma]aukar hoto da su.

Da can dai bikin Gala anayi masa kallon wani abu maimuhimmanci. Yanzu kumabu}atar samun ku]in damasu shirya abin ke nunawamuraran tana neman ta mayarda bikin Gala ya komaGALAUNIYA.

IDAN akwai bikin Galad a

za a iya cewa ya samunasara daidai gwargwado

daga farkonsa har zuwakusan }arshen lokacin da akake~e masa, to bai wuce wandaaka yi a Kaduna awashegarin ranar BabbarSallar da ta gabata ba.Domin bikin ya sha bambanda sauran bukukuwan Galada aka yi a Kano, Kaduna daBauchi wa]anda kusan ba asamu nasarar bukukuwanmai yawa ba a sakamakon}arancin jami’an tsaro dakuma wasu dalilai da sukeda nasaba da }uncin filayenda aka shirya gudanar dawasannin.

An yi bikin a filin wasa naAhmadu Bello, Kaduna. Antilasta tsai da shi da misalin}arfe 5 na yammacin wannanrana ta Litinin tare da antayawa dubban ’yan kallobarkonon tsohuwa dominwatsa su daga filin, ciki kuwahar Kwamishinan Ya]aLabarai da Al’adunGargajiya na Jihar Kaduna,Alhaji Rabi’u Ba}o, wandasha’awa ta kai shi filin ba tareda jami’an shirya bikin sunsan da zuwansa ba bare su yimasa tarba ta musamman. Anyi hakan ne kuwa sabodayadda wasu tsageran yaracikin ’yan kallo suka }i bin}a’idojin zama a fili donkallo cikin natsuwa duk daro}onsu da aka yi.

Gala a Kaduna: BA RIBA!Wasa ya yi }asa, kwamishina da ’yan kallo sun sha barkonon tsohuwa

Wani tsohon fitaccen ]anwasan }wallon }afa maisuna Alhaji Ali Nayara neya shirya bikin, wanda yabai wa mara]a kunya kanji-ta-ji-tar da aka yi taya]awa cewa ’yan wasanba za su halarta ba sabodairin matsololin da akafuskanta a wasubukukuwan irin wannan daaka yi a baya.

Tun da misalin }arfe 9:30na safiyar ranar ’yan wasa dafurodusoshin finafinanHausa suka halarci filindomin gabatar da wasanni dawasu wa}o}in fitattunfinafinai.

[imbin ’yan fim ]in dasuka samu damar zuwa bikinsun ha]a da Shu’aibu Lawan(Kumurci), A}ilu

Mohammed (BabanMulika), Galin Money,Bashir Bala (Ciroki), FatiMohammed, Hauwa AliDodo (Biba Problem), AbidaMohammed, Shehu HassanKano, Sani S.K., Tahir Fagge,Hajara Usman, WasilaIsma’il, Sani Musa (Danja),Musa MohammedAbdullahi, Sani Idris Kauru(Mo]a), Ladi Mutu-Ka-Raba, Yusuf Barau, YakubuMuhammad, A’isha Musa,Tani Umar, Sani Musa (MaiIska), A’isha Ibrahim (Saliha),Balaraba Mohammed,Amina Mohammed(Sangaya), Fati Jafaru(Gudidi), da sauran ’yanwasa masu dama daga Kanoda Kaduna. Cikinfurodusoshi da daraktaci

kuwa akwai SaminuMahmood, Auwalu Marshal,Yakubu Lere, AbdullahiMaikano, Tukur Aliyu,Magaji Sulaiman, Nata’alaAliyu da kuma wani tsohon]an wasa, Haruna [anjuma(Mutuwa Dole).

An yi jawabai na fatanalheri ga harkar fim.Abdullahi Maikano Usman,babban sakataren {ungiyarFurodushoshi ta Arewa, ya yijawabi a madadin }ungiyar,yayin da Alhaji Haruna[anjuma ya yi nasa jawabina madadin }ungiyar ’yanwasa ta Jihar Kaduna wacceyake wa jagoranci. Daga nanaka gabatar da wasanni,wa}o}i da kuma raye-raye nawasu finafinan Hausa da ’yankallo suka da]e da saninsu.

Dandalin Ahmadu Bello ya cika da ’yan kallo... kafin su yi tawaye

Daga SHAFI’U MAGAJIUSMAN, a Kaduna

HO

TU

NA

: Fi

m

42

Page 44: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Wa}o}in kuwa sun ha]a dana finafinan Wasila, Zarge,Sangaya, Tabbas, Imani,Badali da sauransu inda ’yanwasa irin su Fati Mohammed,Sani Musa, Wasila Isma’il,Galin Money, Hauwa AliDodo, da Fatima MaikanoUsman suka cashe.

Wani abin da ya burge’yan kallo a filin shi ne yaddaaka shirya wani wasa na bandariya mai suna Gimbiyawanda kusan dukkan ’yanwasan da ke wurin sun shigacikinsa. A wasan an yi takararneman auren Gimbiya (Biba)ta hanyar bayyana fasahar daAllah Ya yi wa kowane mainemanta da aure kafin ta za~iwanda ya fi burge ta, shikuma ubanta Sarki (ShehuKano) ya ba shi aurenta. ’Yantakarar suna da yawa, kamarsu Mai Ku]i (MusaAbdullahi), Yarima (TahirFagge), Sani Mo]a, SaniS.K., Ciroki, Babban Mulika,Yakubu Muhammad, da SaniDanja. A }arshe sai ta za~iSani Danja saboda iyarawarsa da wa}a. Kuma a}arshen wasan an kece rainitsakanin Baban Mulika daMo]a saboda jin haushinrashin samun auren Gimbiyada dukkansu suka yi. Su mamasu rawa daga HukumarAl’adun Gargajiya da Fasahata Jihar Kaduna sungwangwaje a bikin.

An fara samun matsala nea sakamakon amince wa ’yankallo su baro wajen zamansusu je dandamalin wasa su yiwa ’yan wasa li}i. Samunwannan damar ta sanya wasutsagerun yara suka ri}a wucegona da iri a yayin nunasoyayyarsu ga ’yan wasanbayan da suka samu damarzuwa kusa da su kuma dadamansu da man ba li}inyake kai su ba; don haka saisu }i komawa wajenzamansu. Da haka wasa-wasafilin ya yamutse. Tilas aka~oye ’yan wasa sai an samunatsuwar da ta dace.

A }arshe dai da aka kasasamun natsuwar duk dayawan jami’an ’yan sanda da’yan banga da suke filin saishugaban shirya bikin, AliNayara, ya ba da sanarwar atashi daga wasan ba tare daan kammala abubuwan daaka shirya gabatar wa ’yan

kallon ba. Kumasu ’yan kallo saisuka }i barin filinsai da ’yan sandasuka dinga antayamasu barkonontsohuwa ba}a}}autawa kafinjama’a su farabarin filin baarziki.

Binciken dawakilinmu ya yibayan an kammalabikin ya nunacewa an kyautatawa ’yan wasa dasuka zo daga Kanota hanyar biyansud u k k a n

Sani Musa (Danja) da Hauwa Ali Dodo suna cashewa a Kaduna

’Yan kallo sun yi tsiyar... sun mamaye filin wasa ba bisa ka’ida ba

ha}}o}insu, sa~anin yaddawasu ’yan wasan Kadunasuka ri}a }orafin ba a biyasu nasu ha}}o}in ba yaddaya kamata.

Ali Nayara ya fa]a wawakilinmu cewa sha’awa tashigar da shi harkar fim naHausa da kuma wasuwasannin gargajiya irin sudambe da sauransu. Ya ce ayanzu haka yana nan yanada burin shiga harkar fimtsindun ta hanyar shiryafinafinai da zarar yakammala shirye-shirye kanhakan. Kan batun Gala 2001ta Kaduna kuwa, ya ce dukda ’yan matsalolin da akasamu an samu nasarar yinbikin ba wai samun nasara taribar ku]i ba.

Alh. Ali Nayara43

Page 45: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Sharhin FinafinaiSharhi ko rahoto kan wasu daga cikinfitattun finafinan da aka yi cikin ’yankwanakin nan

Sunan Fim: Tsautsayin ShagwabaKamfani: Rima Films Production, SokotoFurodusa/Darakta: Ahmed S. Danjummai’Yan Wasa: Alh. Ibrahim, Hajiya Luli, Samira,

Larai, Danladi, Alh. Danhanya,Amina Jummai Yakubu, dasauransu

Hattara da aljannu masu riki]a!

Sarkin Aljannu da fadawansa

Daga BASHIR ABUSABE

WANNAN shi ne fim]in farko dakamfanin shirya

finafinai na Rima Films yasamu damar fitarwa, dagacikin finafinai da dama da yashirya. Fim ]in ya yi maganane a kan aljannu. Tun da farima Sarkin Aljannu ne akafara nunowa yana yi wajama’arsa garga]in su kiyayizuwa yawo cikin gari dominlabari ya zo masa cewa ana}ona masa aljannu sabodacutar da mutane da suke, sukuma mutane suna }ona suda ayar Allah. Amma sabodakunnen uwar shegu da sualjannun suka yi da wannangarga]in, da yawansu sun cigaba da zuwa cikin gari.

Mabaruka tana ]ayadaga cikin aljannun da sukayi watsi da garga]i. A irinbalaguronta ne ta shigo cikingari a matsayin tsaleliyarbudurwa, ta shiga layin ’yan‘Oga good evening.’ AlhajiGarba mai ku]i ne amma ]ansharholiya. Da yake an ce bakullum ake kwana gado basai ya zo ya rakaci aljanar amatsayin karuwa, ya kai tagidan sha}atawarsa. To fa! Anan ne ya gane cewa ashealjana ce ya ]auko bai saniba. Ai nan take ya gigice itakuma sai ta kama yi masafa]a tana cewa haka suke~ata yaran mutane, ta sa shiyin tafiyar maciji, amma yasamu ya tsere da }yar.

Mabaruka ta zamatsohuwa domin kawai tajaraba wani yaro (Samir) daaka ce yana da kirki, ta zaunatsohowa tana son tsallakahanya shi kuma ya zo yataimaka mata har ta tsallaka.Daga nan sai ta kamu da sonshi. Nan take aka }ullasoyayya har ta ba shi kyautarwani zobe wanda in yabu}aci ganinta to da yamurza zai gan ta. Ashe shikuma akwai wadda yake so,wato Larai ’yar ajinsu, amma

bai samu damar gaya mataba sai wani lokaci da ya jekantin saida littattafai sukaha]u, ita kuma ta amince daya je gidansu.

Ta ]ayan ~angaren kumaLarai ta ha]u da wanishahararren mai ku]i akasuwa yayin da ta je yinsayayya. Ai nan take Alhaji[anhanya ya sai mata kayani}i-ni}i. Bayan soyayya tayi }arfi tsakanin Larai daSamir sai Mabaruka ta farakishi; yaya za a yi Samir yayi watsi da ita saboda Laraibayan ta fi Larai komi?Saboda haka ta ]aukimataki. Da farko ta fara ta kan[anladi mai share-sharengidan su Larai domin ta gacewa shi ke taimaka wa Samirwurin neman Larai, sannankuma da yake tsagera ne harya ta~a yi wa Maburakatsageranci.

Aljana ta ba [anladitsoro har Alhaji ya ce zai

kore shi. Amma shi maAlhajin bai tsira ba, dominya ka]u da ya gan ta kusa dashi a zaune. Daga nan aljanata koma kan Larai inda ta}ara da ba ta tsoro; dagabisani ta shigar mata jiki.

Fim ]in yana yinhannunka-mai-sanda gajama’a domin su sani cewaidan aljannu suka shigamutum, to maganinsa AyarAllah kamar yadda daraktaAhmed S. [anjummai yashaida mani. Daraktan ya yinuni da cewa fim ]in ya ginune a kan a}idar aljannu masushiga cikin jikin mutum. “Saika ga aljani ya shiga jikinmutum ya yi rashe-rashe, arasa magani, ai ta wahala; aje wurin bokaye amma duk abanza, amma }arshenta tilasne a dawo ma hanyar Allah,sannan ka ga an yi nasarawannan aljani ya fita, in mabai yi sa’a ba ya }one.”

Ba shakka fim ]in yana

koyar da ’yan darussa.Misali, irin alhazan nan masubudurwar zuciya, ka ga

mutum ya girmatsofai-tsofai da shiamma bai ri}emutumcin kansaba, sai kawai ya bi’yan mata }ananayana ]auka,wanda }ila ka gawata rana ya rakiciwadda ya yi jikada ita.

Sannan kumaakwai maganaraljanun. Wanilokaci sai ka gaaljani ya shigacikin jikin mutumya yi shame-shame, a yi tawahalar nemanmagani amma sai

an dawo wa ayar Allah wandada farko ba a yi tunanin yinhaka ba sai an ga uwar bari.

Sai dai kash! An tafkawasu kurakurai, domin kuwaan ce mana aljana ce ta riki]eta zama tsaleliyar budurwa.Amma kuma mun ga ga ’yanyatsunta na }afa reras, ankuwa ce ko aljani ya zamamutum to ban da }afarsa, saidai aga kofato.

Hajiya mahaifiyar Laraita yi wula}anci a gabansurukanta, ta nuna a zahiriga wanda take so (Alhaji[anhanya) a gabansa. Baal’adar Malam Bahaushe bace uwa ta yi irin wannanhalin; da ma a ce kaka ce, itaaka fi sami da wannan halin.Sannan Kuma ba’a nunamana yadda ake fitar daaljani ba. Jigon fim ]in bamai inganci ba ne; ma’anaba a gina shi bisa labari maikyau ba. Ko da yake an ce nabiyu na nan fitowa. Munajira.

44

Page 46: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Sharhin FinafinaiSharhi ko rahoto kan wasu daga cikinfitattun finafinan da aka yi cikin ’yankwanakin nan

Sunan Fim: Dan HalakKamfani: Dabo Films, Kano, da U.K. Soro, KatsinaFurodusa: Kabiru NakwangoDaukar Nauyii: Habibu Sani Kofar-Soro KatsinaDarakta: Tijjani Ibrahim Bala’Yan Wasa: Abdullahi Zakari, Kabiru Nakwango, Ali

Nuhu, Umar Yahaya Malumfashi, HindatuBashir, Maryam Mashahama, MaijiddaAbdulkadir, da sauransu

Ruge ya ci karo da ]an halak

Ana daukar shirin Dan Halak

45

Daga BASHIR YAHUZA

RUGE, [an-Agwagwa,Fiya-Fiya! Shin kata~a jin wa]annan

sunaye? Sai dai a cikin fim]in [an Halak, inda suka yidandazo suka kafa watahatsabibiyar }ungiya tafashi da makami.

An kitsa labarin a cikinhikima, koda yake bai shabamban ba da yadda labaranfashi da makami kekasancewa ba, ya Allah a}asashen Turawa ko a nangida, sai dai an yi gwanintawajen warware jigonsa. Waniabin burgewa shi ne yaddaaka nuna halin kirki dadaratta mutane, musammanirin yadda Alhaji (UmarYahaya) ya ri}a gudanar darayuwarsa tare da mutane,iyaye da kuma iyalinsa.

A labarin, magidanciAlhaji yana zaune da matarsa]aya Habiba (HindatuBashir) da ’ya’yansu biyu,]aya namiji ]an kimaninshekara biyar, da }anwarsa’yar shekara uku. Da yakemutum ne mai tanadi, ahankali ya ri}a tara ku]idomin huce wa kansatakaicin zama a gidan haya.Allah cikin ikonsa ya taraN900,000, ya nemi maigidan da yake haya ya sayarmasa da gidan. Ciniki yakaya kan N900,000, tare daal}awarin da safe zai ba daku]in. Ya je banki ya fiddoku]in, ya sa a bayan motarsa.Ya kamo hanyar zuwa gida.Ashe duk abin da ake yiRuge (Kabiru Nakwango) nanan yana lura, domin kuwaya san shi sosai. Ashe shi neshugaban wata tawagar ’yanfashi da makami. Ashe yatura yaransa su bi sawunAlhaji tun daga banki hargida. A wannan dare su Ruge,]auke da adduna da gariyo,suka auka gidan Alhaji,kuma lokacin ma suna farke.Hatta ]ansu Ahmed

(Abdullahi Zakari) bai yibarci ba, }anwarsa ce kawaiA’isha (MaryamMashahama) ta yi barci.

Nan take ’yan fashin sukatsorata Alhaji da makamai,suka tursasa shi dole sai daya kinkimo jakar ku]in nan.Abinka da tsautsayi, tamurya sai ya gane Ruge, donhaka ya ce masa: “Ruge harda kai ake mani wannan?”Dalilin haka nan take sukakashe shi, suka kashematarsa, sannan suka ]aukeku]in. Duk wannan ta’asa akan idon Ahmed aka yi ta,amma shi yana ]aki, ta tagaya gane wa idonsa komai.

Jin labarin mutuwar ]anta,sai ita ma uwar Alhaji zuciyata buge ta ta mutu, aka barAhmed da }anwarsa kawai.A hankali shekaru nashu]ewa har suka girma.Amma kafin sannan da yakeHausawa sun ce ba a marayasai raggo, Ahmed bai zamaraggo ba; zage damtse ya yi,

yana aiki. Tun yana yaro yakegoge mota da dako, yana ciyarda kansa da }anwarsa kumayana yi mata hidimarmakaranta. Da ya girma kumasai ya kama sana’ar hannu, yazama kafinta. A can ~angare]aya kuma, su Ruge sai cinkarensu ba babbaka suke su –kashe su }wace, kuma su sace!Ba su wasa ko ka]an da dukwanda ya nemi tona masu asiri,ko da ]ansu ne na cikinsu,domin kuwa Ruge har matarsaya kashe da ta tashi tona masaasiri.

Ruge na da baligin ]a,Faru} (Ali Nuhu). Sai Allahkuma ya ha]a jininsa daA’isha. Soyayyar da ketsakaninsu ita ce sanadiyyartonon asirin }ungiyar suRuge. Dalilin haka Ahmed yagane wa]anda suka kashemasa mahaifi. Nan take ya]auki al}awarin ramuwargayya, kuma Allah Yataimake shi daga }arshe tareda taimakon kwamishinan

’yan sanda ya samu sa’ar]aukar fansa kan su, indaduk suka ba}unci lahira,sannan tsirarun da suka ragekuma suka shiga hannunhukuma.

[an Halak na ]auke dadarussa masuyawa. Babba

daga cikinsu shi neduk abin da mutumya shuka shi zaigirba. Kuma ya}ara fito dam u h i m m a n c i n’yan sanda a cikinal’umma. Sannanyana }ara nunacewa alheri dan}one, ba ya fa]uwa}asa banza. Dubidai yadda Ahmedya taimakiM a i j i d d aAbdul}adir ya}wace ta dagahannun ’yan iska.Wannan taimakoya sa ta zama mai}aunarsa, ga takuma ]iyar

kwamishinan ’yan sanda.Tsokacin da kawai zan

}ara shi ne yadda fim ]in yakasa kauce wa al’adarfinafinan Turai, inda akefa]ace-fa]ace. Domin kuwaa al’adance duk da cewa anafashi da makami cikinal’ummarmu amma da wuyaka ga mutum ya wucehukuma ya tashi ]aukarfansa da kansa domin kawaiyana ji da }arfi. Har kullummasu tsokaci kan finafinai nanuna cewa, nuna fim maifa]ace-fa]ace kamar [anHalak na iya gur~atazukatan samari, suna nunacewa saboda yawan fitowaririn wa]annan finafinai aAmerika shi ya sa yara kekoyon ta’addanci damuggan halaye. Don hakamu ma a nan kila haka na iyafaruwa (Allah Ya kiyaye).Duk da haka, a iya cewa [anHalak ya ciri tuta!

Page 47: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

wani littafi da Maureen VictorAkpan ta wallafa. Ita dai wannanmata, ’yar asalin }asar Kamaruce wadda ta zauna a Jihar Akwa-Ibom. Amma yanzu ta Musuluntatana zaune a Kano tana auren wani]an }asar Sudan. Shi ya sa mayanzu sunanta shi ne MaureenIkram.

Wakilinmu ya tuntu~i daraktanfim ]in, Tijjani Ibrahim, don jita-bakinsa dangane da manufarfim ]in na Alhini.

Fim: Mutane zu so su jima’anar wannan kalma Alhini.

Tijjani : Abin da ake nufi daalhini kalma ce ta Larabci waddada Hausa take nufin halin }unciko na takaici. Dalilin da ya samuka sa wannan suna kuwa shine har abada shi sunan fim ana yine don a jawo hankalin mutane.

Fim: Wa]anne ’yan wasa necikin fim ]in don ka san ’yanwasa na sa fim ya kar~u gajama’a?

Drakta: Da farko dai akwaijarumar jarumai, watau HauwaAli Dodo (Biba). Akwai kumairin su Abdullahi Zakari, HajaraUsman, Rufa’i Shehu Minjibirda yara sabon jini irin su AliNuhu da kuma wata yarinya data fara tashe amma daga wannanfim ]in sai ta yi aure, watauMannira. Kai akwai shahararun’yan wasa da dama. Akwai suSani S.K., [an Magori da wasuda dama.

Fim: Wane irin sa}o ne kukeso ku isar ga jama’a ta cikinwannan fim?

Tijjani: Ka san cewa shi fimyana tafe da abubuwa kusan ukune: akwai nisha]antarwa, dailimantarwa da kuma sanarwa. ToAlhini labari ne na yadda mutumzai iya tsintar kansa a wani irinhali. Yana kuma koya yintawakkali da kuma ha}uri. Fim]in yana nuna idan aka jure wawani abu, to akan samu nasaradaga }arshe.

Fim: Watau ita Biba ce taketsintar kanta cikin wannan halina }uncin rayuwa?

Tijjani: Sosai kuwa ita Biba cewatau Hafsat a cikin fim ]in. Dafarko dai uwar ita Biba ce kerabuwa da mijinta, sai ta yi ta

ta komawa gida. Wani abinba}in ciki gare ta kuwa shi nesai mijin da ya sake ta ya ceshi sam ba nasa ba ne. Sunan]iyar da ta haifa Zinaru, watauZainab.

A }arshe dai sai ta sami aiki agidan su Kabiru Maikaba daAmina Garba. Saboda Allah baiba su haihuwa ba kuwa, sai sukari}e Zinaru ]iyar Biba tamkar]iyarsu kuma Allah Ya ba sudukiya. To Zinaru ce ke zamabudurwar Ali Nuhu a cikin fim]in. Akwai sar}a}iya da yawa aciki, sai dai an gani idan fim ]inya fito.

Fim: Biba ta kasance tana takarawa daban-daban a cikinfinafinai, shin ko akwai inda tataka irin wannan rawa mai bantausayi sama da Alhini?

Tijjani: Gaskiya Hauwa AliDodo ta na iya yin duk ‘charac-ter stage,’ watau duk sigar da akeso ta fito. A halin yanzu babu wanifim wanda Biba ta shiga halin}unci kuma ta nuna basirarta irinwannan. Sai dai nan gaba.

Fim: Ko akwai yiwuwar yin

Alhini na 2?Tijjani: Ai da ma fim ]in na

]aya da biyu ne. Idan mun sakina ]aya a wata mai zuwa(Afrilu), to kuma sai mu saki nabiyu bayan wata biyu. Domin aika ga ita Biba tana }arama ta tashia cikin fim ]in, to har ta yi aure tahaihu ]iyarta ta girma. Ka gakuwa ai akwai rikici sosai cikiwanda sai a na biyu za a iyawarware shi.

Fim: Yawanci nasarar daraktada dogara ne kan irin goyonbayan da furodusa ke ba shi.Wane irin goyon baya nefurodusan Alhini ta ba ka?

Darakta: Gaskiya ‘ExecutiveFurodusa’ Hajiya Halima Isma’ilAlmajir mace ce wadda ke damatu}ar sha’awar finafinanHausa. Wannan ba shi ne fim ]inta na farko ba. Ta fara yin KaraDa Kiyashi na ]aya da na biyu.Tana sayen labarai ne ta ajiye,kuma sai ta aiko min in duba ingani idan labarin yana da manufa.Shi ma Alhini ai wata mata ce tarubuta littafin ta aiko don a yi fim]insa.

Mun ]an yi wa littafn nata

gyara saboda ya ]an shigo dawasu abubuwan da suka shafirayuwar mutane }asar can. Tosai muka canza su da wa]andasuka dace da namu na nan.

Fim: To ko kai ma ka koyi wataishara ko darasi daga cikin fim]in Alhini?

Tijjani: Gaskiya na ji da]inwannan tambaya. Duk fim ]inda na yi wa darakta sai ka ga yadasa wani tasiri a rayuwata,domin wani lokaci za ka ga abinyana shiga ta. Idan darakta bai jifim ya shige shi ba, to fim ]in zaka ga ba zai kyau ba. Ko wanefim da na yi ina da darasin da nakoya daga gare shi, tun inadaraktan fim a gidan talbijin haryanzu da nake na bidiyo. Kumaba na yin fim sai na ji labarin yashige ni. Ina tabbatar maka cewaAlhini yana ]aya daga cikinfinafinan da suka shiga zuciyata.Shi darakta ai yana mai da kansa]an kallo don shi ma ya yi irinshigar da fim ]in ya yi masa. Aiko magani ne sai likitoci sungwada jikin dabbobi. Idan bai yiba, to ba zai tasiri a jikin]an’adam ba. To fim shi ma hakayake.

Alhini: Shirin da ya shiga zuciyardaraktan daraktoci Tijjani Ibrahim

FIM ]in Alhini yana daga cikin finafinan da jama’a sukaza}u su gani, musamman saboda irin gwanintar da sukaji an ce daraktan daraktoci Tijjani Ibrahim ya sa a ciki. Ainihin

mai fim ]in, wata mace ce mai-kamar-maza (kwari ne babu), HajiyaHalima Isma’il Almajir, wato babbar furodusan shahararren fim ]innan Kara Da Kiyashi.

Asalin fim ]in Alhini wani }agaggen labari ne da aka fassara daga

aure-aure. Bibatana yarinya saiyayanta ya ]aukirenonta a }auye.Bayan wani rikicidai ta dawo garihar ta auriBashir.

To ban dawahalar }auyekuma, a birni mata tsinci kantacikin wahaladomin an shiryamata tuggun daya kai garabuwar aurenta.An saki Biba daciki indaMannira ke hana

Darakta T.J. yana duba labarin Alhini a lokacin daukar fim din

46

Page 48: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Tun fitowarsa a watanFabrairu, fim ]in Muradi 1 yajawo hankalin jama’a a kanyadda aka tsara shi,musamman rawar da AminuShariff (Momo) ya taka amatsayin lalataccen ]anmasu ku]i wanda ya aurida}walwar yarinya(Maijidda Abdul}adir)amma kullum yana cikinmayen giya. Mutane sun yimamakin labarin, babukamar da yake ya bambantada yawancin labaransoyayya da suka cikakasuwar finafinan Hausa.

To, labarin da aka gani aMuradi 1 bai }are ba, domina }arshensa an bartambayoyi da yawa da ba aamsa su ba (kamar yadda Fimta yi nazari a watan jiya), saia kashi na 2. Mun ji an cekashi na 2 ]in zai fi na farkonburgewa. Shin ko da gaskene? Kuma ta wace hanya?Don jin amsar wa]annantambayoyin, wakilinmuASHAFA MURNAIBARKIYA ya waiwayidaraktan fim ]in, TIJJANIIBRAHIM, don samunamsoshi:

Fim: A matsayinka nadarakta, wace irin hikima ceka nuna wajen tsara fim ]inMuradi wadda ta sa ya shabamban da sauran finafinai?

Tijjani: Kamar yaddakullum nake fa]a, aikin fimaiki ne na ha]in kan jama’adaban-daban. Babu wanimutum ]aya da zai ce}o}arinsa ne ko basirarsa ceta sa fim ya ha]u. A cikinwannan fim da muka yi, shikansa furodusan da daraktan]aukar hoto, watauMuhammed Garba, da maikula da kwalliya da kuma}wararrun da muka ]aukamusamman wurin shiryaha]arin mota a na 2, duk suntaimaka }warai. Da na farkoda na 2 dai duk Aminu A.

wannan aiki ne wanda gaba]aya aka taru aka yi har akasamu nasararsa.

Fim: Ana ganin akwaiwasu ’yan gyare-gyare kamarinda ake shan giya cikin wanifalo maimakon a nuno sucikin otal suna shan abinsu.

Tijjani: In ka duba ai munnuna shi wannan yaro, watauAminu Shariff (Momo), ]anmai ku]i ne. Yawancin

yi haka a cikin Muradi na1.

Fim: To su wa]annan ’yanmata abokan shan giyar tasafa, karuwai ne?

Tijjani: E, karuwai nekamar yadda labarin yanuna. Yawanci ai in ka duba,yaranmu na gida ai ba za sufito su ri}a yin wa]annanabubuwan suna a buge ko dayaushe ba. Yawanci in dai ba

giya wasu na ganin kamarta yi tsawo. Me za ka ce?

Tijjani: Gaskiya na jida]in wannan magana daka yi min. Wannan kuwaya faru ne saboda ba ni nena yi editing (tace) fim ]inba. Na so a ce ni ne na yiediting ]in. Furodusan neda kansa ya yi. Ni kaina nasan wannan scene ]in ya yitsawo.

Tijjani Ibrahim (a hagu) suna barkwanci tare da ’yan wasa Ibrahim Mandawari da ‘matansa’Hindatu Bashir da Yahanasu Sani a lokacin daukar shirin Muradi na 2

Shariff ne ya rubutalabarin, shi ne kuma ya}ir}iro labarin, sai dai ni natsara zubin labarin a bidiyo(screenplay). To duk

’ya’yan masu ku]i dakuma manya-manyanmasu ku]i da suke irinwannan harka, duk agidajensu na sha}atawa(guest-houses) suke yi, basu cika damuwa da zuwakulob ba. Ga shi nan munagani, musamman yanzuduk a irin wa]annan gidajesuke yi, ba su zuwamashaya. Can suke zuwasu yi garkarsu a asirce a~oye su gama su kauce. Toka ji dalilin da ya sa muka

masu zaman kansu ba ba zaa sami irin wannan ba.

Dalilinmu na }ir}irowannan ~angare na gidangiya da sauransu shi nekullum ya zama ana wannanshaye-shayen. A wuri ]aya nemuka nuna Didilala (RabiAbdullahi ‘Gwi Da Yara’) bata sha giya ba. Shi ma donmu nuna ko tana cikin mayeko ba ta cikin maye akwaiabin da take yi tana juyasaurayinta.

Fim: Fitowa ta 2 ta shan

Shirin Muradi 2 zai fi burge’yan kallo – inji darakta Tijjani Ibrahim

47

Page 49: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Fim: Watau da kai ne daka rage tsawonsa kenan,kuma fim ]in zai fi kyau?

Tijjani: Ba wai zai fi kyauba. Akwai dai wa]ansuwurare wa]anda da na ragetsawonsu. Domin a fim akwaiabin da ake ce wa ta}aitawarabu (limitation of subject);komai tasirinsa akwaibu}atar ta}aita shi. Kumakullum ya kamata a cedarakta shi ne zai ri}a yin

mutane sha’awa wanda ba asaba ganinsa a fim ba. Watauyadda aka shirya yin ha]aria cikin na biyu.

Fim: Ko motar da aka yiamfani da ita aka yi ha]arinta ci ku]i sosai?

Tijjani: A’a ba ta ci ku]isosai kamar yadda aketsammani ba.

Fim: Su wanene ke cikinmotar lokacin da ha]arin yafaru?

dubi fim ]in za ka ga cewaba laifin ita wannan yarinyaba ce (Maijidda).

Kuma mun yi }o}arincewa mun sami ]an canjigame da yawancin labarunda muke yi domin mutane suri}a samun canji, ba kullumsu raja’a a kan abu ]ayakawai shi ake nunawamutane ba. Muradi na 2 ]innan ya fito da abubuwasababbi da dama a ciki. Ka

editing.Fim: To darakta mu shiga

cikin Muradi na 2. Shin kowajen burge ’yan kallo dakuma isar da sa}o zai zarcena ]aya?

Tijjani: Shi Muradi na 1ya zama kamar shimfi]a,amma abin da mutane za sugani a cikin na 2, wataurigingimun sun fi tashi kumasun fi yawa. Tunda aka farafim ]in har aka gamamatsaloli ake samu, bakamar na ]aya ba da kawaigabatar da ’yan wasan aka yida kuma ’yar shimfi]ar daake yi.

A cikin na 2 an samuabubuwa da dama, kumaakwai wani abu wanda zai ba

Tijjani: Watau ShehuHassan dai shi da matarsaMaijidda su ne za su yiwannan ha]arin har itaMaijidda ta ji mugun rauniwanda zai ~ata mata fuskasosai. Amma shi ShehuHassan ba abin da kesamunsa, kawai }warzanewayake yi.

Fim: Me za ka fa]a gameda sauran gundarin fim ]inwanda jama’a suka zuba idosuna jiran fitowarsa?

Tijjani: A wajen }arshenfim ]in mun yi }o}ari mu gacewa ]an abin da muke sonmu isar shi ne yawancinrayuwa haka take. Kullum arayuwa mutum zai iyakuskure. Koda yake in ka

ga dai an yi amfani da]akin tiyata na asibiti dalikitoci da komai sosai sunyi bayani ga yadda aketiyata sosai.

Fim: A ina ne ake matawannan tiyatar?

Tijjani: E, to, a fuska neake ma Maijidda tiyatabayan ta yi ha]ari, wataufuskarta ta yi dameji sosai.Shi ne ake zuwa a yi matawannan tiyatar. Kuma a nanmun }ara nuna cewa sukansu likitocinmu suna da}warewa, ba sai an kaimutum }asashen waje an yimasa aiki ba.

Fim: To ko a fim na 2Amina (watau Abida) za ta

samu saurayi?Tijjani: A fim yawanci ba

sai ka nuna komai daki-dakiba. A na farko ba mu nunatana da saurayi ba. Amma acikin na biyu masu kallo zasu ga har aure Amina za ta yi.Ita kuma jaruma ce ta biyu(supporting actress). Labaringaba ]aya a kan Zubaida ne(Maijidda Abdul}adir) bakan Amina ba. Amina ba shine ainihin inda labarin ya sagaba ba amma dai tana yinaure a na 2.

Fim: Sai ka }ara bayyanawa masu karatu wata sigainda Muradi na 2 yabambanta da sauranfinafinai.

Tijjani: Kamar dai yaddana fa]a maka tun farko,labarin akwai canjin acting.Mutane za su ga Ali Nuhumun ba shi wata siga daban.Likita ne wanda ya je ya yikaratu a waje, kuma hatttarayuwarsa duk ta sake,halayensa sun canza sabodaya zama likita. Dominlikitoci suna da halin shiruda rashin son hayaniya.

Fim: To ko da Ali Nuhu neza a yi wa Maijidda tiyata?

Tijjani: (dariya) To ai saimutane su jira su duba sugani, sai su gane wanda yayi mata tiyatar.

Fim: Yaushe ne fim Muradina 2 zai fito?

Tijjani: Da yardarUbangiji, kamar yadda mukayi magana da shi furodusaAlhaji Nura Ilu Dambazau,ya nuna cewa ba ya sonyadda na ]aya ya yi tasiri ayi jinkirin fitar da na biyu.Ina sa ran ba za a fi sati ukuzuwa hu]u ba za a saki

Nura Ilu DambazauFurodusan Muradi

48

Likitoci suna yi wa Zubaida (Maijidda Abdulkadir) tiyata a cikin Muradi 2

Page 50: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

SHU’AIBU LAWAN(KUMURCI):

A CIKIN wannan fim daiHafizu Bello ne ke son

ya }ara fito da ni ta wata sigada ba a saba ganina ba. Nafito a matsayin }anen BashirNayaya ([an Magori), kumayayan Hauwa Ali. To agaskiya mun yi wa mutaneba-zata a wannan karo, masuganinmu a sigar mugaye, toza su ga Shu’aibu Lawan amatsayin cikakken kamilikuma natsattse, ba ‘Kumurci’ba!

SHEHU BELLO (maimaida tsohuwa yarinya):

Shirin Shirin HauwaHauwa karramawa ne gakarramawa ne gaBiba, kuma ya fito da sabon saloBiba, kuma ya fito da sabon salo

wa Kabiru Maikaba tsufakuma na da]a masashekaru ta yadda daraktake so ya zama uba ga ShehuHassan Kano. Ita ma Hajjona yi mata kwaskwarimainda na maida ita amaryaga Kabiru, mijin Yaganauwar Shehu Kano.

Hauwa Ali Dodo kuwasiga uku na mayar da ita. Kaga dai na canza matakamanninta ta koma ’yarwahala, na kuma mayar daita mai rashin lafiya, saikuma na canza ta ta komasigarta kyakkyawa.

Gaskiya na yaba da irinrawar da Hauwa ta taka acikin fim ]in, musamman

49

WANNAN fim wa’azin e

ga al’umma da kumanuna illar saurin }yamarmutum ba tare da an bincikiabin da ake zarginsa da shiba. A wannan karon ma, nayi aikin nawa domin na }ara

KABIRU MAIKABA:

WANNAN fim mai sunaHauwa ya tabbatar da wani

haske wanda darakta HafizuBello ke so ya fitar. Shi ya sanyaya fito da wa]ansu mutane dawata sigar da ba su fitowa da ita acikin fim.

A karon farko, Shu’aibu Lawan(Kumurci), ya fito a matsayin maihankali kuma yayan Hauwa AliDodo. Shi kuma Jazuli {azazaya fito a matsayin malaminmakaranta, inda shi kuma Sinana(Dumbadus) ya fito a matsayin]an sanda. Wa]annan kamanninda suka fito da su kuwa sun sa~ada irin rawar da suke takawa amatsayinsu na ’yan ta’adda.

Baya ga wannan, na fito a

MASU kallo sunsan an yi fim maisuna Wasila, aka

sa Wasila Isma’il ta fito aciki. Haka kuma an yiA’isha, inda A’ishaIbrahim ta fito a matsayinjaruma. Wannan kamarwata karramawa ce gajarumai, wato a sanya wafim sunansu.

To, in akwai watawadda ta kamaci a yi matairin wannan karramawar,babu kamar Hauwa AliDodo (Biba Problem).Domin in dai ana maganarfim ]in Hausa ne, toHauwa tana cikin gidangaba.

Don haka ne wanikamfani mai suna ‘HBEntertainment’ da keKano ya shirya fim maisuna Hauwa, inda HauwaAli Dodo ta fito amatsayin jaruma. Kodayake fim ]in ba yana bada tarihin Biba ]in ba ne,amma ya fito da wata sigawadda ta bambanta da tasauran finafinai.

Daraktan shirin, SirHafizu Bello, ba kanwarlasa ba ne cikin matasandaraktocin. Ya riga ya cirituta da finafinan da ya yiwa darakta, wa]anda sukaha]a da U}uba, Karamci,da Jumur]a. Ana jin shirinHauwa zai }ara ]ago shi aduniyar shirin fim naHausa.

Wata majiya da shaidawa mujallar Fim cewa anan gaba kuma, fim ]inda kamfanin ‘HB Enter-tainment’ zai yi shi neFati domin karrama FatiMohammed.

A lokacin da ake]aukar shirin Hauwa,wakilinmu ASHAFAMURNAI BARKIYA yahalarci wurin ]aukarshirin, inda ya zanta da’yan wasan da kumadarakta Hafizu Bello,kamar haka:

matsayin uban Shehu Kano,inda ban ta~a fitowa uba gairin masu shekarun ShehuKano ba. Na kuma fito akaron farko tare da ’yarcikina, watau Mabaru}a, dakuma ]an Hajara a matsayin’ya’yana.

Hauwa Ali Dodo da Shehu Hassan Kano a cikin fim din Hauwa

Page 51: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

yadda ta sha wahala dagazuwa taimako sai ta takasawun ~arawo. Kai, shi maJazuli ni ne na yi masa ~ad-da-kama na yi masa dameji.

BASHIR NAYAYA (DANMAGORI):

WANNAN fim ya nunacewa idan ka ga

mutum a wata sifa mummunaa cikin fim, to ba halinsa bane. Za ka kuma iya ganinsa acikin yanayi mai kyau cikinwani fim ]in. To ashe shi maifa]akarwa duk hanyar da yabi zai iya isar da sa}onsayadda jama’a za su fahimta.Ita kuwa Hauwa Ali, gaskiyata yi }o}ari, kuma na tausayamata. Halin da na ri}a nunamata a cikin fim ]in kuwa aiba wani abu ba ne illa nunahalin ]aukar girman kula da}anne saboda mutuwariyayenmu.

SHEHU HASSANKANO,

Jarumin fim ]in:

A TA{AICE dai shiwannan fim sabon canji

ne yake so ya kawo cikinwannan harka tamu tafa]akarwa. Maimakon ko da

SIR HAFIZU BELLO, daraktan fim]in Hauwa, ya amsa tambayoyinmujallar Fim a kan wannan sabon fimwanda bai fito ba tukuna:

Fim: Darakta ga shi ka kawo wanisabon salo inda za ka fito da wasuwa]anda ake gani da sigar mugaye zasu fito a mutanen kirki.

Hafizu : Bismillahir RahmanirRahim. Abin da ya sa na yi haka shi neya kamata daraktoci da furodusoshi sufahimta cewa a daina barin jarumi a koda yaushe yana fitowa a ~angare ]aya.Ya dace a ri}a samun canjin ‘role’ yaddamutane za su fahimci cewa shi ]an wasako da yaushe zai iya yin kowane irin‘role’ aka ba shi.

Fim: Wane irin sa}o ne wannan fimzai isar ga jama’a?

Hafizu: Muna so ne mu nuna wamutane kuskuren saurin zargin mutumda aikata laifi, ba tare da wata madogarako }wa}}warar shaida ba. Ai ka gaaddinin Musulunci ya yi tsokaci kanirin wannan abu. To shi ne ya sakasancewa fa]akarwa ce muke yi, munyi }o}arin nuna irin wannan,musamman yadda shi Bashir Nayaya a

cikin fim ]in yake zarginHauwa Ali Dodo.

Fim: Me ya sa babban ]anwasa kamar Shehu Kano yakasance yana da uba a cikinfim ]in?

Hafiz: Gaskiya ‘role’ ]in damuke bu}ata ya taka ne yakawo haka. Domin na dubana ga Shehu Kano ne ka]aiya fi dacewa da yin ‘role’ ]in.Shi ya sa muka yi }o}arimuka }ara wa KabiruMaikaba tsufa da shekaruyadda ya fito a matsayin ubaga Shehu Kano.

Fim: Su wanene jarumanfim ]in?

Hafizu : Shehu Kano ne daHauwa Ali Dodo. Shi Shehuba ya shiri da mahaifinsaMaikaba saboda mahaifinyana da wasu halaye marasada]in ji. Wannan ne har ta kaiga Shehu ya bar gidansu. Itakuma Hauwa Ali matsalarsallama daga aiki takefuskanta wadda ke jawo matawasu matsaloli a rayuwarta.

... Fim ]in zai nuna illar saurin yanke hukunci a cikin zargi – Hafizu

yaushe maganar aure kokisansa, ko wani abu, sai aka]auki wannan siga domin anuna wa jama’a illar zargin

abin da mutum bai bincikaba.

Ni ai a wannan fim ]in nafito ne a matsayin saurayi

wanda ya gama makarantahar ma ya fara aiki. Gaskiyawannan sabon fim naHauwa wa’azi ne matu}aga jama’a, musamman dona guji saurin yankehukunci.

50Sir Hafizu Bello

Hauwa (a dama) tare da Yagana a cikin shirin Hauwa

Page 52: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

‘break dance’ da ‘bungalow.’Fim: Shin rawa da kake koyarwa a

iya cewa ta samo asali ne ko kuma kakoyo ta ne lokacin rawar break dance?

Lilisco: E, na samo ta ne a wannanlokacin, domin muna da wani guruf namutum ha]u: ni, da Muntari MusaKwanzuma, da Abubakar Usman,wanda a yanzu yake Faransa, da JohnStephen. Ana kiran wannan }ungiyatamu a wannan lokaci da sunan ‘Cre-ative Dancers.’ A wancan lokacin babuwani gurup da ya kai }arfin namu afannin raye-raye. Mun sha cin gasa awasannin raye-yare na zamani a wancanlokacin.

Fim: Ka je ka koyo wani kwas ne na

musamman a kan rawa, domin na gakana aiki a Hukumar Al’adu ta JiharKano ko kuma kurum haka Allah Yahore maka iya ta?

Lilisco: Kusan zan iya cewa na koyota ne kafin ma in fara aiki da HukumarAl’adun Gargiya. Domin ita hukumarta kira ni ne domin in bayar da irin tawagudunmawar don ta ga cancanta ta. Tanemi in fara aiki da ita a 1988 a lokacinana kiranta ‘Arts and Culture’; dagabaya ne aika mayar da ita ‘History andCultue Bureau.’

A lokacin na zo da ilimina na raye-raye na zamani, ba ni da ilimin raye-rayen gargajiya. Ha]uwata da su nakoyi raye-rayen gargajiya. Kuma a 1988na fara wakiltar Jihar Kano zuwa Legasa wani bikin al’adu inda akan yi rawarzamani da ta gargajiya. Kuma mun yinasara, inda muka zo na uku a gasar. Tobayan dawowarmu ne HukumarAl’adun Gargajiya ta ga amfaninmu,saboda haka ne ta ]auke mu aiki a}ar}ashinta, kuma daga nan ne na }arasamun }warewa ta fannin raye-rayengargajiya har zuwa yanzu.

Fim: Za mu so ka lissafa finafinan daka koyar da rawa a cikinsu.

Lilisco: To kafin nan, dalilin da yasa har aka fara nemana ina koyar da rawashi ne a 1987 mun yi wani fim mai sunaDashen Da Allah Ke So. Ni ne jagabanwannan fim ]in tare da wata yarinyamai suna Talatu wadda ita fim ]in ta nafarko kenan. Ita ce take auren Sani Musa(Mai Iska) a yanzu. A wancan lokacinba wai ba a wa}a a finafinan ba, ammaba a san a yi raye-raye a ]an girgiza jiki

A YAU filinmu na Mutanen |oye ya yi wawan kamu, inda ya za}ulo makuSHU’AIBU IDRIS (wanda aka fi sani da sunan LILISCO). Shi dai Lilisco, ba~oyayye ba ne a filin shirin fim, illa dai ~oyayye ne ga masu kallon fim, in ban da’yan watannin nan da ya soma fitowa fili.

Sana’ar Shu’aibu ita ce koyar da rawa a fim. A nan ya ciri tuta. Shi neummulhaba’isin kusan kowace rawa da aka yi a fitattun finafinai kamar Sangaya,Linzami Da Wuta, Sa’a Ta Fi Gata, Allura Da Zare, Tawakkali, U}uba, da sauransu.Ina masu cewa rawar Fati Mohammed da ta Abida tana burge su? To, Lilisco nemalamin wa]annan matan. Ko a wannan hirar, ya nuna cewa shi ne malamin AliNuhu, domin shi ne ya koya masa yadda ake ]aga }afa da yadda ake juyawa.

Shu’aibu Idris Lilisco ya fara fitowa fili a matsayin furodusa kuma ]an wasa.Shi da Sani Musa (Mai Iska) suke da kamfanin ‘Matasa Film Production’ (masuSa’a Ta Fi Gata da ’Yanci), sa’annan ya fito a cikin fim ]in Taskar Rayuwa.

Wani abu da ke sosa ran Lilisco ba wani ba ne illa kyakkyawar jaruma MaijiddaAbdul}adir. Sun yi nisa a soyayya, amma ga alama ana so a yi masa juyin mulki,ko ma a ce an yi masa. Duk da haka, Sarkin Rawa ya garga]i Abubakar, saurayinMaijidda, cewa in dai har ya tsaya yana ~ata lokaci ba a yi auren ba, to shi fa zaiba shi mamaki. “Ina iya dawowa ruwa in naushi hancinsa!” inji Lilisco. Watoyana nufin zai rama juyin mulkinsa, ya kasa shi. To, Malam Abu, ka ji fa.Wakilinmu KALLAMU SHU’AIBU ne ya zanta da Lilisco kwanan baya a Kano.

Fim: Shin wanene Lilisco?Lilisco: Da farko dai, sunana

Shu’aibu Idris Lilisco. An haife ni aFagge. Na yi karatun firamare a ‘{ofarNassarawa Special Primary School,’ harya zuwa aji biyar ko shida. A lokacinan samu rikicin Maitatsine wanda yasa na yi canjin makaranta zuwa Brigadesakamakon tashin da mahaifana sukayi zuwa Brigade ]in, a 1980. Na }arekaratun firamaren ne a ‘GwagwarwaSpecial Primary School.’ Daga nan nashiga sakandare ta ‘Airport Road’ a1981 inda na }are a 1986. Bayan nagama makaranta, na ]an zauna gida nawani lokaci. Daga baya na soma motsajiki ta hanyar raye-raye lokacin yayin

51

Wa}a da rawa ne suke}ara armashin fim

Har yanzu banha}ura da Maijidda ba

M U T A N E N | O Y E

Page 53: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

ba. To a lokacin na shigo da rawa. Nayi rawa ni ka]ai. To saboda wannanrawa ta }ayatar sai ‘Sarauniya Films’suka neme ni muka zauna da Auwalutare da Aminu muka yi magana dominin koyar da rawa a cikin fim ]in suna Allura Da Zare wanda watayarinya A’isha suka yi a cikin rawarwa}ar “Na Gangaro.” Wannan yaburge jama’a sosai. Sai kuma a fim]in mu mai suna Sa’a Ta fi Gata, indana koyar da Sani Musa rawa domin alokacin ba a san komai ba na rawa.Ko rawar warwaro bai iya ba, bai iyakomai ba.

Bayan nan ‘Sarauniya’ sun sakekirana domin in koyar da rawar“Sangaya”. Kafin wannan lokaci na sanAli Nuhu amma ba ma wata hul]a dashi, sai dai in mun ha]u mu gaisa yakama gabansa in kama nawa. Lokacinda na koyar da rawar “Sangaya” akwaishi Ali Nuhu, Biba da Fati Mohammed,kuma kowane cikinsu akwai rawar daza a koya masa. Saboda haka sai da na]auki kwana takwas ina yi masu train-ing. Cikin ikon Allah kowa ya haddaceirin abin da ake so ya yi, aka je aka yishooting ]in Sangaya. To fitowarwannan fim ya bun}asa harkar raye-rayea fim. Bayan nan sai Nura, mai fim ]inAl’ajabi, ya nemi in yi training ]inrawar Al’ajabi part 2. Na koyar da FatiMohammed, Abida da Ali Nuhu daAminu Asid irin abin da za su yi. Bayanna koyar da su aka zo aka yi wannanshooting ]in. Daga nan sai ’Yanci,wanda ni ne furodusansa. Ni na ha]aduk raye-rayen da ke cikinsa wandaSani Musa da Maijidda Abdul}adirsuka yi.

Sai kuma ‘Sarauniya’ suka sakekirana na yi irin wannan aiki nawa nakoyar da rawa a fim ]in su na LinzamiDa Wuta. Shi ma Maijidda da Nura tareda Ahmed da Tasallah ne suka rausayaa cikinsa. Daga nan kuma na yi Nagari,shi ma na ‘Sarauniya’ ne. Sai kuma nayi na Tawakkali da Samodara da kumawani fim na ‘Fatima Production’ wai shiHaka Allah Ya So. Bayansu ne na yi naU}uba inda na horas da Aminu Momoda Abida. Daga nan sai na yi Nadamawanda Muntari Musa Kwanzuma yafara koyar da rawa a cikinsa ammasaboda wa]ansu dalilai bai samu damargamawa ba. Sai kuma Ikon Allah daTaskar Rayuwa da kuma Mu Sha}atana Ibrahim Mandawari.

Fim: Kai furodusa ne kuma ]an wasa,ga ka kuma mai koyar da rawa. Dagacikin ukun nan, wanne ya fi kwantamaka a zuciya ta yadda in da za a ce kaza~i ]aya shi za ka za~a?

Lilisco: A zahiri a cikin ukun nan bawanda zan iya yarwa. Don kowane na

taso ne a kansa in ban da abu ]aya,watau furodusa. Saboda ita harkarfurodusa ban shiga cikinta ba sai damuka bu]e kamfaninmu na ‘MatasaFilm Production.’ Amma harkar koyarda rawa da wasa na da]e ina yin ta samada shekara takwas.

Fim: Wanne ka fi samun alheri dagacikin guda ukun nan?

Lilisco: A zahirin gaskiya na fi samunalheri ta fannin koyar da rawa.

Dambazau da Rabi’u Harabs duk sunba ni credit ]ina a finafinansu. Dominna lura jama’a suna yin kuskure, donshi fim yadda duk ya tsaru idan ba a sawani abu na nisha]antarwa ba kamarraye-raye, duk sa}on da ake }o}arinisarwa ba zai isa ba. Zamani ne ya kawowannan wa}a da raye-raye; su ne suke}ara armashin fim.

Fim: Wasu suna ganin wa}o}in daraye-rayen suna ~ata al’umma saboda

ana caku]uwa tsakanin maza da mata.Kuma ana ganin sabon tsarin da za afitar nan gaba ka]an, a }ar}ashinKwamitin Shari’a, zai shafi wannan~angaren na fim. Ba ka ganin wannanwata barazana ce ga sana’arka?

Lilisco: Na farko dai, kamar yaddakake waswasin wannan maganar, dukinda malami ya zo ya tsaya a bakin titia zamanin yanzu yana wa’azi, tomawuyaci ne a tarar da mutum ]ai ]aisama da dubu biyu ko dubu ]aya sunasaurare ko jin tafsirinsa in dai ba lokacinazumi ba ne. Wa’azi abu ne mai amfaniga mu Musulmi, amma yawancinjama’a sukan shagala su bar wannanabu. To amma ni a matsayina na maikoyar da rawa, na tabbatar da cewa sunada amfani da abu ]aya ne lokacin da zaka yi fim ]in ka duba ka ga akwai waniabu ]aya da zai janyo hankalin mutumya kalli wannan fim ]in. Kuma shi fimkamar yadda malami zai fito bakin titi

Fim: Galibin masu kallonfinafinanmu ba su san wanene yakekoyar da rawa ba. Saboda hakawa]anda suka yi rawar a fim su akeyabawa. Yaya kake ji idan ka ji irinwannan yabon da ake yi wa wa]andakai ka koyar da su?

Lilisco: Ni kaina wani lokaci abinyana ]aure mani kai, domin sau da yawamutum zai zo ya nemi ka koyar da rawaa fim ]in sa, ya zo da annashuwa dakomai, amma idan ka gama ba zai yitunanin cewa ai ka taimaka masa a~angare kaza ya ba ka credit ]in ka ba.Amma mutane biyu ko uku suna burgeni ta wannan ~angaren, su ne ’yan‘Sarauniya’(Auwalu da Aminu), dominduk aikin da na yi masu sukan ba nicredit ]ina ta hanyar sa sunana a fim]in ko a kwalinsa, kuma su ba ni watakyauta ta girmamawa; sai kumakamfanina da nake ciki dole ne a ba niha}}ina na furodusa. Kuma Nura Ilu

M U T A N E N | O Y E

Rawar Sa’a Ta Fi Gata wadda Idris Lilisco ya koyar

HO

TO

: M

atas

a Fi

lm P

rodu

ctio

n

52

Page 54: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

ya yi bayani ko wa’azi, to haka fimyake; shi ma wa’azi ne. Domin duktsiya za ka tarar da fim ]in nan yanada wani abu ko da }waya ]aya namora.

Fim: To yaya za ka yi wa’azi da rawa?Lilisco: Rawa ai ba wa’azi ba ce,

amma tana }ara kawo nisha]i. Lokacinda ka fara kallon fim ka taho tiryan-tiryan ranka ya fara ~aci domin kanaganin wa]ansu abubuwa na fa]akarwaranka yana ~aci kafin ka zo kan lokacinda za a yi hukunci sai a ce bari a ]an sama wani abu da zai ]an sanya ranka yayi sayi.

Fim: An ce Fati ba ta iya rawa ba acikin Sangaya. Laifinka ne ko laifintane?

Lilisco: Fati, zancen ba ta iya rawa aSangaya ba ni ba laifi ba ne. Na farkosannan ni ina gani ma ta yi }o}ari.Dalilin kuwa lokacin da ta fara zuwatraining na Sangaya mun samu tsawonkwana uku muna training kafin ta zo –kai ya ma fi kwana uku, ya kai kwanahu]u. Biba kuwa ta riga Fati zuwa.Saboda haka ina ganin ba laifinta bane tunda wani abu ne da ke bu}atartsawon lokaci a koyar.

Sannan kan zancen caku]a maza damata a raye-raye, ina ganin in ba kusheda hassada ba, duk mai kallonfinafinanmu zai ga da wuya wa}a ta zoba tare da ma’ana ba. Ma’ana, akwaiginshi}un yin wannan wa}ar, kumabayan wannan mawuyaci ne ka ga maceda namiji sun kama hannu ko sun ri}ejuna ko a ga sun rungume juna. Babu

wannan. Na tabbatar da duk finafinanda na koyar da rawa cikinsu ba wandaza a nuna inda mace ta rugume namijiko sumbatar wani. Duk inda nakekoyar da rawa sai na tabbatar da maza~angarensu da mata daban.

Fim: Wa]anne wahalhalu kakanfuskanta wajen koyar da rawa?

Lilisco: Duk mutumin da aka ce bashi da ilimin abu sai an koya masa kasan ba abu ne mai sau}i ba.Na ]aya, sufurodusoshi sukan so a koyar da rawacikin gaggawa domin in aka bi }a’idayana iya ci masu ku]i ko kuma su ce gawa]anda suke so a koya mawa alhali niina da }wararru wa]anda ba zan shawuya wajen koya masu ba. Duk wannanyakan kawo wahalhalu wajen koyar darawa. Saboda in ba wanda ke }wararrezan koya mawa ba, maimakon a ce zankoyar da step hu]u (wato takin }afahu]u) sai ka ga step biyu kurum zaniya koyarwa.

Fim: An ce Abida tana ]aya dagacikin gwanaye a fannin rawa. Kana shanwata wahala wajen koyar da ita?

Lilisco: E, Abida gaskiya a zahirikamar yadda mutane suke fa]i tana da}o}arin haddace rawa kuma tana da}o}arin ri}e ta. Kuma mawuyaci neidan ana nuna mata abu ta yi wasa; tanatsayawa ta yi shi kamar yadda aka nunamata, kuma tana iya }o}arinta ta ga takama wannan abu. Kuma ganin }o}arinnata na son ta iya ]in ya sanya ta zamamai }wazo a kan harkar.

Fim: Shin tunda kai ma’aikaci ne aHukumar Al’adu ta Jihar Kano, akwai

wani kaso da kakan ba su, ko kuwaduk abin da ka samu naka ne?

Lilisco: Idan aikin da zan yi yadanganci ayyukana na ofis, to dolene in sanar da ofis cewa don Allah a]an ba ni dama domin zan yi aikikaza. Hukumar Tarihi da Al’adunGargajiya tana bu}atar ta ga mutummai }wazon inganta al’adungargajiya. Idan na nemi a ba ni damazuwa wajen wani aiki irin na koyarda rawa, to shugaban ~angaren danake yakan ba ni wannan damar. Wanilokaci kuma idan na ga da hali nakanba da wani abu ko kuma in biyadomin a je a yi wannan abu. Wani sa’ilinkuma idan ya danganci }arshen sati tona san wannan lokacin ba na aiki bane, nakan yi da kaina.

Fim: Da ina da ina ka je ta dalilinwannan sana’a?

Lilisco: To alhamdu lillahi a Nijeriyadai kusan ba inda }afata ba ta je ba. Nakuma je Ghana, Cape Coast, Libya, daVenezuela, Nijar da Kamaru.

Fim: Iyali fa?Lilisco: Ina da mata ]aya tal, sunanta

Sa’adatu Musa, da kuma ]ana ]aya,Abdullahi Idris.

Fim: Maganarku da MaijiddaAbdul}adir fa. Ina aka kwana?

Lilisco: (Shiru na tsawon lokaci. Canya nisa) Hm! Wannan babbar maganarce, domin Maijidda Abdul}adir ni daiban san ta ba sai ta abu biyu. Allah neya ha]a mu da ita ta hanyar ‘SarauniyaFilm Produciton’ da aka neme ta ta yiLinzami Da Wuta bayan da MaryamMashahama ta kawo ta. Ni ne na ba sutraining ]in rawa cikin fim ]in. Bayanan }are ne sai Ubangiji Allah Ya ha]asoyayyarmu da ita.

Dangantakar soyayyarmu ta }ara}arfi ne lokacin da muka kira ta dominyin fim ]in mu na ’Yanci. Daga nansoyayyarmu ta yi }arfi har duk wanifurodusa ya san ni da ita. Har muka yial}awarin aure tsakaninmu; na yial}awarin cewar zan aure ta, ita mahaka. To amma a lokacin da nakenemanta, akwai wani wanda ke zuwawajenta, saurayinta, ana ce masaAbubakar. Da farko ban san shi ba, tagabatar da shi a wurina, ni ma ta gabatarda ni a wurinsa. Idan ya zo ya same nida ita yakan taking excuse daga wurina(ya ro}e ni in ]an ba shi fili). Haka nima idan na zo na same shi nakan ha}ura.Har ta kai ta kawo muna ’yar kunyarjuna tsakaninmu. Muka zama abokai.Allah da ikonsa soyayyarmu ta yi }arfitsakanina da ita. To na ]auke ta amanaba don in yaudare ta ba. Wasufurodusoshi sun ji da]in ganin zan aureta, ganin cewa zan rufa mata asiri.Domin tun jama’a suna yabawa da ita,

M U T A N E N | O Y E

Idris Lilisco (na farko a gaba) tare da jama’arsa lokacin rawar “Ruwa NaMalale” a bikin Gala da aka yi a Kano, ran 4 ga Maris, 2001

53

Page 55: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

lokaci guda za ta ~ace. Kuma idan ni taaura to ba wai ta ~ace ba ne domin tadawo hannun ]an wasa ne wanda za ari}a jin labarinta a gunsa. Saboda hakaina ganin abin alfahari ne a ce munatare da ita.

To, bayan tafiya ta yi tafiya neMaijidda ta yi wani abu wanda ya sosamani rai. Wannan abu yana ]aya dagacikin abubuwan da suka karya manizuciya na ga cewar kamar ba ta ba daamanna da ni ba. Kuma na ga ni ina sonta ne bisa gaskiya domin ni aurenta zanyi, to amma na share wannan zancen.

Idan ba ka manta ba, akwai wanilokaci da aka yi hira da ita (a mujallarFim) inda daga baya ta }aryata zancena.To in za ta }aryata zancena cewa ni bamasoyinta ba ne ko ba mu yi al}awarida ita ba, to ai mutane shaida ne, kumaakwai furodusoshi da yawa wa]andasun san tsakanina da ita. Kuma kai daka yi mata interview idan ta }aryata aia gabanka aka yi kuma ka ji lokacin data fa]a. Saboda haka ni wannan ba waniabin ba}in ciki ba ne tare da ni.

Fim: To Lilisco daga wancan lokacinzuwa yanzu kukan ha]u da ita? Kumaina aka kwana?

Lilisco: Muna ha]uwa da ita, kumayadda ta saba ba ni girma da darajatada }imata duk tana ba ni. Kuma sa’ilinnan ni na san Maijidda sona bai fitadaga cikin zuciyarta ba, kamar yaddani ma ban yada ita baki ]aya ba.

Fim: Za a yi ragas kenan?Lilisco: Ba mamaki idan ta kasance

a yi ragas ]in a yi ragas domin shi(Abubakar) ya tsaya yana wasa yanacewa bayan Sallah za su yi aure, Sallarga shi ta zo }aramar, har an doshiBabbar Sallah. To idan babbar ta zo tawuce (ba a yi ba) na san ba mamakiyana neman ya ru]e ta ne. To ganinwannan, ina iya dawowa ruwa in naushihancinsa!

Fim: Kana da wani abu wanda kakeganin ba ka fa]a ba a cikin wannanhira?

Lilisco: Abu ]aya ne }waya ]aya dayake sosa mani raina. Game da Ali Nuhune. Ali Nuhu abokina ne a yanzu. Akwailokacin da na ga wasu finafinaiwa]anda ni na koyar da rawa a cikinsu,kamar Mu Sha}ata inda aka yi hira dashi ya nuna cewa shi rawa ya taso ne dashau}inta kuma ya iya ta. Na yi mamakida bai nuna cewa akwai wani mutum]aya wanda yake taimaka masa ko yakenuna masa wa]annan abubuwan rawaba, wato ni.

Wannan abu ya ba ni mamaki dominna san cewa duk yawancin finafinan daAli Nuhu ya fito ni nake koyar da rawaa cikinsu, in ce masa ga yadda zai yi,kuma bai isa ya canza wani abu in bawanda na ce masa ba. Ya kamata yanuna cewar ni ne na koya masa dominba lallai ba ne sai an ga fuskarta ba.Domin jama’a da dama suna ji na ammaba su san ni ba in ban da fim ]ina ]innan na farko da na yi wasa a cikinsa,wato Taskar Rayuwa.

An sami }arin haihuwa a gidanmawallafin mujallar Fim

KWANA 18 dayin sunan ]an

da aka haifa masa aKaduna, mawallafinmujallar Fim,Malam IbrahimSheme, ya sami}arin haihuwa,lokacin daamaryarsa MalamaBinta ta haifa masa]a namiji a Kano, aranar Asabar, 10 gaMaris, 2001.

Bayan kwanabakwai, a ranar 17ga wata, aka yi bikinsunan yaron, wandaaka haifa a asibitin‘Arewa Surgery’ dake Hotoro. An ra]amasa suna Mubarak.

An yi taron suna agidan MalamIbrahim Sheme dake Layi na 12,Shagari Quarters.Iyaye da ’yan’uwada abokan arziki sun hallara wurinbikin, wanda aka soma tun da safehar zuwa dare.

An yi addu’o’i tare da ro}on AllahYa albarkaci Mubarak da iyayensa,sannan an wadatu da kayan ciye-

ciye da na sha.Mubarak ]an fari ne ga

mahaifiyarsa Binta, wadda malamace a Jami’ar Bayero da ke Kano. Al-lah Ya raya Mubarak, Ya sa masaalbarka, amin.

Mubarak Ibrahim

Furodusan Taskira ya sami }aruwa[AYA daga cikin mutanen das u k a

fara shirya fim na bidiyo aKaduna, Alhaji Abdullahi Sa’iduBello, ya sami }aruwar haihuwa.Matarsa Malama Maryam ta haifamasa ’ya mace a ranar Talata, 6 gaMaris, 2001, a Kaduna.

An yi bikin suna a ran 13 ga wata,aka ra]a wa yarinyar suna Afra-Nafisah. ’Yan’uwa da abokan arzikisun halarci bikin, cikinsu har da wasudaga cikin masu harkar fim a Kaduna.

Shi dai Abdullahi, wanda aka fisani da la}abin ‘Architect’ sabodairin sana’arsa, shi ne furodusanfinafinai biyu, Taskira 1&2 da kuma[an Duniya, a cikin 1997/8. Shi neshugaban ‘Multi-DimensionalFilms.’ Amma ya shafe shekaru yanayi wa shirin fim yajin aiki sabodawasu dalilai, kuma ya }i yin hira da’yan jarida. Mun ji an ce yana shirindawowa ruwa. Allah Ya sa haka ne.

Afra-Nafisah Abdullahi

54

Page 56: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Advert

Dawayya

55

Page 57: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA da IRO MAMMAN

BIKIN nunin finafinan Afrika mafi shahara a nahiyarmu, mai suna “Pan African Film and Television Festival” (FESPACO), ya ci ya cinye kwanan nan a

birnin Wagadugu (Ougadougou), hedikwatar }asar Burkina Faso da ke nan Afrikata Yamma. An yi rugun]umi, an ba ido da ciki abincinsu, kuma }wa}walwa ta yi aiki.

A karon farko, wani ]an Nijeriya mai suna Newton Aduaka ya sami nasarar cinkofi a gasar. Aduaka, wanda haifaffen }asar Birtaniya ne kuma ]an asalin JiharAnambra, fim ]insa mai suna Rag ka]ai ne wanda ya samu cin wata kyauta dagacikin finafinan da aka shirya da harshen Ingilishi da suka fito daga }asashe renonIngila. To, wannan ka]ai ya haifar da surutai da nuna rashin gamsuwa daga }asashenda ke magana da harshen Ingilishi, suna cewa an nuna masu bambanci.

Kamar kowane shekara biyu, an shirya bikin na bana a birnin Wagadugu. Shi nena 18. An kuma kwashe kwanaki takwas (daga ran 24 ga Fabrairu zuwa ran 3 gaMaris) ana gudanar da shi. Fim ]in Rag mai tsawon minti 90 ne ya samu kyautarzama fitaccen darakta na farko da ya fara shiga gasar. Wannan kyauta tasa ita ce tauku mafi daraja a bikin.

An wuce an bar baya da }ura

Bikin nunin finafinai na Afrika da aka yi a bana a }asar Burkina Faso ya burgemahalarta, to amma ya bar wa]ansu ’yan fim suna gunaguni

Ingarman Yennenga, kyautamafi daraja a bikin

Wasu mahalarta bikin a Wagadugu. Abdulkareem Mohammed ne a gaba ya dan durkusa, yana sanye da baje

56

Page 58: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Rag ya samu ]aukakadomin sati uku kafin a yi bikinsai da ya ci wata kyautar awani bikin nuna finafinai daaka yi mai kama da wannan abirnin Los Angeles a Amerika.

Kimanin masu shiryafinafinai 1,200 ne da suka ha]ada daraktoci har ma da masu]aukar hotuna suka halarcibikin. A wurin, an gabatar dasama da finafinai 100 gagidajen sinima na birnin, ankuma nuna guda 29 gamahalarta, wa]anda 20 dagacikinsu sun shiga gasa ne.

Babbar kyauta dai a wurinbikin ita ce wadda AyouchNabil ]an }asar Morokko yasamu daga fim ]insa mai sunaAli Zaoua. Ya sami kyautarku]i har seifa miliyan biyar(CFA 5m). Shi kuwa Aduakaya sami seifa miliyan biyu(CFA 2m). Wani fim mai sunaBintou na Fanta Regina Nacro,’yar }asar Burkina Fasso, shine ya sami kyautar fim ]in daya fi ]aukuwa.

Baya ga wa]annan an rabakyaututtuka da dama ga sauranfinafinan da suka yi fice.Sauran ’yan Nijeriya da sukayi takara a gasar sun ha]a daOmonike Akinyemi, ]anasalin Jihar Ondo ammamazaurin birnin New York naAmerika. Shi ne ya yi fim ]inNelcy Bodega. Sai kuma AyoSonanya wanda ke zaune abirnin London wanda kuma

shi ne ya yi fim ]in Spin.Sai dai kuma wani abin da

ya biyo baya shi ne irin}alubalantar da aka yi waal}alan wasan ya rage wabikin kwarjini. {orafe-}orafenda aka yi kuwa sun ha]a dacewa mafi yawan kyaututtukamanya 23 da aka bayar, in banda wadda Aduaka ya ci, an bada su ne ga ’yan }asashe renonFaransa. Da ma tun farko ansoki al}alan ba dakyaututtukan, ganin cewa watamace ’yar }asar Afirka taKudu mai suna LetebeleMassemola-Jones ce ka]ai ta

zama al}ali daga cikin }asashemasu magana da harshenIngilishi.

Daga cikin wa]anda suka yikukan an tabka magu]i har daNewton Aduaka wanda yala’anci yadda aka gudanar daal}alancin wasan. “Ni ganinake kawai wannan bu]i nena }asashe renon Faransaamma ba na }asashen Afrikaba,” inji shi.

Wani fim kuma da ake ganinan yi masa rashin adalci shi neYellow Card, na wani ]an}asar Zimbabwe mai sunaJohn Rilber. Su kuwa ’yanAfrika ta Kudu sun yi zargincewa an ~oye finafinan dasuka aika, sai bayan lokacinaikawa ya wuce aka fiddo su.

Wannan abin takaici ne yasa al}ali Letebele Massemola-Jones ta rubuta takardar saukadaga kujerar al}alancin. Kodayake dai wata majiya ta shaidawa mujallar Fim cewa “dagabaya an bai wa Jones ha}urita koma al}alancin nata.”

Wani abin burgewa a bikinna bana shi ne wani taro namusamman da aka yi a kan illarcutar AIDS. Kwamitin UNDPna Majalisar [inkin Duniya, a}ar}ashin daraktansa nasadarwa, Djibril Diallo, ne yashirya taron. A nan ne har akakawo wani mai fama da cutar,Mamadou Sawadogo, wandaya nuna yadda cutar take

ragargazar al’ummar Afrika.A bikin FESPACO, akan

shirya walima iri-iri, wata tagwamnati, wata kuma tajama’a daban daban. Walimarda ta fi bun}asa ita ce waddaShugaban Burkina Faso,Blaise Campaore, ya shirya wadukkan daraktocin dafinafinansu suka kai matakin}arshe na gasar. Ammamutane da dama ba su samihalarta wannan walimar basaboda sun yi ~atan hanya, koba su shirya ba lokacin da za atafi.

Akwai wata walima waddafurodusa Fanta Regina Nacrota shirya a }auyensu can nesada Wagadugu. Ita Fanta, ’yarasalin Burkina ce, amma tanazaune a Faransa. Fim ]intaBintou ya }ayatar a bikin, yanaba da labarin wahalar da ’yanmata ke sha a Afrika inda ba adamu da ilimantar da su sosaiba.

Fanta ta burge mahalarta dayadda ta ]auke su dagahamsha}in otal ]in Hotel Re-lax, inda ta zauna a lokacinbikin, ta kai su }auyensu. Acan ta shirya abinci da abin shaa kan teburan gargajiya.Mahalarta ba}a}e da fararesun ri}a kwasar abinci tare dakore }udajen da suka jiwo}anshi su ma suka yi dandazodon ]ibar nasu rabon.

Kash! ’Yan fim na Hausa

YADDA BIKIN FESPACO YAKE

Ku]in da ake kashewa wajen shirya shi: A}alla Sefa miliyan 900

Masu ba da ku]in shirya shi: Tarayyar Turai (EU), Majalisar[inkin Duniya (ta hanyar hukumomin UNESCO da UNICEF),Hukumar Agajin {asashe Renon Faransa (wato ‘AgenceIntergouvernmentale de la Francophonie’),}asashen Denmak,Siwden, Faransa, Jamus, da Burkina Faso

A 1997 A 1999’Yan biki masu rijista 5,019 4,672Furodusoshi 208 127Dillalai 20 33Masu shirya fim 426 388’Yan wasa 150 187Daraktocin bikin 11 17’Yan jarida 539 549{asashen da suka shiga 79 84

Manema labarai sun kewaye Mweze Ngangura, furodusan da ya ci kyauta mafi daraja abikin ‘FESPACO’ na 1999 da fim dinsa Pieces d’identite

HO

TO

: D

isco

very

/Afr

ique

Mag

azin

e

57

Page 59: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

ba su zuwa bikinFESPACO duk da bun}asarda sana’arsu ta yi. A duk }asarHausa, mutum ]aya ne yahalarci bikin. Kai dai bar su dashirya Gala.

Mujallar Fim ta tuntu~iAlhaji AbdulkareemMohammed, shugaban{ungiyar Masu Shirya Fim taNijeriya (MOPPAN) reshenarewacin }asar nan wanda dashi ne aka ci har aka cinyebikin na Wagadugu.Abdulkareem ya shaida manacewa tabbas an yi rashin adalcia wurin al}alancin domin inji

ce maras wadata. Bayan Ya}inDuniya na 2 (1946) ne }asarta jawo ra’ayin masu shiryafim daga }asashen Turai(musamman Faransa) sabodayawan al’adunta da wuraremasu ban sha’awar kallo, watomutane irin su Jean Rouch.Bayan }asar ta sami ’yanci,wasu masana irin su Guy deMoal sun za~i }asar (lokacinana kiranta Upper Volta) donshirya finafinai.

Fim na farko da aka yi a

}asar shi ne ‘A minuitl’independance’ (wato ’YanciDa Tsakar Dare), kumama’aikatar ya]a labarai ta}asar ta ]auki nauyinsa a cikin1961. Daga gare shi aka farasamun daraktocin fim a }asarwa]anda suka yi suna ashekarun 1960. A cikin 1962har shahararren daraktan nan]an }asar Senegal, SembeneOusmane, ya yi fim ]in‘Borom Sarret’. Amma kumasai a Wagadugu ne aka kafa

FESPACO.A cikin 1968-1969 ne aka

fara tunanin shirya bikin.Wa]anda suka yi tunaninwasu mayun shirin fim ne a}ar}ashin Claude Prieux,daraktan cibiyar al’adu ta‘France-Upper Volta.’ Sauransun ha]a da MamadouSimpore, daraktan ofishinsadarwa da gidan waya; daOdette Sanogho, shugabangidan talbijin; sai kumamembobin }ungiyar shirin

Daga IBRAHIM SHEME

A BANA, bikinFESPACO ya cikashekara 32 tun da aka

fara shi. Shi ne bikin nuninfinafinai na Afirka wanda yafi kowane bun}asa. Biki newanda duk wani ]an fimwanda ya amsa sunansa aAfirka ba zai so a yi shi ba tareda shi ba. Akan yi shi a dukbayan shekara biyu, kumaa}alla mutum 5,000 ne sukanhalarce shi a birnin Wagaduguna }asar Burkina Faso.

A wannan biki, }asashemasu magana da Faransanci nesuke mamaye komai, sunabarin }asashe irin Nijeriya dake magana da Ingilishi sunazama ’yan kallo. A }asasherenon Faransa irin ita kantaBurkina, yawancin finafinanda ake yi ana yin su ne dafaifan sinima (wato ‘celluloid’),maimakon faifan bidiyo irinwanda aka fi amfani da shi aNijeriya. Yin fim da faifansinima ya fi tsada, kuma an fiba shi daraja a harkar fim aduniya. Ko banza, fim ]in daaka yi da faifan sinima ya fiinganci wajen fitar hoto dasauti ra]au.

Lallai Burkina ta yi sa’a tayadda har ta kasancehedikwatar shirin fim a Afirka,duk da yake ’yar }aramar }asa

Tarihi da tasirin bikin baje kolinfinafinai na Afrika (FESPACO)

shi kowa ya yi tsammanin Yel-low Card zai yi nasara sosai.

Haka kuma ya bayyanacewa akwai hujjoji da sukanuna cewa ’yan Afrika taKudu sun aika da finafinansuda wuri. “Kuma akwai recorda rubuce na ranar da al}alansuka sami finafinan.” Wannanne inji shi ya harzu}a al}aliLetebri Jones har ta saukadaga al}alancin da farko.“Kuma a gabana ta rubutatakardar sauka, a gabana kumata mi}a,” inji shugaban naMOPPAN.

Abdulkareem Mohammed

ya yi ro}o ga daraktoci dakuma furodusoshin finafinanHausa da su ri}a halartar irinwannan biki. Ko dai ba sushiga ciki ba kuwa ai da sunri}a samun kasuwarfinafinansu }warai da gaske.Sai kuma ya nuna takaicinsana ganin cewa harshen Hausashi ne na biyu a Afrika wajengirma bayan Suwahili ammakaf wurin bikin nunin finafinanbabu fim ]in Hausa a ciki.

Abdulkareem ya yi bayanikan darasin da ya koyo dagabikin na Wagadugu. Ya ce, “Aina koyo darussa da dama. Kaga dai har yanzu an bar

Gaston Kabore (a hagu), furodusa dan kasar Burkina Faso, da Baba Hama (a tsakiya),sakatare-janar na FESPACO, suna duba wata kasida

HO

TO

: D

isco

very

/Afr

ique

Mag

azin

e

mutanenmu masu shiryafinafinan Hausa a baya. Yakamata a ce suna zuwa ko donsu ri}a samun kasuwa. Kumaa wurin gasar can baya ai kaga ba a yin la’akari dafinafinan bidiyo amma dagabaya suka fahimci }asashe irinsu Nijeriya da Ghana duk nabidiyo suke yi, sai suka yardada haka.

“Ban da wannan kumagaskiya su }asashe renonFaransa sun fi mu maidahankali wajen ingantafinafinansu. Haka nan kumasuna samun tallafi bisa ga mu.To dole sai mun tashi tsaye.”

58

Page 60: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

A gaskiya, bikin FESPACOya bun}asa. Mahalarta sukanga irin finafinan da ake yayi koake so, su ga kayan aiki nazamani, su tattauna matsaloli,su kuma yi musayar adireshi atsakaninsu. FESPACO babbarkasuwa ce ga duk wani ]anfim. A cikin 1999, mutum8,000 suka halarce shi sannanan nuna finafinai 32.

Duk wanda ya je bikin zaice lallai Afrika ta ci gaba. Aganin Jean-Piere Clain,daraktan cibiyar harshenFaransanci ta Wagadugu,“FESPACO ya kasance ]ayadaga cikin al’amuran da sukacimma nasara a Burkina Faso.Muhimmin al’amari ne. Ya yidaidai da bikin nuna finafinaina duniya da ake yi a Cannes(a Faransa). Za ka iya saduwada duk wani mai ji da kansa afagen fim na Afrika a wannanwurin. Da]ewar da ya yi yatabbatar da cewa yana datagomashi mai kyau.”

Ita ma furodusa AlimataSalembere, cewa ta yi,“Finafinan da ake kawowa a

yau suna da matu}ar ingancida kyawun fasaha. Muna dagwanayen daraktoci,marubuta, ma’aikata da ’yanwasa. Hatta yadda akegudanar da bikin ya inganta. Asaboda masu tsara shi ba suhutawa a duk tsawon shekara,a gaskiya FESPACO yananan har illa masha Allahu.”

Anya kuwa! Domin kuwatun lokacin da ’yan fim da sukafito daga }asashen da kemagana da Ingilishi suka farahalartar bikin, sun fahimcicewa ana nuna masu bambancia bikin. Ana maida su saniyarware. Wannan ya haifar dagunaguni da nuna ~acin rai.Babu ma kamar a bana da ]ayadaga cikin al}alan ta aje aikintana al}alanci sabodabambancin da ta gani.

Wata majiya ta shaida wamujallar Fim cewa in ba a yida gaske ba, to ha]in kan bikinzai lalace ta yadda }asashen daba su gamsu ba za su iya shiryanasu bikin nunin finafinan,musamman a Afrika ta Kuduinda akwai masana’antar

shirya fimwadda takebun}asa ahankali. Wasu’yan Nijeriyama sun faratunanin shiryanasu bikin,musamman dayake Nijeriyace kan gabawajen shiryafim a Afrikabaki ]aya,koda yakefinafinan daake shiryawaduk na bidiyone.

Ko yaya taje ta dawo dai,ba wanda zaice bikin baidace ba, ko baitsaru ba. Saidai ajizanci irinna ]an’adamkawai!

Za a yi tarona gaba a cikin2003.

Alhaji A.A. AbdulrasheedShugaba

Shaguna Masu Lamba 6 da 7, da 8, Babbar Tashar Mota ta Kawo, Kaduna, Tel.: 062-314033

A shagon ALHAJI ABDULRASHEED ne ka]ai za ku samiingantattun finafinan Hausa na da da kuma na yanzu wa]anda kefitowa a kowane mako.

Za a kuma samu finafinan Indiya tsofaffi da sababbi; ga Chanis,da kuma finafinan Makosa; ga na addini Hausa da Turanci, gakuma finafinan bidiyo CD iri-iri sai an darje.

Akwai kuma kaset-kaset na rediyo na Hausa da ke fitowa akowane mako, da dai rediyo kaset iri daban daban.Kayayyakinmu suna da sau}in farashi ga masu sari ko sayen ]ai]ai.

Ziyarce mu a shagunanmu da ke Babbar Tashar Motar Kawo indaake shiga motar Zariya da Kano.

GANI YA KORI JI!!

GWARZAYEN FINAFINAN DASUKA CI LAMBARINGARMAN YENNEGADAGA 1972 - 2001

1972 Le Wazzou polygame, na Oumarou Ganda(Nijar).

1973 Les Mille et une mains, na S. Ben Barka(Morokko).

1976 Muna Moto, na Pipa Dikongue (Kamaru)1979 Baara, na Souleymane Cisse (Mali)1981 Djelli, na Fadika Lancine Kramo (Kot di

Buwa)1983 Finye, na Souleyman Cisse (Mali)1985 Histoire d’une rencontre, na Brahim Tsaki

(Aljeriya)1987 Sarraouina na Med Hondo (Mauritaniya)1989 Heritage Africa, na Kwaw Ansah (Ghana)1991 Tilai, na Idrissa Ouedraogo (Burkina Faso)1993 Au nom du Christ, na Roger Gnoan M’Bala

(Kot di Buwa)1995 Guimba, na Cheick Oumar Cissoko (Mali)1997 Budd Yam, na Gaston Kabore (Burkina

Faso)1999 Pieces d’identite, na Mweze Dieudonne

Ngangura (Kongo)2001 Ali Zaoua, na Ayouch Nabil (Morokko)

60

Page 61: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

da dala miliyan 100 daga ku]in tikitin shiga sinima a Amerika,}asar yawancin ’yan kallo ba su damu su kalli fim ]in da ba naTuranci ba. ‘Crouching Tiger’ yana da fassarar Turanci a kansa.

An ba Peter Pan ]an }asar Hong Kong kyautar Jarumi MaiTsara Fim (Best Cinematography) saboda yadda ya tsara fa]ace-fa]acen da ke cikin ‘Crouching Tiger’ ta hanyar amfani dasiddabaru na zamani inda ake nuno ’yan wasa suna shallakerufin gidaje da kuma tsalle a kan doguwar gora. Shi Peter Panbai ta~a cin kyautar Oscar ba a da, duk da yake yana daga cikinshahararrun ’yan fim a Hong Kong. Ya yi aiki da fitattundaraktocin Chaina irin su John Woo da Tsui Hark.

Wani zakaran shi ne wani ]an Chaina mai suna Tan Dunwanda ya shirya ki]an da ke cikin fim ]in (wato shi ne AleeBaba ]in finafinan Chaina!). An ba shi kyautar Gwarzon Ki]ana Asali (Best Original Score). Tan Dun abokin daraktan shirinne, kuma ma}wabcinsa a birnin Nu Yok na Amerika.

Mutum na hu]u da aka ba kyauta a fim ]in shi ne Tim Yip,

Daga IRO MAMMAN

A RANAR Lahadi, 25 ga Maris, 2001, masu sha’awarfinafinai a duniya suka ba idanuwansu abinci wajenkallon bikin ba da kyautar Oscar ga ’yan fim a Amerika.

Bikin shi ne mafi shahara a duniya wanda duk wani mai yin fimyake so a ce ya halarta, to bare kuma a ce ya ci kyauta. Ana yinbikin a birnin Los Anjalis, hedikwatar shirin fim a duniya (‘Hol-lywood’).

A bana, wasu finafinai guda biyu ne aka yi hasashen za suwawashe kyaututtuka mafi girma a bikin. Su ne ‘Gladiator’ dakuma ‘Crouching Tiger, Hidden Dragons.’ Haka kuwa aka yi.Amma kamar kowace shekara, finafinan da Turawa suka shiryane aka ba kyaututttukan da aka fi so, wato Jarumin Darakta daJarumin Fim. An na]a Steven Sodebergh Jarumin Darakta dafim ]insa ‘Traffic,’ aka ba ‘Gladiator’ Jarumin Fim. Duk da haka,an ba ‘Crouching Tiger’ kyaututtuka hu]u, har da kyautarJarumin Fim Daga {asashen Waje. Shi wannan fim, na }asarTaiwan ne wanda aka yi da harshen Chanis.

Fim ]in da ya zo na uku, ‘Traffic,’ ban da kyautar JaruminDarakta, ya sami wasu kyaututtukan uku. Ya ci kyautar GwarzonLabari da kyautar Gwarzon Tacewa. Shi ma, Steven Soderbergh(daraktan Erin Brockovich) ne ya yi daraktansa. An kashe dalamiliyan 46 wajen shirya shi.

Daraktan ‘Crouching Tiger,’ wato Ang Lee, shi ya kusa cinkyautar Jarumin Darakta a wata gasar wadda ba ta kai ta Oscarba, wato gasar da Majalisar Daraktocin Fim ta Amerika (Direc-tors’ Guild of America) take shiryawa. Wannan shi ne karo nabiyar a cikin shekaru 53 da aka hana wanda ya ci gasar Direc-tors Guild kyautar Oscar a wannan ~angaren.

Duk da haka, ‘Crouching Tiger’ ya }ara fito da ’yan fim ]inChanis, domin jarumar cikinsa, Michelle Yeoh, da jarumi ChowYun-fat, sun kasance farin wata sha kallo a wannan biki wandakusan dukkan ’yan fim da suka shahara a duniya suke halarta.

Darakta Ang Lee ya ciri tuta da wannan fim mai ba da labarinyadda rikici da damuwa suka kusa ruguza iyalin wani gida. Acewarsa, ya yi wannan fim ]in ne domin ya cika wani buri dayake da shi tun yana yaro. “Kowannenmu yana so ne ya cikaburinsa na yarinta… Wato ya tuno da wata }asar Chaina da take~acewa daga tunaninsa a hankali,” inji shi, yayin da yakehannunka-mai-sanda ga yawancin ’yan wasan da ke cikin shirin,

Chanis Sun Ciri TutaA Amerika, A Bikin

Shirin ‘Crouching Tiger, Hidden Dragons,’ya ci kyaututtuka a bikin fim na duniya, amma‘Gladiator’ ne Gwarzon Shekara

Steven Soderbergh, Daraktan Daraktoci

wa]anda aChaina akahaife su ammasuna zaune awaje.

Fim ]in‘Crouchng Ti-ger’ ya ciri tutaa tarihin fimtun ma kafinwannan ranar.Shi ne fim nafarko wandaba na Turanciba da ya ciza~en Oscarhar guda hu]u,kuma fim nafarko daganahiyar Asiyada aka za~adon zamajarumin fim abikin. Bugu da}ari, shi ne fimna farkowanda ba naTuranci ba daya sami sama

61

Page 62: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

wanda ya ci kyautar GwarzonTsara Hoton Fim (Best Art Di-rection).

Lallai Chanis sun nuna waduniya cewa su ma ba kanwarlasa ba ne. Shi kuma GwarzonFim na bana, wato ‘Gladiator,’daga Ingila ya zo. Fim ]in ya}ara ]aga jarumi RussellCrowe, wanda ]an asalin}asar Nu Zilan ne wanda yatashi a }asar Ostireliya. Yakuma bun}asa sana’ar wasa tajarumi mai mara baya Beniciodel Toro, ]an asalin }asar PutoRiko. Su biyun nan, ]aya yaci kyautar Gwarzon Shekara(Best Actor), ]ayan kumaGwarzo na Biyu (Best Sup-porting Actor). Daga yanzu,kowannensu ya zama babbantauraro, wato a Turance ‘super-star.’

An ba ’yar wasa Julia Rob-erts kyautar GwarzuwarShekara (Best Actress) sabodarawar da ta taka a matsayintsaleliyar lauya a cikin fim ]in‘Erin Brockovich’, inda ta fitoda sunan Erin Brockovich.Wannan shi ne karo na farkoda wannan fitacciyar jarumarta ci kyautar Oscar.

Bikin Oscar na bana (wandakuma aka sani da sunan ‘Acad-emy Awards’) ya bambanta dairinsa na baya. A bana, an luracewa labaran zamanin da(‘Gladiator’) da na }asashenwaje (‘Crouching Tiger’) dawani mai kama da ‘chamama’(‘Traffic’) su aka ba fifiko. Harta kai ga ’yan jarida sai sunsami tafinta don su yi hira da’yan wasan ‘Crouching Tiger’domin a wurin, su jarumanTuranci bai ishe su ba.

A hirarsu da ’yan jarida,jarumai suna ta murmushi

kamar gonar auduga. Del Toro,wanda ya fito ne a matsayin]an sandar }asar Mezikowanda ba ya cin hanci darashawa, ya yi godiya gaal’ummar Amerika da Mezikoda Poto Riko. Shi ma RussellCrowe, godiya ya yi ga Allah,da }asashen Amerika, Ingila,Nu Zilan da Ostirieliya.

Bikin na Oscar ya nunayadda furodusoshi dagaAmerika suke tafiya }asashenwaje suna ]aukar nauyinshirya fim, kamar yadda Dou-glas Wick da David Franzonisuka yi a fim ]in ‘Gladiator,’sannan wasu furodusoshinsuna zuwa Amerika daga wajedon neman jarin da za su yifim, wato kamar yadda AngLee mai ‘Crouching Tiger’ yayi kenan. Duniyar ta zama]aya kenan.

Ta fuskar kasuwanci, an luracewa a yanzu akwai

makekiyar kasuwar cinikin fimidan an fito daga Amerika.Misali, lokacin da aka sako‘Gladiator’ a gidajen sinima,abin da aka samu a Amerika acikin ’yan kwanaki ka]an(‘box office’) shi ne dalamiliyan 187, to amma an samitsagwaron ku]i har dalamiliyan 263 a }asashen waje.

Haka kuma a da, finafinaimasu fassara (wa]anda ba naTuranci ba) ba su cika samunkasuwa ba a Amerika. Toamma ‘Crouching Tiger’wanda ke da fassara daTuranci, da ‘Traffic’ wandayawanci da harshen Isfaniyaaka yi shi sannan aka fassarashi da Turanci, kowannensu yasami sama da dala miliyan 100daga ’yan kallo a Amerika. Bashakka, ‘Crouching Tiger’ nefim ]in }asar waje marasTuranci da ya fi kowane fimkar~uwa a Amerika a tarihi.

Mahala r tabikin sun gafinafinai iri-irimasu tsari danuna gwanintakala-kala.

Wani abinmamaki daburgewa shi neakwai wani fimda ba kowa yasan da shi ba,wanda ku]ika]an ma akakashe wajen

yinsa, wato ‘Pollock.’ Shiwannan fim yana ba dalabarain wani mai zane ne(painter) wai shi Jackson Pol-lock. To, wannan fim dai shiya taimaka wa Marcia GayHarden ta ci kyautarGwarzuwar Jaruma ta Biyu(Best Supporting Actress),wato ta bi bayan Julia Roberts.Ita kuwa Gwarzuwar Shekara,Julia Roberts, tun daga 1990take jiran ta ci kyautar Oscar.Fim ]in ‘Pretty Woman’ ne yafara fito da ita a cikin 1990.Babu kamarta a cikin jarumaimata da ke yin fim da Turancia duk duniya. Sau biyu anaza~arta don cin kyautar Oscara farkon shekarun 1990 ammaba ta sami sa’a ba sai a bana.

Da ta ci kyautar, sai ta dubidaraktan fim ]inta na ‘ErinBrockovich,’ wato StevenSoderbergh, ta gode masa. “Agaskiya ka sanya ni na zamababbar ’yar wasan da ban ta~azaton zan iya zama ba,” inji ’yarwasan mai shekaru 33 dahaihuwa, lokacin da takekaranta jawabinta na kar~arkyauta.

Sai bayan ta sauka dagadandamalin kar~ar kyautarsannan ta tuno ba ta gode waainihin Erin Brockovich tagaskiyar ba, wadda tana nan daran ta tana aiki a birnin LosAnjalis na Amerika. Sai JuliaRoberts ta ba ta ha}uri, takuma gode mata.

Kyautar da aka ba JuliaRoberts ce ka]ai mutane sukeda tabbacin tilas ita ]in ne za aba tun ma kafin a yi bikin.Sauran sai dai canki-fa]i. Dukda haka jarumar ta ce ta yimurna da aka za~o ta dagacikin shahararrun jarumai matairin su Juliette Binoche, EllenBurstyn, Joan Allen da LauraLinney, aka ba ta kyautarGwarzuwar Shekara.

“Ina }aunar duka duniya.Ina cike da farin ciki. Nagode!” cewar jarumar.

Fim ]in ta na gaba, sunansa‘America’s Sweethearts,’ watoMasoyan Amerika. Sai mungani.

Tare da rahotonnin BobTourtellotte, Sonya Hepinstallda Jill Serjeant na kamfanindillancin labarai na Reuters.

Jarumi Benicio del Toro (a hagu) da Jacob Vergas amatsayin ’yan sanda a cikin ‘Traffic’

MANYAN KYAUTUTTUKAN DA CIKA CI A BANA

Best Picture GladiatorBest Director Steven Sodernberg (Traffic)Best Actor Russell Crowe (Gladiator)Best Supporting Actor Benicio del Toro (Gladiator)Best Actress Julia Roberts (Erin Brockovich)Best Supporting Actress Marcia Gay Harden (Pollock)Best Foreign Language Film Crouching Tiger, Hidden DragonsBest Cinematography Peter Pan (Crouching Tiger)Best Original Score Tan Dun (Crouching Tiger)Best Art Direction Tim Yip (Crouching Tiger)Best Adapted Screenplay TrafficBest Film Editing Traffic

62

Page 63: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Advert

Ibro Tela

Page 64: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001 63

IBRO TELA

Page 65: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Advert:

Hamayya

64

Page 66: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

1985, kawai sai na ji an na]a ni janarmanaja na ‘Nigerian Film Corporation’!”

“Na tashi na je Legas, amma sai bansamu komai ba sai babban ofis ba kayanaiki ba ma’aikata. Da haka muka fara harwajen shekara biyu ba ma aikin komai.Na buga na buga har Allah Ya taimake nida wani permanent secretary, wani ]anTibi. Saboda muna wasan Tibi da Fulani,ya fa]a wa gwamnati cewa a ha]a ‘FilmUnit’ da ‘Film Distribution’ da suke sayofinafinai daga Amerika suna ba gidajensinima na }asa. Sai muka je Jihar Filatomuka same su, suka ce za su ba mu ofisda fili. A lokacin gwamnan Filato ma yaje wajen minista ya ce ya ji ‘Film Corpo-ration’ suna neman fili, ya ce to shi zai bamu ofis da gidajen zaman da sauransu,kuma ministan ya amince. Wannan shi neyadda aka yi har hedikwatar ‘Film Cor-poration’ ta koma Jos.”

Hukumar Shirya Fim ta Nijeriya a}ar}ashin Mista Brendan Shehu ta cimmanasarori da dama. Misali, ta shirya wasufinafinai, wanda yana cikin ayyukan data sa a gaba. A cewar Shehu, “Da an so ayi wani fim a kan [anfodiyo, kuma da baa yi ba wasu Amerikawa suka ce za su yi,

haka wasu ’yan Nijeriya suma suka ce za su yi. Ammaduk abin bai yiwu ba. Shi neda muka koma Jos na matsakan mu samu kayayyakinaikin da suka kamata a‘Nijerian Film Corporation,’ba komai sai an je Turai ba.Sannan kuma muka kafa‘Film Institute’ (makarantarkoyon shirya fim) donkarantar da yara.”

Mista Shehu ya yi maganakan irin finafinan nan da aka shirya tunzamanim mulkin mallaka a }asar nan, yayi amanna da cewa in aka fitar da su za suyi kasuwa da farin jini a wannan zamani.“Ka ga kamar fim ]in Baban Larai nafarko, da za a mayar da shi a home videomutane da yawa za su saya,” in ji shi. “Toka san fim yana da tsada, in ba ’yankasuwa suka sa hannu ba gwamnati baza ta ba da ku]i ba. Abin da ya sa haryanzu ba mu ci gaba ba kenan. Akwaiwasu finafinai da Adamu Halilu ya yi –su Shehu Umar, su ‘Kanta of Kebbi’, dawani kuma ‘Moment of Truth,’ da daiwasu masu yawa. Ba kamar bidiyo ba ne,

TARIHIN shirin fim a Nijeriya koa Afrika ba zai kammala ba sai

an sa sunan Mista Brendan Shehu a layinfarko. Domin irin gudunmawar dawannan bawan Allah ya bayar ga harkar,ba ta misaltuwa. Ga wa]anda ba su sanshi ba, shi dai Brendan Shehu shi netsohon Janar Manaja na Hukumar ShiryaFinafinai ta Nijeriya (‘Nigerian Fim Cor-poration’) da ke da hedikwata a Jos kafinwanda ke ri}e da mu}amin a yau ya hau.A cikin FIM ta ne muka ba ku labarin barinaikinsa.

Mista Shehu ya fara aiki a RediyoTalbijin Kaduna (kamfanin BCNN) acikin 1962 bayan ya bar makaranta; sune ma na biyu da aka ]auka aiki a wurin.An ]auke shi da matsayin ‘Studio Assis-tant,’ wato mai kula da ]akin ]aukarshirye-shiryen rediyo. “Wasu cikinmu natalbijin wasu na rediyo,” in ji shi.

Bayan shekara biyu suna aiki, saiTurawan da suke aiki da su za su tashi.Turawan suka ce wasu cikin su ’yanNijeriya ]in su je su yi karatu, wasu sukoyi aikin talbijin. Shehu ya yi sa’a akace ya je ya koyi aikin fim. Suka je Turaisuka koyo wannan aiki, shi da YusufMohammed (wani mai aikin ]aukar hotoda kyamarar talbijin). Da suka dawo, saishi Brendan Shehu ya sake komawaBCNN.

“A wannan lokaci da na dawo kumaTurawan suntashi,” in ji MistaShehu wandaasalinsa Bafillacene, Kirista. Ya}ara gaya wawannan mujallarcewa, “A karatunda na je na yo, nakoyi aikin edit-ing da script writ-ing (wato tacemajigi da rubuta labarin wasa). Sai yakasance bayan dawowata aikin da aka bani a talbijin ba fim ne ba, sai aka ce filmeditor kawai. Ya kasance ba mutane ammaga aiki. Don haka na yi ta }ir}irar wasushirye-shirye da ake nunawa a talbijindocumentaries (batutuwan zaman }asa),kamar wani shiri mai suna ‘LookingAround’ da makamantansa.” Haka sukayi ta yi har wajen shekara 12, har Shehuya zama ‘Senior Producer’ (babbanfurodusa). A lokacin duk shirye-shiryensaana nunasu a talbijin, musamman lokacinya}in Biyafra (wato ya}in basasarNijeriya). A cewar Shehu, idan masu

kyamara sun ]auko hotuna, shi ne yakeha]awa a nuna a talbijin.

A cikin 1976, gwamnatin Jihar Kadunata wancan lokacin ta shirya kafa ‘FilmUnit’ (wato Sashen Majigi). “Sai sukagayyace ni domin in zo in kafa masu. Na

je (amma) ba kayan aiki. Kuma a lokacinAdamu Halilu yana ‘National Film Unit.’Sai na je na same shi don ya ba ni aronkyamara tunda ina da cameraman, UsmanGaladanchi da kuma soundman Aliyu{an}ara. Sai muka yi short documentary(guntun shirin wayarwa) mai sunaKaduna State At A Glance, har gwamnatita yi mamaki, ta ce ai za a iya yin fim. Saiaka ba ni ku]i musamman na je Turai nasayo kayan aiki. Da na dawo, muka cigaba da shirya finafinai na documentarieskamar na zaman lafiya da na al’adunmuda ayyukan gwamnati da sauransu. A

Yadda muka kafa HukumarShirya Fim ta Nijeriya

Hira da Mista Brendan Shehu

Mista Brendan Shehu

65

Hira da Brandan Shehu: SHAFI’U M. USMANRubuta sharhi. IRO MAMMAN

Page 67: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

aikin fim na celluloid (fim na sinima) nada tsada. Yadda za a mayar da su zuwakaset na bidiyo ku]i ne masu yawa, babugwamnatin da za ta ba da ku]in da za kayi wannan aikin. Su kuma ’yan kasuwa,za su ji tsoron zuba ku]insu don tunaninwata}ila ba za su samu riba ba. Wannanshi ne abin da ke kashe mu.”

Mujallar FIMFIM ta tambayi BrendanShehu shin ko bai ganin akwai riba in da’yan kasuwan za su sanya hannu, ga kumatunanin jibge finafinan a gidajen tarihi baida wani tasiri ga al’ummar }asa?

Sai ya amsa: “To ita dai gwamnati, tunkafin in bar wurin, na yi na yi na yi, abinya gagara, har muka so mu ha]a hannuda Hukumar Talbijin ta {asa (NTA)(amma) da aka ga yawan ku]in sai kowaya gudu.”

[aya daga cikin nasarorin BrendanShehu a hukumar da ya jagoranta shi neshirya fim ]in Kul~a Na |arna, kuma shine darektan fim ]in. A halin yanzu anmayar da shi zuwa faifan bidiyo. To, munji an ce wasu sun yi zargin wai bai ji da]inhakan ba saboda tunanin wai ba za a samuribar fim ]in sosai ba ta wannan hanya.Shin shi bai yarda da mayar da finafinansinima zuwa na bidiyo ba ne?

Shehu ya ce, “To ai ni na ba su, da naje Turai. Ka san wannan fim ya kai ni}asashen duniya. Saboda duk wanda yayi fim na sinima, za a neme shi a Turai.Abin da mutanenmu ba su gane ba kenan.Don ka shirya fim na bidiyo ba a damuwada kai. Amma ka ga in ka shirya majigi akan (faifan)celluloid (na sinima) ko’inain ana bikin nuna majigi, za ka iya halarta.Ka ga da na yi wannan fim (na Kul~a Na|arna) na kai Burkina Faso, na je Milaninda na samu award (lambar yabo). Bayanmun gama Milan, Holland suka aiko naje. Daga nan kuma na je Los Anjalis,Amerika. {asar Faransa ta ]aukinauyinmu ni da wasu Yarbawa. A lokacinshi ne ka]ai fim na Hausa cikin faifansinima a wannan lokaci. To da a yanzuwani zai sake yin na Hausa on celluloid,abin da zai faru da shi kenan.”

Ina masu shirin fim na Hausa? {alubalegare ku! Mun san za ku so ku san a yanzuin mutum ya ce zai shirya irin wannan fimzai kashe kimanin zunzurutun ku]i harn a w a ?Mun yi wa Brendan Shehu wannantambayar. Sai ya kada baki ya ce, “Mutumzai kashe fiye da naira miliyan 20 don yafitar da fim mai kyau.” Ya }ara haske:“Amma shi ma wannan }arancin abin damutum zai iya kashewa kenan fa. Ammaka ha]a da bidiyo inda wasu suke kashedubu 50 ko]i dubu 100 kacal! Koda yakeko na biyo in kana son ka yi fim mai kyau,

miyar ba zata yi da]i bakamar in daka ha]amata komaida komai daya kamata.”

Tir}ashi!Mista Shehuyana dagac i k i nmutanen dasuka yiamanna dac e w af i n a f i n a nbidiyo daa k eshiryawa ayanzu sunab u } a t a rg y a r a

hanyar samun ku]i sai suka fa]a,” in jishi. Su kuma mutane masu kallo ba wurinzuwa, ko fim bai yi kyau ba haka nan zasu saya dole; don yanzu in kana son kasha}ata in kai ba mashayin giya ba ne daza ka je gidan giya, ina za ka? Don hakadole ka zauna ka kalli bidiyo. Sabodahaka kowane fim aka shirya sai su zaunasu kalla in yai kyau ko bai yi kyau ba, indai ya ]an ba su dariya kawai shikenan.”

Shehu ya yi amanna da cewa }ungiyarfurodusoshin finafinan Hausa ta Arewawadda aka kafa a Katsina za ta iya yingyara kan wannan harka. Amma ya ce bakafawar ba ce matsalar, a’a samun ha]inkai ]in ne. “Don yanzu kowa neman ku]iyake yi. Bayan an kafa an ce ga abin daza a yi ga abin da za a hana, wani yanaiya tsalle ya ce ku ke ciyar da shi ko kukuka yi masa kaza da kaza? Amma da}ungiyar tasu za ta kafu sosai – a ce wandabai yi fim irin kaza ba, ba za a yarda yashiga kasuwa ba – da an samu gyara. Kaga kamar finafinan da ake yi a Kano ]innan suna kwaikwayon al’adun Indiya ne.Me ya sa ba za su yi na al’adunmu ba?Me ya sa ba za su yi fim na tarihin}asarmu ba? Kawai sai finafinan love naIndiya da Turawa! Kai ka ta~a ganin aal’adun Hausawa saurayi da budurwasuna love suna kiss?”

Wakilin FIM bai ta~a gani ba. Ammawakilin namu ya nuna wa Mista Shehucewa wasu furodusoshi suna tsoron insuka komo ga yin finafinai na al’adutsantsa ba za su samu kasuwa ba, waijarinsu zai karye. Sai }wararren mai shiryafim ]in ya amsa, “Ai dole a saya! In da baa yin irin wa]annan na love ]in har a saba,don ba wurin zuwa kamar yadda na ce abaya?”

Mutane za su so su san tunda BrendanShehu ya aje aikin gwamnati, me yake cikine? Shin yana shirin shirya finafinai neko kuwa?

A cewar Shehu, “Shirya fim sai da ku]i.In za a kawo ku]i sai in yi fim. Ni abin danake yi yanzu shi ne aikin documentriesda adverts (wato shirye-shiryen talbijin nafa]akarwa da tsara talla a talbijin). Ni daiba ni da ku]i. Kuma misali mutum ya cibashin naira miliyan guda ya zo ya shiryafim na bidiyo, ya zai yi in ba a samu ku]inba saboda piracy (satar fasaha) ya yiyawa?”

Shehu ya ba da wata shawara, kamarhaka” ’Yan kasuwa ya kamata su goyibayan wannan harka. Da ’yan kasuwa zasu ha]u su goyi bayan ’yan fim to da anci gaba. Kuma su ’yan fim su tsare gaskiyaa dangantakarsu da ’yan kasuwa.Shawarata ita ce ’yan kasuwa su ba daha]in kai wajen shirya finafinai naal’adunmu da tarihin al’ummominmu,kuma a ri}a shirya finafinai na sinima (cel-luloid).”

za ka iya kashe fiye da naira miliyan biyu.Al’amarin kamar girkin miya ne, in ka ceza ka sa daddawa kawai ka bar sauran,

matu}a. A ganinsa, “A gaskiya suna ~atayaranmu da al’adunmu. Amma da a cemuna da }a}}arfan }ungiya ta masushirya wa]annan finafinan, to da su za suce ga irin fim da za a yi, in ka wucewannan wurin da aka tsayar da kai, to baza a nuna fim ]in ka ba. Amma a yanzukowa yana abin da ya ga dama ne, bakuma a Arewa ka]ai ba, ko’ina ne a }asarnan. Ka ga fim na Inyamurai daYarabawa,tsafi! Kowa dai na neman ku]i. Shi ya sahar yanzu ba mu tashi ba. Ka ga }asashekamar Burkina Faso, su Mali da Senegal,a kullum suna ‘film festival’ (bikin nunafinafinai) na celluloid. Ka ta~a jin shi aNijeriya?”

A’a, ba mu ta~a ba. Amma ai muna daHukumar Tace Finafinai ta {asa(NFVCB) a Abuja. Shin Brendan ba yaganin za ta iya... Ko kafin mu rufe baki,sai ya kar~e a fusace, “Wane Film Cen-sorship Board? Ba ka ganin blue films(finafinan tsiraici) har a }auyuka? Agidajen sinima ma za ka gani, ba wandaya damu. Amma kyau dai kowace jiha ta}asar nan ta samu irin wannan hukuma takanta don al’adu da addinin mutanen jihar.Domin fim da za a nuna a Legas ya daceda al’ummar wurin, ba za a iya nuna shi aKano ba, don bambancin al’ada... Ka gafita tsirara a wajen wasu ba wani abu bane, amma mu a nan Arewa wannan waniabu ne da ba kowa ke son gani ba.”

{wararren daraktan yana ganin cewayawancin matsalolin suna faruwa ne dagasu masu shirya finafinan. “Mafi yawa dagacikin furodusoshi ba su san aikin fim bakuma ba sa zuwa su koya, kawai sun ga

Duk wandaDuk wandaya yi fim naya yi fim nasinima, za asinima, za aneme shi aneme shi aTurai. AbinTurai. Abin

dadamutanenmumutanenmuba su ganeba su ganeba kenan.ba kenan.

Don kaDon kashirya fim nashirya fim nabidiyo ba abidiyo ba adamuwa dadamuwa da

kai.kai.

66

Page 68: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001 67

Fitaccen jarumi, Ahmed S. Nuhu,ya yi bayani a kan rawar da yataka a Mujadala, da burinsa na yinaure da kuma komawa makaranta,sa’annan ya kare dan’uwansa AliNuhu a kan sukar da jarumi Isa A.Isa ya yi masa kwanan baya.

Fim: A lokacin da fim ]in ku naMujadala ya fito, mutane sun kalle shi datunani iri-iri. Me kake ganin mutane sunfuskanta game da wannan fim?

Ahmed: Assalamu alaikum. Ni na jida]in yadda mutane suka kar~i wannanfim. To amma mata suka fi ba ni mamaki.Ka san mata ba su so a ci wa ’yan’uwansumutunci. To yanayin yadda na fito na takarawar gani ga Abida da Fati Mohammed,a dai yawan finafinan da ake yi gaskiyaba a samu jarumin da ya fito ya haukata’yanmata a lokaci ]aya kama ta ba.Saboda su (su Abida) yara ne da ake so;mata ’yan’uwansu na }aunarsu. To daMujadala ya fito, mutane sun kar~e shi.Na samu wasi}u da dama, wasu su ce donme na wula}anta Abida, wasu kuma Fati?Wasu kuma cewa suke ba kyau ne da niba ballantana in wula}anta ’yan matandon suna so na. Wasu yadda suke sonAbida sun ga tashin da nake yi in tafi inbar ta lokacin da ta nuna tana so na, shi neabin ke }ona masu rai, su wai lallai ya zaa }are a cikin Mujadala na 2? Zan auriAbida ne ko zan auri Fati? Kai, har masuna rubuto min wasi}a wai don Allah inje in ba Abida ha}uri kan wula}ancin dana yi mata. Sai dai duk ba su ganin cewaabin shiri ne ba, ba da gaske ba ne!

Fim: To ba su yi la’akari da irinwula}ancin da ka yi wa Fati ita ma ta ramasaboda ka je gidansu ta kore ka?

Ahmed: E, a lokacin da Fati ta rama agaskiya duk mutum mai ilimi idan ya yitunani ya ga duk matar da ta ce tana sonka, kai kuma ka wula}anta ta har ka samijinya a asibiti, to in har ta taso ta zowurinka, ka tabbatar ita mai }aunarka ce.Saboda ni abin da ya sa, naje wurinta tawulan}anta ni ba don komai ba sai donna ga ta je wurina a asibiti tana koke-koke.Ta shiga matsanancin hali a kaina, shi yasa na je wurinta. Don ta wula}anta ni, niwannan ba komai ba ne wurina, don niina tunanin a kanta zan iya rasa rayuwatasaboda ta shiga wani irin hali don so na.

Fim: To tunda wannan abu ya faru ahaka, a kashi na 2 na fim ]in da zai fito zaka yi }o}ari ka wanke kanka kenan?

Ahmed: Gaskiya ni idan son samu ne,to in }ara wula}anta su! Ni na gaji haka.In ka lura, duk yawancin finafinan da na

ban ji da]in wannan wa}ar ba. Don harmafarkinta na yi.

Fim: Ba ka ganin irin wannan rawar daka taka a }arshe zai janyo maka ba}in jini,musamman ga mata?

Ahmed: E, gaskiya sai dai in ba suha}uri saboda yanayin abin da ake ba nikenan. Amma in sun tuna su matan, ai anyi don soyayya ne. To soyayya babu abinda ba ta iya haifarwa gaba ]aya.

Fim: Mun ji an ce bayan Mujadala yafito furodusoshi da yawa sun yi maka caasaboda ka burge su, suna so kuma ka fitocikin finafinansu. Ko za ka iya fa]a manawasu daga cikinsu?

Ahmed: Wasu furodusoshi ba su sanyadda nake yi ba ko ya nake acting ba saia Mujadala. Zan iya gode wa (darakta)Tijjani Ibrahim da ya wanke ni ya fitar dani kunya a idon jama’a. Saboda acting ]inda ya sa ni, wani lokaci har haushi nake jiidan ya ri}a ce min in yi kaza ko in yikaza. To yau ga shi ya wanke ni. Ina godewa kamar irin su Aminu Shehu, AwwaluSarauniya, Ibrahim Dambazau, ba donkomai ba ne suna ganin irin acting ]in danake yi da kuma irin }wazon da nake yi,ga shi kuma mun saba da su.

Fim: To kuma wani abin da muka ji shi

ne furodusoshin nan suna son sa ka wasada Fati ne. Kome ya jawo haka? Shin kazama wani sabon Ali Nuhu kenan kai ma?

Ahmed: (dariya) Shi kansa Ali Nuhu,ranar nan sai da ya tsokane ni a gida yakecewa... Ita ma Fati ]in idan ta zo ta sameni da Ali takan ce min, “Zo mana sabonangon tunda na watsar da tsohon!” Sai tari}a yin wasa tana cewa, “An ci moriyarganga!” Ta koma ga }ane, ba don komaiba sai don ta ga mun dace da juna a cikinfim ]in Mujadala; da ma ba mu ta~a fitowa

Na saba wula}anta ’yan mata – Ahmed S.Nuhu... amma fa a fim!

fito nakan wula}anta ’yan mata. Ammakada jama’a su ]auka haka nake a waje.Ni mutum ne mai fara’a koda wanelokaci, sai dai yanayin labari ne – yaddaaka ba ni haka zan yi a cikin fim. To ammawula}anta su a fim ni a gaskiya akwai indasuka ci min mutunci daga Abida har Fatia wata wa}a (a kashi na 2). Ni wannanwa}ar a gaskiya a zuciyata har ga Allah

a matsayin saurayi da budurwa a cikin fimba sai a Mujadala. Ni burina ya cika(tunda) na yi fim da Fati, na yi da Abida,na yi da Maijidda. Ni a yau ko yanzu nadaina fim na gode wa Ubangiji.

Fim: Yaushe Mujadala 2 zai fito?Ahmed: A makon farko na watan Afrilu,

insha Allah.Fim: Wasu na cewa ka auri Maijidda.

Ba ka ganin yadda aka ri}a ce wa Ali yaauri Fati za a dawo a ce Ahmed sai kaauri Fati?

Ahmed: Gaskiya mutane masu rubutomin wasi}a cewa in auri Maijidda ba susan cewa abokina ne zai auri Maijidda ba.Na san yanzu wasu finafinai kamar suNazari, Lalura da Jafa’i da sun fito za a ceya kamata mu yi aure da Fati.

Fim: Mun san budurwar Ali tanaKaduna. Kai taka a ina take?

Ahmed: Ni har yanzu ga shi nan daiina ta canke-canke ne. Kwanaki na ce saiAli ya yi aure kafin ni in yi; gaskiya yaddana kai wannan matsayin }arshenta ma inriga Ali aure. In har ya ce sai ya tsaya yashirya, to ni sai in yi farat ]aya in riga shi.

Fim: A ina budurwar take?Ahmed: Har yanzu ban samu ba. Har

yanzu ina ]an bincike ne sai na samu

Page 69: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

wadda ta dace da ni, mai hankali. Ka sanhar yanzu wasu mutane suna ]auka mu’yan iska ne. Wasu na ]auka ai mu ba zasu iya ba mu ’yarsu ba. Ba su san sana’amuke yi ba. Ba wai mun rasa sana’a bane shi ya sa muke wannan abin. Kowayana da iliminshi da Allah Ya ba shi.Kuma yana da ]an rufin asiri bakingwargwado da Allah Ya ba shi.

Fim: Kwanan baya ]an wasan nan IsaA. Isa ya yi magana a kan ]an’uwankaAli inda ya ce furodusoshi ne na Kanosuka ]aga Ali har aka san shi. Ya ce to suyanzu ga shi sun fito suna ja da shi kumaya daina ]aga wa mutane kai. Menenera’ayinka kan wannan magana da Isa yayi?

Ahmed: Ka san mu yara ba mu dahankali; idan mutum yana rarrafe har yafara ta-ta-ta, to bai san irin maganar da zaiiya fa]a ba. Isa ya je ya sake tunani, koya je ya yi ilimi, ya shiga makaranta yagano menene harkar fim? Shi fim da kakegani ba wani abu ba ne, }wazo ne; ammasai ka karanci abin. Ni har yanzu ban ]aukiIsa wani actor ba; ba don ya zagi yayanaba ko wani abu (sai don) saboda yanaover-acting (wuce gona da iri a wasa). Kasan idan kana yin wasan fim, ba kai ba neza ka fa]i abin da kake yi. Jama’a ne zasu fa]a a cikin gari, kuma muna samunbayaninsu cewa overacting yake yi.

Ba zan ta~a mantawa ba, lokacin da akayi Akasi, to kafin ya fito sai (Isa) ya yi tazuwa wurin furodusoshi da abokanensayana cewa ai ya cinye ni a Akasi. Sai dafim ]in ya fito kuma sai mutane suka dingakukan cewa me ya sa yake over-acting?Saboda haka Isa idan zai wannanmaganar, to ya natsu ya san me zai ce. Aini ne yanzu daidai sa’ansu da zai ta~a, baAli ba.

Fim: Ko kana ganin wannan maganatana da ala}a da batun Ali da Kanawa ]innan?

Ahmed: Ka san duk mutumin da akace cikakken Bakano ne, to ya san wasanda ke tsakanin Zazzagawa da Kanawa.Don haka ni ina ganin wa]anda suka yiwannan magana kamar irin Isa ]in, in akayi bincike sai ka ga ’yan Nijar ne; sun daishigo gari sun zama wani abu, sai su cesu ’yan Kano ne.

Kuma ba Ali ne ya yi wa}ar nan ba.Miming ya yi. Amma wasu mutane da basu da ilimi sai su yi ta fa]a: “Ai Ali ya ceKanawa na da gyambo!” To, su yi tunanifa, ba shi ne yai abin ba. Kuma shi a nanKano aka haife shi.

Fim: Kana jin wannan magana ta shafeka kai kanka?

Ahmed: E, wannan magana ta shafe nidon an ce ma wai an min duka a ‘FaggeWelfare.’ Abin ya ban mamaki. Har wani

ya zo a ranar ya ce ya zo duba ni ne an cean yi min duka. Kuma ga shi ranar nan nashiga Fagge, su wallahi da]in abin masuka ji. Saboda su (’yan Fagge) su necikakkun ’yan Kano. Duk mutumin da keFagge ya san menene ala}ar Zazzau daKanawa. Sai dai kawai matasa su ]an yi

aka kafa shari’ar Musulunci a Kano akakori karuwai to kuma an hana mu yin fim.Ina za mu koma? To yau burinmu ya cikaan ha]a mu da malaman da suka fahimcikan abin, an kuma soke mana wa]ancandokokin. To wannan ne ’yan ba}in cikike wa hassada. A da sun ]ebi ruwa sun

Ni har yanzu ban ]auki Isa wani actor ba; ba don ya zagiyayana ba ko wani abu (sai don) saboda yana over-acting(wuce gona da iri a wasa). Ka san idan kana yin wasan fim,ba kai ba ne za ka fa]i abin da kake yi. Jama’a ne za su fa]aa cikin gari, kuma muna samun bayaninsu cewa over-act-ing yake yi.

wasanni da dariya haka.Fim: To Ahmed bayan waccan doka da

aka kafa wacce ta hana yin fim sai kumaaka soke wannan doka aka yi wata daban.Ga shi kun dawo harkar yin fim gadan-gadan. Kai yanzu ina ka sa gaba?

Ahmed: Ai ni abin ya ban mamaki (da)mutane suka ri}a aika wa Gwamna farincikinsu na hana yin fim. Ina so su fahimta:mu fa wa’azi muke wa mutane domin sugane abubuwan da ake yi. Ni alhamdulillahi burina ya cika. Da, wani wurin maba na iya zuwa don har nuna mu ake anacewa, “Ga ’yan iskan nan an dakatar dasu!”

Ni abin da ke }ona min rai shi ne daake ha]a mu da karuwai. Saboda yadda

zuba a }asa sun sha. Yanzu sai su ]ebiruwan kwata su je su yi wanka da shi.

Fim: A }arshe bayan Ali ya zamafitaccen ]an wasa, yanzu ya zamafurodusa har ya yi fim guda biyu. Kaiyaushe za ka yi naka fim ]in?

Ahmed: Ni idan Allah Ya yarda kwanannan zan yi. Amma kada mutane su ]aukadon ku]i zan yi. Ba don komai ba ne saidon ra’ayina ne kuma don in aje tarihi.Don ina ganin ba da jimawa ba zan barharkar fim in koma karatu.

Fim: A ina?Ahmed: A Kaduna. In da rabon in dawo

harkar fim, shi kenan, in kuma babu, toya zama tarihi.

Fim: Ahmed, mun gode.

Abokan Mujallar Fim

Mujallar Fim tana da masoya a ko’ina cikin }asar nan. A nan, wasu gungun matasane a Tudun Wada, Kaduna, masu }aunar mujallar, suka yi hoto na musamman dontaya mu murnar buga mujallar ba fashi har tsawon shekaru biyu. Daga hagu: Musa,Salisu Salinga, Ahmed, Sadiq, Isah, da ‘Lagos Guy.’ Sun yi hoton a harabar ‘S.U.S.Video Production’ da ke Lamba PA 3, Ibrahim Taiwo Road, Tudun Wada, Kaduna.Allah Ya bar mu tare!

68

Page 70: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001 69

ABDULLAHI Alhassan Jallah neshugaban Majalisar Matasa na{aramar Hukumar Fagge, a Jihar

Kano. Majalisar ta ha]a dukkan}ungiyoyin matasa da ke yankin. Sukanyi taro a wani shahararren wuri da ke kusada sakatariyar {aramar Hukumar Faggecikin birnin Kano mai suna DandalinMatasa, ko kuma ‘Welfare’ kamar yaddaaka fi saninsa. A wannan dandali ne ’yanfim ]in Hausa sukan taru a kowace ranada yamma, ya-Allah domin su yi taro na}ungiyoyinsu ko kuma dai su sadazumunci a tsakaninsu. Kafin }addamar daShari’ar Musulunci, mutane sun yi sukarcewa dandalin matattarar ’yan iska ce indamaza da mata ke cu]anya ba kunya batsoro. Su Abdullahi Jallah sun ta~a yinwani yun}uri na tsarkake wurin, ta hanyarfito da }a’idoji. Misali, tilas kowa yawatse daga wurin kafin }arfe 8 na dare,sannan ba a yarda wanda ba memba na

wata }ungiyar wasan kwaikwayo ya shigadandalin ba, haka kuma ko memba ]insai ranar da }ungiyarsu ke da taro sannanzai shiga dandalin, musamman mata.

To, tun a wancan lokaci muka yi watahira da Jalla, amma ba mu samu damarkawo maku ita ba sai a yau. Abin juyayishi ne wakilanmu sun lura da cewa an farakomawa ’yar gidan jiya a dandalin, watoana dabdala da she}e aya kamar da. Yanzudai ga Jalla:

Fim: Shugaba za mu so ka gabatar dakanka.

Abdullahi: Ni Sunana AbdullahiAlhassan Jalla, kuma na yi firamare aFagge kafin in tafi sakandare ta ‘AirportRoad,’ Kano. Kuma tun ina sakandare, ajiuku, na fara harkar }ungiyoyi, kuma harkawo yanzu ita nake yi.

Fim: Ka ba mu ta}aitaccen tarihinkafuwar wannan }ungiyar taku.

Abdullahi: To wannan }ungiyar da akafi sani da Majalisar Matasa ta {aramarHukumar Fagge, duk da cewa akwai ta akowace }aramar hukumar Jihar Kanokuma da uwarsu ta jiha wacce Alhaji SaniDawaki Gabasawa yake shugabanta,

gaskiya wannan majalisa ta da]e kumaakan yi sabon za~en sababbin shugabanniduk bayan shekara hu]u. Mu a halin yanzumuna da kusan shekaru biyu a karagarmulki.

Fim: Shin wannan wuri da kuke taruwawa ke da shi tsakanin ku da hukuma?Kuma menenen tarihin kafuwarsa?

Abdullahi: Wannan Majalisar Matasada aka fi sani da ‘Social Welfare,’ wuri nena gwamnati, ita kuma Majalisar tana}ar}ashin Ma’aikatar Al’adu, Matasa daWasanni ne ta jiha. Shi kuwa wannan gida,zan iya cewa kusan shekaru 30 da sukawuce ana amfani da shi a wannan matsayi.Mu kuwa mun samu a}alla shekara 10muna zuwa gidan tun ba mu da yawa, gashi a halin yanzu mun yi yawa har tunanimuke yi mu rage yawan jama’a.

Fim: Wa]anne matsaloli kuka fuskantakafin ku wayar da kan jama’a har sukafara tururuwa zuwa wannan wuri?

Abdullahi: Yadda aka yi mun bihanyoyin da muka wayar wa mutane kaihar suka san muhimmancin wannan wuria gare su, ka ga a}alla a {aramar HukumarFagge kawai muna da }ungiyoyi har 300da wani abu. Mukan bi }ungiyoyin nan

]aya bayan ]aya mu gabatar da kanmutare da manufofin wannan Majalisa, kumamu jaddada masu cewar duk wata}ungiya laimarta ita ce Majalisar Matasata }aramar hukumarmu kuma muna}ar}ashin jiha. Saboda haka duk watamatsalarsu in suka zo da ita gare mu, wacceza mu iya yi sai mu yi masu, wacce ba zamu iya yi ba kuwa sai mu kai sama.

Fim: Kamar wa]anne irin matsaloli nekuka fi samun kokawa a kai?

Abdullahi: Kukan da muka fi samudaga }ungiyoyi shi ne, yawanci sunacewa suna da rajista da ma’aikata;ma’aikatar nan da suke magana a kai}ar}ashin gwamnati take amma su ba suga wani taimakon da ma’aikatar nan takeba su ba a matsayinsu na ’ya’yanta, alhalinkuma ma’aikatar nan tana nemantaimakon }ungiyoyin a duk lokacin dabu}atar hakan ta taso. To a irin wannan

hali mu ne muke shiga tsakani donmagance duk wata ~araka da ka iyaaukuwa.

Fim: Ita wannan majalisa taku ba ya gataimakon da kuke samu daga wajenmutane, akwai wani tallafi da gwamnatike ba ku?

Abdullahi: Gaskiya Jiha dai mun sangwamnati tana taimaka masu, amma mudai kam a wannan }aramar hukuma babuwanda yake taimaka mana a yanzu illa shishugaban }aramar hukumar na wannanlokaci, Alhaji Suleiman; babu abin da zamu ce masa kamar Allah Ya saka masa daalheri. A yanzu haka akwai wani zaurenmatasa da aka ce za a gina a kowace}aramar hukuma wanda idan aka gamaginin akwai wata }ungiya daga Turai dasuka ]auki nauyin sanya kujeru da teburada sauran kayayyakin aiki a dukkanningine-ginen. Mun zo mun samu shugaban}aramar hukuma muka fa]a masa halinda ake ciki, a take ya ce a dubo wannanwuri da }iyasin ku]in da za a kashe wajenaikin.

Fim: Kamar hedikwatarku kenan?Abdullahi: E. A bayan Wapa filin da za

a yi ginin yake. Kuma shi shugaban mun

Abdullahi Alhassan Jallah

Page 71: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 200170

same shi da nufin ya sama wa majalisarmota domin zirga-zirgar halartar tarurrukada wasu ayyukan, kuma ya yi al}awarinbiya mana wannan bu}ata.

Fim: Wannan wuri ya riga ya zamawani dandalin ha]uwar matasa wanda zaniya cewa kusan a nan Arewa babu irinsawajen ha]a ’yan wasa, amma abinmamaki sai ka ga babu wasu kayayyakinjin da]in da ya kamata a ce akwai su awurin irin su talbijin, wuraren zama masukyau, da sauransu. Ko me ya sa hakan?

Abdullahi: A shekarun baya duk irinwa]annan abubuwan akwai su a wannanwuri, amma babban ]akin taro na wannangida da ya yi gobara akwai abubuwa masudama da suka }one, ciki kuwa har da irinsu talbijin da bidiyo.

Fim: Amma a yanzu da dukkanwa]annan abubuwa babu su, shin sakacine na gwamnati ko kuwa?

Abdullahi: A yanzu dai mun yankeshawarar mu sake tunkarar shugaban}aramar hukuma da wannan matsala.Abin da ya sa muka jinkirta shi ne baikamata ka damu shugaba da matsalolinkaba; tilas a ri}a ]an saurara masa. Ya-muya-mu sai muka zartar da shawarar tundamuna da }ungiyoyi ya kamata mu rin}ashirya wasannin da za mu dinga zuwawasu garuruwan da }auyuka muna ]ansamo ku]a]en da za a farfa]o da wannanwuri.

Fim: Kun fara yin haka ]in?Abdullahi: Ba mu fara yin hakan ba

tukuna saboda muna sauraron al}awarinda gwamnatin Jihar Kano ta yi mana nagyara ]akin taron da ya yi gobara.

Fim: Kasancewar wannan wurimatattarar samari da ’yan mata ce, tundaan kafa Shari’a yanzu a wannan jiha waneshiri kuke yi don ganin wannan majalisaba ta zama mafaka ba ga ~ata-gari atsakanin mata da maza?

Abdullahi: Alhamdu Lillahi, a da in kazo gidan nan za ka gan shi barkatai }ofabu]e ga kowa. To duk wannan abu saimuka ga bai kamata mu zura wa malamaiido kawai a kan maganar Shari’ar nan ba,ya kamata mu ma mu taimaka masu.Saboda haka sai muka ga maimakon mubar wurin nan sakaka, kowa ya ga damaya shigo, sai muka tsaida shawarar a yanzusai wanda muka san ]an }ungiya ne zamu bar shi ya shigo.

Kuma kamar matan da muke tare da suwa]anda muke fatan Allah Ya kawo masumazajen aure, muka sa masu dokar dukwacce za ta zo wurin nan dole ta sakayanta na kamala ’yar mutunci. Kuma acikinmu akwai masu yin aure ya-mu ya-mu tsakanin mazan da mata. Kuma akwaiwani shiri da muka yi na tanadar wakowace mace hijabi wanda a duk lokacin

da za ki zo wurin dole kiyi amfani da shi. Kumamun haramta wa kowaceyarinya yin soyayya dawani saurayi – ko dakuwa ]an }ungiya ne –a wannan wuri; duk mainemanki ya bi kigidanku. Bayan mungama harkokin }ungiyagabanin magariba kowaya kama gabansa.Wanda kuwa duk yasa~a wannan doka zamu hukunta shi. Mutanesuna yabawa kanwannan mataki da muka]auka.

Fim: Da farashugabancin wannan}ungiya zuwa yanzuwace nasara kake ganinka samu?

Abdullahi: Nasarorinda na samu a kanwannan al’amari ba zaniya fa]insu ba. Ita kantaMajalisar Matasa wasuma ba su san ta ba kamaryadda na fa]a maka abaya. A wannan lokacinne ma ai mutane sukesanin menene MajalisarMatasa. Ka ga wannan aiba }aramin ci-gaba bane, ni a wurina.

Fim: A yanzu wanekira gare ka ga ita{aramar HukumarFagge da kuma}ungiyoyin da sukezuwa wannan wuri?

Abdullahi: Kiran dazan yi ga }ungiyoyin dasuke zuwa wannan wurishi ne ha]in kai, shi neabin da ya fi dacewa atsakaninmu, musammana kan dokokin nan damuke kafawa don cigabanmu. Kiran da zanyi ga }aramar hukumakuma shi ne abin da takeyi na alheri ga matasa taci gaba. Ta }ara wayarda kan matasa a harkokinyau da gobe. A }arshe,ina kira ga MajalisarMatasa ta Jihar Kano data ba da himma wajenwayar wa matasa kai kanmuhimmancin shari’arMusulunci da aka kafa.

SUNA: Abdullahi Ahmad ChiromaSUNAN RANA: BabannanShekaru: 26MAHAIFA: Shara]a Phase I, Kaida {afa, KNMATSAYIN KARATU: Difiloma.AURE: Da niyya!WASU FINAFINAI DA KA FITO CIKINSU DASUNAN DA KA FITO DA SHI: Uwargida (SufetoHabibu); Ajali ([an sanda); Gwi Da Yara (Sallama);

Auri Saki (Nura); Uwa Mai BadaMama (Lauya).

WA[ANDA KA FI SO: Dukkansu.WA[ANDA KA TSANA: Babu.KAYAN DA KA FI SON SAWA: Kayan da aka

yarda Musulmi ya sa.’YAN WASAN DA KA FI SO: Kowa da kowa.YANAYIN DA KA FI SO: Sanyi.ABIN DA KA FI SON A YI MAKA KYAUTA DASHI: Turare.HALAYEN DA KA FI SO GA Mace: Kunya daaddini.KA TA|A HA[UWA DA MAI IRIN WANNANHALIN?: {warai kuwa.INDA KA FI SO KA ZIYARTA: Kabarin Manzo.ABIN DA KA FI SO KA KARANTA: Al}ur’ani.ABIN DA BA KA SO: Girman kai da wula}anci.ABIN DA BA KA SO A YI MAKA A CIKIN JAMA’A:

Muzantawa da }arya.KA IYA MOTA?: A’a.KAYAN LAMBU: Kowanne.ABIN DA KAKE SO KA ZAMA: Jarumi.

Mun maimaita wannan filin saboda kuskuren da akasamu a watan jiya. A gafarce mu. – Edita

MMUU S SANAN ’Y ’YANAN W WASAASA

Abdullahi Ahmad Chiroma

BabannanBabannan

Page 72: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

mu dawo. Kuma iyayena daita kakar tawa da mukazauna da ita a Saudiyya duksuna nan a nan Kano.

DA haka Ladi, waddaaka fi sani da Mutu-Ka-Raba tun lokacin

da ta fito a matsayin jarumarfim ]in Mutu Ka Raba, ta faraba mu labarinta. To, da kuka jiLadi ta ce ta tafi Saudiyya tunkafin ta }are makaranta, a can]in ma ba ta yi karatun ba.Dawowarsu daga {asa MaiTsarki a yanzu za a kai shekara12.Ladi ta shiga harkar fim a

wajen 1998 a lokacin da ta fitoa cikin Al’ajabi. Daga wancanlokaci zuwa yanzu, a cewarta,ta yi finafinai sama da 30. Yaaka yi a cikin shekara biyu tayi har 32? Wannan tambayar,mun yi wa Ladi ita. A cewarta,ta ha]a ne har da wa]anda tafito a cikinsu ba a matsayinjaruma ba. Su ko wa]anda tafito a matsayin jaruma acikinsu, guda hu]u ne: MutuKa Raba da Kash! (sai dai baifito ba), sai Arziki Da TashinHankali da kuma wani wandaba a kammala shi ba a lokacintattaunawarta da mujallar Fim

Ni dai sunana Ladi Mutu-Ka-Raba. An haife ni a Zangocikin birnin Kano a gidan Alhaji Hassan Na Jami wandayake kaka a gare ni. Ina ganin a yanzu zan kai shekara 25da haihuwa. A nan na girma. Makaranta kuwa na yi, alokacin ina Gya]i-Gya]i na fara firamare. Daga nan saimuka tafi Saudiyya ni da kakata. A can na girma kafin

Duk da yake tana daga ciki’yan wasa mata wa]andataurarinsu ke haske a yanzucikin wannan harka, Ladi bata yin gasa da kowa. Kowanata ne, inji ta. “A gaskiyamatan da ke wannan industry]in gaba ]aya ba wadda ba taburge ni, kuma duk’yan’uwana ne. Tsakani daAllah ba zan ce wannan ta fiwannan ba. In kuwa na fa]ihaka, na yi buturci, dondukkansu nawa ne,” inji ta acikin dabara da siyasa.Ya aka yi take son kowa da

kowa haka?Ladi: “Yes, ni haka nake; duk

wanda zai yi mani dariya, tonawa ne. Kuma a cikinsu nibabu wadda ta ta~a nuna manicanjin fuska.”To a cikin ’yan wasa maza fa,

ko Mutu Ka Raba tana da wanigwanin da ya fi burge ta? Anan ma sai ta wayance, taamsa: “A mazan ma ba zan ceyau ga gwanina ba. Dukkansuabokan aikina ne, ’yan’uwanane kuma zan ce ba ni dasaurayi a cikinsu. A cikinsu bawanda ya ta~a canza manifuska a gaban idona, sai dai koa bayan idona wannan ban sani

wajen }arshen shekarar 2000.A cikin finafinan da ta yi duka, Ladi ta ce babu wanda take so

kamar Mutu Ka Raba, “don dalilin shi ya zama mani suna ‘MutuKa Raba.’”Ladi ta bayyana ra’ayi a kan }orafin nan da ’yan wasa kan yi

kan cewa furodusoshi ba sa biyansu ha}}o}insu yadda yakamata. Ta ce: “A gaskiya ni ban ta~a yin wani fim da furodusaya ri}e mani ku]ina ba. Kuma kan ha}}in abin da ake biyan’yan wasa, wani wasan za ka sha wahala ka samu ku]i ka]an,wani kuwa ba za ka sha wahala ba amma ka samu ku]i maiyawa.”

71

Page 73: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

ba. Don haka kowane dagacikinsu ina wasa da dariya dashi kuma ina son su.”Jarumar ta }aryata maganar

nan da wasu ke yi cewa wainamiji ba zai ba mace matsayinjaruma a fim ]insa ba sai idanmasoyiyarsa ce ko akwai watahul]a a tsakaninsu. “{aryane,” inji Ladi a fusace, ta }arada cewa, “kodayake kowa agaskiya kansa ya sani. Donhaka kaina na sani. Ni ba wanifurodusa da ya ta~a zuwa yace ni yau Ladi zan sa ki a fimamma zan neme ki. In ma sunayi wa]ansu, Allah Shi nemasani; kaina ka]ai na sani.Wallahi ni ba wanda ya ta~ace da ni Ladi zan saki a fimamma zan yi kaza da ke. In nafa]i haka ha}i}a na }onanamana saboda na ]aukialhaki.”To shin wai ko ita kanta tana

da saurayi cikin masu harkarfim? Ladi ta yi irin dariyar nantata, ta amsa, “Ai na ce ba nida shi.” E, duk da kyaunta ]innan. “Ai akwai wa]anda sukafi ni kyau.”Maganar aure kuma, cewa

Ladi ta yi, “Ni ko yanzu AllahYa ba ni miji zan yi aure donduniyar nan ni ba a gabanatake ba. Ba abin da ya shigagabana irin gidan miji. Aurezan yi.”To, masu so sai su taya. Amma

fa kada ka ]auka Mutu-Ka-Raba ba ta ta~a yin aure ba.Ta ta~a yi. Da wakilinmu yatambaye ta ko shekararta nawaa gidan miji, sai ya ga fuskartata sauya. Ga alama, ba ta sonzancen. Cewa ma ta yi a cikindamuwa, “Wannan bai taso ba.Kar ka tambaye ni shekaratanawa a gidan miji! Wannan baitaso ba!”Wakilin Fim sarkin bin

diddi}i ne. Don haka duk dagarga]insa da ’yar wasan ta yi,sai da ya bi ta da maganar, yace mata, “Ladi, matsayinki yawuce inda kike zato, kumatunda kika fito da kanki babuwata rayuwarki da ya kamataki ri}a wani ~oye-~oye akanta. Gara ma ki fayyacekomai da a je ana ji-ta-ji-ta akanki.”Ga alama, Ladi ba ta son a

ri}a yin ji-ta-ji-tar a kanta. Donhaka ko da ta nisa sai ta amsa:

]aya: Allah Ya ban mijin aurekuma mu rabu da kowa lafiyakuma a ’yan’uwana masu yinfim maza da mata, wanda baida aure Allah Ya ba shi.” Ta cetana so masu zargin cewa waisaboda ku]in da ’yan wasamata suke samu da kumasakewar da suke da ita na su jeinda suka ga dama su sai abinda suka ga dama shi ne yakehana su yin aure, su daina. Daaka yi mata zancen zargin ma,sai ta tafa hannu ta ce,“Wayyo! na ]aka bai yi kallonna waje ba. A gaskiya da akecewa a ba mu ku]i mu ]aurawannan mu sanya wannanduk ba don da]i ba, sabodakada mutum ya zauna haka ne.Duk da zaginmu da ake yi mumata cikin wannan sana’amuna yinta saboda kada muzauna haka. Na yi imani acikinmu duk wadda ta samumiji za ta yi aure.”

A kan batun Shari’a, Ladi tace tana maraba da ita. Hujjartaita ce, “Shiga ce ta Musulunciduk muna yi; abin da aka hanaduk mun kiyaye, kuma da macan ba ma yi. Yadda mukegaban iyayenmu bai kamata ace muna wa]ansu abubuwaba. Ita wannan Shari’a da ta zoba yadda za ta yi da mu. Ya zaa yi? Allah bai ba mu mijinaure ba, dole mu ha}ura.”

Ba ta da nadamar shigartasana’ar fim ko ka]an, inji ta.“Ba zan ce kaico ba tunda Al-

Ladi tare da su Asiya Muhammad

KOLI TRADING COMPANYNo. U.8, Katsina Road by Roundabout, Kaduna

Mu, KOLI TRADING COMPANY, dillalai nena kowane irin finafinai – na Hausa da naKudancin Nijeriya, na }asashen waje dana wasanni kamar }wallon }afa, kokawa

(wato wrestling) – da kuma sababbinkaset-kaset na bidiyo da rediyo, har ma

da na CD.Muna maraba da masu sari da kuma masu

SAI KUN ZO!A tuntu~e mu aBabban ofishinmu da ke:Lamba U8, Katsina Road

ko a Reshenmu da ke:Lamba U4, Katsina

ko kuma ta wayar tarho: 062-241170 ko 062-240228

Sayen nagari, maida ku]i gida!

“Na samuw a j e ns h e k a r ashida ag i d a nmiji.”To ’ya’ya

fa, ko tanada su? “Inada baby] i t a ,U m m u l -Salama,”inji Ladi.K a m a r

k o w a c e’yar wasada ta yisuna, burinMutu-Ka-Raba shine ta yia u r e .“ B u r i n a

lah Ya nufe ni da yin ta. Dukmutumin da ka ga ya shigawani hali ba yin kansa ba ne,Allah Ya }addara mashi.Saboda haka ni wannan sana’aban shige ta da nufin in je inri}a yin aikin banza ba. Shi yasa ba zan ce kaico ba a wannansana’a. Na shiga wannan harka

72

don fa]akar da jama’a maza damata, yara da manya.”A }arshe, mun so mu ji daga

Ladi, a yau a ce baban Salmaya zo ya bu}aci ta koma gidansaa matsayin matarsa, za ta yardata koma ]in?Amsar Ladi Mutu-Ka-Raba ita

ce: “{warai zan koma.”

Page 74: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

M UHAMMAD AUWAL IBNHAMISU FUNTUWA (wandakowa yake kira Auwal Hamisu

Funtuwa) matashin furodusa ne wandayake zaune a garin Funtuwa cikin JiharKatsina. Ya yi finafinai guda hu]u, acikinsu har da Da Wa Zan Kuka? (wandamuka ba ku labarinsa a fim ta 8 (ta Agusta2000), da kuma wani sabo wanda bai fitoba mai suna Halin Rayuwa. Shi neshugaban kantin bidiyo mai suna ‘Al-Karama Ventures’ da ke Funtuwa. Auwalhazi}in ]an kasuwa ne, kuma ]an wasa.Yakan fito a finafinan da ya shirya. Donjin inda Auwal ya sa gaba, wakilinmu yasadu da shi a garin Funtuwa inda sukatattauna kamar haka:

Fim: Bari mu fara da jin dalilin da yasanya ka shiga yin fim na Hausa.

Awwal:(sallama) Tun farko ni maisha’awar kallon finafinai ne na waje, harya zo ga shi a yanzu sun zo gida ana ta yi,sai na ga ya dace ni ma in ba dagudunmawata wajen ya]a wa]annanfinafinai da ake ta yi don bun}asa harshenHausa da kuma addininmu na Musuluncibaki ]aya.

Fim:A wace shekara ka shiga harkar?Awwal: Na fara harkar finafinai a 1997,

bisa wani tayi da aka yi mani na in taimakama wani kulob mai suna ‘Bayajidda’ dasuka fara shirya wani fim mai suna KowaYa Kwana Lafiya. Daga baya sai na ga nima ya kamata in ]auki harkar tawa takaina. Don haka daga baya na yi fim ]inaKura 1&2 a 1998. A 1999 na sake yin wanifim ]in mai suna Da Wa Zan Kuka? Awannan shekarar kuma, 2001 ga fim ]inanan Halin Rayuwa.

Fim: Akwai lokacin da muka samulabarin ka karaya da yin wannan harka tafim a sakamakon fim ]inka, Da Wa ZanKuka? Muna son ka yi mana }arin bayani.

Awwal: A gaskiya ban karaya da shiba, don fim ]in ya shiga wuraren damutum bai ta~a tsammanin zai shiga ba.Har daga Saudiyya, Ghana, Togo, Benin,Nijar an ba ni labarin fim ]in ya kai. Kasan dai ita hidimar rayuwa yadda take, komenene akwai nasarori da matsalolinsa.

Fim: Ya zuwa yanzu finafinai gudanawa ka yi?

Awwal: Yanzu ina da guda hu]u a}asa. Na farko kamar yadda na fa]a akwaiKowa Ya Kwana Lafiya1&2 da kuma DaWa Zan Kuka?, sai wannan sabon HalinRayuwa.

Fim: Shin wannan fim da yake bai fito

Muna tarbiyyantar da mutane ta hanyar fim– Auwal Hamisu Funtuwa

ba ko za ka gaya mana ’yan wasan da kec i k i n s a ?Awwal: Alhamdul-Lillahi, mun yi amfanida }wararrun ma’aikata kamar su BashirMudi Yakasai, Tahir Fagge, da kuma shikan shi daraktan za~ar ’yan wasa (cast-ing director), Ibn Mohammed Salisu Ado.Akwai kuma ’yan wasa kamar su WasilaIsma’il, Ali Nuhu, Hindatu Bashir, UmarYahaya Malumfashi, Hajara Usman,Jamila Haruna da kuma wasu fitattun ’yanwasa.

Fim: Wane labari shi wannan fim ]inyake bayarwa?Awwal: To shi fim ]in Halin Rayuwawani abu ne da kan faru a wasu gidaje.Alal misali, Umar Yahaya a wannan fimyana da ’ya’ya 12, amma kowanne uwarsadaban, wanda haka ya haifar da ba susamu isasshiyar tarbiyya ba da ya sanyashi kansa a }arshe abin ya dame shi, akari}a sako masa ’ya’yansa daga gidanmazajensu kamar yadda shi ma ya ri}a yiwa ’ya’yan mutane. Lokacin da aka sakomasa ’yarsa (Hindatu Bashir) ya ]aukiwani mataki da ya so ya tarwatsa gidanbaki ]aya.

Fim: Wane darasi kake ganin wannanfim zai iya karantar da masu kallo?

Awwal: Alhamdu-Lillahi duk wandaya kalli wannan fim zai samu darussadaban-daban masu yawa. Misali, masuyawan aure-aure za su }aru da wasudarussa na illar hakan. Haka kuma masusakin ’ya’yansu ba tarbiyya su ma akwai

kalla, ko da ba Hausa ba ne kuwa. Kumafinafinan da ake nunawa a satilayet sun fifinafinan namu muni. Kuma fim ]inHausa ba wani muni gare shi ba. Shi fim]in Hausa gyare-gyare ne ya kamata akawo cewa ya kamata a yi kaza a dainakaza, kamar yadda shi ma tarbiyyantar damutane yake yi.

Fim: In aka ci gaba har aka kafa dokarhana sayar da fim a Kano, ya kake ganindokar za ta shafi fim ]inka?

Awwal: Maganar sayar da fim a Kano,wani abu ne da duk wani ]an kasuwa nafim a Arewacin Nijeriya ta shafe shi.Amma mu abin da muka yi imani da shi,Allah (SWT) dukkan rayuwar ]an Adamda arzikinsa a hannunsa suke. Sabodahaka shi Allah in Ya rubuta maka kazababu shakka dole sai kazan nan ya sameka. Ga wa]anda suke yin finafinai ammasu ]auka su je waje su sayar dafinafinansu. Alal misali }asar Indiya sunayin fim ba za su fara sayarwa ba sai a birninLondon.

Fim: Yanzu furodusoshi a nan Funtuwamasu shirya finafinan Hausa ku nawa ne?

Awwal: Mu biyu ne kacal, daga HajiyaBilkisu Salisu Ahmed sai ni da nake rufamata baya.

Fim: To akwai wani shiri a tsakaninkada ita ta yadda za ku bun}asa harkar yinfinafinai a Funtuwa?

Awwal: Idan Allah Ya so ya yarda za agani.

Auwal Hamisu Funtuwa

darasi a kansu. Haka kuma matan daba sa ma mazajensu biyayya akwaiabubuwan da za su koya a wannan fim.Kuma shi wannan fim ya zo da wanisabon salo na nisha]antarwa ta hanyarraye-raye da wa}e-wa}e.

Fim: Me ya bambanta shi dawa]anda ka yi a baya?

Awwal: Akwai bambancin sosai.Ka ga kamar za~ar ’yan wasa yabambanta shi da sauran finafinaina nabaya. Haka kuma suturu ma yabambanta wannan da na baya. Hakakuma ma’aikatan da suka yi aikin dakayayyakin aikin duk sun sha bambanda na baya.

Fim: Wace illa dokar hana yin fim aKano za ta iya jawo wa harkar shiryafim ]in Hausa?

Awwal: Mu dai abin da muka sanizance na gaskiya ba zai yiwu a ce anhana sayar da fim ba. Ba don komaiba, in dai har mutum na da bidiyo todole ne fa ya nemo masa abin da zai

73

Page 75: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

T A T T A U N A W A

74

MANNIRA S. Abdullahi ce muka ba kulabarin aurenta a Fim ta watan jiya, indamuka ce ta yi aure ba zato ba tsammani.To, kamar yadda muka gaya maku, munyi hira da jarumar dab da za ta yi auren,inda ta ce mana lallai za ta yi aure ba dada]ewa ba. Mun ]auka irin barazanar nance ta ’yan wasa mata. To, sai ko Mannira(wadda muka kira Mannira Abdul Ganiyua wancan labarin) ta yi auren. Kamaryadda muka al}awarta maku, ga waccanhirar da muka yi da ita a Kano:

Fim: Ki fara gabatar da kanki ga masukaratu.

Mannira: Sunana Mannira S. Abdullahi.An haife ni a unguwar Ayagi, Kano. Nayi makarantar firamare a Warure, tasakandare kuma a Dala. Na }are a 1999.Kuma a wannan shekarar ce na shigawannan harkar fa]akarwa.

Fim: Akwai masu tsokacin cewa harkarfim tana dakushe zummar makarantar yaramatasa, musamman mata. Kin nuna 1999kika }are makaranta amma ba ki ci gabada zurfafa karatunki ba; a maimakon hakasai kika tsunduma cikin harkar.

Mannira: A gaskiya ni ba harkar fim tahana ni zurfafa karatu ba tunda sha’awace kawai ta sa na tsinci kaina a cikinwannan sana’a.

Fim: To menene ya ba ki sha’awa harkika shiga harkar?

Mannira: Babban abin da ya ba nisha’awa har na shiga wannan harka bayaga irin darasi da fa]akarwar da ’yan wasake yi wa al’umma shi ne domin ni ma inga kaina a cikin kaset, in sanya in kalla,domin a gaskiya iyayena ba su so shigatacikin wannan harka ba. Sai dai daga bayasaboda }aunar da ke tsakanina da su yasa suka }yale ni.

Fim: Ya kika yi kika shawo kansu harsuka zo suna so yanzu?

Mannira: E, to! Kamar yadda na cemaka ne: soyayyar ]a da mahaifi gameda kyakkyawan bayanin da na yi masuna alfanun fa]akarwa ya sanya suka canzara’ayi suka yi mani addu’a da fatan alheria sana’ar.

Fim: Da wane fim kika fara, kumafinafinai nawa kika yi ya zuwa yanzu?

Mannira: A gaskiya na yi finafinai dadama. Domin za su kai takwas ko fi; wasuma ba su riga sun fito ba tukuna. Ka]andaga cikinsu sun ha]a da Taskar Rayuwa,Alhini, Martani da Marainiya 2; sauransun ha]a da Gwi Da Yara inda na yi scene]aya. Na kuma fito a Sa}o da Sakamako.

Fim: Daga cikin wa]annan finafinai dakika lissafa akwai wa]anda kika fito amatsayin tauraruwa?

Mannira: E. Kamar a Alhini ni cejarumar shirin, haka ma a Taskar Rayuwa.

Fim: Wanene ya fi burge ki daga cikinsukuma menene dalili?

Mannira: Duk fim ]in da na yi babuwanda bai burge ni ba. Amma Alhini yafi kwanta mani a zuciya saboda irin alherida taimakon da nake yi a cikinsa.

Fim: Duk rawar da aka ba ki za ki iyatakawa a fim?

Mannira: E to, a gaskiya ba kowace irinrawa zan iya takawa a fim ba. Domin kafinin amshi kowane role sai na duba script]in da storyline sannan zan iya yi.

Fim: Kamar wane iri ne ba za ki iya yiba?

Mannira: A gaskiya ba na son role ]inda zai sa in yi rashin mutunci.

Fim: To ai a matsayinki na ’yar wasankwaikwayo kina fa]akarwa ne. Ba ki

ganin idan za ki taka irin wannan rawarkamar ba fa]akarwar kuke yi ba kenan?

Munnira: E, to, bisa wannan dalilin nafa]akarwa zan iya yi!

Fim: Na san kowace irin sana’a mutumyake yi ba zai rasa fuskantar wasumatsaloli ba. Ke wace irin matsala kikata~a fuskanta wadda ba za ki manta da itaba?

Mannira: A gaskiya ba za a rasa ba,domin zan iya tunawa na ta~a zuwa waniwasa na Sani Uba a garin Daura, JiharKatsina, inda na kamu da rashin lafiyawanda ya sa na ji location ]in da garinsun fita cikin zuciyata. Kai, sanadiyyarwannan al’amari, da ji na yi kamar kofim ma ya fita raina kwata-kwata.

Fim: Shin irin kallon da ake yi wa ’yanwasa mata da ke sana’ar fim na rashinkintsuwa ya ta~a buge maki }waringwiwar yin wannan sana’a?

Munnira: Ana irin wa]annanmaganganu wanda kuma a gaskiya yana~ata mani rai, har ma wata sa’a in ji kamarin daina wannan sana’a. Amma tundawasu fa]a kawai suke yi bisa zargi sabodaba su san wannan sana’a ba suna cewamu ’yan wasa ’yan iska ne, to amma balallai ne a ce duk ’yar wasa ’yar iska ceba, saboda yawancinmu duk daga gidaniyayenmu muke fitowa mu yi wannansana’a.

Fim: Da gaske ke Bayarabiya ce?Munnira: E, ni ’yar }abilar Yarbawa ce.

Amma ba ni ba, ko babana a Kano akahaife shi.

Fim: Menene burinki wannan sana’a?Mannira: Babban burin ’ya mace kamar

ni ba zai wuce aure ba, wanda nake saran yi nan gaba ka]an.

Fim: Wanda za ki aura ]in shi ma ]anwasan kwaikwayo ne?

Mannira: A’a, shi ba ya wasankwaikwayo.

Fim: Bahaushe ne?Mannira: {warai kuwa Bahaushe ne.Fim: Shekararku nawa kuna soyayya

da shi?Mannira: Mun kai kamar kimanin

shekara biyu da shi yanzu muna soyayya.Fim: Ku ’yan wasa kukan yi }orafin

cewa furodusoshi ba su biyanku ha}}inkukamar yadda ya kamata. Haka ne?

Mannira: E, to, nikan ji ana irin wannankoken amma ni gaskiya na gamsu da abinda furodusoshi da na yi ma aiki suka biyani.

Masu zargin ’yan wasa mata suna~ata mani rai – Mannira

Mannira S. Abdullahi

Page 76: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Maryam tare da angonta Akilu Mohammed (Baban Mulika)

Ranar Asabar, 24 gaFabrairu, 2001 rana ceta farin ciki da tarihi a

Bayan shekara 20 sunasoyayya, ’yan wasa biyu– Baban Mulika daMaryam–sun zama amare!

‘Allah Ya amfana!’

Amarya (Maryam):

“Aurena da Baban Mulika ba tahanyar wasa muka }ulla shi ba, Al-lah kawai Ya yi ikonsa wajen ha]a nida A}ilu har ga shi mun yi aure. Agaskiya tun kafin auren nan ni na yibankwana da wasan kwaikwayo.Domin da man sha’awa ta kai ni cikinharkar. Tunda na daina Allah Yaamfana abin da na yi na baya.Shawara ga takwarorina mata masuyin fim wa]anda suka yi aure: donAllah mu daure ha}urin zama damazajenmu. Wa]anda kuma suke dasha’awar yin auren amma ba su samuba Allah Ya ba su mazaje nagari.”

‘Ban makara ba!’

Ango (Baban Mulika) :

“An yi kata-kata a tsawon shekarumasu dama da suka gabata kanyiwuwar aurena, har wasu da sukajahilci al’amarin suka ri}a ganin na

makara da yin aure. To ban makaraba kuma ban yi sauri ba. Amma agaskiya farin cikin da nake da shi kanwannan auren nawa da Maryam, banda bakin da zan iya bayyana shi, saidai ina bayyana godiyata tamusamman ga ]imbin jama’ar dasuka halarci ]aurin auren dabukukuwan da suka biyo bayanaurenmu da Maryam. Allah Ya ha]ani da ita ba ta hanyar wasankwaikwayo ba kuma mun fahimcijuna daidai gwargwado.

“Kiran da zan yi ga amaryar tawashi ne mu }ara fahimtar juna sannanmu gaji iyayenmu wajen ha}uri dahalayen juna. Ita ta gaji mahaifiyarta

r a y u w a rjarumi A}iluMohammed( B a b a n

Mulika). A ranar ceshahararren ]an wasanya yi amarya, wato

Malama MaryamM o h a m m e d ,

al’amarin da yaketa bege da

g w a g w a r m a y a rganin ya tabbata a}allashekaru 20 da suka

gabata zuwa yanzu da AllahYa tabbatar da abin.

[aurin auren, wandaaka yi a Unguwar Kudu,

Unguwar Rimi,Kaduna, ya samu

halartar furodusoshinfinafinan Hausa da na

wasu wasanninkwaikwayo na rediyo

da talbijin da sukaha]a da YakubuLere, Abdullahi

Maikano Usman,Jafaru Adamu, UmarHassan, Saminu

Mohammed Mahmud, daYakubu Idris. Akwai’yan wasa irin su Sani

Idris Mo]a, Nuhu Isah dasauransu tare da ’yan’uwa da

abokan arziki inda akacika gidan ]aurin auren

ma}il don shaidar dawannan auren.Bayan ]aurin auren, a

yammacin ranar an yi walimartaya ma’auran murna aharabar Hukumar Al’adunGargajiya da Fasaha ta JiharKaduna inda aka ci aka sha

tare da garga]i da addu’o’infatan alheri ga ango daamarya wacce ita mata’yar wasa ce da ta ta~afitowa a fim ]in Dare[aya a matsayinshugabar mata.

* Bayan an kammalabikin, wakilinmu yatuntu~i ango da amaryardon jin ta bakinsu kanauren:

da ta yi ha}uri da mahaifinta har akasame ta, ni kuma in gaji ubana daya yi ha}uri da mahaifiyata haraka haife ni. A }arshe zan yiamfani da wannan damawajen bayyana kuskuren dawasu ke yi wajen ]aukarcewa dukkan matan fim bamasu mutunci ba ne ko kumaba sa yin aure, duk da cewa akwai~ata-gari. Ita amaryata Maryam inada tabbacin ba ta a cikinsu.”

75

Page 77: Mujallar FIM

FIM, AFRILU 2001

Ni na kama Hitler!Ba ka gaba

NA }araso cikin birnin Kano, cike da farinciki. Wani ~angaren kuma alhini ke cikeda ni. Ba wani abu ba ne ya sanya mani~acin rai face in na shafa kaina na ji shirabi da rabi da gashi, rabi kuma babu.Haka dai na rarrafo har zuwa gida. Nabu]e ]akina na zaro ku]ina na sake tusasu, na gan ni da N1,500 – domin na kasheN70 a mota. Na sake kaya, kana na yiwanka na fito domin na bai wa natulaha}}insa. Na }arasa wajen [an Ismo MaiShayi. Ganin gara~asa, ni ne har da cewaa fasa mani }wai guda hu]u. Aka soyemin su; ga shayin sai tururi yake yi. Nafara kwasar shayi sai da na ji natula ya yidam-dam sannan na fara ba da labari.

[an Ismo ya dube ni. “Mazari, yaukuma me ya faru na gan ka kan naka rabia aske rabi kuma da gashi?”

Nai zumbur na shafa kaina, na tuna. Nantake na gintse, na karkace. “Na tunolokacin da muka je Ya}in Duniya na 2 ne.”

[an Ismo ya yi dariya. “Mazari manya,me kuma ya faru a wajen ya}in har kaaske kanka rabi da rabi?”

Na yi ’yar dariyar ya}e. “Lallai [anIsmo har yanzu ba ka san ni ba! Ai wato awannan lokacin duk wanda ka gani daaskakken kai rabi, to ba }aramin jarumiba ne. Wato a wannan lokacin, ba namantawa, idan zan kwanta barci bakina abu]e nake barinshi.”

“Ko meye dalili?” [an Ismo yatambaye ni.

Na yi dariya. “Saboda ha]iya. Ai awannan daren duk bom ]in da aka harbobakina yake shigewa, sai dai in safiya tayi in yi gyatsa haya}insa ya fice. To a cikinirin halin ne wani bom guda ]aya ya }ifashewa. To har yanzu bai fashe ba; duklokacin da ya ]an juya min to sai na yiwannan askin kana in yi fareti sannannake samun sa’ida.”

Wani can a gefe ana ce masa Ri}a-ri}iya kalle ni kana ya yi murmushi.

“Ashe Mazari an yi bajinta!”Na kuwa ji da]in yabon da ya yi min.

Na karkace kaina na ci gaba, “Ai wannansam ba komai ba ne a cikin kundinjarumtata. Ai Hitila da kake jin labarinsaTurawa suna }aryar su suka kashe shi;}arya suke yi! Ni ]in nan Mazari ni nakama Hitler da hannuna na sa shi a kuttuna taho da shi nan Lanjeriya. A yanzuyana yi wa Na Iro Mai Kotso amshinwa}a.”

[an Ismo ya kalle ni. Ya ce, “Tabbasko ni na ji wannan labarin a wajen Zubairuna {ofar Mazugal.”

Na dube shi. “Ka ji ba!”Na tashi na koma gefe na fyace majinar

da ke hancina, kana na dawo.Auwalu Gauraka ya dube ni. “Mazari

sai a zagaya kemis ko, don na ga mura naneman ta yi ma mugun kamu.”

Na ~ata rai. “Haba Gauraka! Ai ni inina mura sai dai in sha}a tokar bom. Don

a yanzu haka ma na aika a auno minkwano uku. Ka san a can aunar da ita akeyi saboda irinmu.”

Na tafi na bar wajen. Ban zame ko’inaba sai wani shagon aski, na shiga na zauna,aka gyara min kaina na fito sumul da ni.Na sake ta~a aljihuna na ji shi dam daku]i. Na yi dariya na }ara gaba na nufi]akina, na kwanta.

Gari na wayewa sai na nufi masallacina yi sallar Idi, kana na dawo gida nashiga sa}e-sa}e. Can sai na tuna yau faSallah babu wata harka da ta wuce ta fata.Na fito da ku]ina. Ina zuwa na tarar dawani dattijo tare da wasu samari suna tadoka ciniki, shi kuma dattijon ya }i yasallama. Na tsaya. Ko da na fahimcicinikin fata ake yi, sai na janye tsohon gefeguda muka yi sabon ciniki na biya na kamabuhu na cicci~a, sai gida. Na je na ajiyefata ta kwana biyu saboda ta }ara tsada.Na kasa fahimtar wani abu. A kullumgidana }ara dagulewa yake yi da ]oyi.

Na shigo na ]auki fata na fita da ita. Banzame ko’ina ba sai wajen T.H. Mai Fata.Na je na ajiye buhu. T.H. ya fito. Na bu]ebuhu. Ina bu]ewa }udaje suka ce da waaka ha]a su in ba da wannan fatar ba. Abintakaici, }udajen da suke Ha]eja ma saida suka kawo ziyara.

Na kau da kaina, na fara zaro fata. Dukwadda na ]auko sai ta yanke, gashi yasullu~e saboda ru~a.

T.H. ya kalle ni. “Mazari a yi ha}uri a]ebe ta domin ko angulu ka ajiye mawannan ba ta ci.”

Na tuna da ku]ina. Na zauna na cikuka, kana na tattare fatata na }ara gaba,}udaje suka kuwa yanyame ni, mukakuwa zuba.

Ba wani abu ba ne ya ba ni takaici facein na tuna ku]ina N1,500 da }udaje sukebi a halin yanzu.

Mu ha]u a fitowa ta gaba!

76

A Fim ta watan gobe

Shin ka san yadda ake shirya fim ]in Hausa? Mujallar Fimta lura cewa yawancin ’yan fim suna ~oye yadda suke yin

fim, kada ba}o ya sani!To, abin ~oye ya fito sarari! Domin kuwa mujallar Fim za tayi bayani a kan yadda ake shirya fim fim dalla-dalla, kumakyauta! In ma kana so, za ka iya shirya naka da kanka, idan

har ka bi sharu]]an shirya shi ]in!

A TARBE MU A FITOWARMU TA GABA A SHA LABARI