24
MAGAMA Yuli 2011 1 Sifili Na 17 Lamba ta 2 Rajab / Sha'aban Nijeriya: Bayan Za~e Mujallar Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta

Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

  • Upload
    lylien

  • View
    246

  • Download
    2

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 1

Sifili Na 17 Lamba ta 2

Rajab / Sha'aban

Nijeriya:BayanZa~e

M u j a l l a r O f i s h i n J a k a d a n c i n A m i r k a a N i j e r i y a K y a u t a

Page 2: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 2

’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya Tare Da Jakadan

Amurka, Mista Terence McCulley

A RANAR 19 ga watan Mayu, 2011 ce, Jakadan Amurka a

Nijeriya, Mista Terence McCulley, ya shirya wata liyafa don yin godiya ga ‘ya’yan }ungiyar masu fasahar yin abubuwa ta Nijeriya wato “Society of Nigerian Art (SNA)”, game da abubuwan fasaha da suka nuna a gidansa bayan da ya gode masu game da karamcinsu sai Jakada McCulley ya yi amfani da bikin wajen ciyar da dangantakar al’adu gaba a tsakanin Amurka da Nijeriya ta fasahar da ake iya gani.

A lokacin da aka ambata shi ne wakilin Shugaba Barack Obama da jama’ar Amurka a Tarayyar Nijeriya sai Jakada McCulley ya lura da al’ada ya za~i fasahar yin abubuwa na Amurka daga sashin fasaha a cikin shirin ofishin jakadancin don nuna ta a gidansa

da ke Abuja. Sai dai kuma abin ba}in ciki ba

a sami abubuwan fasahar ba. Jakada McCulley ya bu}aci a yi

taro kan abubuwan fasahar Nijeriya don nuna su a gidansa saboda son da yake yi wa fasahar gani da ido da iliminsa a kan al’adun Nijeriya masu yawa.

Jami’in Ofishin Harkokin Jama’a na Ofishin Jakadancin da shugabannin }ungiyar masu fasahar yin abubuwa ta Nijeriya suka tattaro kayayyakin fasaha daga sassan }asa don nuni na musamman.

Akwai kayayyakin fasaha da sassa}e - sassa}e guda 33 na masu haza}a su 21 da aka nuna. Godiya ta musamman ga shugaban SNA, Mista Uwa Usen da Malam Muhammad Sulaiman na Cibiyar Al’adu ta Abuja game da goyon

bayansu da yadda suka daidaita nune-nunen yadda ya kamata.

‘Ya’yan SNA da dama da suka halarci liyafar sun ha]a da Mista Uwa Usen da Furofesa Jerry Buhari na Sashin Fasahar yin abubuwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Game da muhimmancin bikin, Furofesa Buhari ya yi sharhi kamar haka: “Wata dama da na samu da aka nuna fasahata ta yin abubuwa a gidan Jakadan Amurka. Na tabbata su ma sauran masu yin abubuwan fasaha suna jin yadda na ke ji. A gaskiyar magana, a kullum zan ci gaba da }aunar wannan girmamawar. Ina fatar a ce manyan jami’an gwamnatin Nijeriya da suka ha]a da gwamnoni da ministoci za su ]auki nauyin yin irin wa]annan bukukuwa. Ina farin cikin zuwa don halartar wannan

Daga James Moolom

Fuskantar {alubale

Duba shafi na 19

Page 3: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 3

Sashen Hul]a da Jama’a na Ofishin Jakadancin Amirka, da ke Nijeriya, ne take buga Mujallar

MAGAMA. Adireshinmu shi ne Sashen Hul]a da Jama’a, Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya, Gida Mai Lamba 1075, Titin Harkokin

Jakadanci,Yankin Tsakiyar Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wayar tarho (09) 461-4000,

Wayar Tangaraho 09-461-4305.

OFISHINMU NA LEGAS {aramin Ofishin Jakadancin Amirka, Sashen Hul]a da Jama’a, Lamba 2, Titin Broad Street. Akwatin Gidan Waya, P.O. Box 554, Legas,

Nijeriya. Wayar Tarho, 01-2632577, 2634868, 2633395. Yanar-Gizo, [email protected] ko

a shiga http://Nijeriya.usembassy.gov.

MA’AIKATAN WALLAFA MUJALLAPETER R. CLAUSSEN

(Babban Jami’in Hul]a da Jama’a), JENNIFER TINA D. ONUFA (Jami’ar Hul]a da Jama’a),

DEBORAH MACLEAN (Jami'ar Watsa Labarai), SANI MOHAMMED (Edita)

ISHAKA ALIYU (Mai Ba Da Shawara Game Da Wallafawa)

Abubuwan Da ke CikiAbubuwan Da ke Ciki

Terence McCulleyJakadan Amirka a Nijeriya

Jaw

abin

Jak

ada

Ina taya ‘yan Nijeriya musamman masu yi wa }asa hidima (NYSC) murna, saboda

haza}ar su da himma da kuma sadaukarwa a lokutan za~u~~ukan shugaban }asa da ‘yan majalisu da na gwamnoni da ya gudana a watan Afrilu, 2011. Ina kuma taya shugaban }asa, Goodluck Jonathan murnar nasarar za~e da kuma rantsarwar da aka yi masa na kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu, 2011.

Ya dace ‘yan Nijeriya su zamanto masu alfahari game da rawar da matasan suka taka wajen samun nasarar za~u~~ukan da aka

Gaisuwa Ga Masu Karanta Mujallar Magamagudanar, wanda masu sa ido na gida da kuma na waje suka bayyana da cewa ba a ta~a irin sa a tarihin siyasar Nijeriya ba. Na jinjina wa wa]annan matasa a bisa rawar da suka taka da ta shafi rayuwar su a matsayin su na ‘yan Nijeriya.

Babu shakka jinsin ku sun bauta wa }asar ku da alfahari, sannan gudunmawar da kuka bayar ya nuna za a samu manyan gobe masu kyawun manufa wa }asar su.

A wannan mujallar ta MAGAMA, (kuma ta uku tun da na zo Nijeriya), al}iblarta za ta kasance ne a kan muhimmancin gudanar da mulki a bisa turbar gaskiya da kuma gudanar da dimokura]iyya mai ]orewa da kuma yadda za a samu nasarar tattalin arzi}in }asa. A daidai lokacin da }asarmu Amurka ke shagalin murnar samun ‘yancin kai, ranar 4 ga watan Yuli, an tunatar mini da cewar, dimokura]iyya na bu}atar aiki tu}uru. Tun da an kammala ya}in neman za~e har ma an gudanar da za~u~~uka, yanzu an ]aura ]amarar gudanar da aiki tu}uru ]in. Yanzu lokaci ne da shugabanni da ‘yan Nijeriya za su rungumi juna don gina }asar su.

Har ila yau, }unshe a wannan mujalla ta Magama, shi ne wani sabon dandali na yara da za a ri}a nunawa a talabijin, mai suna "Sesame Square", wadda gwamnatin Amurka tare da mutanenta suka ]auki nauyin gudanarwa domin ilimantar da yaran Nijeriya.

Ana gudanar da shirin ne kamar yadda aka gudanar da irin wannan shiri a Amurka, shi ma mai suna "Sesame Street." Wannan muhimmin shiri da aka }ir}iro na Nijeriya, ya gabatar da ‘yan wasa kamar su Elmo da Grover wa]anda makwafin su a nan Nijeriya su ne Kami da Zobi. Ni dai na ji da]in saduwa da su, ina fatar kai ma za ka ji da]in saduwa da su.

Akwai kuma rahoton bincike kan }ididdiga na ~angaren ilimi a Nijeriya wadda gwamnatin Amurka tare da hukumar taimako ta ci gaban }asa da }asa ta Amurka suka ]auki nauyi.

Daga }arshe kuma, a matsayina na ba}o a Afirka ta Yamma, kuma Jakadan Nijeriya, na gamsu da ayyukan fasaha na Nijeriya. A da babu hoton komai a bangon gidana, amma yanzu }ungiyar Fasaha ta Nijeriya ta bani gudunmawar ayyukan fasaha da dama wanda na li}a a bangon gidana.

Babu shakka an karrama ni da wa]annan hotuna na fasaha don sun }ayatar mini da gida na. Yanzu ina jiran ayyukan fasaha daga Amurka wato, "Arts in the Embassy" (Fasaha daga ofishin Jakadanci). Duk labaran da ke wannan mujalla ta musamman ce, ina fatar za su gamsar da kai!

Terence P. McCulley, Jakadan Amurka A Nijeriya.

Fuskantar {alubale .................................................................................2

Bayanan {ididdiga Kan Ilimi Don [aukar Mataki................................................................................4

Mazauna Tsaunukan Jos Sun Fara Darawa.......................................6

Bayan Za~u~~uka...................................................................................8

Harkar Kasuwanci Na Bu}atar Shugabanci Mai Kyau Don Ta Ha~aka ...........................................................................13

Tabbatar Da Tsaro A Kan Iyakar Nijeriya........................................16

{ara Fahimtar Juna Tsakanin Mabiya Addinai...............................17

An Samar Da Sabon Dandalin Yara A Nijeriya Mai Suna “Dandalin Sesame”.............................................23

Page 4: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

Taimakon da Hukumar Raya {asashe ta Amurka (USAID)

da sashen Raya }asashe na Ingila (DFID) suka ba Nijeriya ya sanya Nijeriya a yanzu tana da amintattun bayanan }ididdiga kan ilimi wa]anda za a iya dogara da su wajen ]aukar mataki. Tsohuwar Ministar Ilimi, Furofesa Ru}ayyatu Rufa’i, ce ta fa]i haka a wajen }addamar da rahoton shekara - shekara na Safiyon Bayanan {ididdigar Ilimin Nijeriya (NEDS) ta 2010 a Abuja, ranar 16 ga watan Mayu.

NEDS - Safiyo ne da ya shafi kowa a game da bu}atar makaranta

da tabbatar da bayanan }ididdiga a kan ]aukar yara a makarantu da ke cikin }idayar jama’ar }asa da kwatanta bayanan }ididdiga kan ilimi a tsakanin jihohi. Misali, kaiwa ga samun ilimi da ingancinsa. Hukumar yawan jama’a ta }asa (NPC) ce ta aiwatar da NEDS tare da ha]in gwiwar ma’aikatar ilimi ta Tarayya da Hukumar Ilimi bai-]aya (UBEC). An gudanar da safiyon ne a 1990 da na 2008 da taimakon USAID da (DFID) kuma da samun taimakon fasaha daga Cibiyar "Research Triangle Institute (RTI)".

Jakadan Amurka a Nijeriya, Mista Terence P. McCulley, ya sadu da mataimakin shugaban

}asa na Tarayyar Nijeriya, Akitek Namadi Sambo, a wajen }addamar da rahoton Safiyon Bayanan {ididdigar Ilimin Nijeriya (NEDS) ta 2010 da Rahoton Bayanan {ididdigar Ilimi a Abuja.

Ana sa ran cewa, ta safiyon, za a cike gi~in da ke tsakanin manufofi da ingancin ilimin da aka bayar da tabbatattu kuma ingantattun bayanan }ididdiga wa]anda suka wajaba don tsara dabarar bi kan ilimi da aiwatar da shi.

Wannan zai taimaka wa gwamnatin Nijeriya wajen kaiwa ga samun ilimi don kowa da kowa da shirin ciyar da }asa gaba.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da NEDS ya gano: 1. Duk da dai an sami }aruwar

zuwa makarantar firamare ta ba yabo ba fallasa daga 1990

Bayanan {ididdiga Kan Ilimi Don [aukar Mataki

Jakadan Amurka a Nijeriya, Mista Terence McCulley

(na biyu a dama) yake amsar rahoton daga hannun

Mataimakin Shugaban }asa, Akitek Namadi Sambo, a wajen

}addamar da NEDS a ofishin Jakadancin Amurka a Abuja.

Daga Idika U. Onyukuwa

MAGAMA Yuli 2011 4

Page 5: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 5

zuwa 2003 amma tun daga lokacin zuwa makarantar yana nan yadda yake.

2. Kashi daga cikin ]ari na yara masu shekaru 6 zuwa 11 da ke zuwa makarantar firamare ya }aru zuwa kashi 51 daga cikin ]ari (51%) daga 1990 zuwa 2003 kuma zuwan ya }aru zuwa kashi 61 har zuwa 2008.

3. Akwai yiwuwar yara masu shekaru 6 zuwa 11 a yankunan birane su halarci makarantar firamare fiye da yaran da ke yankunan karkara.

4. Barin makarantar firamare ba a }are ba, ba muhimmiyar matsala ce a Nijeriya ba. Yawan masu barin ya ci gaba da zama }an}ani a 2003 zuwa 2008. Masu barin makarantar firamare suna da yawa amma an sami raguwarsu a 2010, musamman a sakamakon ~ullo da ilimin bai-]aya (UBE) wanda ya bayar da damar kaiwa zuwa ajin }arshe.

5. Kashi daga cikin ]ari na matasa masu shekaru 12 zuwa 17 da ke zuwa makarantar sakandare ya }aru daga kashi 24 zuwa kashi 44 daga 1990 zuwa 2008.

6. An cike gi~in da ke akwai a tsakanin matasa maza da mata ya zuwa 2008. A yanzu akwai daidaiton matasa maza da mata da ke zuwa makarantar sakandare.

7. Akwai yiwuwar matasa masu shekaru 12 zuwa 17

a yankunan birane su tafi makarantar sakandare fiye da na yankunan karkara a dukkan shekarun.

8. Duk da }aruwar zuwa makarantar sakandare da ake samu, sai ga shi a Arewa maso Yamma, ana da kashi 24, kuma a Arewa maso Gabas ana da kashi 22. Wa]annan yankuna suna da }an}antar masu zuwa makaranta idan aka kwatanta su da saura (NAR). Kudu maso gabas suna da kashi 59 kuma Kudu maso Kudu suna da kashi 58. Sun sami }aruwar maki 10 da 6 a sakandare (NAR) kuma suna kusa da cimma shiyyar Kudu maso Yamma mai kashi 65 (NAR).

9. Game da ilimin manya, ana samun }aruwar masu ilimi a tsakanin maza da mata masu shekaru 20 zuwa 24.

10. Ilimin mata masu }ananan

shekaru yana }aruwa a tsakanin 1990 zuwa 2008. Kashi 61 daga cikin ]ari na mata a 2008 suna iya yin karatun Boko idan aka kwatanta da kashi 49 a 1990.

Ku]a]en Da Ake Kashe Wa Karatun Firamare Na Yaro

Haka kuma NEDS a 2010 ya tara bayanai a kan yawan ku]in da magidanta suka kashe a kan karatun kowane yaron makaranta a shekarar karatu ta 2009 zuwa 2010.

A jihar Legas, ana kashe Naira 28,185 a karatun yaro ]aya a yayin da ake kashe Naira 23,277 a jihar Ribas. Kowace daga cikinsu ta nunka adadin da ake samu na Naira 7691 sau uku. Yankin Abuja (FTC) na bi masu da kashe Naira 18,004. Jihohin Zamfara da Jigawa suna kashe ku]i mafi }an}anta a kan karatun yaro.

A Zamfara, ana kashe Naira 1,220 a yayin da a Jigawa ake kashe Naira 1,387 a kan karatun

Duba shafi na 20

Renon manyan Nijeriya na gobe

Page 6: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 6

}ar}ashin hukumar yawan jama’a da ‘yan gudun hijira da masu

Jin ana da abin yi, yana }ara }aruwa a wani }aramin }auye

da ke }asar tsaunukan Jos. Godiya ga ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a Abuja wato Karen Mehring da Ann Flynn wa]anda suka raba wa magidanta 63 buhunan iri da kayan noma don taimakawa wajen gyara gonakinsu.

An yi wa manoma ta’adin gaske a }auyen Ratsat, kamar yadda aka yi a wurare da dama a yankin a sanadiyyar ta’annatin }abilanci da na addini, da aka fuskanta a jihohin Filato da Bauci daga Janairu zuwa

Daga Karen Mehring

Ma’aikatan ofishin Jakadanci Ann Flynn da Karen Mehring (a tsakiya) suna tare da jami’an }ungiyar Red Cross ta Nijeriya don raba wa manoma iri da magungunan }wari a Jos. Hoton ofishin jakadanci wanda Daniel Mehring ya ]auka.

Mazauna Tsaunukan Jos Sun Fara Darawa Mayun 2010. Rikicin a wannan yanki ya ci sama da rayuka 700 da lalata gidaje da shuke-shuke da sito-sito na iri da kayan noma da musulumin da ke zaune a gidaje. Gwamnati ta tura sojoji don su dawo da bin doka da oda a yayin da ofishin jakadancin Amurka shi ma ya taimaka.

Jami’ar kiyaye ha}}in ]an-Adam ta ofishin jakadancin Amurka, Ann Flynn, ta rubuta wasi}ar neman taimakon dala 25,000 daga Gidauniyar Julia Tafi a Yunin 2010. An yi amfani da ku]in ta ba ‘yan gudun hijira taimako a cikin sauri da kariya a

Wata mata cikin farinciki ta ]auki

taimakon irin shuka da kayayyakin

noma da maganin }wari da aka ba ta, za ta gida. Hoton

Ofishin Jakadanci da Daniel Mehring

ya ]auka.

Page 7: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 7

Mazauna Tsaunukan Jos Sun Fara Darawa

}aura ta Amurka. An bayar da ku]in ga hukumar agaji ta Nijeriya (Red Cross (NRC).

An taimaka wa magidanta 100 a }auyukan Ratsat na Kiristoci da Lere na Musulmi don su sake gyara gonakinsu. An ba kowane magidanci iri na masara da na dawa da na gya]a da na waken soya da sababbin kayayyakin noma. Ma}asudin yin haka shi ne su sami isasshen amfanin gona don amfanin kawunansu da sayar da rarar da ba su bu}ata.

A lokacin da wakilin }ungiyar suka isa a ranar Talata, 24 ga watan Mayu, to, jami’an NRC sun shirya iri da kayayyakin noma don raba su.

Ann da Karen suna wurin don taimakawa a raba kayayyakin da gode wa jami’an NRC da Dattawan al’umma kuma da saduwa da wa]anda suka amfana.

Ann Flynn ta fa]i cewa, “A madadin Jama’ar Amurka, muna farin cikin mu goya baya da taimaka wa jama’ar Nijeriya.” An ba kowane magidanci taimako kuma sun yi amfani da baro da babura wajen kai abubuwan da aka ba su gidajensu. A yanzu suna bu}atar ruwan sama don shuke-shukensu su tsiro!

Daga nan sai wakilan }ungiyar suka bar yankin don ziyartar wanda aka ba shi taimakon kai-da-kai na musamman na Jakadan Amurka (SSH) na 2010 a kudancin Jos. An kafa makaranta ta Open Doors For Special Learners a 2005 kuma an gina gini na farko da taimakon kyautar SSH.

Makarantar a yau tana da sababbin gine-gine guda uku wa]anda aka gina su da gudunmuwowi daga cikin gida da taimakon gidauniya.

An mayar da gini na ainihi ]akunan koyon sana’o’i da gyara jiki. Taimakon 2010 da aka samu don yi wa sababbin gine-

“Irin shuka da kayayyakin noma da magungunan kashe }wari wa]anda za a raba wa manoma su. Hoton Ofishin Jakadaci da Daniel Mehring ya ]auka.

Wata mata mai goye da ]anta tana tunanin yadda za ta kai nata kason irin shuka da kayayyakin noma da magungunan }wari zuwa gida. Hoton Ofishin Jakadanci ya sa Daniel Mehring ya ]auka.

Page 8: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 8

A cikin sahihiyar ingantacciyar dimo}ura]iyya, za~u~~uka

su ne tushen farko na samar da ingantacciyar gwamnati da za ta kare ha}}in marasa rinjaye, a kuma tabbatar da yin jawabai na gaskiya da zai bayar da damar bin doka da }a’ida ya kuma bayar da damar samun }ungiyoyi masu zaman kansu.

An kuma tabbatar da cewa za~e shi ne sahihin samun jigon gwamnati.

Ta hanyar barin jama’a su za~i wanda zai yi masu kyakkyawan shugabanci, don haka za~e shi ne ainihin tushen farko na samar da sahihiyar dimokura]iyya tare da aiwatar da ita. Samun ingantacciyar dimokura]iyya, tana bu}atar muhimman abubuwa da dama.

Bugu da }ari a kan za~e, dimokura]iyya na bu}atar

kundin tsarin mulki musamman wajen tafiyar da gwamnati.

Samar da cikakken ‘yanci, rungumar harkokin addini ko kuma tsirarun }abilu a kare masu dama da ‘yancinsu musamman wajen samun kyakkyawan shugabanci da sauran abubuwa.

Domin gina ingantacciyar dimokura]iyya, dole ne jama’a su samu yanayin tafiyar da lamurransu a dimokura]iyyance ta fuskar al’ada da kuma bin doka

da oda da zai samar da wani yanayi tsakanin za~u~~uka da kuma masu yun}urin kawo wa tsarin za~en cikas.

A matsayinta ta sakatariyar Amurka, Hilary Clinton, jawabin da ta gabatar a jami’ar Georgetown “Dimokura]iyya ba wai tana nufin za~e ba ne kawai, domin za~en shugabanni, a’a har ma ta ha]a da samun ‘yancin jama’a da kuma ‘yancin aikin jarida da samar da ~angaren shari’a mai cin gashin kansa, gaskiya da samar da ingantattun cibiyoyi da kuma kare ‘yancin jama’a ba tare da nuna wani bambanci ba.

A tsarin dimokura]iyya, girmama ‘yanci, shi ne za~in shugaba a ko da yaushe domin shi ne ainihin dalilin yin shugabancin.”

(Washington D.C. ranar 1 ga watan Disamba, 2009).

Bayan Za~u~~uka BABBAN LABARI

An samo wannan ne daga cikin wata mu}alar da aka rubuta a cikin “Washington File” da Eric Bjornhund Clauya, kuma masani {wararre wanda ya samar da }ungiyar }asa a kan lamurran dimokura]iyya da aka }ir}ira domin tabbatar da samar da sahihiyar dimokura]iyya da samar da kyakkyawan shugabanci. Da Alexandra Abboud, wani marubuci a Washington File, kuma wannan mu}ala an buga ta ne tsakanin ha]in gwiwar “Washington File” da ofishin dimokura]iya na }asar Amurka a ta}aice duk suna }ar}ashin cibiyar samar da bayanai ta }asa da }asa ta Amurka.

A dimokradiyya ba kawai jamaa na da yanci bane, suna da hakkin a dama da su a siyasa, yin haka zai kare musu yancin su walwala. Sani Mohammed ya dauko hoton.

Page 9: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 9

Samar da canjin gwamnati bayan za~e, wani abu ne muhimmi. A tsarin samar da ingantacciya kuma lafiyayyar dimokura]iyya, wanda ya fa]i a za~e zai mi}a wa wanda ya samu nasara cikin kwanciyar hankali da ha]in yin hakan, wanda aka kayar zai ci gaba da zama tare da tarin gudunmawarsa da }arfinsa, musamman tsarin }asa da halayen dimokura]iyya da kuma al’adun jama’a.

Haka kuma in ana son samar da tsarin girmamawa ga abokan siyasa, wanda ya samu nasara yana taimakawa a gina tsarin bambance-

kanta duk suna }o}arin kare doka ne da za’a iya gani }uru-}uru da ya yi daidai da samun cikakken ha]in kai da ke tafiya daidai da kare ha}}in bil’Adama, manufarsu da kuma yanayinsa baki ]aya.”

Tsarin kiyaye doka da oda ya ha]a da halaliya, tsayawa kan gaskiya, yin komai kan gaskiya da tantance bayanai. Samar da abubuwa na halal na bu}atar doka ta samar da sassauci da za a yi amfani da su domin samun tattaunawa bisa tsarin dimokura]iyya.

Samar da tsarin yi wa kowa adalci ya ha]ar da samun daidaiton

bambancen da ta}aita samun sar}a}iya tsakanin jama’a da zai kawo wa dimokura]iyya ci gaba.

Kiyaye Doka Da Oda Dimokura]iyya tana da

bu}atar girmamawa, musamman kiyaye doka da oda da yake bu}atar samun inganci ba tare da nuna damuwa a kan abin da zai fito daga za~e ba. Cibiyar tsaro ta }asashen duniya ta bayyana wannan kiyaye doka da oda da cewa “yayin da dukkan mutane, cibiyoyi da sauransu da suka ha]ar da na gwamnati da masu zaman kansu, da ya ha]a da jiha da

yin amfani da doka bin diddigin tsarin adalci, kiyaye al’amuran kowa har da masu zaman kansu da samun ingantattun ayyukan shari’a. Kuma hakan ya ha]ar da samun }arfafa dokoki.

Samar da doka da za ta kare ‘yan }asa na taimaka wa ‘yan }asa wajen kafar tushen dimokura]iyya. Saboda irin wa]annan dokoki a tsarin sahihiyar dimokura]iyya na samar da ‘yancin jama’a, biyayya da samun kar~uwa ga jama’a na }in amincewa da sakamakon za~e. A duk }asar da ake bin dokoki tsakani da Allah, kuma ake samun }arancin tashe-tashen hankula, ana

“Wannan wani lokaci ne na shugabannin Nijeriya tare da

mutanensu su ha]u wuri ]aya domin gina gobe, domin sun cancanci yin tsarin dimokura]iyya mai jam’iyyu da yawa da zai biya bu}atar dukkan ‘yan Nijeriya baki ]aya, musamman

matasanta da suka yi aiki tu}uru domin ganin an samu nasdara a za~en da ya gabata, wanda kuma shi ne abin da

yake yin bayanin yadda Nijeriya za ta kasance.

A matsayin }asar da ta fi kowace }asa yawan jama’a a Afirka, Nijeriya za ta iya nuna ainihin abin da yake shi ne

zai iya yiwuwa, lokacin da mutane daga jam’iyyu da dama, }abilu da dama daga tushensu daban-daban za su iya zuwa

tare domin ganin daban za su iya zuwa tare domin ganin ]orewar zamani lafiya da za su samar saboda iyalinsu kuma su samar wa iyalansu makoma ta gari. A yau, Nijeriya na da wata damar samun tarihi da za su iya matsawa gaba domin

mayar da }asarsu wata }asa mai ci gaba a Afirka. Kamar yadda

na gaya wa shugaban }asar Nijeriya Jonathan, yana da kyau mu }ara

}arfafa dangantakarmu ta yadda za a samu damar wannan jama’ar da kuma masu zuwa nan gaba su zauna cikin

kwanciyar hankali da lumana, a samu ]orewar dimokura]iyya.” (Shugaba

Obama, a ranar 4 ga watan Mayu, 2011).

Mutanen gari na kwalfen man fetir daga wani kuddufi mara tsafta a garin Fatakwal Nijeriya inda ake yawan samun malalar mai dauke da guba.

Amurka da Nijeriya sun fuskanci sabunta makamashi.

MAGAMA Yuli 2011 9

Page 10: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 10

samun daidaituwar al’amura. Amma samun bambance-

bambance tare da matrsalar take doka, na kawo take ha}}in jama’a. In an samu wadatattun dokoki, jama’a na iya }in girmama doka a wani lokaci, ana iya samun tunzurin jama’a da zai yi jagorancin rashin amincewa da duk wani sakamakon za~en da zai fito.

Wannan shi ya sa shugaban }asar Amurka Dwight D. Eisenhower, ya bayyana, cewa yadda za a iya nuna abin da yake a cikin kundin bin dokoki, shi ne yana nufin yin amfani da shi a kowane lokaci domin a tuna, “shin me ya faru ko zai faru idan ba tsarin bin doka da oda?

Tsarin bin doka da oda ya ha]a da girmama ‘yancin jama’a da bin duk wata }a’idar da ta dace a samu kafin fitowar sakamakon za~e.

A dimokura]iyya, dawowar za~u~~uka ba zai shafi kare ‘yancin fa]in albarkacin baki ba ko kuma yin magana, ko ‘yancin manema labarai ko kuma ‘yancin ~angaren shari’a.

Sababbin shugabanni ba tare da yin la’akari da yadda suka zo kan

A wani tsarin ha]in gwiwa, na }asar Amurka da Nijeriya

hukumar samar da makamashi da sanya jari sun yi wani taro.

Charles W. Corey, wani marubuci a mujallar Washington File ya rubuta wannan }asidar.

A ci gaba da batun samar da ingantaccen sahihin makamashi a Nijeriya, wani nazari ne da aka yi tun daga farko a wajen taron ha]in gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka kan batun samar da makamashi da kuma zuba jari wanda aka yi a ofishin Amurka a ranar 10, ga watan Yuni 2010.

{asar Amurka da Nijeriya sun sanya wa takardar bayan taro hannu, kuma }asar Amurka ta yi al}awarin cewa za ta yi dukkan mai yiwuwa ta taimaka wa Nijeriya domin a samu ‘yancin da kowa ke bu}ata kan batun makamashi, wanda hakan shi ne ainihin mabu]i a kan batun tattalin arzi}i da ci gaba da aka da]e ana }o}arin samu.

A wajen taron na ranar 10 ga watan Yuni, a }arshen jawabai da aka yi, wanda ya samu halarta daga

}asar Amurka wanda yake kula da batun makamashi na }asa da }asa David Lo Goldwyn da kuma babban sakatare na ma’aikatar man fetur ta Nijeriya, Elizabeth B.P. Emuren, sun sanya wa takardar bayan taro hannu, ta yadda za a }ara ]aukaka batun harkar makamashi a Nijeriya.

Goldwyn ya shaida wa

mahalarta taron, cewa taron farko na ha]in gwiwar da aka yi, cewa Amurka da Nijeriya suna tare a duk wata harka ta ci gaba, da suka ha]a da tireda, samar da tsaro na shiyya, batun makamashi, samar da hasken wutar lantarki domin ci gaba ne a harkar tattalin arzi}i na Nijeriya.

A tsawon kwanaki biyu, Goldwyn, ya ce taron na ~angarorin biyu ya mayar da hankali ne kan batun samar da hasken lantarki, iskar Gas da makamashi a wadace da wa]ansu muhimman wurare da suka ha]ar da samar da hasken wutar lantarki da kuma rarraba ta da samar da iskar Gas.

Taron ya kuma tattauna kan yadda za a samar da canji a }asa baki ]aya musamman kan batun wutar lantarki “Muna son wannan al’amari ya tabbata domin }ara hasken wutar lantarki a samar da shi a hanyar da ta dace.”

Hanyoyin samun wannan canji su ne kamar haka, ya ce sun ha]a da “bayanin yadda farashi zai kasance a kasuwa, yadda za’a sanya batun biyan ku]i, da kuma yadda za’a duba lamarin tafiyar da komai.” Wannan zai ba masu zuba jari su samu damar zuba jarinsu.

Goldwyn, ya ce }asar Amurka a shirye take ta yi aiki domin }asar Nijeriya ta samu cikakkiyar damar cin moriyar wannan abu...(ranar da aka sa), hanyar ci gaba (da kuma) yadda za’a samu wannan canje-canjen da kuma jaddawalin yadda abin zai kasance.

Hadin gwiwar }asar

Amurka Da Nijeriya Kan Harkokin Dimokura]iyya Da Kuma Samar Da

Kyakkyawan Shugabanci

Duba shafi na 21

Page 11: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 11

Dimokradiyya ta kafu ne a kan turbar mulkin masu rinjaye da 'yancin mutum.Hoton ofishin jakadanci wanda Sani Mohammed ya ]auka.

shugabancin ba, za su iya ko dai su kira wa]annan abubuwa a cikin tambayoyi ba tare da yin barazana ga duk wani ]an }asa ba, da ya ha]ar da wa]anda suka goyi bayan ]an takarar da ya fa]i.

Sakamakon haka, girmama tanadin doka zai }ara kuzarin mi}a mulki daga wannan zuwa wata za~a~~iyar gwamnati. Wanda ya fa]i kuma ya }i amincewa ya kar~i sakamakon za~e, zai iya samun kansa tare da rashin samun goyon baya, ‘yan }asa za su iya kallon abin a matsayin wani abu daban, mafi sau}i a matsayin wanda ba ya son girmama doka,

kuma mai yin barazana ga al’adunsu. Kuma ‘yan }asa za su iya goyon bayan tashe-tashen hankula ko kuma su goyi bayan ]an takara wanda ya }i amincewa da sakamakon za~e a wata }asa inda ake bin doka tare da kiyaye ha}}in jama’a.

A }asar Amurka, kotun shari’a mai zaman kanta tare da kotun ]aukaka }ara ta }asar a matsayin wata hukumar da ta fi kowace hukuma su ke da damar tabbatar da ganin gwamnati ta girmama tsarin doka da oda, domin an yi halitta da matsayin jama’a duk ]aya ne musamman a }ar}ashin doka.

Al}alin kotun ]aukaka }ara ta }asar Amurka, Anthony Kennedy, a wajen taron }ungiyar lauyoyi ta }asar Amurka., a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2005 a wajen taron, mai taken taron }asa da }asa kan kare doka da oda, ya bayyana abin da ya yi imani da shi da cewa su ne

"A duk inda za ta kasance gwamnatin

jama’a, wadda jama’ar suka samar, }a'idar

amana iri ]aya ce, a kan duk wanda ya kasance

kan madafun iko."

Page 12: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 12

abubuwa guda uku na kiyaye doka da oda.

Gwamnati ita ce da ta tsaya •kan doka Duk jama’a ]aya suke ba wani •bambanci. Nijeriya da }asar Amurka

suna }o}arin sabunta samar da makamashi.

Yadda ake ]ibar mai ta hanyar da ba ta dace ba a shekarar 2006 daga gur~atatten kududdufai a Oshie kusa da Fatakwal, a Nijeriya inda guta mai ]auke da mai suka zama tamkar ruwan dare.

A }ar}ashin doka Doka kuma ta yi bayanin, cewa •“kowane mutum yana da tasa martabar da kuma darajar da Allah ya ba shi kasancewarsa mutum.

Gwamnatin “Da Ke {o}arin Kiyaye Doka Ba Mai {o}arin Take

Ha}}in Jama’a Ba.” John Adams wanda da shi da

Thomas Jefferson sun yi wani cikakken bayani kan ‘yanci da suka rubuta a shekarar 1776 a kan tunaninsu da gwamnati, “janhuriya wani lardi ne na kiyaye doka, ba wai na take ha}}in jama’a ba.”

A tsarin dokoki na }asar Amurka rarraba iko kamar yadda yake }unshe a cikin kundin tsarin mulkin }asar, shi ne a tabbatar da cewa ~angarori uku na gwamnatin }asar, na ‘yan majalisa (da ake kira wani taron masu yin dokoki), ~angaren shari’a (shi ne kotuna) da kuma ~angaren zartarwa (shi ne shugaban }asa da ministocinsa), ana ba su wani }arfi da zai kasance wani ~angare ne kawai zai iya

aiwatarwa. Wannan matakin rarraba

ayyuka zuwa bangarori uku, kamar yadda wa]anda suka samar da tsarin suka bayyana, shi ne a tabbatar da cewa wani mutum ko taron jama’a ba za su tattare dukkan }arfin doka a hannunsu su ka]ai ba, don haka za a samar da wata gwamnatin da ba za a tafiyar da ita ta hannun wa]ansu tsirarun jama’a ba, don haka ake son dole sai dai a samu dokar da jama’a za su samar da ita kuma wa]anda mutane suka za~a.

Wa]ansu misalai kan hakan, sun ha]ar da ikon shugaban }asa na samar da doka da kuma samun dokar majalisa su samu damar tattaunawa a kanta ta hanyar samun ‘yan majalisa masu rinjaye.

Saboda }asar Amurka ta yi wani taro ne na wa]anda aka za~a, wa]annan mutane su ne ke da alhakin tabbatar da jin da]in mutanen da suka za~e su.

Kamar yadda Kennedy ya bayyana, cewa wannan al’amari an yi shi ne domin samar da “cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa doka dole ne ta amfani jama’a.”

Kotun }oli, ita ce kotun da ta fi kowace kotu a }asar Amurka, za ta tabbatar da doka a jihohi da }ananan hukumomi da kuma tarayya baki ]aya, dokar ba ta taka ’yancin jama’a ba, kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin }asar.

Koda kuwa taron majalisar }asar ya yi dokar da ta samu taimakon shugaban }asa, aka kuma mayar da ita doka, mutumin da abin ya shafa yana da iko ko damar

ya rubuta takardar koke a game da abin da yake gani an take masa ha}}i da kuma ‘yanci musamman game da kundin tsarin mulkin }asar. Amma in ana son wannan tsari ya yi amfani, ya zama dole sai an samu ‘yancin kotuna da duk ~angaren shari’a.

Kamar yadda kotun }oli a ta bakin Al}ali Sandra Dayo’ Connor, samar da ~angaren shari’a mai zaman kansa ba abu ne mai sau}i ba. “Samun ‘yancin ~angaren shari’a ba shi ne zai samar wa kansa da lamarin da kowa zai ga harkar da inganci ba,” inji ta.

“Yana da wahala a samar da lamarin, amma kuma abu ne mai sau}i ga kowa ya rusa dukkan lamarin.

|angaren shari’a mai zaman kansa ba wani al’amari ba ne da zai yi wa ~angaren za~a~~u wata barazana. Al}alai da lauyoyi a }asar Amurka suna }o}arin tsare ayyukansu ne da yake a fayyace kan abin da ya dace, al}alai su aiwatar da wanda bai kamata ba.

Domin tabbatar da ‘yancin ~angaren shari’a a }asar Amurka, taron lamarin shari’a ya fayyace komai (wanda ya kasance babban mai shari’a a }asar Amurka tare da mambobinsa sun ha]ar da manyan masu shari’a daga gwamnatin tarayya da kuma shiyyoyi), da duk suka amince da wata doka da ]abi’a.

Taron majalisar al}alai yana da kwamitoci da ke tabbatar da ganin kowane al}ali ya yi, kuma ya yi bayani idan da akwai wani }orafi. Bayanin maganar ku]i ana

Duba shafi na 20

Page 13: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 13

SANYA jari a }asar waje ba shi da tabbacin samun kishin

}asa,” in ji shugaban }asar Ghana, John Atta Mills a lokacin da ya halarci wani taro na kasuwanci.

Shugaban ya ci gaba da cewa, “ana son harkar kasuwanci ko zuba jari ne a inda ake marhabin da ita.”

Shi dai shugaban }asar ta Ghana yana wannan bayani ne a bisa la’akari da cewa hamsha}an ‘yan kasuwar Amurka da }asashen da suka ci gaba, ba haka kurum suke zuba jarinsu a }asa ba, sai sun tabbatar da cewa, lallai ilaila akwai zaman lafiya ta fuskar siyasa

da mutunta dokokin }asa da kuma yanayin tattalin arzi}in }asa mai kyau.

Duk wani mataki ko shawara a kan manyan jari, ba a yin sa a bisa son rai ko kuma a bar shi kara zube, amma a kan dube shi ne ta irin fasalin da aka ba shi, wala’alla ko }asa za ta ba shi muhimmancin da ake bu}ata na samar da gwamnati mai kyau don a samun kasuwanci mai ha~aka.

Mista Scott Eisner, babban darakta ne a cibiyar kasuwanci da ta shafi }asashen Afirka da ke Amurka.

Ko shakka babu }asashen da

suke ci gaba sun kasance gaba-gaba da manyan kamfanoni ke bu}atar sanya jari, shi ya sa ‘yan kasuwar }asar Amurka ke neman samun damar yin harka a can. Sanya jari a irin wa]annan }asashe na da riba ainun.

Misali, ana samun sau}i daga ma’aikata da yawan albarkatun }asa da kuma masu sayen kayayyaki da dama. Sai dai kuma a harkar kasuwanci ta duniya akan samu ‘yan bambance-bambance a wa]annan }asashe da ka iya kawo cikas ga manyan ‘yan kasuwar duniya ta yadda za su samu kasuwanci mai ha~aka.

Irin wa]annan cikas suna da

Harkar Kasuwanci Na Bu}atar Shugabanci

Mai Kyau Don Ta Ha~aka

Daga Scott Eisner © eJournal USA

BABBAN LABARI

MAGAMA Yuli 2011 13

Page 14: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 14

wuya a shawo kansu, sun ha]a da rashin tabbas na ]orewar mulkin siyasa da rashin samun ma’aikata masu ilimi da rashin yanayi mai kyau na gudanar da kasuwanci, sannan ga rashin abubuwan jin da]in rayuwa. Duk wa]annan na iya hana kamfanonin }asar Amurka zuwa baje kolinsu har ma su yi gasa da wasu.

Irin wa]annan matsaloli da ka taso suna iya kawo cikas ga duk wani riba da za a samu idan aka yi la’akari da yawan jarin da za a sanya. A shekaru 21 da suka wuce, cibiyar kasuwanci ta }asar Amurka, ta wallafa wani kundi mai taken: “Twelve Rules for International Investors,” ma’ana, “dokoki 12 ga manyan masu zuba jari.”

Ma}asudin wannan kundi shi ne a wayar da kan gwamnatocin }asashen waje irin }a’idojin da manyan kamfanonin Amurka ke amfani da su wajen zuba jari a }asa. Mujallar Forbes, na amfani da wannan dokoki ne wajen gano }asar da ta fi fice a harkar kasuwanci.

Mulki Bisa Adalci Na Jawo Sanya Jari A {asa.

Wasu daga cikin sharu]]an sanya jari (kamar girma ko yawan ciniki ko kuma kasancewar albarkatun }asa), na bayar da }warin gwiwar ba za a ri}a samun canjin gwamnati ta yadda aka ga dama ba. [ayan-biyu ko Allah ya albarkaci }asar da ma’adinai ko kuma babu.

Idan babu kasuwancin kirki a }asa, babu dokar da za a sanya ta canza irin wannan kasuwanci don ta girma, amma kuma gwamnati na da ‘yancin ]aukar matakin da ke huruminta. Shin }ayyade haraji na da wahala ne, ko gudanar da kasuwanci na da sau}i, kuma kai tsaye ake yin sa, shin ana yawan samun cin hanci da rashawa, sannan akwai adalci a yadda ake gudanar da shari’a?

Gwamnatoci na da damar kafa dokoki masu kyau da za su bayar da hurumin yin kasuwanci cikin yanayin walwala da zai jawo hankalin masu zuba jari su shigo }asa don yin kasuwanci.

Misali a nan, shi ne

kamfanonin }asashen waje na bu}atar garanti ko tabbacin gwamnatoci na samun tsaro kan jarin su ko da an samu matsalar siyasa ko na tattalin arzi}in }asa. Manyan kamfanoni na lura da cewar idan ma’aikatanta da kayayyakinta da kuma sauran jarinta na fuskantar matsala saboda rashin kwanciyar hankali a mulkin }asa, to, fa ba za ta sanya jarinta a irin wannan }asa ba, saboda yin kasuwanci a wannan }asar na tattare da ha]ari.

Wani abin sha’awa, shi ne ba wai kamfanonin Amurka na neman hul]ar kasuwanci kawai da }asashen da ake mulkin dimokura]iyya ba ne. Abin da irin wa]annan kamfanoni ke bu}ata shi ne kwanciyar hankalin }asa, wadda ita ce babban ginshi}in gudanar da kasuwanci mai riba, saboda shi ne babban makamin da zai tsare wa ]an kasuwa jarinsa.

Baya ga samun }asa mai kwanciyar hankali, ana bu}atar ma’aikata masu ilimin zamani da zai }ara jawo hankalin zuba jari na }asashen }etare kai tsaye. Kamfanonin Amurka na gudanar da kasuwanci na zamani kuma na musamman.

Akasari kamfanoni 500 kamar yadda wata mujalla ke auna nasarar kamfanoni ta nuna, sukan gudanar da kasuwancinsu a sabon wuri tare da hangen nesa.

Da]in da]awa wa]annan kamfanoni kan kafa rassa ne tare da tabbatarwa suna da isasshen kayan aikinsu, kuma suna son ganin sun ]auki ma’aikata ‘yan

MAGAMA Yuli 2011 14

Page 15: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 15

}asar da suke kasuwancin. Sun lura da cewa, ‘yan }asa ne

kawai za su iya shiga lungu da sa}o don samun yanayin kasuwanci mai kyau fiye da ‘yan }asashen waje.

Har ila yau, kamfanonin sun amince idan sun taimaka wajen ci gaban rayuwa a }asar da suke kasuwanci ta hanyar ha~aka tattalin arzi}insu, su ma za su samu ribar daga kwastomominsu.

Babban dalilin da ya sanya kamfanonin Amurka ke samun nasarar kasuwanci a }asashen }etare shi ne yadda ba sa katsalandan a tsarin mulkin }asar da suke zuba jarinsu. Irin wannan ha]in kai na samar da gagarumin alfanu ta hanyar saka jari a }asa wanda a }arshe yana samar da ayyukan yi ga ‘yan }asa.

A kuma tamu fahimtar, yana da kyau a ce yawan al’ummar }asa na da ilimi ko }warewa ko masaniya musamman ta fannin fasaha da kimiyya da kamfanonin Amurka za su ]auka aiki. Kamfanonin su lura da cewa babbar matsalar }asashe masu tasowa, shi ne rashin ilimi, shi ya sa yawancin kamfanoni na la’akari ne da ilimin fasaha da kimiyya a matsayin matakin farko na sanya jari a }asa. Daga nan sai a dubi yawan abin da za a kashe na aiwatar da kasuwancin da kuma lokacin da za a kashe na gudanar da kasuwancin.

Baya ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin }asa da kuma }wararrun ma’aikata da kamfanoni ke la’akari da su wajen zuba jari a }asashe masu tasowa, akwai wa]ansu muhimman abubuwa da

suke bu}ata. Mai sanya jari na bu}atar

tafiyar da al’amuran gwamnati bisa tsari da tsafta mara magu]i, sannan kuma lokacin da za a canza wani tsari, ya dace mai jari ya sani, musamman }a’idojin da suka shafi kasuwanci da manyan kamfanonin waje har ma da na cikin gida.

Har ila yau, ‘yan Amurka masu sanya jari na bu}atar yanayi mai yi wa kowa adalci na tafiyar da kasuwanci a }asa. Duk wani kamfanin Amurka na biyayya ga hukuncin hukumomin ya}i da cin hanci da rashawa na }asar da suke kasuwanci, a don haka muddin suka tsoma kansu cikin bayar da cin hanci da rashawa, za su fuskanci shari’a a Amurka. A don haka yana da wahala }warai da gaske wani kamfanin Amurka ya yi nasarar kasuwanci a }asar da ta shahara a cin hanci da rashawa.

Wani makamin da zai kwa]aitar da sanya jari a kamfanonin Amurka, shi ne bin dokar }asa bisa tsari da gaskiya. Kamfanoni na son ganin }asa ta shahara wajen bin }a’idar dokokinta sau da }afa. Suna bu}atar ganin idan an kai }arar su ko kuma su sun kai }ara, an gudanar da shari’a bisa adalci.

Har wa yau, kamfanoni na bu}atar yanayin kasuwanci mai kyau da walwala.

Jami’an gwamnatin Amurka da suka halarci wani taro a asirce da cibiyar kasuwanci ta Amurka a shekarar 2009, kan yadda }asar Amurka ke kallon Nahiyar Afirka, sun ce akasarin }asashe masu tasowa suna matu}ar

}o}arin ganin sun jawo hankulan masu sanya jari ta hanyar gudanar da canje-canje da zai samar da yanayi mai kyau don gudanar da kasuwanci a }asashensu.

Wa]annan }asashe a cewar su, su ne za su iya jawo hankalin sanya jari daga manyan }asashe kai-tsaye wato (FDI), ba tare da tsananta bincike ba. Gyaran kawai da ake bu}ata, shi ne samar da biza na kasuwanci cikin sau}i da kuma samar da wani hurumi da zai sa mai sanya jari a hanya don gano yadda zai gudanar da harkokin kasuwancinsa cikin sau}i.

A bayyane yake, cewar akwai }asashen da suka yi nasarar jawo manyan jari daga manyan kamfanonin }asashen waje. Wa]annan }asashe sun ha]a da }asar Panama da kuma Ruwanda, ka]an ke nan.

Misali, }asar Panama, gwamnati ta bai wa ‘yan kasuwa masu jari na cikin gida da }asar waje jerin gara~asa don gudanar da kasuwanci cikin sau}i a }asar. A cikin gara~asar, gwamnati ta ba ‘yan kasuwa rance don biyan haraji da kuma }ayyade ku]in biyan harajin kaya ba tare da canji ba.

A wannan shekarar, Bankin duniya ya bayyana }asar Ruwanda a matsayin }asar da ta fi kowace }asa mai tasowa zama wadda ta bu]e }ofofinta domin masu sanya jari su sami sau}in gudanar da kasuwanci ba tare da tsangwama ba.

Wani misalin, shi ne a }asar Singapore, wadda }aramar

Duba shafi na 23

MAGAMA Yuli 2011 15

Page 16: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 16

Wakilai daga hukumomin jami’an tsaro na soja da ‘yan

sanda da ma’aikatan gwamnati da sauran ma’aikata da aikinsu ya danganci tsaro suka gudanar da taron mako guda kan }arfafa tsaro tsakanin }asa da }asa. Shi dai (TSS), wato }ungiya ce da ke samar da horo kan tsaro tsakanin }asa da }asa, tare da ha]in gwiwar “U.S. AFRICOM,” suka ]auki nauyin koyar da wani shiri tsakanin farin kaya da soja wadda ta samar da damar da za su yi aiki tare saboda wani yanayi mai barazana da ke tasowa a duniya, da kuma tabbatar da ganin Nijeriya ta ci gaba da kasancewa jagora a shiyyar Afirka ta Yamma.

“Akwai wasu canje-canje cikin sauri a duniya da barazanar tsaro

ke fuskantar Nijeriya a yau. A shirye-shirye na baya, guda 7 na TSS a Nijeriya, sun du}ufa ne ba kawai kan wayar wa gwamnatin Nijeriya da mutanenta kai ba, kan wannan barazana, hatta masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro da kuma }ungiyoyin jama’a duk sun fahimci, cewar wannan lamari ne da ke bu}atar a tunkare shi tare da ha]in kai,” a cewar Birgediya Janar (Mai Ritaya) Jones Arogbofa (]an Nijeriya), ne ya yi wannan bayani.

Haka shi ma Birgediya Janar (Mai Ritaya) Russ Howard na Amurka ya jaddada cewa, “TSS ya bai wa Nijeriya damar tattaunawa kan matsalar tsaro da ta addabe ta.

Ya ci gaba da cewa, abu mafi muhimmanci, shi ne TSS ta bai wa ‘yan Nijeriya damar da suka

tattauna da kuma }ir}iro hanyoyin da za su magance matsalar tsaro a }asa da kuma na shiyya.”

{wararru na gida da na waje da kuma hukumomin farin kaya duk sun halarci irin wannan taro wadda hakan ya nuna irin muhimmancin taron a shiyyar tsakanin hukumomi da sojoji da fararen hula.

Manyan ba}i masu jawabi, sun ha]a da LTC Abdourahamane D eing daga }ungiyar (ECOWAS) da Mista Oliver Stolpe (UNODC), da Mista Gbenga Mabo (NDLEA), da Charles Agbo da Air Commander A.A. Bankole (NEMA). Dukansu sun gabatar da }asidu da za su taimaka wa wa]anda suka halarci taron nan gaba. v

Tabbatar Da Tsaro A Kan Iyakar Nijeriya

Dokta Pita Agbese, wani }wararren ]an Nijeriya yake yi wa wasu sojoji

da farin kaya lacca kan rikicin addini }abilanci

Page 17: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

Tabbatar Da Tsaro A Kan Iyakar Nijeriya

masallata 2,000, sannan akwai makarantun boko na firamare da kuma na }an}anan yara (Nursery).

Mista Stafford, ya ce ya ziyarci wannan masallaci ne domin ya isar da sa}on shugaban Amurka, Barrack Obama na son cika burinsa, na inganta dangantaka da Musulman duniya domin kawo zaman lafiya da ha}uri da fahimtar juna.

Ya kuma lura da cewa, lallai Musulunci na taka muhimmayar rawa wajen tabbatar da adalci.

A lokacin da yake jawabin maraba a madadin babban limamin, Dokta A.A. Rufa’i, ya bayyana ziyarar babban jami’in Amurkar da cewa ziyara ce na kawo ci gaba ta fannin inganta zamantakewa tsakanin addinai da kuma tsakanin Amurka da Nijeriya.

Babban limamin ya ci gaba da cewa ya da]e yana bin diddigin bayanan Shugaba Barack Obama kan manufofinsa na }asashen waje, kuma ya gamsu da cewar manufofin nasa akwai niyyoyi masu kyau wanda addinin Musulunci ya aminta da su.

Ya jinjina wa Obama da gwamnatinsa a bisa kyawawan a}idunsa na kawo zaman lafiya da fahimtar juna.

Har ila yau, limamin ya ce, “yan uwanmu da ke }asar Falas]inu, su ka]ai ne al’ummar da ba

Ranar 30 ga watan Mayu, babban jam’i a ofishin jakadan Amurka Joseph Stafford ya ziyarci birnin

Ibadan ta jihar Oyo don saduwa da manyan malaman Musulunci da na Kirista da sauran mabiyansu. Ma}asudin wannan ziyara shi ne don samar da hanyar fahimtar juna tsakanin addinai don zaman lafiya tare da gina kyakkyawar dangantaka tsakanin }asar Amurka da mutanen Nijeriya.

Wa]anda suka raka jami’in, sun ha]a da jami’in hul]a da jama’a kan al’adu, Peter Piness da mai taimaka masa, Clemeson Ayegbusi.

Tawagar ta ziyarci babban masallacin Ibadan da Masallacin da ke jami’ar Ibadan da kuma babban cocin da ke Jami’ar Ibadan.

[aya daga cikin malaman musuluncin, sun bayyana ziyarar jami’in, da cewa abin tarihi ne. Sheikh Busari Shuarau Aruna na III, ne ya kar~i ba}in. Shi dai Sheikh Aruna shi ne uban }ungiyar limamai na jihohin kudancin Nijeriya.

Babban masallacin da Mista Stafford ya ziyarta, an gina shi ne a shekarar 1964, kuma yana ]aukar

{ara Fahimtar Juna Tsakanin Mabiya Addinai

Daga Clemeson Ayegbusi {wararre Kan Al’adu

Malamin addinin musulunci Docta A. A. Rufa'i yake shigar da Babban Jami'i a ofishin Jakadar Amurka, Joseph Stafford wani masallaci a Oja Oba da ke Ibadan.

MAGAMA Yuli 2011 17

Page 18: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 18

su da }asarsu domin kawai Isra’ila ba sa son su samu.” A madadin Musulman Kudu maso Yammacin

Nijeriya, limamin ya yi kira ga gwamnatin Amurka da mutanenta su hanzarta samun hanyar da mutanen Falas]inu za su samu }asar kansu.

A ta}aitaccen bayaninsa, Mista Stafford ya nuna muhimmancin saduwa da Musulmai a Nijeriya da kuma muhimmancin addinin Musulunci a Nijeriya. Ya kuma nuna yadda }asar Amurka ke mutunta Musulunci a duniya, da yadda suke da addinin Kiristanci da na Judaism.

Musulunci ya yi hani da duk wani tashin hankali da sunan addini. Da yake jawabi dangane da kira kan kawo }arshen rikicin Isra’ila da Falas]inawa, sai Mista Stafford, ya ce Amurka na mutunta addinin Musulunci kuma tana iya }o}arinta don ganin an samu fahimtar juna a }asashen Gabas ta tsakiya.

A lokacin da ya shirya masa liyafar cin abinci na musamman, a fadarsa, Baba Addini na }asar Yarabawa, Alhaji Arisekola ya ce, kashi 75 daga cikin mutane miliyan 10 da ke Ibadan duka Musulmai ne. Ya jaddada cewar addinin Musulunci, addini ne na zaman lafiya tare da kowa. Ya gode wa gwamnatin Amurka a game da gudunmawarta na ci gaban Nijeriya.

A nasa jawabin, har ila yau, Mista Stafford ya jaddada cewar, Musulunci addini ne da ya yi watsi da amfani da shi domin tayar da hankali, sannan ya yaba wa }ungiyar nan ta kyautata dangantaka tsakanin

addinai wato (NIREC). Daga bisani, Mista Stafford ya tattauna da

malaman Musulunci a masallacin Jami’ar Ibadan, tare da shugabannin }ungiyar ]alibai Musulmai na Jami’ar.

Babban limamin da wani Furofesan Larabci da addinin Musulunci, Dokta Abdulrahaman Oloyede sun nuna godiyarsu ga ziyarar da jami’in ke yi zuwa ga Musulman Nijeriya.

A nasa sa}on, Mista Stafford har ila yau, ya jaddada yadda Amerikawa Musulmai suka agaza wajen ci gaban {asar a shekaru da dama. Bayan kammala ziyarar masallacin jami’ar Ibadan, sai Mista Stafford ya ziyarci wata majami’a da ke kusa da masallacin.

A wannan coci, ya sadu da shugabanta, Furofesa Reuben Arowolo da Faston cocin, Rabaran Timothy Olatunji da mataimakinsa, Rabaran Oyelade. Mista Stafford, ya ce dalilin ziyararsa cocin, shi ne don inganta fahimtar juna a tsakanin addinai.

Shugaban cocin ya ce, wannan ziyara na da muhimmanci a tarihin wannan majami’ar, ya kuma gode wa Mista Stafford a bisa ziyarar da ya kai musu.

Daga }arshe an zagaya da jami’in cikin cocin, ya kuma nuna aniyar cocin na ci gaba da gudanar da aiki tare da ofishin Amurka a Nijeriya kan harkokin dangatakar addinai. v

Daga hagu babban jami'ia a ofishin Amurka Joseph Stafford yake jawabi ga al'ummar Musulmi a masallaci, daga dama, CG Stafford ne yake gaisawa da babban limamin kasar ibadan Shekh Busari Suarahu Aruna bayan ya amshi wasu litattafai. Clemmenson Ayegbasi ya dauko hoton.

Page 19: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 19

yaro guda. Wannan yana nuni }arara cewa, ku]in karatu a jihohin Kudu da ake kashewa kan karatun yaro ya fi na jihohin Arewa.

Haka kuma bambance-bambance a tsakanin shiyyoyi na yin nuni da haka. Jihar Legas mai kashe Naira 25,185, ke kan gaba a shiyyar Kudu maso Yamma sai Jihar Ondo mai bi mata da Naira 11,304 a yayin da ake kashe wa karatun yaro ku]i mafi }an}anta na Naira 8,470 a Jihar Ekiti. Dukkan adadin da ake kashewa ya zarta na tsaka-tsakin adadin da ake kashewa a }asa.

A shiyyar Kudu maso Kudu, Jihar Ribas ce ta farko, inda ake

kashe wa karatun yaro guda 23,277 sai Jihar Delta mai bi mata da Naira 10,033 da Jihar Bayelsa mai adadin 6,892 da ake kashe wa karatun yaro kuma wannan adadi ne mafi }an}anta a shiyyar. Naira 6,992 da ake kashewa a jihohin Bayelsa da Akwa Ibom ka]an ta gaza tsaka-tsakin adadin da ake kashewa a }asa.

A shiyyar Kudu maso Gabas, Jihar Abiya ce ke kan gaba da kashe Naira 13,462 a kan yaro guda a yayin da ake kashe Naira 5,861 mafi }an}anta kan karatun yaro guda. Tsaka-tsakin abin da ake biya na Naira 6,208 a jihohin Ebonyi da Enugu ya gaza tsaka-tsakin adadin

a }asa da ka]an. A shiyyar Arewa ta Tsakiya,

ana kashe ku]i mafi girma na Naira 18,004, sai Jihohin Kogi da Kwara masu bi mata da Naira 7,422 da Naira 7,320. Ana kashe a}alla Naira 3,006 mafi }an}anta a karatun kowane yaro a Jihar Filato a cikin wannan shiyya. Tsaka-tsakin adadi da ake kashewa a jihohin Binuwai da Neja da Nasarawa da Jihar Filato ya gaza tsaka-tsakin adadin da ake kashewa a }asa.

Ya cancanci a lura cewa, tsaka-tsakin adadin da ake kashewa a kan karatun kowane yaro a shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas ya gaza na adadin na }asa. Ga dukkan alamu, iyaye da

Daga shafi na 5

Duba shafi na 21

Bayanan {ididdiga Kan Ilimi Don [aukar Mataki

gine filasta da fenti don rage zaizaya da matsanancin yanayi na sararin samaniya na Nijeriya ke haddasawa. An yi wa gine-ginen filasta da fenti kuma aka rufe kogo a cikin wata hu]u da suka gabata.

Makarantar tana bayar da karatu da koyon sana’o’i ga yara da matasa na}asassu. Kuma akwai darussan aji da koya sana’a da girki da koya aikin lambu da yin kyandir da ]inki tare da ba ]alibai dabarun

dogaro da kai. Har ila yau, ana koyar da yin

magana da amfani da ga~o~in jiki. A halin yanzu ana ci gaba da ]aukar ]alibai bayan da suka tarwatse saboda ta’annuti na bara. Kuma ana fatar sake samun ]alibai ]ari (100) nan da zangon karatu na gaba. Kuma makarantar tana taimaka wa yaran makarantun gwamnati wa]anda ke da matsala a wajen karatu da rubutu. Ana

gudanar wa iyaye da masana ilimi tarukkan bita da tuntu~a don su }ara fahimtar bu}atun ilimi na musamman da na}asassun yara ke bu}ata.

Ofishin Jakadancin Amurka yana farin cikin taimaka wa jama’a da al’ummomi na Nijeriya. Don neman }arin bayani a game da taimako da albarkatun ilimi sai ka ziyarci yanar gizonmu a:http://nigeria.usembassy.gov v

Mazauna Tsaunukan Jos Sun Fara Darawa Daga Shafi na 7

Duba Shafi na 23

taron liyafar daga Zariya.” A cikin jawabinsa na barka da

zuwa, Jakada McCulley ya gode wa masu fasahar yin abubuwa saboda ba shi damar ganin yadda fasahar ‘yan Nijeriya take.

Da]in da]awa, ya nuna gamsuwar ma’aikatan Ofishin Jakadancin Amurka game da karamcin masu fasahar yin abubuwa da aikin da shugabannin SNA suka yi a cikin hanzari da suka }awata kyawun

gidan. Ambasada McCulley har ila yau, ya nuna jin da]insa da damar da ya samu na gabatar da ]an Nijeriya mai haza}ar yin abubuwa

Fuskantar {alubale Daga shafi na 2

Page 20: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 20

bu}atarsa. Dimokura]iyya wani al’amari

ne da ke tafiya tare da masu rinjaye da kuma ‘yancin mutum ko da guda ]aya ne.

Domin kauce wa matsalar cin hanci da kar~ar rashawa. Dukkan wa]annan ~angarorin, kamar yadda O’ Connor, ya ce “Dole a tabbatar da samun bambanci da zai ba jama’a damar su samu ko da ‘yar }aramar gamsuwa ce wajen tafiyar da harkokinsu da kuma daraja da mutuncin al}alan da ke aiki.”

Amma duk da haka al}alan da za su tabbatar da bin }a’idar ayyuka, dole ne sai an kira shi ya yi cikakken bayani in suka kasa bin }a’idar aiki.

“Al}alai dole ne su zama masu ‘yanci, ba wai a ce za su iya ko suna da za~i, domin su suna da ‘yanci dole sai sun aiwatar da aikin kamar yadda ya kamata,” inji Kennedy.

Girmamawa Da Kuma Matsaya Bayan Za~e

Dimokura]iyya ta }ir}ira wani al’amari da jama’a za su yi tsammani da kuma ganewa, da suka ha]a da girmama doka da kuma fitowar sakamakon za~e ko za~u~~uka.

Tana bu}atar girmamawa na bayan za~e ko za~u~~uka. Da yake bayani a }asar Masar a shekarar 2009, shugaba Obama ya }arfafa cewa, wa]annan su ne shika shikan gaskiya.

A duk inda za ta kasancegwamnatin jama’a, wadda

jama’ar suka samar, }a'idar amana iri ]aya ce, a kan duk wanda ya kasance kan madafun iko. Dole ne ya tsare doka cikin girma da arzi}i ba tare da taka doka ko }a’ida ba, kuma dole a kare ‘yancin marasa rinjaye, da kuma halartar samun rungumar kowa da kuma daidaitawa, dole ka sanya bu}atar jama’arka a bisa komai da suka hada, har da biyan bu}atar jam’iyyarka domin bu}atar jama’a ta fi ta jam’iyyar da kake.

In aka kasa samun wannan ]an]anon za~e kawai, ba zai ta~a samar da sahihiya kuma ingantacciyar dimokura]iyya ba.”

“(Cairo jami’ar Cairo, }asar Egypt ranar 4 ga watan Yuni 2009)

Shika-Shikan Dimokura]iyya. Dimokura]iyya ta wuce samar

da gwamnati tare da ~angarorinta kawai, ta ha]a har da samar da taron jama’a da }ungiyoyinsu a kuma samar da daidaito da fahimtar juna tare da aiwatar da gyaran duk wani abin da zai kawo bambanci a tsakanin al’umma. Dimokura]iyya tana }o}arin tabbatar da samar da dukkan }a’idoji ne domin amfanin jama’a.

Ainihin Shika-Shikan

dimokura]iyya:- Dimokura]iyya gwamnati ce da •jama’a ke da }arfin fa]a a ji kai tsaye ko kuma ta hanyar wakilan da jama’ar suka za~a. Tsarin dimokura]iyya ya •ta' alla}a ne da ba ainihin masu rinjaye da kuma dukkan jama’a dama da ]aukacin matakan

gwamnati, dama tun daga gwamnatin tarayya zuwa na }ananan hukumomi damar samun fahimtar juna domin tabbatar da ganin gwamnati ta aiwatar da dukkan abubuwan da suka dace. Dimokura]iyya wani tsari ne •da ke nuna samun fahimtar juna domin kowane ~angare ya samu cikakkiyar damar aiwatar da ayyukan da ya dace ga al’umma, ta yadda kowa zai tabbatar da ainihin ‘yancin da yake da shi cikin kundin tsarin mulki, musamman damar fa]in albarkacin baki, damar yin al’amuran addini, damar samun kariya a }ar}ashin doka, da kuma damar samun aiwatar da harkokin siyasa kamar kowa, tattalin arzi}i da kuma rayuwar jama’a baki ]aya. Dimokura]iyya tsari ne da ke •}o}arin tabbatar da yin za~en gaskiya da kuma adalci da ke ba duk wa]anda shekarunsu suka kai damar za~en wanda suke bu}ata. 'Yan }asa a tsarin •dimokura]iyya ba wai suna da damar ne kawai ba, har ma da damar shiga a dama da su cikin al’amuran siyasa da zai bayar da damar kare ‘yanci da duk wata dama. Al’ummar da ke aiwatar da •tsarin dimokura]iyya suna }o}arin ganin an aiwatar da tsarin rungumar juna wajen sasantawa da tabbatar da daidaituwar duk al’amuran baki ]aya. Kamar yadda wata mace

Daga shafi na 12

Page 21: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 21

iyayen goyo a shiyyar Arewa maso Gabas suna kashe ku]i mafi }an}anta ta fuskar karatun firamare. Suna kashe a tsakanin kashi ]aya daga cikin shida na rabin tsaka-tsakin adadin da ake

kashewa a }asa. Misali, a Jihar Borno, ana

kashe Naira 3,650 mafi girma a shiyyar. Kuma ana kashe Naira 1,220 mafi }an}anta a Jihar Bauci.

Kuma da wuya a sami yiwuwar a kashe wa yaro ku]i kan karatun

firamare a shiyyoyin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da a wasu jihohi a shiyyoyin Arewa ta Tsakiya fiye da jihohi a shiyyoyin Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas na }asa.

Bayanan {ididdiga Kan Ilimi Don [aukar MatakiDaga shafi na 19

Daga shafi na 10

mai kamar maza Mahatma Gandi ta bayyana “{in amincewa da faruwar al’amura yadda suka faru shi ma tamkar rikici ne da zai yi wa tsarin dimokura]iyya tarna}i.” Dimokura]iyya ta kasu zuwa

abubuwa guda biyu ne kawai kai-tsaye da kuma samun wakilci.

A tsarin dimokura]iyya na kai tsaye ‘yan }asa ba tare da samun wani shisshigi ba ta hanyar za~e ko kuma na]i duk za su iya shiga cikin harkokin ]aukar wani matsayi, kuma wannan tsari ya ha]a da har masu marasa rinjaye a cikin jama’a ko a wasu }ungiyoyi, ko al’amaran wa]ansu }abilu, ko kuma wa]ansu }ananan rassa na }ungiyoyi a misali.

Idan ’yayan wata }ungiya za su iya ha]uwa a cikin wani ]aki su tattauna wa]ansu al’amura, su kuma cimma ‘yarjejeniya ko kuma gudanar da za~e har a samu masu rinjaye.

Wa]ansu daga cikin jihohi a

}asar Amurka, bugu da }ari wa]ansu wurare sun tabbatar da bayar da canjin doka ko kuma damar a yi kiranye ga wakilin da aka za~a ko kuma }uri’a lokacin gabatar da wa]ansu al’amura a jihohi lokacin za~e.

Wa]annan al’amura da kuma aikatasu, su ne ainihin yanayin samun dimokura]iyya na kai tsaye da ke bayyana damar masu rinjaye. Wa]ansu ayyuka da dama suna da alamun aiwatar da dimokura]iyya kai-tsaye.

A }asar Switzerland, da yawa daga cikin wa]ansu matakai masu muhimmanci kan al’amura da suka ha]a da samar da harkokin lafiya, makamashi da samar da ayyukan yi duk wa]ansu al’amura ne da ake yi ta hanyar za~en da jama’a za su aiwatar.

Kuma wa]ansu za su iya yin gardamar cewa, hanyar kafar sadarwa ta yanar gizo ita ma hanya ce ta aiwatar da dimokura]iyya kai-tsaye, kamar

yadda take bayar da }arfi ga gungun ‘yan siyasa domin samar da ku]i domin gudanar da wa]ansu al’amura.

Bugu da }ari kuma, a yau wani al’amarin da ake ganin cewa shi ne ainihin tsarin dimokura]iyya na gama-gari ko garin da ya zama na mutane 50,000 ko kuma }asar da ke da jama’a miliyan 50 da za a iya za~en jama’ar da za su zauna su yanke wani hukunci, samar da dokoki, ko kuma su gabatar da wa]ansu aikace-aikace domin jama’a su ci moriyar lamarin.

Editoci: Ra’ayoyin da aka bayyana a cikin wannan ma}ala, ba wai dole ne sai sun yi daidai da irin ra’ayi da kuma tsarin Amurka ba ko gwamnatinta)

Za ka iya samun yin karatun }arin bayani a addireshin yanar Gizo kamar haka: http://iipdigital. usembassy.gov/st/english/publication/2010/01/20100126154105 mlenuhreto.850166. htm1# axzz1nw Mnkuh3. v

‘Daga mahangar gwamnatin }asar Amurka” Ya ce “Muna murna mu taimaka ta kowace hanya da za mu iya, kuma za mu taimaka ta kowace hanya,” musamman ta

hanyar hukumomin }asar Amurka da ke ayyukan ci gaba na }asa da }asa (USAID).

Masu samar da harkar wutar lantarki mai zaman kansa, zai zama wani mabu]i ga batun

samar da hasken wutar, ya ce kamar yadda yake jinjina wa Nijeriya a ko da yaushe a bisa }o}arinta na gyaran ~angaren samar da fetur da ya ha]a da tabbatar da gaskiya. v

Amurka Da Nijeriya Kan Harkokin Dimokura]iyya ............

Page 22: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 22

tsibiri ce da babu albarkatun }asa, amma kawai manya-manyan masana’antu kuma ]aya ne daga cikin }asashen duniya mai alfahari da ingantacciyar rayuwa a tsakanin al’ummarta.

Ana iya kwatanta }asar Koriya ta kudu da ma}wabciyarta Koriya ta Arewa wadda ake zaton tana da albarkatun }asa. Sai dai Koriya ta Kudu tana gaba wajen }asashen da suka ci gaba ta ha~akar rayuwar al’ummarta, amma kuma Koriya ta Arewa ta dogara ne ga taimako daga }asashen waje don ciyar da jama’arta.

Wani misali da ya kamata a yi garga]i a kai, shi ne yadda kwanan nan, }asar Ecuador ta bayyana sakamako mara da]i kan manufofin gwamnatin }asar ta fuskar dankwafar da yanayi mai kyau na gudanar da kasuwanci, kamar }wace jari ko aikin mutane.

Yanayin kasuwanci a }asar ta Ecuador ya ta~ar~are, sannan gwamnatin }asar ta }wace duk wani kamfani mallakar ‘yan }asar Amurka ba tare da biyan diyya ba shekarun baya.

Misali, }wace rijiyar mai wadda jarinta ya kai dalar Amurka biliyan ]aya, yin katsalandan a gudanar da shari’a na }asar, a yanzu kuma tana neman }wace mallakar ayyukan bincike na kamfanonin }asashen waje.

Sakamakon wa]annan halaye na gwamnatin }asar Ecuador ya sanya rashin wani jari na kasuwanci daga }asashen waje,

yanzu yanayin rayuwar }asar, tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007 ya zube }asa warwas, idan aka kwatanta da sauran }asashe na Latin Amurka da ke ma}wabtaka da su, kamar Venezuela da Boliviya, kamar yadda hukumar tattalin arzi}in }asa ta Latin Amurka da Caribbean }ar}ashin majalisar ha]a kan Duniya (UN) ta ce.

Wani babban na}asu wajen binciken da kamfanonin da ke neman zuba jari, shi ne na rashin samar da muhimman abubuwan ci gaban rayuwa.

Babban misali shi ne na rashin amfani da albarkatun gona da ba a amfani da su. A }asashen Afirka marasa sahara, na nan tattare da }asar noma, sai dai akasarin abincin da ake nomawa iyakarsa gida, ma’ana ba a nomawa don kasuwanci.

Rashin kyakkyawar hanya a irin wa]annan }asashe, na hana kwasar amfanin gona zuwa kasuwa, a don haka akan samu ru~ewar wasu kayan abincin kafin a kai ga masu saye.

Idan za a samu ha]ewar hanyoyin mota da na jirgin }asa har zuwa ga tashar jirgin ruwa da ma na sama tsakanin manyan kasuwannin al}arya, da an samu kamfanoni masu sha’awar kayan gona na zuba jari a wannan ~angaren.

Wutar lantarki da hanyoyin sadarwa na da muhimmanci a ci gaban tattalin arzi}in }asa, kamar harkokin sufuri. Shin za a iya

samun yanayin da mai saye da mai sayarwa da ma’aikaci da mai ]aukar aiki za su ri}a yin magana a kai ta hanyar waya? Kamar dai yadda ake maganar azancin nan na cewar, “lokaci ne na neman ku]i.”

A wata ziyara da muka kai wani kamfanin masaka a }asar Ethiopia, an shaida mini cewar idan kamfanin zai kar~i wani sabon zane na tufafi, dole ne ma’aikaci ya je wani gari wanda sai ya yi tafiyar awa 4, sannan ya sanya zanen a faifan CD, sannan ya sake dawo da shi don mi}a wa kamfanin.

Idan aka samu kuskure wajen sabon zanen, dole sai an sake irin wannan tafiya don gyara. Wannan ba hanya ce ta gudanar da kasuwanci mai inganci ba, amma a }asa mai }arancin fasaha ko na’urar zamani irin ta “internet,” ana samun irin wannan cikas ]in.

Akasarin abubuwan da manyan kamfanonin Amurka masu zaman kansu ke bu}ata, don gudanar da kasuwanci, ba sa bu}atar manyan jari. Babban abin bu}ata, shi ne gwamnatin }asa ta kasance tana da yanayi mai kyau na gudanar da kasuwanci. Idan za a samu mulki ko gwamnatin da babu tashin hankali, babu cin hanci da rashawa, ta samar da yanayin kasuwanci cikin natsuwa, mai ilimantar da al’ummarta, ana iya gina abubuwan more rayuwa ko daga masu sanya jari a }asa ko kuma taimako irin na }asa da }asa.

Bayanin Edita: Ra’ayoyin da aka bayyana a wannan ma}ala ba manufofin gwamnatin Amurka ba ne. v

Harkar Kasuwanci Na Bu}atar Shugabanci Daga shafi na 15

Page 23: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

MAGAMA Yuli 2011 23

A ranar 16 ga watan Mayu, 2011, Jakadan Amurka a Nijeriya,

Mista Terence P. McCulley ya sami sababbin ba}i masu suna Kami da Zabi. Sai dai wa]annan ba}i mutum-mutumi ne da suke zance, wato MUPPETS, kuma suna zaune ne Sesame Square (Dandalin Sesame). Sesame Square shiri ne na yara da ke koyon abubuwan kiwon lafiya da kuma ]aukar darasi kan ]a’a.

Sauran yara za su iya kallon shirin Kami da Zabi a gidan talabijin na NTA da }arfe tara da rabi na safe, duk ranar Asabar da kuma ranakun Lahadi da }arfe biyar da rabi na yamma. A tashin farko na shirin Sesame Square, ya }unshi gudanar da shirin yara na tsawon rabin awa sau 26 don ilimantarwa ta fannin lissafi da tsafta da kiwon lafiya (wadda Ta }unshi rigakafin cizon sauro da wayar da kai kan ciwon sida) da koya wa yara yadda za su girmama kansu da al’adarsu da kuma fahimtar halayyar al’adun wasu.

Hukumar taimaka wa ci gaban }asashe (USAID) ta ]auki nauyin gudanar da “Sesame Square” da kuma ha]in gwiwar kamfanin sadarwa na Ileke Media da }ungiyar da ke aiwatar da shirin ilimantarwa, wa]anda suka }ir}iro da Sesame Street. v

Fuskantar {alubale Daga shafi na 19

An Samar Da Sabon Dandalin Yara A Nijeriya Mai Suna “Dandalin Sesame”

Wannan hoton Uwa Usen ne tare da Jakadan Amurka McCulley, daga bayansu fasahar zanen, Uwa Usen ne.

wa gwamnati da ‘yan kasuwa da ‘yan diflomasiyya da shugabannin }ungiyoyin al’umma da za su ziyarci gidan. Da]in da]awa, shi

Ra'ayinka: Idan ka samu wannan mujallar MAGAMA, muna bukatar ra'ayinka game da ita. Ka aiko mana da bayanai ta emal:[email protected], ko kuma:[email protected]. Ka aika mana da lambar wayarka domin mu aiko maka da sa}onni ta wayar salula.

A nan ana iya ganin Ambasada McCulley yana tattaunawa da Zobi da Kami. A }asa kuma ma’aikatan ofishin Jakadan Amurka a Nijeriya ne tare da mawa}iyar Nijeriya, Onyeka Onwenu da mataimakin shugaban Sesame Street a hoto. Idinka U. Onyukwa ne ya ]auki hoton.

mai fasahar da jami’an gwamnatin Nijeriya duk sun halarci bikin.

Lallai bikin fage ne da aka yaba da aikin fasahar da aka nuna, kamar yadda Jakada McCulley ya ce a cikin raha, “ba mu tattauna siyasa ba.” v

Page 24: Rajab / Sifili Na 17 Lamba ta 2 Mujallar Ofishin Jakadancin ... Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya Kyauta MAGAMA Yuli 2011 2 ’Ya’yan {ungiyar Masu Fasahar Yin Abubuwa Ta Nijeriya

CROSSROADS | Nigeria April 2011 Elections Special 24MAGAMA Yuli 2011 24

Labaran Mambobin IRCManufar cibiyar samar da bayanai ta IRC shi ne don ha~aka diflomasiyyar }asar Amurka don ta samu mutunci da daraja a Nijeriya ta hanyar

ganawa da gudanar da aiki tare da kuma ya]a labarai ga hhukumonin Nijeriya da sauran cibiyoyin da ke ya]a manufa da ra’ayin al’umma a kan al’amura da suka shafi manufofin Amurka. Kana iya yin rajista a http://tinyurl.com/ircregistration don neman bayani, ana kuma iya

rubuta mana: [email protected] (north) and [email protected](south).

Vol. 4 No. 1 & 2 Maris/Afrilu 2011

Ranar Yanayin {asa Ta Duniya: Ci Gaban Da Muka Samu Lisa P. Jackson Ta Rubuto Ranar 22 Ga Watan Afrilu Da {arfe 1:37 EDT. A duk shekara idan ranar yanayin duniya ya juyo, ya kan ba mu damar duba yun}urin da muka yi a kan }arin lafiyar mu da muhallinmu. A bana ranar yanayi duniya }ar}ashin shugabancin Barack Obama na alfaharin }o}arin da muka yi don ganin a cikin shekaru biyu yadda muka kare iskar da muke sha}a da ruwan da muke sha da yin nin}aya a ciki da kuma unguwannin da muke gina gidajenmu da makarantunmu da inda muke sana’o’in mu. A wajen kare iskar da muke sha}a, da farko mun kafa tarihi, kamar samun kafar yadda za a ri}a amfani da fetur yadda ya dace. Za a yi amfani da hukumar sufuri don gano yadda }ananan motoci da manya na Amurka za su ri}a amfani da fetur yadda ya dace ba tare da ~arnatarwa ba, da kuma }ir}iro da sinadarin Sulfur Dioxide na farko a cikin shekara hu]u. A watan da ya gabata ma mun sake kafa wani tarihin na farko irin sa na samar da sinadarai masu kyau na Mercury da Arsenic da sauran guba da ke cikin iska da ke fitowa daga injunanmu na janareto. Wa]annan abubuwa masu inganci na bu}atar makamashi daga }asar mu domin tabbatar da sarrafa kimiyya domin kawar da guba, kuma canji ne wadda zai iya kare rayuwar al’umma a }alla guda dubu 17 da kuma guje wa kamuwa da ciwon bugun zuciya. A tsakanin matasan mu kuwa, sabon tsarin zai taimaka wajen kare ha]uran kamuwa da ciwon Asma har sau dubu 120 da kuma na ciwon Masha}o guda dubu 11 tsakanin }ananan yara. Mun ]auki }wararan matakai domin inganta ruwan Amurka. Misali, ana ]aukar matakan farfa]o da }oramun da kuma kulawa da su don samar da kashi 95 na ruwa mai kyau da Amurkawa ke amfani da su. A }oramar Chesapeake, ana wani gagarumin shiri domin kare rawar da ta shafi rayuwar mutane miliyan 17. Shekara ]aya bayan da ruwan sama da iska ya yi ~arna da kuma malalar mai wadda har ta shafi jiha ta Louisiana, ya sanya har shugaban }asa, Barack Obama ya na]a ni shugabantar kwamitin farfa]o da ~arnar da iskar ta haifar, tana nan tana }ir}iro da gagarumin shiri, ba kawai don ta ci gaba da farfa]o ko gano irin ~arnar da iskar ta yi ba daga mummunar iskar da kuma malalar fetur a ruwa, wadda ba a ta~a ganin irin sa ba a tarihin Amurka, amma za mu dubi al’amuran da suka addabi shiyyar na shekaru da dama. Duk abubuwan da muke yi, muna yi ne da ha]in gwiwar unguwanni domin farfa]o da hanyoyin samun ruwa a birane. Muna kuma aiki da makarantu da ‘yan kasuwa ta yadda za a samu ta hanyar kimiyya da fasaha a zamani masu zuwa, da kuma taimaka wa unguwanni wajen samun wuri mai dausayi ko mai yalwa ta yadda za a kaucewa duk wata iska mai ]auke da guba. Sa’ilin da muke }o}arin kare ruwan da ke gudana a unguwanninmu, har ila yau, muna }o}arin kare }asar da al’umma ke gini a kai. Muna ta tsaftace unguwanni kamar yadda dokar shugaban }asa ta bu}aci a aiwatar. Muna tabbatarwa kowace unguwa da ta ha]a da na masu }aramin }arfi sun samu wurin zama. Mun }ara azama wajen fa]a]a tattaunawa a kan muhalli. {ara karanta }arin bayani a: http.//I.usa.gov/IBvDvN.

Kyautar Litattafai Ta Hanyar Yanar-gizo e journal USA:

[a’a Da Bin Doka (Littafin ya fito ranar 26 ga watan Afrilu, 2011)

A al’ummar da ke mulkin dimokura]iyya, ana baiwa jama’a damar kula da tsaron inda suke ko unguwanninsu da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ana baiwa ‘yan saude }arfin su tsare ko su bincika ko su kama duk wani mai laifi, har suna da ikon amfani da }arfi idan hali ya bu}aci yin haka. Amma kuma hukumar ‘yan sanda na tabbatar da cewa jami’an su na gudanar da aikin nasu a bisa kyakkyawan ]a’a. Idan basu tabbatar da irin wannan ]a’ar ba, ana iya samun rashin yarda tsakanin su da al’umma, hakan na iya ~ata zumuncin da ke tsakanin jami’an tsaro da al’umma wadda yake yana ]aya daga cikin ginshi}in mulkin dimokaru]iyya. Akwai }arin bayani a http://bit.ly/kChKyr (online).

Tattalin Arzi}in Amurka A Ta}aice (Ya fito ranar 26 ga watan Afrilu, 2011)

Wannan littafi da aka sake bugawa a shekarar 2011, ya nuna yadda gasa ke canza yanayin tattalin arzi}in Amurka, ya kuma nuna yadda ake ci gaba da muhawara ta hanyar tarihi game da rawar da gwamnati ke takawa a tattalin arzi}in Amurka. Akwai }arin bayani a http://bit.ty/mDyUgV.

PODCASTS Wuraren Sha}atawa Masu Dausayi A Amurka.

(Ya fito ranar 12 ga watan Afrilu, 2011)

Shekarun baya masha}atar Zion ta sayar da ruwan kwalba ga ba}i da yawan su ya kai dubu 60 a shekara ]aya. Akasarin kwalaban da aka shanye ruwan an jefar da su ne a kwandon shara ko an jefar a filin masha}atar. A yau, sai dai ba}i su zo da ruwan kwalbar su, ko kuma su ]ura ruwa a kwalbar da aka yi amfani da su. Tafiyar Da Ha]in kan al’umma A Amurka

(Ya fito Ranar 12 ga watan Afrilu, 2011)

Wani tsohon shugaban }asar Amurka mai suna Calvin Coolidge ya yi wani bayani a shekarar 1920 cewa “Babban harkokin Amurkawa, shi ne kasuwanci.” Wannan abin lura ne a lokacin da ake samun nasara ko riba a tattalin arzi}i. A daidai lokacin da batutuwa kamar makamashi da tsaro da canjin yanayi babu su. Akwai }arin bayani a http://bit./y/iw/wmx.

A Ziyarcemu A:-

Rosa Park Education and Information Centre, Sashin Hul]a Da Jama’a Ofishin Jakadan Amurka. Plot 1075 Diplomatic Drive, tsakiyar Abuja, Nijeriya. Tarho: (234)-9-461-4000 Fax: (234) 9-461-4011. E-mail: [email protected] Ana bu]ewa 9.00 a.m. Litinin zuwa Alhamis. 9.00 a.m. - 12 noon Juma’a.

Witney M. Young Information Resource Centre Sashin hul]a Da Jama’a, Ofishin Jakadan Amurka

Da Ke Legas. Lamba 2 titin Broad, Legas Nijeriya.

Tarho: (234) - 703 - 150 - 2444, (234) - 703 - 150.4867 Fax: (234) - 1 - 263 - 5397. Fax: (234) - 1 - 263 - 5397.

E-mail: [email protected]

Ana bu]ewa da }arfe 9 zuwa 3 na yamma ranar Litinin da zuwa Alhamis sai kuma ranar Juma’a da }arfe 9 zuwa 12 na rana.