24
Sifili 19 Lamba 3 Mujallar Ofishin Jakadancin Amirka A Nijeriya Kyauta Nuwamba/Disamba 2013 Muharram/Safar 1435 Fitowar Bazara

Motsa Jiki

  • Upload
    vutuyen

  • View
    254

  • Download
    3

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Motsa Jiki

MAGAMASifili 19 Lamba 3

Mujallar Ofishin Jakadancin Amirka A Nijeriya Kyauta

Nuwamba/Disamba 2013 Muharram/Safar 1435Fitowar Bazara

Page 2: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 2

Shi dai wasan yara na dandalin Sesame da ake gudanarwa a

Nijeriya, kwaikwayon irinsa ne da ake yi a Amirka mai suna ‘Sesame Street’. A yanzu haka gidan talabijin na }asa, wato NTA ya fara nunawa, ]auke da }ayatattun shiri na yara na mutum-mutumi da aka la}aba wa sunannaki Kami da Zobi. An fara shirin ne a watan Mayu na shekarar 2011, kuma an }ir}iro ne don ilmantar da iyali musamman yara mata

game da haruffan ABC da }irgen 123, da kuma inganta iliminsu kan tsafta da kiwon lafiya. Wa]annan abubuwa ne masu muhimmanci a }asar da ke fama da }arancin baiwa yara ilimi tun wuri da kuma fama da cututtuka kamar zazza~in cizon sauro da }anjamau. An }addamar da wannan sabon shirin ne mai la}abi “Shiga runtsin Kami da Big Bird” a makarantar yara da ke

Ushafa a }aramar hukumar Bwari da ke Abuja.

A cikin wannan sabon shirin da na bara, za a

fassara da harshen Hausa. Gwamnatin Amirka }ar}ashin

Wasan Yara Na Dandalin Sesame Ya Dawo

Abokan Elmo a lokacin da aka }addamar da sabon shirin dandalin Sesame, a makarantar firamare da ke Ushafa, a Abuja, ranar 12 ga watan Satumba, 2013. Idika Onyukwu ya ]auki hoton.

Duba shafi na 17

Maria Brewer, Embassy Charge with Elmo

Page 3: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 3

Gaisuwa ga makaranta Mujallar MAGAMA.Sunana James F.

Entwistle, sabon Jakadan Amirka a Nijeriya.

Ina mai farin cikin wanan damar da na samu domin wakiltar

Shugaba Barack Obama da kuma kasata a Nijeriya. Ba da da]ewa ba na kasance Jakadar Amirka a }asar Kongo shekaru uku da suka wuce. Nahiyar Afirka na da matukar muhimmanci a gareni. Na fara aikin jakadanci a shekarar 1981 a {asar Kamaru. Na kuma yi aiki a {asar Nijar inda na ha]u da matata Pamela Schmoll.

Mun kasance masu sa’a da kuma jin da]in dawowa kusa da }asar da na fara aikin jakadanci. {asar Amirka da Nijeriya na da tarihin kawance na tsawon lokaci kan al’amurra na cigaba. Na ji dadin cewar }asashen mu na da tarihi masu kamanni, ga misalai guda uku. Na farko shine }asashen mu sun taba fa]awa cikin yakin basasa a don haka mun fahimci cewar sasantawa da kuma gina }asa na ]aukan

tsawon lokaci da bukatar jajircewa.Na biyu shine }asashen mu

na fama da matsalar tsaro kuma wajibi na a tunkari magance matsalar ba tare da an ci mutuncin ]an-Adam ba da kuma bin doka. Na uku shine akwai kalubalen neman makamashi ba tare da lalata muhalli ba da kuma kulawa da rayuwar mazauna inda ake hako makamashin.

Ina mai tabbatar muku cewa }asar Amirka na tare da ku musamman a lokacin da kuka yunkura wajen cigaban }asar ku.

Kofar ofishi na a bu]e take ga duk mai bukatar inganta rayuwar sa. Na yarda cewa Nijeriya na da kyakyawar makoma kuma zumuncin da ke tsakanin mu zai kara ha~aka cikin shekaru masu zuwa.

Ina mai matukar farin cikin kasancewa a wannan }asa.

Ana bugawa duk bayan wata uku daga ofishin hul]a da Jama’a na Jakadancin

Amirka da ke Nijeriya. A rubuto duk wata wasi}a zuwa ga; Edita, sashin

hul]a da Jama’a, Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya, Gida Mai Lamba 1075, Titin Harkokin

Jakadanci,Yankin Tsakiyar Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nigeria.

Lambar tarho: (09) 461-4000. Fax: 09-461 4305

OFISHINMU NA LEGAS {aramin Ofishin Jakadancin Amirka, Sashen Hul]a da Jama’a, Lamba 2, Walter Carington

Crescent, Akwatin Gidan Waya, P.O. Box 554, Legas, Nijeriya. Wayar Tarho, +234-703-150-4867/2444. Yanar-Gizo, [email protected]

ko a shiga http://Nijeriya.usembassy.gov.

MA’AIKATAN WALLAFA MUJALLAVICTORIA SLOAN

(Babban Jami’ar Hul]a da Jama’a), DEHAB GHEBREAB (Jami’ar Hul]a Da Jama’a),

RHONDA FERGUSON-AUGUSTUS (Jami’ar ya]a labarai)

SANI MOHAMMED (Edita)ISHAKA ALIYU (Mai Ba Da Shawara

Game Da Wallafawa)

Wasan Yara Na [andalin Sesame Ya Dawo 2

Wasanni Na Samar Da Ha]in Kai 4

{wallon Kwando, Ya Baiwa ’Yammata {warin Gwiwa 5

Ilimi Gishirin Zaman Duniya 8

Tunawa Da Ha]arin ranar 9/11: Wurin Ta’addanci

Ya Komo Wurin Ziyara 9

Tafiyar [aukaka 11

A Rungumi Sana’a 12

Neman Zaman Lafiya A Jos 14

Shagalin Tunawa Da Wa}o}in Daniel Pearl Ya

{ayatar A Abuja 18

Dakarun Sojojin Ruwa Na Amirka Sun {arfafa

Na Nijeriya 19

Sabon Bayani Kan Neman Ilimi A Amirka 20

Abubuwan Da Ke Ciki

James F. EntwistleJakadan Amirka A Nijeriya

Sa}

on J

akada

Page 4: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 4

Wasanni Na Samar Da Ha]in Kai

Motsa jiki wata hanya ce ta ]aukaka, amma dole ne sai

an yi aiki tu}uru kafin a kai gaci. Ba dole ba ne kowane

ko kowace ’yar wasa ta yi fice, amma dole ne duk ]an wasa ya koyi }abli da ba’adin wasan kafin a yi da shi ko da ita. Nasara a

Akwai abubuwan da ake amfana cikin motsa jiki fiye da annashuwar samun nasara a wasanni, in ji Sani Mohammed, Editan Magama. Kuma }wararre a sha’anin ya]a labarai. Motsa jiki ba hanya ba ce ta samun lafiya, da inganta jin da]in jiki da kuma samar da nisha]i kawai ba. Motsa jiki, yare ne da ke ha]e kan al’ummar duniya da ya zarce maganar al’ada da ]an }asanci, kuma yana da muhimmanci wajen gina }wazo da rayuwa, musamman ga matasa. A kullu-yaumin rayuwa ta }unshi, ina aka dosa da aiki tu}uru da koyo daga al’umma da tsayin daka komai tsanani da yin taka-tsantsan da kiyaye gajiya da daidaita rayuwa don ci gaba. Akan samu ci gaban }warewa a kullum wajen wasan }wallon kwando da tsere da wasannin tsalle-tsalle da makamantansu, a duk duniya, wa]annan su ne manufa da sashin wasanni na gwamnatin Amirka ke bun}asawa a shirin ofishin Jakadanci. Shirin wasanni na ofishin Jakadanci na shekarar 2013, ya nuna ha]in kai a harkar wasanni da al’adu da jin da]in al’umma.

{aramar Jami’ar Ofishin Jakadancin Amirka, Maria Brewer take baiwa marayu kyautar }wallo.

Koyawa Manyan Gode Sana'ar Gudanar Da Rayuwa

Tsohon ]an }wallon kwando, Detlef Schrempf yake koya wa matasa dabarun wasan. Sani Mohammed ya ]auko hoton.

Page 5: Motsa Jiki

harkar wasanni, ko kuma shiga harkar na iya inganta tattalin arzi}i da jin da]in matashi. Harkar wasanni, ko kuma shiga harkar na iya inganta tattalin arzi}i da jin da]in matashi. Harkar wasanni na kawar da camfi na bambancin ’ya mace da kuma ]a namiji, ya kuma taimaka ga cu]anya a wajen gida.

Akasarin matasan Nijeriya, an fi sanin }wallon }afa a matsayin wasan da ya fi shahara. Amma akwai matasa da yawa da ke }aunar }wallon kwando, a Nijeriya. Suna iya tunawa da wani ]an Nijeriya da ya

yi fice a }wallon kwando a Amirka mai suna Akeem Olajuwon, wanda ya zama cikin mutane 50 da suka yi fice a }wallon kwando a

Amirka a tarihin wasan. Don haka suna cike da mafarkin zamantowa kamar Akeem Olajuwon.

{wallon kwando na

Karamcin ofishin Jakadancin Amirka, tare da ha]in gwiwar

wata }ungiya mai zaman kanta mai suna “Hope4Girls,” wato }ungiya mai baiwa ’yammata }warin gwiwa (H4G) wadda Mobalaji Akiode ta }ir}iro, sun yi wani shiri kan shugabanci na shekarar 2013.

Shirin ya yi armashi inda aka samu halartar ’yammata 62 daga Jihohi 17 na Nijeriya, har na tsawon mako ]aya ana ta sha’ani kamar wasannin }wallon kwando da taron }arin ilimi da al’adu daban-daban.

Wa]anda suka }ara kawo gudunmawa, sun ha]a da kamfanin Adidas da Victoria’s Secret Pink da gidauniyar Ovie Brume da Nike Art Gallery da Media Concern da gidauniyar Youth Empowerment, da gidauniyar Better Afirka da Domino’s

Pizza da Super Sports da talabijin na AIT da NTA da gidan talabijin na Channels. Wannan ha]in gwiwa ya baiwa ’yan matan }warin gwiwa ga rayuwarsu sosai.

Akwai masu horarwa guda 6, tare da ’yan sa-kai da babban ba}o da shahararren

]an wasan nan daga }ungiyar WNBA wanda ya yi wasa tsakanin shekarar 1997 – 2004 da }ungiyar Sacramanto Monarchs, wato Ruthie Bolton. Wannan sansani da ake tara yara, shi ne mafi girma da ya }unshi mutane da sashi daban- daban, musamman

{wallon Kwando Ya Baiwa ’Yammata {warin Gwiwa

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 5

Page 6: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 6

]aya daga cikin wasannin da suka yi fice a Amirka da ma duniya, mutane da dama na yin wasan }wallon kwandon.

Babu mamaki a lokacin da wasu tsofaffin shahararrun ’yan wasan }wallon kwando masu suna Detlef Schrempf da Tamika Raymond suka zo Abuja, matasa da yawa suka fito domin su }aru da }warewarsu na wasan }wallon kwando a shiri na

musamman kan koyon wasan, da aka gudanar a Abuja ranar 19 – 25 ga watan Satumba, 2013.

Nijeriya, }asa ce mai }arfin tattalin arzi}i, kuma shugaba ce a harkar siyasa a shiyyar Afirka ta Yamma, kuma babbar }awar Amirka, ba kawai a nahiyar Afirka ba, a duk duniya.

Wa]anda suka shirya wannan sha’ani sun ha]a da ofishin jakadancin Amirka

{wallon Kwando Ya Baiwa ’Yammata {warin Gwiwa.

da ke Abuja da }ungiyar }wallon kwando ta Nijeriya, da hukumar wasanni ta Abuja da wata }ungiya mai zaman kanta mai suna “Open Mic Forum” suka tara yara manyan gobe don koya musu sababbin dabaru na }wallon kwandon da ziyara kan inganta musu harkar ilimi da al’adun gargajiya da aiki na sa-kai da jin}ai da kuma agaza wa marayu.

Hukumar ilimi da al’adu da sashin wasanni na gwamnatin Amirka, ita ce farko wajen shirya wasanni na diflomasiyya. ’yan wasa da masu bayar da horo, na ziyartar makarantu don koyar da matasa a duniya, kuma sukan yi cu]anya da matasan wajen ba su }warin gwiwa kan muhimmancin ilimi, da gudanar da kiwon lafiya da mutunta kowa. Hukumar har ila yau, na agaza wa wasu

6

ganin yadda }ungiyar H4G ta gayyato mata kurame a shirin.

Jami’ar Jakadancin Amirka, Rhonda J. Watson ta yi jawabi kan yadda yaran matan za su taimaka wa kansu don inganta rayuwarsu wajen amfani da baiwar da Allah ya ba su. Masu ya]a labarai na }asa da na waje sun nuna alfanun ayyukan }ungiyar H4G kan ’yammatan Nijeriya, kuma an yaba da gudunmawar wa]anda suke taimaka wa shirin. Wani wakili daga Babban Bankin Nijeriya ya

Duba shafi na 22

Page 7: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 7

marasa wakilci da ku]i da sanya su cikin shirye-shiryensu.

Tun a shekarar 2003 ne hukumar ilimi da al’adu, da sashin wasanni na Amirka suka gayyaci a}alla ’yan wasa dubu ]aya daga }asashe 60 zuwa Amirka don su shiga wasanni, kuma suka aika da ’yan wasa fiye da 220 zuwa }asashe fiye da 50 a shirin wasan Jakadanci.

An fara wasan }wallon kwandon cikin ni’ima, dalilin ruwa da aka yi a wannan safiyar a garin Abuja, hakan ya sanya an samu }warin gwiwa na koyon muhimman abubuwa game da wasan }wallon kwandon ga matasa maza da mata da yawansu ya kai 300. Masu horar da wasan, wato Detlef da Tamika, sun himmatu }warai wajen koya wa matasan dabarun wasan, da suka }unshi guje-guje da tsalle-tsalle da yadda za a ri}e }wallo har a samu nasarar jefa ta a raga. Har ila yau masu horar da wasan sun yi aiki tu}uru, ba tare da gajiyawa ba da sauran }warraru, kuma tsofaffin ’yan wasa da masu horarwa, inda suka ha]u da matasan Nijeriya suka yi mahawara da su game

yin jan aiki da yarda da juna da yin gaskiya a dukkan rayuwa.

Shugaban }ungiyar }wallon kwando na Nijeriya, Tijjani Umar, ya ce koyar da ’yan makaranta wasan }wallon kwando na da muhimmanci wajen ha~aka wasan a Nijeriya. Ya shawarci matasan da su mayar da hankali sosai don koyon wasan, saboda damar da aka samu daga }wararrun.

da rayuwa da kuma }warewa kan wasanni da ha]in kai da mutunta juna da

Tamika Raymond ke koya wa ’yan makarantar sakandare dabarun }wallon kwando a Abuja. Hoto daga Sani Mohammed na ofishin jakadancin Amirka.

Hoto na sama, Marayu ne suka ]auki hoto da jami’an jakadancin wasanni a Abuja. Daga }asa kuma, mahalarta horo kan wasan }wallon kwando ne a Abuja. Hoto daga Sani Mohammed da Idika Onyukwu.

Duba shafi na 20

Page 8: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 8

Ranar 5 ga watan Satumba, a wani taro na musamman kan karatu a bayyane ko

da }arfi, kuma a lokacin bikin ilimi na duniya na shekarar 2013, }aramar Jami’ar Jakadancin Amirka da sashin ya]a labarai, Dehab Ghebreab, ta fa]i cewar, “Ilimi hanya ce ta yaye talauci da rage mace-macen yara da cimma daidaito tsakanin jinsi da ci gaban }asa, da zaman lafiya da ]orewar ci gaba da kuma dimokura]iyya.”

Ranar 8 ga watan Satumba, rana ce ta bikin ilimi na duniya, kuma yana tuna mana da yadda ilimi ke taka rawa wajen rayuwar al’umma. Taken wannan rana na bana, shi ne “Ilimi a }arni na 21.”

Ilimi Gishirin Zaman DuniyaNijeriya na fuskantar }alubale

wajen inganta iliminta. Akwai raguwar iya karatu, musamman tsakanin manya. Ana samun }aruwar neman ilimi. Domin taimakawa wajen maganin }alubalen, Jami’ar ta ce, Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya ya aiwatar da shirye-shirye domin inganta al’adar karatu tsakanin ’yan Nijeriya ta hanyar samun labarai na cibiyoyinsu a Nijeriya da Amirka.

Ghebreab ta }alubalanci marubuta da su yi amfani da damar shirin “A karanta da }arfi,” domin su inganta baiwarsu ta rubutu. Ta ce, “fiye da shekara ]aya da ta wuce, ofishin jakadancin Amirka da

ke Legas tare da ha]in gwiwar gidauniyar masu fasaha ta Amirka da Afirka, suka }ir}iro shirin karatu da }arfi, inda matasa masu rubuce-rubuce ke nuna bajintarsu. Muna ]aukar nauyin wannan shirin tun a shekarar 2012 a kowane wata, kuma ya samu halartar masu sha’awar rubutu, kuma suna son bun}asa baiwarsu, inda suke samun jagora.

Ta kammala jawabinta da wani bayani da tsohon shugaban Amirka, Benjamin Franklyn ya yi cewa, “Idan kana so a ci gaba da tuna ka bayan mutuwarka, to ka yi rubutun da za a ri}a karantawa ko kuma ka yi abubuwan da za a

yi rubutu a kai.”v

Jami’ar ya]a labarai daga ofishin jakadancin Amirka da ke Legas, Dehab Ghebreab ke jawabi a taron yin karatu a bayyane. Hoto daga Kester Abudu.

Page 9: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 9

Bayan kammala sati uku, daga 15 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Afrilu na shekarar 2013 a matsayinsa na wanda ya halarci wani shiri na }asa da }asa kan shugabanci, wani shiri na musaya da gwamnatin Amirka ke ]aukar nauyi, Innocent Odoh, mai ]auko rahoto daga Jaridar “Blue Print,” ya fa]i cewar, lallai inda aka yi ha]arin Jirgin Sama na 9/11, ya zamanto wajen ziyara don tuna mummunan lamarin. Ga bayaninsa:

Shirin }asa da }asa kan shugabancin gaskiya a harkar gwamnati da yin

kasuwanci a Amirka, ya kawo mahalarta daga }asashe 18 daga Afirka. {asashen sun ha]a da Benin da Botswana da Cadi da Cote d’Ivoire da jamhuriyar Kongo da Djibouti da Ethiopia da Ghana. Sauran }asashen sun ha]a da Kenya da Malawi da Nijar da Nijeriya da Senegal da Swiziland da Tanzania da Togo da Uganda da kuma Zimbabwe.

Babu shakka akwai nisha]i da abin tunawa game da ziyara a Amirka, da gaskiya da ]a’a da ladabtarwa da gine-gine na wajen ayyuka da kuma ]orewar bin hanyar mulkin dimokura]iyya. {asar Amirka, }asa ce da ke da tarin jinsin al’umma da addinai da al’adu na al’umma. Akwai Amirkawa farar fata, da Amirkawa ’yan Afirka da Latinos da Amirkawa ’yan }asa da Amirkawa ’yan Asiya. Tsarin mulkin Amirka ya bayar da ’yancin kai ga dukkan

al’ummar da ke }asar.Wayewar kai ya sanya wannan

ha]in gambiza na al’umma na son }asar Amirka irin wanda kowa ke }auna bil-ha}}i da gaskiya da kuma kishi.

A nawa ganin, ziyara zuwa wajen tunawa da inda aka yi ha]arin jirgi na ranar 9 ga watan 11, wato 9/11, wani babban lamari ne saboda irin sa}on da ke ciki. A wajena, abin alfahari ne ziyartar dogon ginin da a da shi ne ginin kasuwanci na duniya. An tuna

Wurin Ta’addanci Ya Komo Wurin

Ziyara

Tunawa Da Ha]arin

Ranar 9/11:

Hoton Innocent Odoh a lokacin da ya ziyarci wajen tunawa da wa]anda

suka mutu a hadarin ranar 9/11.

Page 10: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 10

da mutane 2,983 da suka }unshi mata da maza da }ananan yara da suka hallaka a ranar 11 ga watan Satmba, 2001 da kuma na ranar 26 ga watan Fabrairu, 1993, inda }ungiyar al-Qaeda ta }wace jirgin sama da suka yi amfani da shi wajen afka wa dogayen gine-gine guda biyu.

A cewar sanarwar gwamnati na tunawa da 9/11, “Karrama da tuna wa]anda suka rasa rayukan su, da dubban da suka rayu ne ya sa barin ba}i suna zuwa suna ha]uwa don ha]in kai a dalilin ranar 9/11.

“Tsakanin ginin, akwai jerin alamu na ainihin dogayen ginin guda biyu. “Akwai sunayen duk wa]anda hatsarin ya rutsa da su da aka zana a jikin tagulla.”

{asar Amirka ta nuna fasaha wajen }ayatar da wurin ha]arin inda jama’a daga duniya suke ta kwararowa don kashe }war}watar ido da sunan ziyara. Har yanzu ana ci gaba da tsara gine-ginen wurin, lamarin da ke nuna yadda Amirkawa ke da }wazon sake mayar da duk wani abin da suka rasa kamar yadda yake ko ma ya fi na da, har wa yau, sake mayar da ginin na tunatar da ni }wazon Amirkawa.

Darasi ne ga Nijeriya da sauran }asashen duniya da ke fama da hare-haren ta’addanci da su fahimci cewar Amirkawa sun baiwa gwamnatinsu goyon baya wajen inganta harkokin tsaro ba tare da sanya ra’ayin siyasa ba kamar yadda yake a Nijeriya.

Abin da ta’addancin 9/11 ke koya wa duniya, shi ne mugun

harin da aka kai a }asar Amirka, ya baiwa ’yan }asar }warin gwiwa ne na zamantowa al’umma ]aya, }asa ]aya masu so da }aunar }asarsu duk runtsin da aka shiga.

Duk da cewar, }asar Amirka ta girgiza }warai ganin wannan harin ta’addanci shi ne mafi girma garesu bayan na Pearl Harbor, duk da haka sun dun}ule waje ]aya wajen ya}i da ta’addanci.

A daidai lokacin da na tsaya kusa da bangon da aka zana sunayen matattun, ina kallo, sai na fusata }warai saboda wasu dabbobin mutane suka rasa abin yi, sai sha’awar kisa, abin ya bani takaici. Sai dai kuma da na tuna irin }arfin halin Amirkawa da dabarunsu, sai na canza tunanina.

Yadda aka inganta inda aka kai harin ta’addancin 9/11 ya zama wajen ziyara da cibiyar

al’adu, ya nuna irin tunani na ci gaba da masu tsarin ci gaban Amirka ke da shi. Bayan an yi kaca-kaca da ginin, kamar ba zai gyaru ba, yau ga wurin da aka kaiwa harin ta’addanci ya zama wajen samun ku]in shiga na miliyoyin dalar Amirka.

A daidai lokacin da nake hangen dubban mutane na kai-komo a wannan wuri, sai na lura da jinsin mutane na ta harkokinsu ko da daga ina suka fito, babu tsangwama. Wa]ansu daga cikin mutanen, sun jingina da bangon da aka zana sunayen matattun suna shafawa, suna tuna irin wahalar da matattun suka sha kafin mutuwarsu a ranar Talatar.

Babu shakka an samu sabuwar rayuwa, a inda aka kai ta’addanci na ranar 9/11 inda aka gina wani ginshi}i da zai ri}a zama sabo kullum.

Alal-ha}i}a, }asar Amirka na da ]aukaka!v

Rayuwar dare a Ground Zero.

Page 11: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 11

A ranar Asabar, 28 ga watan Satumba ne, }aramin Jakadan Amirka a Nijeriya, Jeff Hawkins tare da

matarsa, Anne suka jagoranci ma’aikatan Ultima Studio su 28 don kallon gasar ki]a da wa}a da rawa wanda kamfanin MTN ya shirya na Afirka ta Yamma.

[akin taro ya cika ma}il da matasa da iyalai da masu gasa da al}alai, da masu shirya gasar da masu horarwa.

Fiye da makwanni shida ’yan Nijeriya da sauran ’yan }as ashen Afirka ta Yamma suka kasance li}e da akwatunan talabijin ]insu, inda suke kallon wani shiri na matasa masu baje basirar su a gasar rawa da wa}a. Gasar ta }unshi na }asashen Nijeriya da Ghana da Laberiya da kuma Saliyo, sannan an gayyato maka]a da mawa}a sanannu zuwa gasar a tsakanin matasa har na tsawon makwanni shida. Masu kallon shirin sun jinjina wa kamfanin MTN da cewa, shirin ya }ayatar fiye da kowane shiri irinsa.

Matashi Olawale Ojo shi ne ya zama zakara a gasar da wa}arsa mai salon Asa. Gasar wanda shi ne karo na shida da kamfanin MTN ke shiryawa, ya samu halartar wasu daga }asashen Afirka ta Yamma.

Olawale, ]alibi ne daga Jami’ar Ladoke Akintola da ke Ogbomosho a Jihar Oyo.

Ya kasance shi ne matashi na 6 da ya lashe gasar inda ya samu kyautar Naira miliyan 5 da sabuwar mota da kuma kwangilar ]aukar wa}o}insa a faifai. Iyayen sa su ma sun halarci wurin gasar, kuma sun taya ]ansu murna.

Wanda ya zo na biyu shi ne Patience Immaculate inda ya samu kyautar Naira miliyan 3 da mota, a yayin da na uku, ita ce Margaret Cephas inda ta samu Naira miliyan 2 da mota.

Niniola Apata na 4 da Naira miliyan 2 a yayin da na 5 da na 6 suka samu kyaututtukan ku]i.

Ofishin jakadanci ne ya samar da tikiti da

]aukar nauyin shirya tafiya wajen nisha]i.v

Tafiyar [aukaka{aramin Jakadan Amirka Jeff Hawkins tare da matarsa Annie ne yayin da suka

mi}a wa Olawale Ojo kyautar gasar nisha]i da ya lashe.

Page 12: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 12

Daga wannan bayani na Shugaba Barack Obama, wata }wararra

kan sana’a, Sarah Green ta }alubalanci matasan Nijeriya da su taimaka wajen rage rashin aikin yi ta hanyar samar da sana’a don ci gaban sauran al’umma. Green ta yi wannan maganar ne a lokacin da take zantawa da wasu matasa masu sana’a da kuma masu yi wa }asa

hidima a Abuja, ranar 2 ga watan Oktoba 2013.

Ita dai Sarah Green, ta zo Nijeriya ne tun ranar 28 ga watan Satumba zuwa 5 ga watan Oktoba a ci gaba da wani shiri na gwamnatin Amirka kan ci gaba da kuma baiwa matasa abin yi.

Ganin yadda rashin aikin yi ya yi katutu, har ana }iyasin ya kai kashi 60 cikin 100, a dalilin haka ya sanya yanzu aikin

gwamnati ke da wuyar samu tsakanin matasan da suka kammala jami’a. Amma wannan ba wani abu bane da ya addabi Nijeriya kawai, duk duniya ce a cewar, Sarah Green. Ya dace matasan Nijeriya su mi}e domin fuskantar }alubalen, kar su shantake }unci ya dame su, su gaza yin ho~~asa wajen taimaka wa

Sarah Green Daga Amirka Ta Fa]a Wa ’yan Nijeriya

A Rungumi Sana’a

Daga James Moolom, Jami’ in Al’adu.

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 12

“Ka tambayi kanka wai shin wane irin yun}uri harkar sana’arka ke yi wajen sama wa mutane aikin yi ko kuma kawo canji a unguwarka. Manyan masana’antu da suka yi nasara ba sun kafa sana’ar ba ne don yin ku]i ne ba da farko, amma tun farko suna da tunanin yadda kayan sana’ar tasu zai kawo canji a rayuwar al’umma, sai ku]i ya biyo baya” – Shugaba Barack Obama.

Sarah Green ce ta ]auki hoto da masu yi wa }asa hidima

Page 13: Motsa Jiki

A watan Agusta na shekarar 2010 ne, Ba}o Kantiok ya halarci wani taro na shugaban

}asa tsakanin matasan Afirka” (PFYAL).

Shirin na matasa 115 daga Afirka, ya samar musu da damar ha]uwa da Shugaba Barack Obama, inda suka tattauna a wani ]akin taro a fadar shugaban }asa.

Kantiok na ]aya daga cikin mutane 3 daga Nijeriya. Shugaba Obama ya ci gaba da saduwa da irin wa]annan matasan ta hanyar }ungiyar matasan shugabanni (YALI), wani yun}uri na saka jari kan manyan gobe daga nahiyar Afirka a kuma }arfafa dangantaka tsakanin Afirka da Amirka.

Wannan shiri ne tsakanin fadar shugaban }asar Amirka da ha]in gwiwar ma’aikatar }asar wajen Amirka da hukumar ci gaba na }asa da }asa na Amirka (USAID) da kuma hukumar ha~aka zaman lafiya na Amirka.

A lokacin da aka za~e shi ya halarci shirin, Kantiok na aiki ne a wata }ungiya mai zaman kanta da ke taimakawa wajen ci gaban unguwanni a kudancin Kaduna.

Tun da ya dawo Nijeriya Kantiok ya ci gaba da gudanar da harkoki da dangantaka da shirin gwamnatin Amirka na musaya

game da ci gaban unguwanni.v

Tsohon [alibi Da Ya Fi Fice Na Wannan Watan

rayuwarsu, in ji Sarah Green. Maganin irin wannan matsala, shi ne su rungumi sana’ar taimako a unguwanni. A duk duniya idan matasa sun rungumi sana’a, sannan suka sanya }uduri a zuciyarsu, sukan }ir}iri aiki, kuma su taimaka wa unguwanninsu. Sarah Green ta horar da mutane 200 a lokacin taron }arin ilimi, ta kuma jefa musu }alubale da wannan tambayar, “za ka ci gaba da zama rayuwarka na }ara ta~ar~arewa, ko za ka yi wani abu a kai?

Ta samu awanni 3 tana tattaunawa da matasan game da yadda za su inganta rayuwarsu, sannan su }ir}iro wa kansu aikin yi don su taimaki

unguwanninsu.Sai dai fa wasu masu yi wa

}asa hidima da ke halartar taron, sun shaida wa Sarah cewa, “akwai fa bambanci a }asarsu, saboda muna da matsaloli, kamar na cin hanci, rashin wutar lantarki mai ]orewa, rashin tsaro da

kuma rashin ku]i. Yanayin a }asarmu ba shi da da]in gudanar da sana’a,” sai Sarah ta ce, wa]annan matsaloli ne ke addabar ku, ko akwai wasu matsalolin daban? Za ku iya ci gaba da rayuwarku ba tare da sai kun jira komai sun daidaita ba, ko kuma ku nemi magance abin ku samu matsala.

A Kaduna, Sarah ta sake irin wannan jawabi gaban jami’an gwamnati da shugabannin unguwanni da matasa masu sana’a da ’yan makaranta na Jami’a da wakilan banki. Ta yi magana game da gina al’adar neman sana’a, a kuma ri}a }ara wa

masu son sana’a }warin gwiwa.

{ungiyar cinikayya tsakanin Amirka da Nijeriya ne ta shirya taron na Kaduna.

Har ila yau, Sarah ta sake gudanar da wani taron makamantan wa]anda ta

gudanar a baya, wannan karon a otal ]in Valencia da ke Abuja, ranar 3 ga watan Oktoba. Taron ya ta’alla}a ne kan yanayin sana’a da sana’ar taimaka wa unguwa. A }arshen taron, sai Sarah ta bayar da

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 13

Duba shafi na 20

Page 14: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 14

[an majalisar dokokin Amirka, Christopher Smith

tare da jami’in ofishin Jakadancin Amirka, da ke Abuja Gregory Simpkins da Editan Mujallar Crossroads suka tafi garin Jos domin ganawa da mutanen da suka gamu da masifar }ungiyar ’yan Boko Haram. Sun je ne domin tattauna yadda za a

samu zaman lafiya a Nijeriya tare da shugabannin addini da jami’an gwamnati. Christopher Smith, [an Majalisar Wakilai ne na majalisar dokokin Amirka, kuma shugaban kwamitin harkokin Afirka da na kiwon lafiya da na ’yancin [an Adam da na }ungiyoyin }asa da }asa.

Da farko tawagar ta sadu da sakataren Jama’atu Nasril Islam, Dr. Khalid Aliyu, inda suka tattauna matsalar rikicin

Fulani makiyaya a Jos, inda aka kawo shawarwarin yadda za a magance lamarin ta hanyar doka.

A tattaunawar, an lura da cewa akwai matsalar batu kan wane ne asalin ]an }asa da kuma maganar yadda shanu ke ~arna a gonakin manoma.

Dr. Khalid Aliyu ya nuna cewar, rashin ha}uri da mutunta juna ya shiga tsakanin mazauna garin Jos, inda ta kai yanzu an yi watsi da tsohuwar hanyar da ake bi

Neman Zaman Lafiya A JosDaga Idika U. Onyukwu

Editan Crossroads

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 14

Marayu da ’yan gudun hijirar rikicin Boko Haram daga Yobe,

suka ]auki hoto da jami’ar ofishin jakadancin Amirka. Idika

Onyukwu ya ]auki hoton.

Page 15: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 15MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 15

ta sasantawa kan matsala in ta taso, tsakanin Fulani da manoma. Ya ce da ’yar matsala ta faru, babu ha}uri da taka-tsantsan sai rikici ya kaure.

Tawagar, ta ziyarci cocin Katolika na St. Finbarr Parish, a Rayfield, inda wani ]an ta’adda ya ta~a kai hari a lokacin da ake cikin cocin ranar 11 ga watan Maris, 2012, inda mutane 11 suka halaka, fiye da 22 suka jikkata – Tawagar ta tattauna da wa]anda suka rayu lokacin harin inda suka bayyana abin da ya faru.

Bugu da }ari ’yan gudun hijira daga jihohin Borno da Yobe da ke Jos, sun bada ba’asin abin da suka gane wa idonsu na rikicin da ya koro su daga gidajensu. Wani tsohon shugaban }ungiyar Kiristoci (CAN), ya ce ya bar gidan sa da ke Maiduguri tun farkon shekarar 2013, a lokacin da aka yi wa rayuwarsa barazana.

Ya ce ba da da]ewa ba da barinsa, ya samu labarin an kashe mataimakinsa. Shi ma wani ]an gudun hijirar, ya yi bayanin cewa, a 2011 wani ]an Boko Haram ya shigo gidansa da tsakar rana ya ce masa ya bar addinin da yake yi, da ya }i sai ]an Boko Haram ]in ya fito da bindiga a aljihunsa ya harbe shi a

~angaren fuskarsa. Ya ]auka na mutu, amma an yi mini aiki na tsawon awa 12, kuma wata }ungiyar Amirka mai suna, “Voice of Christian Martyrs” ce ta ]auki nauyi.

Bayan kammala taron, sai ]an majalisar dokokin Amirka ya ziyarci motar da aka yi amfani da ita don kai harin, inda aka girke ta a wuri na musamman, kuma aka rubuta sunayen duk wa]anda suka mutu domin tunawa da su.

A jawabinsa, ]an majalisa Smith ya jajenta wa wa]anda harin ya rutsa da su a cocin da wasu mutane biyu cikin 40 da aka yanke amusu }afa, sakamakon raunin da suka samu, kuma wata }ungiya daga Amirka ta ba su }afar }arfe.

Har ila yau, tawagar ta sadu da jami’an gwamnati a gidan gwamnatin Jihar, sun tattauna da Barista Timothy Baba Parlong, mataimaki na musamman kan zaman lafiya,

[an majalisar dokokin Amirka Christopher Smith a lokacin da ya ziyarci cocin Katolika na St. Finbarrs, Jos, ranar 12 ga watan Maris, 2012. Hoto daga Idika Onyukwu.

Tawagar da ta halarci gidan gwamnatin Jihar Filato. Idika Onyukwu ya ]auko hoton.

Page 16: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 16

da ]an majalisar dokokin Jihar, Honorabul Joyce Lohya Ramnap da Honorabul Kaneng Fulani, mai wakiltar Barikin Ladi. Dukkansu sun yi bayani kan abin da suka sani na rikicin Jos. Honorabul Kaneng, ta ce rikicin Fulani da manoma a Barikin Ladi kan labi ne ba na addini ba ne tsakanin Musulumi da Kirista, kuma abin da ya }i ci, ya }i cinyewa.

Ta yi hasashen cewa, muddin aka magance zaman banza tsakanin matasa, aka baiwa Fulani wajen kiwon su, sannan aka ]auki matakin da ya dace na kawo zaman lafiya, komai

zai daidaita.Daga bisani ]an majalisar

na Amirka ya gana da babban Bishop ]in Katolika na Jos, Ignatius Kaigama, inda Bishop ]in ya yi magana cikin damuwa game da kawo zaman lafiya a Jos. Ya ce cocin sa ya bu]e tattaunawa

kan ha]in kai da zaman lafiya tare da musulmai, inda mabiya addinan suka zo }ar}ashin lema ]aya kan neman zaman lafiya.

Kaigama ya ci gaba da bayanin cewar, ha]in kan da ya samu tare da limamin

babban masallacin Jos, Balarabe Da’ud ya haifar da ]a mai ido a lokacin rikicin na Jos a 2012. “Da ba don wannan mataki da ni da limamin Jos muka ]auka ba, da Jihar Filato ta }one” in ji Kaigama.

Ya nemi taimakon ku]i don ha~aka cibiyar ha~aka zaman lafiyar da ya }ir}iro daga gwamnati da manyan }ungiyoyin }asashen waje, musamman, a cewar sa, “]imbin matasan da basu da aikin yi na taimakawa

[an Majalisar Amirka, Smith tare da Acibishop Ignatius Kaigama na Jos. Hoto daga Idika Onyukwu.

Babban limamin Jos, Balarabe Da’ud na biyu daga dama da mu}arrabansa, tare da ]an majalisar Amirka, Smith.

Duba shafi na 22

Page 17: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 17

Ellen Peterson, ta fara aikin hul]a da al’umma a

watan Oktoba, 2015 a sabon ofishin al’umma kan diflomasiyya, matsayin da take lura da arewaci, musamman kaiwa ga matasa ta hanyar }ungiyoyi masu zaman kansu. Ta zo Abuja daga Washington DC bayan ta zama jami’a a }asar Tanzania. Ta ta~a zama jami’ar ya]a labarai a Baghdad, }asar Ira}i, ta kuma ziyarci }asashen Tijuana da Mezico da Doha da {atar. Tana jin yaren Faransanci

da Larabci da Sifananci.v

Jami’ar Harkokin DiflomasiyyaEllen Peterson

Wasan Yara Na Dandalin Sesame Ya Dawo

hukumar ci gaba ta }asa da }asa ta ]auki nauyi tare da ha]in gwiwar }ungiyar ha~aka ilimi mai zaman kanta (wato mai shirya Sesame Street) da wata cibiyar wayar da kai mai suna Ileke Media da ke Nijeriya ke shiryawa.

An fara nuna shirin na uku a ranar 12 ga watan Satumba, 2013 da }arfe 9.30 na dare. Sauran shirin za a ri}a nunawa kowace ranar Asabar da }arfe 9.30 na safe, sai

ranakun Lahadi da Talata da Laraba da kuma Alhamis da }arfe 5.30 na yamma a gidan talabijin na NTA.

“Fiye da shekaru goma kenan gwamnatin Amirka ke agazawa wajen inganta ilimi. A matsayinmu na }awaye, muna aiki tare domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimi mai inganci. Wannan aiki ya samar da bu}atar da

ake so na tsawon lokaci ta hanyar gina ginshi}in ci gaban Nijeriya,” a cewar Maria Brewer, jami’a a ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya.

A cikin wannan sabon shirin wasan yaran mai taken “Shiga runtsin Kami da Big Bird,” wa]annan mutum-mutumin za su yi wa sabon direbansu, Didi wasu tambayoyi, kuma zai ba su amsa ne ta hanyar tu}a

su ta hanyar siddabaru. A wannan tafiyar ce, masu kallo za su ga abubuwan da suke so, kamar fuskar yara da muryarsu da labarai na Nijeriya. Da kuma manyan ba}i da suka ha]a da mawa}a kamar Sasha da Nomoreloss.

Da]in da]awa, shirin dandalin Sesame kan ilimi ana iya samu a duk duniya a karon farko, ta hanyar

17

Sababbin Zuwa

Victoria Sloan ce sabuwar jami’ar bayar da shawara kan Hul]a da

Jama’a na ofishin Jakadancin Amirka da ke Abuja, ta iso }asar cikin tsakiyar watan Oktoba, 2013.

Wannan sashe na al’amuran al’umma, shi ke kula da duk wata mu’amala ta ya]a labarai da kuma duk wani lamarin musaya kan ilimi da al’adu na Amirka.

Victoria ma’aikaciya ce kan harkokin }asashen waje, kuma ta yi wata bakwai a Abuja tana aiki a matsayin jami’ar al’adu a shekarar 2010. Ta ri}e matsayin jami’ar ya]a labarai a Baku, }asar Azerbaijan, kafin nan, ta ri}e kwatankwacin matsayin a Astana da Almati a }asar Kazakhstan da Riga a Latvia da Tbilisi da Georgia. Ta fara aikinta na }asar waje ne daga

Kiv a }asar Ukraine.v

Victoria Sloan – Mai Bayar Da Shawara Kan Hul]a Da

Jama’a

Sarkin Ushafa ne yake kar~ar tsaraba daga

yaran makaranta. Hoto daga Idika Onyukwu.

Daga Shafi na 2

Duba shafi na 20

Page 18: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 18

Amfani da ka]e-ka]e da raye-raye don neman zaman lafiya, ya sanya

wata cibiya mai harka irin wannan, mai suna “Open Mic Forum,” tare da ha]in gwiwar ofishin Jakadancin Amirka da ke Abuja suka shirya wasan sha}atawa domin }arrama ranar duniyar ki]a da wa}a na marigayi Daniel Pearl ranar 23 ga watan Oktoba, a Abuja. Wasannin sha}atawar ya }ayatar sosai inda aka yi wasan kwaikwayo da sauran ki]e-ki]e da rawa da wa}a daga maka]a da mawa}a daban-daban a cibiyar Cyprian Ekwensi.

Daniel Pearl ]an jarida ne, kuma maka]in gogen zamani da ya yi yawon duniya, ya yi abokai saboda sha’awar sa na ka]e-ka]e.

An ta~a sace shi a }asar Pakistan lokacin da yake binciken

wani labari da yake aiki a kamfanin jaridar “The Wall Street Journal.” Daga baya wa]anda suka kama shi suka hallaka shi. Tun daga ranar sai iyalansa suka ri}a karrama shi da shagulgula na ki]a da wa}a don wa’azin mutunta juna.

A jawabinta, Babbar Jami’a a ofishin Jakadanci na Amirka a Abuja, Maria Brewer ta ce gamuwar mawa}a da maka]a a taron tuna ranakun wa}o}in Daniel Pearl na bana, ya nuna gaskiyar cewa, ki]a da wa}a na da muhimmiyar rawar takawa wajen cike gurbin tattaunawa

Shagalin Tunawa Da Wa}o}in Daniel Pearl Ya Kayatar A Abuja

game da bambancin al’ada. Ta ci gaba da cewa, idan

mutane sun halarci irin wannan shagali, sai su manta da bambancinsu, saboda }aunar ki]a da wa}a. “Ha]in kai don ]an-Adam,” shi ne taken tunawa da Duniyar ki]a da wa}a na Daniel Pearl na bana.

Mawa}a sun she}e ayarsu, har ta kai ga sanya ’yan kallo na }walla. Misali wasu mawa}a masu sunan Hip Hop on wheels suka yi wa}a suna nuna yadda ake zubar da jini a Nijeriya, har ma suke tambayar, cewa, “Mu nawa kuke son kashewa?”

Shi ma wani mawa}in mai suna Big Daddy, wa}a ya yi kan zaman lafiya. “Kana bu}atar zaman lafiya, ina bu}atar zaman lafiya, Afirka na bu}atar zaman lafiya” in ji mawa}in. Shi ko, Six foot plus, wani mawa}in, a kan bauta, ya yi tasa wa}ar inda yake cewa, masu bautar da mutane cewa ya isa haka.

Ita ko Julieta, Shahaduhun

Ryta ke cashewa lokacin bikin tunawa da wa}o}in Daniel Pearl a Abuja. Hoto daga Idika Onyukwu.

Shi ma Six Foot Plus ya cashe a bikin. Idika Onyukwu ya ]auko hoton.

Duba shafi na 20

Page 19: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 19

Sojojin ruwa na Amirka sun yi wani atisaye da takwarorinsu na }asashen

Neitherlands da Birtaniya da Sifen da na Nijeriya, mai taken “Africa Winds” (Guguwar Afirka), wani shiri mai manufar }arfafa harkar tsaro a harkokin ruwan Nijeriya.

Atisayen na kwana 21, an fara ne tun ranar 17 ga watan Oktoba, kuma shiri ne na ha]in gwiwa a tashoshin Afirka (APS), kan ha]in kai game da tsaro na dakarun sojojin ruwa na Amirka (NAVAF). An }addamar da atisayen ne cikin wani jirgin ruwa mai suna “Royal Dutch Navy Amphibious Support Ship”

(HNLMS Rotterdam), wanda ya iso Nijeriya ranar 14 ga watan Oktoba.

An gudanar da atisayen ha]in gwiwar ne a Legas da Kalaba da Oron, kuma an yi ne kan yadda ake kai hari don kare ta’addanci da fasa bututun mai. A cewar hukumar atisayen ta Amirka ~angaren Afirka (AFRICOM), manufar atisayen har ila yau, shi ne a gina tsaro na ruwa ta hanyar wayar da kai.

Aiki da hukumomin APS da AFRICOM da NAVAF na ha]in gwiwa na }asa da }asa da gwamnatoci da }ungiyoyi masu zaman kansu (NGOs), don inganta ha]in gwiwa

tsakanin }asashen Afirka don su tsaya da }afafunsu wajen tsare harkokin ruwansu da hanyoyin ruwa da harkokin tattalin arzi}insu.

Shirin APS an kawo shi ne a matsayin wata dabara don koya wa dakarun sojojin Afirka hanyoyin }warewa da gwanancewa a sana’arsu, har ma da masu lura da ga~ar teku da kuma masu harkar jirgin ruwa. Shirin APS ana yin sa ne ta hanyoyi da dama, wanda ya ha]a da ziyartar jiragen ruwa da jirgin sama da inda ake bayar da horo.

Harkokin APS sun ha]a da

Duba shafi na 21

Dakarun Sojojin Ruwa Na Amirka Sun {arfafaa Na Nijeriya

Hoton sojojin Nijeriya lokacin kar~ar horo kan ta’addanci, a Legas.

Page 20: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 20

manyan wayar hannu ta zamani, ga masu amfani da ita a Nijeriya.

An yi amfani da wannan na’ura a lokacin }addamar da shirin Dandalin Sesame karo na 3 a lokacin da aka nuna wa yara abubuwan da ke }unshe cikin shirin Dandalin Sesame a cikin wayar hannu a karon farko.

“Yana da kyau }warai a ci gaba da shirin Dandalin Sesame tare da aiki da hukumar USAID da gidan talabijin na NTA zuwa ga iyalin da yaran Nijeriya” in ji H. Melvin Ming,

shugaban shirin Sesame. “Aniyarmu ce mu taimaka wa kowane yaro ya samu ci gaban rayuwa yadda ya kamata, kuma muna da }warin gwiwar bayar da abin da ya kamata mai inganci, don ha~aka ilimi da kiwon lafiya da sauran abubuwa don gyara yaran Nijeriya bisa kyakkyawar makoma ko kuma don su zamanto yara manyan gobe.”

Dandalin Sesame karo na uku, kamar sauran, an shirya ne bisa shawarwarin masu ruwa da tsaki a harkar

ilimi, kamar ma’aikatar ilimi da ta kiwon lafiya. Shiri ne na rabin awa, har sau ashirin da shida da ake nunawa a talabijin, don koyar da ilimi da kiwon lafiya da tsafta da sarrafa bola ta zamanto wani abin amfani, a yanayin da zai baiwa yaro ]aukaka na al’ada da kuma ladabi da fahimta na zamantakewa. Har ila yau, shirin zai jaddada kariya da yin allurar rigakafin cutar }anjamau da ta cizon sauro, da bayar da ilimi kan kariya ga sauran cututtukan yara.v

Wasan Yara Na Dandalin Sesame Ya DawoDaga shafi na 18

Daga shafi na 13

A Rungumi Sana’a

Marigayi Micheal Jackson ce, kuma mawa}iya, ita ma, cewa ta yi a nata wa}ar, “wa]anda ba su }aunar zaman lafiya, su yi ha}uri mu samu zaman lafiya, su daina tayar da hankula a Nijeriya domin }ananan yaran da ake mayar da su marayu, saboda kashe musu iyaye.

Tim Bello ma ya }ayatar a

irin wasan kwaikwayon da ya gabatar da tawagarsa, inda ya nuna cewa, “Ni ke sanye da takalmi, kuma ni na san inda yake suka ta”.

Wani wanda ya ta~a zama zakara a gasar maza, wato “Big Brother Africa,” na shekarar 2009, Chuwang Pam, ya ce kowane wasa ya }ayatar, kuma akwai darasi ga ’yan Nijeriya. Musamman,

Chuwang ya ji da]in wasan mawa}an Hip Hop On Wheels, inda suke tambayar cewa ina muka yi ba daidai ba? Ya ce akwai tunani }warai da gaske a wa}ar tasu. Age Beeka, wani mai buga jita ya yi wa}a kan “ha]in kai don l’umma.” Wasan ga baki ]aya sa}o ne kan ci gaba da samar da zaman lafiya da ha]in kai a Nijeriya.v

Dagaa shafi na 18

Shagalin Tunawa Da Wa}o}in Daniel Pearl...

kyautar wani tsari kan yadda za a gudanar da sana’a har guda biyar. Mutane 60 ne suka halarci taron, dukkan su matasa wa]anda suka samu goyon bayan

}ungiyar ci gaban matasa. Sa}on Sarah ya ta’alla}a ne kan neman magance talauci tsakanin matasan Nijeriya.

Sarah Green na aikin ha]in gwiwa ne da Empact Organisation,

(www.empact.com) wa]anda ke ya}i da matsalar rashin ku]i da kuma taimakawa wajen gudanar da rayuwa mafi dacewa. Gwamnatin Amirka ce ta ]auki nauyin zuwan Sarah Green Nijeriya.v

Page 21: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 21

Daga shafi na 20

Daga shafi na 19

atisayen ha]in gwiwa da ziyartar tashoshin ruwa da bayar da horo da ziyartar unguwanni da ke kusa da ruwa a }asashen Afirka.

Burin, shi ne gina harkokin ruwa na }asashe da kuma }ara dam}on zumunci tsakaninsu don

tabbatar da tsaro a ruwa. Manufar, shi ne a samu

yanayin dacewar }asashen za su nuna ikonsu ta hanyar doka a hanyoyin ruwansu da wuraren gudanar da harkokin tattalin arzi}in su da kuma kawar da haramtacciyar hanyar kamun

kifi da safarar mutane da na miyagun }wayoyi da satar mai da fashin jirgin ruwa.

APS har wa yau, na bayar da horo ta ~angaren kariya da }warewa wanda zai baiwa }asa ikon ]aukar matakin kare ruwansu.v

Dakarun Sojojin Ruwa Na Amirka Sun {arfafaa...

Tun farko a lokacin da aka yi bikin maraba da manyan ba}i masu horar da wasan }wallon kwandon, Jami’i a ofishin jakadancin Amirka da ke Abuja, Maria Brewer, ta shawarci matasan Nijeriya da su yi amfani da wannan damar don inganta wasanninsu. A cewarta “Idan kun yi aiki tu}uru za ku yi nasara a makaranta da wasannin motsa jiki da kuma rayuwarku.”

Ta ce, jakadun wasanni na Amirka ’yan sa-kai ne, da }ungiyoyinsu suka za~o kuma suna masu alfahari kan wasannin da suka yi fice. Gwamnatin Amirka ta za~o su, kuma wakilai ne kan ayyuka da al’adu masu kyau na }asar Amirka.

Don ci gaba da ya]a manunfarsu game da wasanni, Detlef da Tamika tare da ma’aikatan jakadanci da ke Abuja sun raba }wallayen

kwando da riguna da sauran kayayyaki ga gidan marayu a garin Gwagwalada, Abuja. Yaran da yawansu ya kai 77 sun amfana da sa}wanni daga Jakadun wasanni da kuma Jami’ar ofishin Jakadanci, wato Brewer.

Har wa yau sun mi}a wasu kayayyaki daga }ungiyar wasan }wallon kwando ta Amirka da ofishin Jakadanci ga yaran, kuma sun yi zane da fenti tare da masu sana’ar zane a jikin bango don jin da]in marayun.

Tamika Raymond, ]aya daga cikin masu horar da wasan }wallon kwando, shahararriyar jakada ce wadda ta yi tafiye-tafiye zuwa }asashe kamar Malawi da Caina da Ukraine a madadin gwamnatin Amirka.

A lokacin da take makarantar Jami’a, Raymond ta yi fice a wasan }wallon kwando, wato a Jami’ar Connecticut, inda ta lashe

gasanni. Ta kasance ta shiga a dukkan wasanni na }wallon kwando da ta yi a shekarar 2002. Ta yi wasa a kulob ]in Connecticut.

A ci gaba da wasanninta na }asa da }asa, a shekarar 2010, ta horar da babban kulob ]in }asar Indiya a gasannin }wallon kwando na nahiyar Asiya.

Shi ko Detlef Schrempf, }wararre ne a fagen }wallon kwando, inda ya samu shekaru 16 yana bugawa. Ya yi fice }warai da gaske a lokacin da yake wasa a Jami’ar Washington, inda ya zo na biyu a }warewa kuma ya yi wa }asar Jamus wasa a gasar Olimfik a shekarar 1984 da 1992.

Yanzu kuma a matsayinsa na shugaban gidauniyar Detlef Schrempf, yana agaza wa }ungiyoyi da ke baiwa yara }warin gwiwa game da rayuwarsu, da kuma iyalai daga arewacin }asar Amirka.v

Wasanni Na Samar Da Ha]in Kai

Page 22: Motsa Jiki

MAGAMA | Nuwamba/Disamba 2013. Muharram/Safar 1435. Fitowar Bazara 22

Neman Zaman Lafiya A Jos

zo ya gani, kuma ya yaba da shirin H4G, kuma yana da burin samun ha]in gwiwa don ci gaba da shirin don ya ]ore.

Ga baki ]aya shirin ya }ayatar, kuma ya baiwa ’yammatan }warin gwiwa da sauran wa]anda suka halarci shirin kuma ya nuna cewar wasanni ka iya taimaka wa yaran cimma burin rayuwarsu.

An za~i ’yammata 20

daga Jihar Legas don ci gaba da samun horo kan wasan, }ar}ashin kulawar }ungiyar }wallon kwando ta Jihar Legas, }ar}ashin sabuwar }ungiyar ’yan }asa da shekaru 17. Kowace yarinya ta koma gida da sabon yunifom da takalma da }wallo da riguna da kuma sabon ilimi da kawaye da kuma }warewa.

Wani babban al’amari da ya faru a sansanin, shi ne za~en Mobalaji Akiode da

aka yi don ba ta lambar yabo. Wani gidan talabijin na duniya mai suna ESPNW da kamfanin }era motar Toyota, sun }ir}iro wani shiri na musamman don karrama gwanaye mata da suka taimaka wajen inganta rayuwar mata da ’yammata a garin su. A don haka, an za~i Mobalaji ta kasance cikin wa]anda za a baiwa lambar yabon a }asar Amirka.v

{wallon Kwando Ya Baiwa ’Yammata {warin Gwiwa

wajen kunna wutar rikici a Jos da wasu ~angaren Nijeriya.”

Tawagar, har wa yau ta ziyarci babban masallacin Jos, inda suka ha]u da Imam Balarabe Da’ud da mu}arrabansa. Limamin ya yi musu bayanin cewar ]aya daga cikin musabbabin rikicin na Jos, shi ne maganar wane ne ]an asalin garin Jos. Ya tambayi ]an majalisar a bisa misali, cewar, “Shekara ta 82, kuma an haife ni a nan Jos, duk da haka wani ya ce ni ba ]an Jos ba ne, to, ni wane ne?

(Akwai batun maganar ]an }asanci a taron }asa da za a yi, saboda haka akwai yiwuwar magance matsalar ta hanyar tsarin mulki).

Bayan dawowarsu Abuja, sai ]an majalisar ya yi taro da ’yan majalisar wakilai na Nijeriya, wanda shugaban majalisar, Aminu Tambuwal ya shirya. Taron kan yadda Nijeriya za ta zamanto }asar da babu ta’addanci cikinta, sannan kuma an tattauna yadda }asar Amirka za ta sanya }ungiyar Boko Haram cikin }ungiyar ta’addanci ta duniya.

A wata tattaunawar, }ar}ashin shugabancin kwamitin ’yar majalisa Beni Lar, wato kwamitin ’yancin ]an Adam, an yi bayani kan matakan da ake ]auka wajen kawar da safarar mutane.

[an Majalisa Smith tare da jami’in Jakadanci Simpkins, sun }ar}are

ziyarce-ziyarcen nasu da ziyartar shugaban Kiristoci na }asa, Ayo Oritsejafor. Daga }arshe ]an majalisar na Amirka ya fa]a wa manema labarai cewa, ya damu }warai, yadda ’yan Nijeriya ke wahala }ar}ashin }ungiyar Boko Haram. Ya ce kwamitinsa zai yi zaman sauraron ra’ayoyin jama’a game da }ungiyar Boko Haram a Washington.

Da aka tambaye shi ko me Nijeriya za ta yi wajen taimaka wa wa]anda suka jikkata sakamakon harin ’yan }ungiyar Boko Haram? Sai ya ce “Nijeriya ta bi sahun Amirka wajen kafa gidauniyar wa]anda suka jikkata bayan harin ta’addanci na 9/11.v

Daga shafi na 16

Daga shafi na 6

Page 23: Motsa Jiki

CROSSROADS | Winter Editon Nov-Dec, 2013 23

MAGAMA Ra’ayin Masu Karatu

Sifili 19 Lamba 3 Nuwamba/Disamba 2013

Kana iya baiwa aboki ko abokin aiki shawarar ya ri}a karanta Mujallar Magama?

• {warai• Wata}ila• Ba yabo, ba fallasa• Babu tabbas• Ba zan ba shi shawarar ba.

Kana da shawara game da yadda za a inganta mujallar?

• Ina da shawara (Ka bayyana shawarar taka)• Babu shawara.

Kai na miji ne ko ke mace ce?• Namiji• Mace

Which range includes your age?• Younger than 18• 18 - 24• 25 - 34• 35 - 44• 45 - 54• 55 - 64• 65 or older• Prefer not to answer

Shekarunka nawa?• {asa da 18• 18 – 24• 25 – 34• 35 – 44• 45 – 54• 55 – 64• 65 – sama• Ba zan amsa ba.

Gaisuwa ga masu karatun Magama – Ga wasu tambayoyi da muke bu}atar amsoshi daga gare ku. A daure na ’yan wasu lokaci don amsa tambayoyin, hakan zai taimaka wajen inganta ayyukanmu zuwa gare ku.

Mun gode.

Tambayoyi: Tsawon wane lokaci kake karanta Mujallar Magama?

• {asa da wata 6• Shekara ]aya zuwa }asa da shekara 3.• Shekara 3 zuwa }asa da shekara 5.• Shekara 5 zuwa sama.

Wane la}abi ka fi so a cikin wa]annan? • Gaskiya da ri}on amana• Gwamnati mai kyau da bin doka• Makamashi• Safarar mutane• Bin doka• Ci gaban tattalin arzi}i da samar da abin yi

• Abinci da tsaro

Yaya za ka kwatanta gamsuwarka idan ka karanta Mujallar Magama?

• Na gamsu }warai• Daidai gwargwado• Ba yabo, ba fallasa• Ban gamsu ba

Ta wace hanya kake samun mujallar Magama?• Ta adireshin yanar gizon e-mail• Ta hanyar yanar gizon ofishin jakada• Cibiyoyin sayarwa da aka kafa na Amirka• Ta hanyar aikawa da sa}o.

Ka aika da takardar amsar tambayoyin zuwa sashin ya]a labarai, ofishin Jakadan Amirka, Abuja

Plot 1075, Diplomatic Drive,Central Business Area, FCT Abuja.

e-mail: [email protected]: 09 – 461 – 4373.

Page 24: Motsa Jiki

Sabon Bayani Kan Neman Ilimi A AmirkaAbuja da Legas

Shugaban }asar Amirka, Barack Obama ya gana da shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ranar 23 ga watan Satumba 2013 a New York.Shugabannin

sun jaddada }udurinsu na ya}i da ta’addanci, da kuma kawo }arshen ta’addancin da ke aukuwa a arewacin {asar. Shugaba Obama ya bayar da muhimmancin ya}i da ta’addanci ta hanyar inganta tattalin arzi}i don samun aikin yi da kyautata ’yancin ]an Adam. Har ila yau, Obama ya }arfafa cewa Amirka za ta goyi bayan gudanar da gaskiya a gwamnati. Ana iya kallon Bidiyon a yanar gizon youtube a http://bit.ly/HiLoG/Tsokaci daga shugaba Obama kafin taro da shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya: http://I.usa.gov/HchlqgY.

EJ/USA: Goal! Abinci. Lafiyar jiki. ’yan kallo.Ka karanta bayani game da kimiyya da ke baiwa Amirkawa lafiyar jiki ta hanyar yanayin bi da rayuwa, da yadda ake gabatar wa ’yan birni yanayin rayuwa.

Bayanan da aka bayar a }asa, ana iya samun su a cibiyar samar da labarai da ke Abuja da Legas. Domin zama mamba sai a yi rajista a – http://tinyrl.com/ircregistration, domin }arin bayani, sai a rubuta zuwa ga: [email protected](north) da kuma [email protected](south).

Cibiyar Ilimi ta Amirka da ke Legas da Abuja, na samar da bayanai masu inganci cikakku game da duk karatu a makarantun Amirka ga duk mai bu}ata. Don neman }arin bayani game da karatu a Amirka, sai a ziyarci wannan adireshin: http://www.educationusa.gov.

Inda ake samun shawarwari game da ilimi a Amirka: Ofishin Jakadan Amirka da ke AbujaPlot 1075, Diplomatic Drive, Central District Area, AbujaTelephone: 234-09-4614251/4241/4257; Fax: 234-09-4614334/4010; Email: [email protected]: http://www.facebook.com/educationusa.abuja

Legas:U.S. Consulate General, Public Affairs Section,2 Walter Carrington Crescent; Victoria Island-Lagos.Telephone: 01-460-3400/2724/2725/3801/3802E-mail: [email protected]

Ga Baje Kolin Kwaleji Da Sana’a, Na 2013:Ilimin Amirka tare da ha]in gwiwar hukumar Abuja, suka shirya baje koli kan kwaleji da kuma sana’a a Abuja. Hukumar Abuja ta bayar da wurin da

aka baje kolin kyauta.Fiye da ]alibai da malamai da masu bayar da shawara 1,600 suka nemi bayanai daga wakilan makarantu da ke Amirka a lokacin baje kolin.v

Kana Bu}atar Karatu A Amirka?

Whitney M. Young. Information Resource Centre

Sashin hul]a da Jama'a, {aramin ofishinJakada, Lamba 2 Walter Carrington Crescent,

Victoria Island, Legas, Najeriya.Tarho: 01-460-3400Fax: 01-1-261-2218

e-mail: [email protected] bu]ewa ranar Litinin zuwa Alhamis

Daga }arfe 9.00 a.m. zuwa 12.00 p.m. ranar Juma’a.

A aika da duk e-mail zuwa ga [email protected] (Arewa), [email protected] (Kudu) ko [email protected].

Rosa Parks CenterSashen hul]a da Jama'a na Ofishin Jakadancin AmirkaPlot 1075 Diplomatic Drive, Central District Area,Abuja, Najeriya.Tarho: 09-461-400 Fax: 0-9-461-4011e-mail: Ircabuja elstate.govAna bu]ewa daga }arfe 9.00 a.m. - 4.00 p.m.Litinin zuwa Alhamis.9.00 a.m – 12 noon Friday

Ga Adireshen mu kamar haka: